Showing 183001 words to 186000 words out of 365757 words

Chapter 62 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1498

karya fito ya ganni, nakoma cikin gida ina juya wad'annan zantuka na abbamu da bak'onsa, masu tsananin wahalar fassara, mi bak'on yake nema a wajen Abba dahar yake ik'irarin sun basa zunzurutun kud'i naira na gugar naira, d'ai-d'ai har miliyan d'ari biyar? Amma dukda yawansu Abba bai firgitaba balle mik'a wuya?, sannan wanene Galadima kuma? Miyake nufi da labarina zai shiga duniya? Na shiga uku ALLAH karka bama bawannan damar cutar da rayuwata ko ahalina gaba d'aya.

Munubiya data lura da halin danake cikin ta sakani gaba da tambayar, tun ina k'ok'arin 6oye mata Dan kar hankalinta itama ya tashi, harna fito fili na sanar da ita gaskiyar abinda naji da kuma gani, harma Wanda na aikata.

Hankalin Munubiya ya tashi sosai itama, nanfa muka Shiga kullawa da kwancewa Munason gani gaskiyar lamarin, amma mun kasa kama bak'in zaren, fita kuwa mun koma yintane a d'arare saboda tsoron furucin mutuminnan.

a wata ranar talata da Abba zai dawo daga tafiya sai innarmu ta sakamu gyaran d'akinsa saboda kanta namata ciwo. muna tsaka da aikin sai muka tsinci wani file da yasha k'yak'yk'yawar adana a awani akwati dake cikin wardrobe d'in Abba, to dama da biyu muke aikin, harda bincike akan Neman hasken maganganun da mukaji ranar, jikinmu har rawa yake muka bud'e wannan file, a shafin farko mukaci karo da wani Abun daya kuma rikita tunaninmu .

=�G�<���



*_Tabbataciyar wasiyya ga ahalina, koda ace na kwanta dama kafin cimma burina ko mik'a wannan sak'on amana ga Wanda ya cancanta, to na shaida muku da cika umarnina na ida nufina a garesu 'ya'yana ko 'yan uwana, inason Ku isar da wannan amana da aka bani ga ahalin wannan masarauta............ ._*



 iya nan rubutun ya tsaya, muka bud'e shafin na biyu kozamuga sunan masaurar da Abba ke magana da k'arashen zancensa, amma sai sunayen mutane muka gani a k'alla sunkai goma. Wucewa mukayi shafi na uku, a dai-dai wannan lokacin Abbanmu ya shigo d'akin batare da mun Ankara ba, wata hargitsatstsiyar tsawa mai tsinka hanji ciki da zukata ya daka mana yana fad'in  ku harkunkai girman da zakumin bincike a d'aki a matsayina na mahaifinku? mi kuka sani akan wannan takardar dahar kuke binciken abinda ke cikinta? Yaushe kuka koma la6e? . haka Abba ya rikice gaba d'aya muma ya rikita mu, ya dinga zabga masifar dahar tajawo hankalin jama'ar gidanmu, indai tak'aice maka bayani har innarmu saida fushin Abba ya shafa ranar, hakanne yasani fahimtar Abba ya gane naji komai a ranar. munshiga damuwa a time d'in matuk'a, dukda hak'urin da muka bashi yak'i saurarenmu, ya d'au tsawon lokaci yana fushi damu kafin ya daina. bayan komai ya daidaitane kuma wani yammaci mun fito daga school saiga motocika a jere suna tsula uban gudu a titi, wucewarsu tamkar iska yasakani fad'ar bak'ar magana ga manyan k'asarnan har 'yan uwana na tayani. Sai kuma mukaji sunanka a bakin wani saurayi da 'yammata biyu. Wannan ganinaka ne yasakani dawoma Munubiya da abinda ya wuce, saboda sunan Galadima da mukaji saurayinnan ya ambata, sai muka dinga tunanin kokaine Wanda muka ta6aji a furucin bak'on Abba?. ga kuma sunan masarauta da muka gani a rubutunsa, dukda bamuji sunan ainahin masarautarba kuma, balle mu tabbatar da kaid'inne.. Ganinmu dakai na biyu kuma saika bani haushi, dan ganinka mutum mai yawan izza, sainaga bebekin Abba daya saka kansa had'ari akan Wanda shi baima damu da damuwar kowaba sai tasa gakuma tarin girman kai Dana hango tartare dakai . (Kafayi hak'uri, gaskiyata nake fad'a, guntun murmushi kawai Galadima yamata baice uffanba) taci gaba da fad'in  Wannan ne dalilin yimaka tsak'i a asibiti, idan har baka mantaba, har dogarinka d'aya yataho da zummar d'aukar mataki amma ka dakatar dashi da fad'in ya barni .



Galadima ya murmusa alamar bai mantaba.

Nace,  ka tuna kenan? .

 Na tuna kwarai da gaske, dan bancika manta abuba saidai idan na d'aukeshi mara muhimmanci, amma a time d'in ai banga face nakiba, shiyyasa banida tabbacin kece, saidai na muku kallo d'aya a lab da muka iskeku keda sisters d'inki, ni nama zata Ku 'yan uku ne ai .

 Umyim, amma a time d'in babuma Wanda zai d'auka Kasan da zamanmu a lab d'in, dan gaisuwar da ake maka ma, kamak'i amsawa sai d'aga hannu, hakanne ya tunzurani na fito daga lab d'in, dasu munu sukace kainema kabada jinin da za'a sakama feena ban yardaba .

Baki Galadima ya d'an ta6e yana shafa kwantaccen sajensa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in  bazaki fahimta bane yalla6iya. yanzu labarin da kika bani ya farune duk a wace shekara? .

Na d'an ya mutsa fuska ina fad'in bamai nisa bace, dan ko 2years cikakku baza'a k'ulla ba, Muna Exam d'in NECO nema, dan har results d'inmu suka fito aka fara biyan JAM Abbanmu ya biyama sauran 'yan uwanmu amma banda ni da Munubiya, sai baba k'aramine ya biya namu, so munfara karatu dai babu dad'ewa muka shirya da Abbanmu saboda magana da dad d'insu Ayusher yamasa Yakuma sake bashi hak'uri. tundaga nan komai yazama Normal. Amma kaikanka yakamata kayi mamakin yanda a kwanaki kad'an na amince da tayin auren Contract d'in da kukaimin, dukda ba waccan binciken namu kawaine keda alak'a da amintar tawaba, akwai wani dalili daya shafi ahalina .

Mik'ewa Galadima yayi yana salute d'ina, yace,  kin cancanci yabo my friend, dukda tabbas a farkon aurenmu kema kina cikin zargina akan turoki akai gareni tun farko, amma yanda kike halayyarki da d'abi'unki sai kika kauda hankalina, a tunani na dukkan mutum dazai kwantarmin dakai yaringa nuna tsorona to tabbas wannan mutumin sunamsa *MAGE MAI KWANCIYAR 'DAUKAR RAI* a wajena, amma kece mutum ta farko kuma mace data iya mayarmin murtanin magana kai tsaye, batare da shakka ba, sai dai inason Sanin minene alak'arku da Muftahu to? .

 muftahu kuma? babu wata alak'a bayan wadda kasani, dan tare Na fara ganinku ai .

Takowa yay zuwa inda yake zaune a da, ya koma saman kujerar ya zauna,  kin tabbatar babu alak'a ta kowane fanni? .

 miyasa kake kokwanto? inhar zaka kasa gaskatani a nan bai kamata ka aminta da zancena Na farkoba kenan? .

Ya murmusa yana fad'in  kozaki gaji Abba ne? .

Nace,  akan me? .

 jaridanci mana, naga kin shahara wajen iya bincike .

Mik'ewa nayi saboda k'afata tafara yaamm alamar jinina yana buk'atar motsawa, nafara d'an takawa. hannaye kawai ya hard'e a k'irji yana bina da kallo, saida nad'an zagaya d'akin kafin nabashi amsa da fad'in  yalla6ai kasan wani Abu kuwa? .

Kansa ya girgizamin kawai.

Nace,  humm nifa nan daka gani, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo .

 really? .

 baka buk'atar jayayya .

Ya d'aga kafad'a yana ta6e baki,  hakane kuma .



Sharesa nayi na zauna a bakin gadon danna d'an mik'e, a haka najawo filo na kwanta k'afafuna a k'asa.

Tasowa yayi ya dawo ya zauna saman k'aramin table d'in gaban sofa, jinai kawai ya kama k'afata ya d'ora saman cinyarsa yana matsamin a hankali.

Da mamaki na d'ago kai na kallesa.

Ido d'aya ya kannemin yana d'an ta6e gefen bakinsa, ya maida kallonsa ga k'afar.

Sabon salo, na fad'a a raina. a fili kuma nace,  yalla6ai kaine......

Bai bari na k'arasa ba yay saurin fad'in,  ba dole na taimaki lafiyar abin cikin kwan ba .

Harara na dalla masa ina janye k'afata, ya kalleni da mamaki,  ya haka? ko haushi kikajine? .

 miye zai Sani jin haushin? saika bari idan yafito duniya ka matsa tashi k'afar .

 oh ni Sameer naga ta kaina .

 zama kaga ta k'afa bata kaiba, Sunan nakama bazaka iya fad'arshi da r ba .

 oh nan kuma kika dawo? .

Matsawa nayi baya saman gadon sosai batareda na bashi amsaba. shima saiya taso ya hawo gadon, hakan yasani yunk'urawa zan sauka na bar masa, fan nasan hawan nasa bazai haifar da d'a mai ido ba, yasa hannu ya rik'eni,  yalla6iya ai saikin maimaita mikika fad'a dalla-dalla .

 lah wasafa nake maka, kaga rigar wankace a jikinka kaje ka cire kar mura ta kama ka .

 Ai kinga dai-dai kenan . Yay maganar yana k'ok'arin kwance igiyar rigar.

Hannunsa nayi azamar rik'ewa ina marairaice face alamar yaji tausayina.

Baki ya ta6e yana ture hannuna, na kuma k'ank'ame nasa nak'i bari. Murmusawa yayi, ya kwanto gefena tareda sakani jikinsa ya rungume.

 Nace please wankama zanyifa, zafi nakeji .

Maidani yayi ya kwantar, cikin kunnena yace,  kedai fad'i gaskiya, ko kina son a....... .

Rufe bakinsa nayi da tafin hannuna ina kukan shagwa6a, ya shiga k'ok'arin cirewa amma nak'i bari, shi dariyama na bashi, irin wannan hak'ilo haka. duk yanda yaso na barsa k'i nayi, saida barci yafara fisgata hannun ya zame.

Kansa ya girgiza kawai yana murmushi, a fili ya furta  mai bakin tsiwa . Ya k'are maganar da sumbatar goshinta yana gyaramata kwanciya a jikinsa.

Ya tsira mata idanu yana kallon yanda take fidda numfashi a hankali, a zahiri idonsa a kanta, amma zuciyarsa maganganunta taketa cud'awa, shi baima ta6a ganin mace yarinya k'arama mara tsoro da shiga rikita-rikita irinta ba, bata gudunma shiga had'ari? ya sauke ajiyar zuciya yana tashi zaune, k'afafunta yashiga mammatsa mata a hankali, aikam harda gyara kwanciya su madam munaya, yad'an murmusa, yasan ko'a d'azun tanaso fa, amma iyayi yasata hanashi ya mata. Ya d'auki tsawon lokaci yana mammatsa mata jikinma gaba d'aya, yayinda zuciyarsa kuma ke tattance bayananta dalla-dalla, daga k'arshe sauka yay daga gadon ya fice zuwa d'akin sirrinsa, duk abinda tafad'a yasamu sabon file ya bud'e masa, baya wasa da evidence komai k'ank'artarsa, balle ma nata ya wuce Na wasa, ya dad'e yana rubuce-rubucensa kafin ya koma kan Computers, sunan SD kawai ta ambata masa, dan haka yafara searching gameda SD d'in kawai, babu abinda ya fahimta akan hakan, dama baiyi tunanin fahimtarba, waya ya d'auka ya kira Nuren, bayan sun gaisa yace,  Nureddin acikin yaransu Tanderu kasan SD? .

 SD! SD! kai anya kuwa? amma dai ina zuwa bani mintuna 30 .

 ok saina jika .

Galadima Na yanke wayar ya nemo number d'in Abba da bakowa ya sani d'innanba yafara aiki a kansa, dukkan Contact d'in ciki suka bayyana, d'aya bayan d'aya ya dinga binsu yana nazarin adadin kiran da aka ta6ayi, sau nawa aka kira Abba sau nawa ya kira shima? Mafi yawa ma kiransu yafi yawa, yad'an murmusa yana wasa da tsinken hannunsa a kan la66a da nazarin yanda zai 6ullo musu, dan duk hanyar daya kamata yayi bincike an d'auki mataki a kanta, tsawon lokaci bai fahimci komaiba, sai zuwacan wata dabara tafad'o masa, nutsuwa yay yana sarrafa Computer's d'in cikin tsantsar kwarewa da gwaninta, ya kafa musu tarko ne a wayar innarsu Munaya, dan ya tabbata watan watarana zasu iya kira ko sak'o, amma abinma haushin saiya iske wayar inna a kashe, ya dafe kansa, saifa da yacema dady aringa barin wayar a kunne.

Babu shiri ya d'auki waya ya kira daddy, bayan sun gaisa yaymasa maganar kunna wayar innar. cikin mamaki Dady yace,  ai a kunne take koda yaushe, Change ma baya k'arewa nake kuma sakata, idankuma zan zo nan nakan sanarma Jafar shima ya kula, amma ina zuwa dai .

Galadima ya amsa da to, amma k'asan zuciyarsa tana mamaki. babu dad'ewa Abba ya sake kiransa,  Ashe Change ne ya k'are babu dad'ewarnan ban lura ba, amma gashinan Na sakata .

 to Dady, Na gode sosai .

Sunayin sallama da Dady Kiran Nuren Na shigowa, d'agawa yayi, Nuren yace,  inagafa brother hanya d'ayace dazata saka musan shi wanene SD d'in, dan abinda Na lura dashi baya amfani da hakan ta kowanne fanin yanar gizo, maybe da full name yake amfani. yanzu zan sayi ticket insha ALLAH zanje domin bincika a wajen Malam Saminu, nasan ya magantu yanzu, zai amsa mana dukkan tambayarmu .

 ok hakan yayi, idan ka fahimci bai saniba karka takurashi, ka binciki yarinyarnan itama, koma ka fara bincikarta dan ita bama wayo ta cikaba sosai, k'ila kafi samu cikin sauk'i a wajenta, abinda yasa Malam saminu baison fad'ar komai, babbar 'yarsa cikin 'ya'yan Alhaji balala wani ya mata ciki, kuma sun dai-daita akan idan ta haihu za'ama yaran aure, wannanne yasakashi tsoron fad'ar komai, dan karya lalata waccan alak'ar, dan tabbas yasan yana fad'a auren bazai yuwuba, to nima banason shiga hak'in kowanne ahali akan aikina, shiyyasa nabashi dama kaga bankuma waiwayarsa ba, yanzu haka yarinyar ta haihu kwana hud'u kenan, amma shi yaron ya kawota nan Dubai ta haihu ne, a nufinsu bayan haihuwar da sati d'aya zasu dawo Nigeria a d'aura musu aure sannan su dawo Dubai d'in, dan Alhaji balala baya son abinda zai 6ata record d'insa, kuma mamar yaronce ta Dage sai anyi auren dan ita mutuniyar kirkice, dan haka mu bama Malam Saminu wannan damar .

Ajiyar zuciya Nuren ya sauke, cikin mamaki yace,  duk ya akayi kasan wannan brother?  .

galadima ya murmusa, yana fadin  Nuren kenan, to bara nayi copy d'in my mata, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo, nasha fad'a maka bada kwanji kawai ake yak'i ba, sai anhad'a da dabarun tunani dana nazari, so kad'an nafad'a maka daga abinda ya shafi Malam Saminu, kaidai saina jika kawai, a time d'in da zakuyi maganar ka tabbatar ka had'a Communication dani ok? .

 babu damuwa aljanin munaya .

Dariya sosai Galadima ya shiga tuntsurawa da iskancin Nuren, wato shima ya maida Aljani yau, wlhy yaronnan yagama rainashi, wai Aljanin Munaya, d'an iska zan kamaka ai.

Kashe komai yayi ya fito daga d'akin, bai koma cikiba saiya sakko k'asa, ya iske Sauban kad'ai a falo, shima shigowarsa kenan daga asibiti yake.

Galadima ya zauna yana fad'in  jirgi sarkin tashi daga ina? .

Dariya sauban yayi, yace,  kai Yaya, nine kuma jirgin? .

 Kamafi jirgi ai. Wane shiri kakeyi gameda zuwa bautar k'asarka Nigeria .

Sauban ya 6ata fuska kamar zai fasa ihu  yaya yanzu fa ca za'ayi saina koma 9ja har zaman 1year? .

Hararsa Galadima yayi,  to zakayi anan k'asar ne? .

 Ni Yaya ALLAH da anayi da nayi, a manta da bautar k'asar kawai mana, nayi joining masters d'ina .

K'aramin tsaki Galadima yayi, yay crossing k'afarsa yanama Sauban wani kallon bammasan amsar dazan bakaba, saida ya d'auki wasu mintuna sannan yace,  rashin yin ai bazai zama matsalar kowaba sai taka, bakuma zaka gane hakanba sai nan gaba idan ALLAH ya kaika inda bakayi zatoba, idan kace bazakayiba it's better, nidai ai nayi nawa ko. tashi kabani waje .

Ganin ransa ya 6aci Sauban ya marairaice fuska zaiyi magana, amma sai Galadima ya d'aga masa hannu, sannan yamasa nuni da k'ofa alamar ya fice masa.

Fita Sauban yayi yabarsa, shifa tsakani da ALLAH zaman masarautar ne baya son yi shi kad'ai.

Galadima ya girgiza kai kawai yana fad'in  ALLAH ya shiryeka, gata kasamu tunda katashi kaga komai basai ka nema ba .

Jakadiya data fito ta rissina tana fad'in  Ashe ka shigo magajin gari, barka da dawowa .

Murmushi Galadima yayi, yanason matarnan saboda halaccin datake wa rayuwarsu,  yauwa jakadiya, ya gidan? .

 lafiya lau Ranka ya dad'e, a shirya abinci ko? .

Agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalla, sai kuma ya maida ga jakadiya,  bar abincinan jakadiya, akwai Inda zanje .

 to ALLAH ya dawo dakai lafiya .

Hannu ya d'aga mata kawai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login