Showing 261001 words to 264000 words out of 365757 words

Chapter 88 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1504

k'wallan dabasan na minene ba.





**************



Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mota d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune.

Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bayan su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi.

Munaya tayi yunk'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake.

Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma kallonsa murya a sanyaye nace,  ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai? .

Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintuna biyu sannan yace,  idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya .

 Hummm . Munaya ta fad'a kawai tana d'auke kai.

Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa,  yalla6ai lafiya? .

 ita ta kawo haka .  yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa .

Tamkar zan tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin magana rad'a yace,  kin fara kewata ne? .

Baya naja da kaina ina tura baki da yamutse fuska, amma sai hannunsa daya sa ya tokareni ya dakatar dani daga matsawar, yakuma matsowa gaf, numfashin junanslmu na sauka a fusakar juna, a hankali yafara hura min iskar bakinsa saman ido, babu shiri na lumshesu, hawayen da suka taru suka zubo, sai kawai ya shiga sumbata ta.

Tuni nabashi had'inkai babu wani gardama, saida yay yanda yakeso da ni sannan kowa yakoma gefe, wata y'ar k'aramar souvenir bag ya d'ora mani a cinya, sannan ya cire luck d'in motar, saida naja wasu Seconds nasamu dai-daita sannan ta bud'e na fice rik'eda bag d'in daya bani, ban yarda nasake koda kallonsa ba.

Shima harta fice bai kuma kallon nata ba.



Jiki a sanyaye nashiga gidan, matan gidanmu duk suna falon innarmu gaida bak'i, ina shiga muka rungume juna nida Munubiya muna hawayen da ita Munubiya tana tayani ne, nikuma bansan dalilin yinsuba>�#�.

Kowa dai da kallon mamaki ya bimu kawai.



Su Aunty Mimi basu dad'eba sosai suka tafi, anbar laraba anan zata zauna damu.

Samha da khaleel harda kukansu.





**************





Bayan komawar su Galadima masarautane yakejin wai ba'aga Harun ba, k'ala bai tofa ba balle nuna alamun damuwa ko jimama.

Saima shirinsa Na tafiya ya fara hankali kwance, yaje yayma mai martaba sallama. Suka wuce airport abinsu, dan jirgin 7:30pm zasubi.............
'<���























*_ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���_*





BOOK 3 =�I�<���7� & 8�





...............Galadima ya shigo murmushi d'auke a fuskarsa, dattijon dake zaune a falon ya d'ago ido yana kallonsa shima fuskarsa d'auke da murmushin, k'arawa Galadima yayi garesa, ya zauna kusa dashi yana fad'in  Baffina kanata jirana ko? .

Kafad'arsa dattijon ya dafa, yace  karka damu d'an baffinsa, nasan aiki mai muhimmanci ne ya tsaidaka. ya k'ok'ari? .

 Alhmdllh baffi, munata fama .

 ALLAH ya dafa mana, yanzu ina shi Darma? .

 Gashi a waje tareda ma'aikata, zamu jira zuwan Sir Isa ne, dan asan miya kamata, bazai yuwu mu had'ashi da su Harun ba .

 Uhm hakan shine dai-dai kam, amma yakamata suma bayanansu kagama tattarasu waje d'aya ka kawomin, kasan abubuwa zasu cud'e mana a tsakaninnan, dan fatana insha ALLAH wannan shine case Na k'arshe dazan fuskanta a rayuwar aikina, shekara 1 kacal ya ragemin cika talatin a matsayin lauya, insha ALLAH kuma zan cikasune bisa alk'awarin gurfanar da dukkan mai hannu akan mai martaba .

Murmushi Galadima yay, idonsa cike da kwalla, ya had'iye Abu mai d'aci yana fad'in  ALLAH ya cika maka wannan buri baffi, lallai ina alfahari dakai amatsayin uba, Kaine ka nunamin hanya alokacin da k'ofa ta rufe min, Kaine ka tsallakar dani a lokacin da gada ta karye ina tsaka da tafiya, ga kuma gagarumin hadad'i mai cike da tarnak'in iska ya taso, badan kaid'in ba da jajircewarka da yanzu ruwan daya zuba ya shafe da tarihina dana ahalina, da ace wani zai saurari labarina saiya d'auka labarin film ne ko novel, ni karan kaina nakanyi zaman yin tunanin anya akwai mai irin rayuwata a k'asarnan? Dan mafi yawa a tatsuniyoyi da hikayoyi akejinsa, saikuma abin mamaki ga nawa a zahiri, a yankin k'asar hausa, yanki mai tsananin ruk'on addini da Al'ada, yanki mai mutunta ahali da zuminci, inhar a shekaru 26 baya za'a iya samun masu irin ayyukan su tanderu lallai akwai abin tsoro kenan a k'arni nagaba da y'ay'anmu zasu mu'amulanta, Baffi da ace d'an Adam Na iya za6ama kansa rayuwa da banzo cikin ahalin jinin sarauta ba, amma Alhmdllh, ina godiya da Ubangiji daya halicceni yakuma San cancantar fitowa daga cikinsu....... . kukane ya sark'e Galadima, Baffi ya mik'a masa handkerchief yana girgiza masa kai alamar kar yayi.

Murmushin takaici Galadima yayi, sannan ya kar6a handkerchief d'in ya tsane k'ananun hawayensa.

Baffi yace,  Muhammad Sameer akwai labarai da tarihin mutanen da yafi naka sark'ak'iya da hargitsi wlhy, sometimes abinda mukan gani a films ko hikayoyin marubuta akwaishi azahiri, saidai inhar bai faru akanka ba ko waninka saikaga tamkar k'anzon kuregene, kasan su mutane sunfi amfani da abinda suka gani da ido wato zahiri, ko suka San Wanda ya Sani wato tabbaci, a shekarun da nayi INA aiki nahad'u da cases da dama masu sark'ak'iya da ban tsoro, nakuma halarci kotuna da Dama domin ganin wasu cases d'in, idan ka samu wani case kai kanka saika ringa kokwanton anya kuwa wannan da gaske ya faru d'in? Amma daka tsananta bincikema saikaga abinda yafi Na farko mamaki, lallai a ranar gobe kiyama wasu zasu kasance cikin bayi masu tsananin kunyata agaban Ubangiji, Dan wata shari'a Ubangijine kawai mai iya mata, mu kammu acikin lauyoyi da alk'alai hummmm . Baffi ya d'an bubbuga kafad'ar Galadima yana murmushi cikin takaici.

Bai samu damar k'arasa magana ba akayi sallama, izinin shigowa ya bada, wani matashin dattijo da shekarunsa bazasu gaza 45 ba ya shigo, baikai girman baffi ba, sannan ya girmi Galadima sosai.

Mik'ewa Galadima yayi yay salute nashi, dattijo ya murmusa yana kama hannun Galadima ya zaunar da fad'in  ni da kai adai bincika mai sarama wani .

Baffi yay dariya,  kudai kuka Sani da gardamarku wacce kullum bata k'arewa inhar kun had'u .

Bak'o mai amsa Sir Isa yace,  wai Yaya naga alhaji Rabilu zaune a waje suna sa'insa da banzan can? .

Nanma dai baffi ne Yakuma darawa, yace,  duk cikin aikine, dukkan wata magana dazai takalesa ya fad'a ai itama hujjace, kasanfa halin Alhaji Rabilu ai, shiyyasa nace masa da irin aikinku ya dace ba siyasa ba .

Sir Isa da yay dariya shima, yayinda Galadima ke murmushi,  Ai yalla6ai yanzu ma aikin dayake mana bashi da banbanci damu d'in, danya bamu damar sanin abinda tsawon shekaru muketa wahala da kaikawon sani .

 Wannan gaskiyane kam Isa, yanzu Yaya za'ayi da Darma kenan? .

Sir Isa ya gyara zamansa, yana saka d'an yatsa a baki alamar tunani, zuwa can yace,  inaga kam saidai mu nema wajen ajiyesa ko yalla6ai ya Adana mana shi, dan yakamata saimun kammala tattara komai a hannunmu bayan yalla6ai Galadiman mu ya dunk'ule kifaye a ragaya, idan sun mik'a wuya shima sai a sakashi a ayari ko? .

Baffi yace,  shawararka tayi kam, inaga yanzu abinda kasaba za'ayi, dan aiki da ilimi yafi aiki da agogo, kaike 6oyewa, kuma kaine akesa kanemo 6oyayye .

Murmushi Galadima ya sakeyi baice komaiba sai jinjina kai. Duk d'insu basu damuba, dan sunsan halinsa Na rashin son hayaniya tuni, ayanzuma suna d'an ganin canji fiye da shekarun baya, shiyyasa suka fara zargin ko (Hikimar matace take aiki?) Dan kad'an daga aikin mace ta tada gari, kuma kad'an daga aikin ta ta gyarashi.

Sund'an tattauna har baba Rabilu shima ya shigo, wayar dayay recoding d'in dukkan musayar yawunsa da SD yabasu, babu Wanda baimasa jinjina ba, Galadima ya d'ora da musu godiyar hidimar da sukeyi a kansa tsawon lokaci.

Suka amsa da cewar lallai mahaifinsa ya cancanci sumasa fiyema da hakan, dan yataka rawar gani shima a tasu rayuwar.



Lokacin da suka fito abinda yabani mamaki shine su Ameer duk salute nasu sukayi suna k'amewa.

Galadima basarwa yay, sai Sir Isa ne yay musu inkiyar su sauke hannayensu, baffi yay murmushi yana kallon Galadima dayak'i kallon kowa ta gefen ido.

Sarkin mota dai yasha jinin jikinsa, musamman Basarwar da yaga Galadima yayi.

SD dake zaune ya zuba tagumi yana kallonsu kawai ya janye hannunsa, cikin jinjina kai yace,  lallai duniya tana cike da abin tsoro, wai Isa kana nufin kaima wani abune a k'asarnan? Kai kuma babban munafuki Brr Usman Audu Tsanyawa! Ba kaine da kanka kaje kasamemu da albishir d'in ajiye aikiba? Ashe wannan k'aramin kwaron d'an cikinku kukema aiki?........

A tsawace Ameer ya katseshi, tareda d'aga hannu zai makeshi amma sai Galadima ya d'aga masa hannu.

Sir Isa ne yay wata y'ar dariya yana matsawa ga Darma, yace,  Idan banda abunga Alhaji shehu kowama irin kune mai tsukakken tunani? Ai abin kallo bai k'are makaba saima nan gaba kad'an, kasan ita mota hanyarta kwaltace, birji ma idan tasamu bitake, balle dagwalon ruwa mai kayan datti, shikam jirgi miye gamisa da wannan? ko d'aga a tashi hanyar babu duk wad'annan, kaga kenan aikwai matuk'ar tazarar banbanci a tsakaninsu, kallon idoma tattancewa yake basai an shiga gasar tabbatarwa ba, kaikuma ai taka ta k'are, sauran shekaru sai a prison d'in dajin SAMBISA zaka idasu .

Dariya SD yayi, ya mik'e tsaye yana fad'in  iyaka dai Ku kaini police station, ina mai muku alwashin kwana d'aya bazanyiba a can, daga can a mik'amu Court, alk'alinma namune masu k'ananun basira, yanzu haka nasan sak'ona ya Isa ga y'an uwana, kafinma Ku kaini station d'in reshe ya juye da mujiya, dan dolene a kamaku da alhakin kamani kunga martabar wasu saita zube, mulkin da akema mutane homa da buri babushi kenan .

Murmushi Galadima yayi, dan yasan dashi yake, yad'an ta6e bakinsa yana cigaba da latsa waya hankalinsa kwance, Sir Isa da baffi da baba Rabilu, su Ameer duk kallon Galadima sukayi, don suji amsar dazai bada, amma saiya basar tamkarma baijiba.

Saida ya kammala abinda yakeyi yay kiran Nuren suka kammala magana sannan ya kalli SD yana murmushi,  Wannan lissafin naka fa ya birgeni Alhaji shehu, saidai albishir d'in dazan maka nima shine, duk wani kira dazakayi ko ayi maka to zai shigo wayatane, yanzu haka driver d'inka yayi had'ari, rashin ganinka a motar kuma zantuka sun baje kowacce kafar yad'a labarai, Na tabbata dukkan labaran rana kaine shafin farko, hakama jaridun gobe masu fita, labarin nemanka da ta Yaya ka 6ata? Shine babban labari, sukuma abokan naka hakan zai tada hankalinsu, saisu fara zargin ko dai d'an tsohon Sarkine Galadima Sameer da wannan aiki?, dole kuma sufara bincike, bayan sun haukata y'an sanda wajen nemanka, daga haka kaga nikuma saina cigaba da samun hujjoji........>�&�<��� kai zaka samin ciwon kai wlhy . Galadima ya karashe maganar da bud'e mota ya shige abinsa.

Su Ameer duk suka shiga k'yark'yala dariya, saboda yanda Darma ya mugun shiga rud'ani da sakin baki yana bin Galadima da kallo harya shige mota.

basu tsagaitaba saida Sir Isa ya tsaidasu ta hanyar d'aga musu hannu, yace,  Alahaji Shehu yadai? Kaji irin aikin masu basira ko? Kai! Kai! Harna tausaya muku lallai. Ameer! Kubi yalla6ai Galadima dashi, shikeda masaukinsa .

Angama ranka ya dad'e. Suka fad'a suna salute nashi.







>�&�<���
@&lallai nimafa yau nashiga ciwonkan Galadima, shin wane laujene cikin nad'i kuma dabamu saniba haka? Nadai fahimci Su Ameer ba y'an iskan matasa bane, kamarma jami'an tsarone?=�F�<���. To Aunty Salama fa? Data kawosu a cakwakiyar. Masu karatu, kumuje zuwa dai, nasan komai yana gab da bayyana lallai kam.9&�&<���
@&�&<���
@&.









__________



Galadima dai kam plaza suka koma, yayinda Nuren ya tari su Ameer a hanya suka bashi SD.



Acikin Plaza Galadima yad'anyi zagaye-zagaye, saida ya tabbatar da komai dai-dai a wajen ma'aikatan sannan ya fito suka d'auki hanyar masarauta.





*******



Bayan fitar Galadima Aunty Mimi sashen su Munaya ta nufa, ta isketa har yanzu tana juya kalaman Galadima dabata fahimtaba.

Bayan sun gaisa tabata Umarnin ta shirya dan za'a kaita sashen manyan gidan ta gaishesu da bangajiya sannan suga yara, inhar zaki tafi wanka bayan kwana d'aya da suna haka akeyi a masarautar, to amma su nasu Munaya yazo da Matsala, tunda gashi sai bayan kwanaki hud'u da suna zasu tafi, matan Sarkine kawai basa zuwa gida wanka.

Kuyangi biyu sukaima Munaya shiri, itadai wannan lamari Na d'aure kanta, haka kawai da girmanka ace komai sai anmaka, dolene mai mulki yake kallon talaka ba komaiba, sauk'inta ma bakomaine Galadima ke bada fuskar ayi mataba, yama hana hadiman masarautar sakewa a sashensa gaba d'aya, sai iya wad'anda ya aminta dasu kawai.



Yaukam tasha kallon kanta a mirror, hakan yakuma tabbatar mata da tuna mata agidanfa SARAUTA take, a kuma matsayin matar mutum mai girman rawani da matsayi a Masarautan.



(Kusan dai mutuniyar taku da jan aji=� �, ai saita kuma tsumewa tana basarwa>�#�).



Suma yaran an musu shirin dake nuna lallai Ubansu waninine a wannan masarauta, sannan suma ababen tattaline ga wannan kujera kwara 1 tal dakowa ke mutuwa da rayuwa a kanta a masarautar gagara badau9&.

Sun sami rakkiyar kuyangi da Aunty Mimi, kowane sashe saida suka zagayashi amma a mota, an farane da fada.

Yau itace ranar farko da Munaya ta shiga Fadar sarkin ta, yaukam taga abin mamaki, musalta yanda wannan fada ta k'awatu ai 6ata lokacine kawai, ammafa lallai komai yaji, ga Sarki hakimce bisa garagarsa cikin kwarjini irinna mutuntakar mulki, sarkinmu kenan kuma sirikinna ta wani fannini, daga ni sai aunty Mimi da kuyangi ukune muka shiga, kowanne d'auke da yaro d'aya a hannu.

Fada cike take mak'il anata fadanci, Su Wanbai da talba duk ana ciki, hakimai da masu manyan muk'amai Na masarauta da wajen masarauta duk an hallara, kasancewar shine zaman farko Na wannan makon, kuma ana saka ran zuwan Governor ne da zaizoma mai martaba jajen abinda ya faru Na 6atan y'an uku, dan labarine daya zagaye kowacce kafa ta yad'a labarai da socia media Na k'asar nan, (kunsan dai abin manya duk k'ank'antarsa saiya fita, balle wannan da yazamo mai girma).



Bayan Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka kwashi gaisuwa, dogarai suka amsa da yawun Sarki, sannan suka kuma gaisheda fadawa.

Daga nanan aka amshi su Abdurrahman, y'an majalissar Sarki sukaita d'auka d'ai-d'ai suna saka musu albarka, da addu'ar fatan alkairi.

Bayan fitowarsu sai sashin iyalan mai martaba, yau ma dai gimbiya zulfa bata fasa nunama Munaya da yaranta soyayyaba, daga Munaya har aunty Mimi basu San komaiba, dan haka sukaji dad'i da sakin jikinsu fiye da sauran matan sarki.

Daga nanan sai sashen Mama Fulani, (kaga manya, Sarautar gagara badau a hannunku take, mama fulaninmu ta mutunci>�8�<���
@&=��, ga irin naku manyan mata=�M�<���)



To kunsan dai mutuniyar taku, yauma dai cikin izzar mulkinta suka isketa, ita dama Aunty Mimi babu ruwanta, tana mata yanda takeso, shiyyasa babu y'ar habaici ko bak'ar magana tsakaninsu kamar Galadima, hakanne yasaka munaya samun tsira daga samun nata rabon, amma mama Fulani bata d'auki yaro ko d'aya ba, a hannun kuyangin ta gansu tana ta6e baki.

Daga Munaya dai har aunty Mimi babu Wanda yay ko tari, to balle kuyangi dasuka zama takalmin takawarta, basu jimaba suka fito, haka sukaita zuwa sashe-sashe, basu sami Kansu ba saida suka Shiga ko ina .

Sun dawo kusanda awanni biyu aka gama loda kayansu a mota Samha da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login