Showing 174001 words to 177000 words out of 365757 words

Chapter 59 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1538

dama haka gidan sarautar yake, dan saidama Galadima yaje da kansa ya shigo dasu. Su Aiyaan anata murna anga 'yan gida.

Ranar dai anan suka yini zir, dazasu tafi Galadima yay muzu alkairi mai yawa tareda godiya ta musamman. Sunji dad'i sosai kuma sunyi farinciki, sunata masa godiya nima ina tayasu.

Da zasu tafi jinai tamkar na rik'esu, aiko harda 'yan kwallana, sauk'inama kawai su Aryaan tare dani.



Kowaccensu tatafi da labarin data gumtsawa uwarta a bayan fage, dansu Zarah dai sun Shiga taitayinsu, sun gane ruwa ba sa'an kwando bane, nanfa hassada da bak'inciki tamkar ta babbake zukatansu, mamansu Yaa hameed hardama Abba ALLAH ya Isa tana sharar kwalla, wai yasan da gidan sarautar amma ya yarda Zarah ta auri d'an sanata, ga aunty khaleesa nanma kullum cikin matsala da miji, dan kishiyarta akwai kissa.





*_ALLAH yarabamu da ciwon hassada fans_*=��





Sati d'aya da zuwansu muka koma India, saboda Company suna Neman Galadima da gaggawa. harda innaro iya bala'i muka tafi>�#�.

A jirgi taita kudundune fuska a gyale wai batason ganin tashin jirgi, duk tsare gidan Galadima saida yayi dariya, Aryaan da Aryaan kam sukaita tsokanarta. Yau babu masifarnan dan bata kulasuba, saima Galadima ne ya hanasu. nikam banza na musu dan tawama ta isheni nikam. Jikina sai ciwo yakeyi, ga cikina na mun ciwo shima kad'an-kad'an.

Khumar da Sauban da Samha sukazo d'aukarmu, muka rungume juna da samha muna farinciki.

Daga nan muka wuce gida, yaukam munashan k'auyancin innaro, ni harma tabani haushi, komai tagani saita tambaya, Kodai su Aiyaan basa abinda takeyi.

Mun iske jakadiyane kawai sai bayi, Su Momma da innarmu suna asibiti, Mudai sama muka haye ni da shi, 'yan biyu kuwa suna wajen Samha ta kasa ta tsare, innaro kuma aka barta da jakadiya.

Ko ina tsaf yasha gyara tamkar mai d'akin na nan, Muna shiga kwanciya nayi bisa kujera, naja bargon saman gadon na lullu6e, kallona yayi da mamaki  k lafiyarki kuwa? .

 zazza6i . kawai nace masa na k'udundune har kaina.

Zama kawai yayi ya zubamin idanu cike da tausayi, ganin zaman bazai masaba yatashi ya shiga toilet, saida ya gama dukkan uzirinsa sannan nima ya had'amin ruwan wanka, tadani yayi, na tashi da k'yar tamkar zan masa kuka.

Yace,  tashi kije kiyi wanka kozakiji dad'i .

Baki na tura masa gaba.

 idan bazaki iyaba tashi muje na miki .  yay maganar cike da basarwa .

Harara na zuba masa sannan na mik'e na nufi bayin. shikuma ya ta6e baki yana wani mikilin Murmushi.

Abincima sai nan ya saka aka kawomin, dan nakasa sauka.

Innaro sai catake wai nacika langyare, dan naga yana shagwa6anine shiyyasa nake ta6ara, ai badaga kaina aka fara cikiba.

Galadima dai murmushi kawai yayi danshi lamarin innaro abin dariya ya d'aukesa, tana buk'atar uzuri.

Bayan nasamu naci abinci daya bani nasha magani, harzan kwanta a sofa yace na koma saman gadon, kamar zanyi magana saina fasa, na tashi kawai na koma.



Yana kammala duk abinda ya dace yafice asibiti domin duba Abie da Abba.

Yaji dad'in yanda yaga canji sosai a jikin nasu su duka, dan raunuka da yawa sun warke a jikin Abba, da bakinshi ma ya amsa masa gaisuwa yana masa godiya, inna da baba k'arami sunata saka masa albarka. maganar da abie ya fara kuwa rungumesa yayi yana kuka Abie nayi, hakama su Momma, a hankali Abie yace  ina d'iyata Muh'd .

Murmushi Galadima yayi, yace,  zuwa anjima zaka ganta Abie, yanzu na barta tana barci zazza6i ya rufeta .

Momma da Aunty Mimi sukace  ALLAH dai ya sauketa lafiya to .

Babu kunya Galadima ya amsa da amin.

Aunty Mimi dake kusan dashi ta doki gefen hannunsa,  kai mara kunya, shine zaka amsa .

Hannu ya saka ya rufe bakinsa yana fad'in  ni jikan Abdul'fatah da Abubakar .

Dak'uwa Momma tamasa tana kai masa duka, ya matsa da sauri yana dariya.

Abie ma murmushi yakeyi, lallai yau yakuma ganin canji tare da d'ansa sanyin idaniyarsa, sukam yaushe rabon da suga irin wannan nutsuwar tare dashi haka, lallai dolene su godema ALLAH da shigowar Munaya cikin rayuwarsa, basu da wani abinda zasu iya biyanta har abadan, saidai suyita mata fatan alkairi da k'yautata rayuwarta.

Saida na tashi sannan muka tafi asibitin muma, wajen su momma muka fara zuwa, Momma da aunty Mimi sukazo suka rungumeni tamkar zasu had'iyeni dan dad'i, nikam duk kunyarsu ta gallabeni, sai 6oye fuska nakeyi, koda zan gaida Abie ban yarda na kalleshiba.

Sauban da Samha sai dariya sukemin.

Duk bak'in halin innaro saida tayi kuka ganin halinda Abie yake ciki, taita kwarara masa addu'a kuwa.

Su momma sunji dad'i, kuma sunata girmamata.

Samha sai dama-dama takeyi dasu Aiyaan, motsi kad'an tace,  ALLAH yasa Aunty gimbiya muma ta Haifa mana irinku . Su Momma sunata amsa mata da amin. Nidai kaina na k'asa saboda kunya, ina lura da Galadima kuwa duk sanda tafad'a saiya murmusa kuma bakinsa ya motsa alamar yana amsawa da amin.

Sosai naji dad'in ganin jikin Abbanmu shima, dan har magana mukayi, jikinsa yayi k'yau sosai, karayunne ma kawai suka rage nakula, amma k'ananun ciwukan duksun warke, to wajene dayake samun kulawa ta musamman. Munaya harda rungume inna, itako ta tureta tana hararta, su Aiyaan kam duk sun d'are bisa cinyarta suna d'okin ganinta da kewarta. Itama tayi kewarsu over, tsakanin uwa da d'a kenan (iyaye mata ga naku fa>�p�>�p�>�p�d'=�M�<���).



Haka muka dawo gida ina farinciki, koba komai nasamu nutsuwa mai yawa a yau d'innan, aiko ban yarda mun kwantaba saida nayi nafilfili domin mik'a godiya ta ga ubangijin sammai sannan na kwanta.

Galadima kuwa muna shigowa d'akin sirrinsa ya shiga yanata aiki.









___________________________





Hankalin Minister ya kai k'ololuwar tashi shida families nasa akan 6atan 'yarsa, farhat, duk wata hanya daya kamata subi sunbita amma babu koda labarin Wanda ya ganta, tun lamarin nabasu mamaki harya koma basu tsoro, ga wani text massage da akama minister d'in d'in kwana 10 daya wuce.



_Idan kana buk'atar 'yarka kana iya mik'a wuya._



Wannan massage ya tsaya masa a rai, har police sun kar6a amma sun gaza gane komai gameda massage d'in ko wannada ya turo shi.

Mahaifiyar Farhat harda kwanciya asibiti, dan ita kad'aice mace a gidan, dan haka suke masifar son yarinyar da mata gata, dudu shekarunta 16 ne kawai, tana wata private boarding school ne a abuja. a binciken da Galadima yakeyine ya gano hakan, kuma yayta bibiyar yarinyar har saida yasamu nasarar saka Nuren ya kwamuso masa ita.







___________________________





Tunda muka dawo India bani da lafiya, kullum innaro cikin min gorin ni ragguwace take, bana wani kulata dan tawa ta isheni, koma uwarmi zata fad'a ta shekara fad'i, bazan yarda mu Raba hali a gidan surukai naba, nakan bar lamarinta a wasan jika da kaka agabansu, amma ni nasan badan hakan takeyimin ba, ita kanta innarmu bata kulata ko kad'an, idan tanayi shiru take mata ma.

Kulawa kam bazanyi butulciba ina samu wajen Galadima dasu Momma, musamman ma jakadiya da Aunty Mimi. Saukina ma cikin bamai tsurfa baneba, komai inaci hankali kwance, kuma ban ta6a amaiba ko wani zubda yawu, saidai zazza6i da ciwon jiki.

Yaudai dole Akash yazo har gida ya sakamin k'arin ruwa, kozan sami sasaauci.

Yini guda yau a gida Galadima yayisa, duk wani motsina akan idonsane.





**************************





*_5 months ago_*=�F�<���=�D�=��





A kwana atashi babu wahala wajen ubangiji, rayuwa ta shud'a, kwanaki nata sauri, a wanni da mintuna kam ai ba'a cewa komai, abubuwa masu yawan gaske sun faru a watanni biyar d'innan, ciki harda warkewar Abbanmu sarai, tamkarma baiyiba, saidai k'afarsa da yakan d'an tizgid'a saboda matsala data samu, shima saika k'uramasa I done zaka fahimci hakan.

Innaro dai dasu Aiyaan tuni suka koma saboda makaranta, sai dai duk Hutu Galadima yakansa azo dasu Aiyaan d'in, hakama Munubiya da yaa marwan sunzo sun mana sati biyu sukaga jikin Abba da Abie.

A wattani biyar d'inna Galadima yaje Nigeria kusan sau hud'u, dukda bai ta6a fad'amin wani abuba ina samun bayanai ga Saleem da sarkin Mota. har yanzu kuma Farhan d'iyar minister tana hannunsa, hakama Malam Saminu driver Alhaji Balala.

Yaran gidanmu masu cikkuna duksun haihu, su Siyama an zama iyaye, naji haushin rashin halartar taron suna ko d'aya, dan dana fad'ama Galadima inason zuwa banza yamin, naci kukana kuwa na hak'ura, sai turomin abubuwan da akayi sukaitayi ina gani.



Cikina ya fito kwarai da gaske, dan yanzu yana cikin wattani 7 da wasi kwanaki, yamin d'as yakuma sakani k'iba, duk kamannina sun canja, kumatuna sunyi manya, dukdai wanda ya ganni zaisan na canja, hakama Munubiya, idan ta turomin hotonta nata dariya kenan.

Tsakanina da Galadima kuwa har yanzu muna a yanda kowa ya sammu, canji d'aya zance ansamu shine nuna yawan tausayinsa akan cikin jikina, dan dukkan wani motsina cikin nuna damuwarsa yake. Idan yana wajen aiki kam yakan kirani sau uku sau hud'u dan yaji lafiyata kawai.

A 6angaren iyayensa da danginsa kam banida abin fad'a sai godiyar ALLAH, dan tamkar a kainane aka fara ciki haka suke nunamin kulawa.

Hakan nama Innarmu da Abba dad'i, hankalinsu na kuma kwanciya sosai akan aurenmu. baba k'arami yakanyi wata d'aya ya tafi Dady kuma yazo, haka suka dingayi har ALLAH yabama Abba lafiya.

Jikin Abie ma said dai muyitama ALLAH godiya, dan bayan magana an kuma samun cigaba 6angaren motsa hannunsa, yanzu kuma maganarsa takan d'an fito yanda akeji, saidai duk wannan cigaban da ake samu babu Wanda yasan dashi, har mai martaba k'aninsa, kaf masarautar gagara badau da dukkan wani makusanci bai San komaiba a kai, dan papi yahana fidda maganar, ko zuwa akai dubashi yakan komane tamkar yanda ya saba kamar da, daga mama Fulani har mai martaba sunzo kusan sau uku dubashi, hakama Muftahu da Harun, 'ya'yan Sarki ma dama suna k'ok'arinzuwa lokaci-lokaci suma. Hakama Hayatuddin Autan mama Fulani. amma babu Wanda aka bama damar sanin wani sirri akan jikin Abie d'in. dagamu sai mu kawai muka Sani.

Dukda fama danake da kaina haka na dage muka cigaba da addu'oin nan, zuwan innarmu ma yakuma sakamu ho66asa saboda taimakon da take bamu, sannan muka raba addu'oin ga wasu musulmai malamai dake nan suma suka cigaba da tayamu, aka cigaba da bama Abie yanasha da wanka, doctors d'in sunyi surutunsu harsun gaji sun barmu, dan munk'i fasa masa amfani dasu, tunda muna ganin haske a lamarin sosai.



A wata ranar talatar da su Abba suke shirin tafiya k'arshen satinne ina zaune a falo ni kad'ai, dan Galadima ya fita aiki tun safe, zafine ya isheni na dawo falon na k'ure AC, dan Galadima ya saka ma na bedroom d'in key saboda k'urewa da nakeyi, gashi inata fama da mura, shi kansa abin cikina ance tana Neman shafarsa. nikam bana iya hak'uri da Abu mai sanyi konasha ko AC.

Sosai na baje ina kwasar dad'ina, sai faman lumshe idanu nake a cikin kujera, gama wayarmu kenan da Munubiya itama tana bani labarin halin son Abu mai sanyin datake a ciki, kullum Yaa marwan fad'a shida mama Rabi'a amma bata d'aga k'afa, data faki ido saita sha, Ayusher da dole ta dawo gidan tayata wasu abubuwan saita gani ta sanarma Yaa marwan, shikuma yay ta jarabar masifa, amma hakan bazai hana gobe tagani ta shaba........

Jinai kawai iskar dake ratsani ta daina shigata, na bud'e ido sai naga Galadima tsaye jikin k'arfen bene daya shigo ta falon ya hard'e hannayensa a k'irji ya zubamin ido ransa a 6ace, hannunsa rik'e da remote d'in ACn.

Tsorone ya kama ni, na tashi zaune ina wani marmar da idanu, da hura kumatu danaketa yi, takowa yayi inda nake, idonsa tamkar zai fad'o dan hararata  k kin rainani ko? bazan hanaki Abu sau d'aya ki daina ba, ki duba muran dake damunki tun cikinnan nada wata 3, shin ke bazaki tausayama kanki baneba? .

Shiru nayi bance masa Uffanba, sai faman kumbura baki dai nake yi.

 kinsan ALLAH idan baki maida wannan bakinba na kamashi saiyayi jini .

Da Sauri na maida bakina, dan ban manta muguntar da yaminba kwana biyu daya wuce, ba k'aramin morata yakeba yanzu, saboda ALLAH yabani ciki mai sakani yawan buk'ata, sai komai ya lafa nayita masa kuka, shikam ya shareni saboda shegen miskilanci da k'asaita, idan na ishesa yace zai makeni, aibashi yace na kawo kaina ba, dan haka nabar cika masa kunne da ihu, anjima ma nazo yi zaiyi tunda ba fyad'e yaminba ninake kawo kaina.

Sometimes nakanji haushin furucinnan nasa, nakuma yi alk'awarin nisantarsa, amma bana iyawa, kona d'auki alwashin saina karya, da yazo yara6u jikina nake mik'a wuya, mugun tunda ya gano lagona saiya dunga bina ta wannan hanyar, duk sanda yaji buk'atata yasan yanda zaiyi ya ra6u da jikina harta kai ga wani abinda nikuma zan mik'a wuya batareda na saniba, saidaga baya nake gane kuskurena.

Ganin namasa banza nak'i tankawa saiya shige bedroom yana tsaki, komawa nayi na kwanta ina share hawaye. ga zafi ya fara addabata.



Kusan mintuna 19 sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa k'ananu, da Alama wanka ma yayi, k'in kallon inda yake nayi harya samu kujera ya zauna, remote ya d'auka ya kunna TV.

Haka mukaita zama tamkar wasu kurame, kusan 30minutes, kiran da Nuren yamasane yasakashi d'agawa, bansan miyake fad'a masaba naga dai ya mik'e ya shiga d'akin sirrinsa.

Na dad'e ina kallon k'ofar, zuwa can nima na yanke shawarar binsa kawai.

Doguwar rigace yellow a jikina, batada hannu, sannan bata kaimin k'asa ba, kad'an ta wuce guywata=�W�, banason kaya masu nauyi saboda jin zafi, sai silifas d'in k'afata jaa mai taushi. cikinan ya kaimin ko ina, jinake kamar na jawo haihuwar na juyeshi na huta.

Ciki-ciki nayi sallama, bai jiniba, hankalinsa nakan Computers d'in d'akin dayake k'ok'arin dai-daitawa, duksun kawo wuta, har k'aton glass d'in dake jikin bango guda na d'akin, ban ta6a d'aukar shima Computer baceba sai yau, dukna d'auka saboda ado aka sakashi a wajen.

Sallamar na k'ara yi, ya juyo yana kallona, idonsa na cikin medical glasses mai haske, dan har kwayoyin idanunsa ina hangowa.

Kamar zai shareni saikuma ya amsa mini, juyawa yayi yacigaba da abinda yakeyi, mikuma yagani saiya juyo, ya jawo kujera ya gyaramin, yay min alamar da ido na zauna.

Babu musu na zauna, ya d'auki remote ya rage gudun AC d'in d'akin, sannan ya juya ga abinda yakeyi.



Yanda yake sarrafa Computers d'in saiya tafi da imanina, kai guy d'innan yasan Computer over.

Bansan lokacinda bakina ya su6uce nace,  yalla6ai ALLAH ya baka .

Juyowa yayi yana kallona da mamakin furucina, ya saka pen d'in hannunsa a baki yana wasa da shi, kafin ya shiga takowa gareni, k'asa nayi da idanuna nabar kallonsa, yaja kujera ya zauna kusa dani, idonsa a kan cikina, ban Ankara ba naji hannun nasa a saman cikin, idanu Na d'ago Na kallesa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in  ALLAH ya bani k'yautar magaji? .

Murmusawa nayi ina girgiza masa kai,  niba haka nake nufiba fa .

 mikike nufi to? .  yay maganar yana janye hannunsa daga cikin nawa .

Fuska nad'an ya mutse, cikin salon yanga nace,  ina nufin ALLAH yabaka nasibin sarrafa Computer's  .

Yanda nayi maganar cikin salo saiya sakashi murmusawa yana ta6e baki,  toni miye namin yanga yalla6iya? saikace kina tare da masoyinki? .

Haushi ya kamani Na dalla masa harara.

Bai kulaniba ya mik'e yana fad'in,  masu cikifa saida uzuri .

Harna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login