Showing 195001 words to 198000 words out of 365757 words

Chapter 66 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1502

gidannan dokace, babu television, babu phones, amma way not nakawo miki irin Hausa novels d'innan danaga mata na karantawa? .

Idonta ya cika da kwalla,  ayya yayana wlhy ban iya karatun hausaba sosai, yana bani wahala .

Ido yad'an zaro waje, yace,  saboda mi? Keba bahaushiya bacene? .

 bahausa mana .  tafad'a cikin turo bani irinnan ta6ararru .

Baki ya ta6e yana kama hanyar fita,  zaki cigaba da kad'aicinki ashe kuwa .

Ganin zai fice da sauri tace,  please ka siyo zan fara koya to .

 it's better .  yafad'a yana ficewarsa .

Saman gadon ta fad'a ta fashe da kuma mai ban tausayi.





Duk abinda ke faruwa Galadima najin komai ta waya, Munaya ma na zauna a sofa har yanzu tana satar kallonsa, amma batajin miyake saurare da ya nutsu haka.

Cire wayar yafara k'ok'arin yi ya jiyo muryar Nuren na fad'in  hello brother kana jina? .

Galadima yace,  eh .

 okay duk kaji aimi ta fad'a ko? .

 duk najiku, saika samin ido akan duk d'unsu, a bincikomin komai daya shafesu .

 indai wannanne insha ALLAH angama, amma ni a ganina banda wannan Shareffuden d'in datace, domin babu wani kamanni a cikin nashi sunan, ballema tace k'anin step mom natane .

 Humm Nuredeen kenan, shifa mak'iyi ba'a rainashi, mutane da yawa sukan d'auki cinnaka ba komaiba, amma idan yacijesu sukan ji cizon har a ransu, dan haka karka ta6a d'aukar mage mafi sauk'i akan kare, itama idan taga nama citakeyi .

 wannan gaskiyane brother, ALLAH yabamu sa'a .

 amin ya rabbi, naji kuna maganar buks da ita, kaje ka samo mata dukkan Wanda take buk'ata, har English novels d'in, sannan ak'ara tanadar mata dukkan abinci mai k'yau datake so .

 insha ALLAH angon Munaya .

Girgiza kai kawai Galadima yayi ya yanke wayar.



Kallon Munaya yayi suka had'a ido, saita janye cikeda basarwa. Shima tashi yayi ya koma gaban mirror, duk uzirinsa yayi ya gama sannan yamatsa ga wardrobe ya ciro kayan dayake buk'ata.

Ganin haka Munaya tazame ta kwanta cikin kujerar yandama bazata gansaba.

Baki kawai ya ta6e yacigaba da saka kayansa.

Bayan yagama yamatsa kusada ita,  tashi ki canja kaya ki rakani wani waje .

Fuska Munaya tad'an yatsina, kamar zatace wani Abu saikuma ta yunk'ura zata tashi kawai, hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune. fita yayi abinsa. Hakan yasata fahimtar zai jirata a falo kenan.



Bata 6ata lokaciba ta canja kayanta da atanfa skt da riga, takawo after dress ta saka sannan ta nad'a Vail d'in rigar, d'as ta fito itada cikinta, kamar ka saceta ka gudu abinka.

Tunda ta fito ya zuba mata idanu, ko k'yaftawa bayayi, saida yaga tana gabda k'arasowa garesa ya basar yana mik'ewa. Gaba yayi tabisa abaya, yandama yake taka steps d'in benen dolene ya birgeka, duk takunsa nakan idonta, yayinda itama take binsa daki-daki a hankali.

Babu kowa a falon, dan haka suka fice basu nemi kowanba.



A mota yana tuk'i da sauraren karatu itakuma tana latsa waya suna charts a families group d'insu. Sai murmushi take zubawa, duk abinda take yana kallonta ta gefen ido. Sun isa wani k'aton shagon saida kayan babies, duk abinda kake buk'ata zaka sameshi indai na yarane daga 1year zuwa 15. Itadai mamaki ya ishi Munaya, miye nawani kawota nan? yabari a haihun mana ma.

Tarba ta musamman aka musu, hakan ya tabbatar ma Munaya yasan mai shagon kenan, dan yanda aketa girmamasu sai abin ke bata mamaki. gashi indiyanci sukeyi bata fahimtar maganganunsu. Itadai tana zaune hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu Galadima da kuma wasu mata biyu da yaransu uku dabazasu wuce 7-7years ba, yaran k'yawawa masha ALLAH, ga wayo.

Galadima ya juyo zai mata magana saiya lura da inda ta zubama idanu, shima shagala yay a kallon yaran, iyayensu na za6ar kaya amma su suna tibirewa sai Wanda sukeso za'a d'auka. Munaya sai zuba murmushi takeyi, dan suntafi da imaninta, shima murmusawa yayi yana lasar lips, kafin ya d'auke kansa ya maida ga Wanda suke maganar.

Zuwa can gardama ta hark'ume tsakanin yaran akan wani game da iyayen ke dubawa maybe zasu saya musu ne. Kuma games d'in suna kusada Munaya ne, d'aya a cikin yaran ya d'akko yazo wajen Munaya yana tambayarta wai  Aunty wannan yafi dad'i aidai ko? .

Munaya bata fahimceshiba, dan yayi maganane da yaren dabata ji, dan haka saitayi murmushi ta tambayesa yanajin English?.

Yaron ya d'aga mata kai alamar eh.

Ta kuma murmusawa, duk abinda ke faruwa a idon Galadima ne.

Da turanci munaya tace,  yarona kai kata6a irin wannan game d'inne? .

Murmushi yamata shima, yace  aunty akwai dad'i ma sosai, ranar saida na cinye kharan a gidansu ma .

 da gaske? . munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa.

Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace,  Aunty na koya miki? .

Munaya ta d'aga masa kai.

Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sai kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace  mikenan to? .

Shima dariyarsu ta yara yayi, yace  Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal .

Sosai abun ya birge munaya, tayi dariya har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta rungume.

Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata suna itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka.

Wadda tace sunanta Radha tace  kiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'an .

Munaya tace babu komai.

Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu.

Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma yasa ya barmusu.

Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai.

Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta tambayesu akan me?.

Suka bata amsa da cewar mijinta bai kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?.

Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta, babu musu tabasu sukayi sallama suka tafi.

Maida kallonta tayi ga Galadima dake zaune yanata latse-latsen laptop tamkar baisan mike faruwaba, da alama yana duba kayane ko wani Abu, dan time to time Wanda yake gefensa yakan nuna masa wani yanki na kayan dake shagon, shikuma ya waiga ya kalla, idan bai hango sosaiba saiya kalla ta cikin Computer d'in dake tareda cctv cameras d'in shagon.

Munaya tace kai mutuminnan akwai son kud'in tsiya, kai komai kana saidawa, wata zuciya tace idan bai nemi kud'iba dame zai kula da mahaifinsa?.  hakane kuma . ta fad'a a fili tana sauke ajiyar zuciya.



Kusan mintuna 15 saitaga ya taso ya nufota. Zama yay kujerar kusa da ita yana fad'in  sorry friend na barki ke kad'ai. kin gaji mu tafi ko? .

Munaya tad'an yamutsa fuska tace  ba sosaiba .

Ya d'an murmusa,  ok tunda baki gajiba kozaki d'an mana taimako ni da abin cikin kwan? .

Hararsa tad'anyi, itafa haushin wannan abin cikin kwan dayake fad'a takeji.

Hannu yasa ya dafe bakinsa yana fad'in  maida wuk'ar .

A tare suka dinga zagayawa cikin shagon, dayake babbane sosai, kayan yarane kuma zalla a wajen, komai bibbiyu take d'auka, baice komaiba, dan yasan dai bai wuce tana had'awa da cikin 'Yar uwarta Munubiya bane. Sund'an d'iba kaya babu laifi, yabada ATM d'insa aka d'auka harda na wad'ancan matan, yaran shagonne suka kai musu har cikin mota.

Yanzuma haka suka taho tamkar kurame.

Kowa da abinda yake sak'awa....

Danja data tsayar damune yasakashi juyowa yad'an kalleni, ganin hankalina nakan wasu yara 'yan makaranta dake mota yace,  dama haka kike da son yara? .

Juyowa nayi Na kalleshi, amma saiya d'auke kai tamkar bashine yay maganarba ma.

Nima maida kaina nayi ga yaran, a kuma time d'inne muka sami damar barin wajen.

Saida muka fara tafiya nabashi amsa da  yalla6ai kenan, waye zaice baison yaro, a duniya babu abinda yafi k'uruciya dad'i .

Kad'an ya juyo yad'an kalleni yana fad'in  really? .

Nima kallon nasa nayi ina fad'in  na tabbata amsarnan kowama zai baka idan ka tambayesa .

Bai kalleniba yanzun kam, hankalinsa naga tuk'insa, yace,  ALLAH ya kawoka duniya lafiya abin cikin kwan .

 shiru namasa bance uffanba .

Har muka isa gida kuma babu Wanda ya sake magana a cikinmu. Saida yay parking motar a harabar gidan sannan ya juyo gareni, ina niyyar bud'ewa Na fita ya ruk'o hannuna. kallonsa nayi da mamaki, yawani ci magani irin babu raininnan, kamar zanyi magana saikuma nayi shiru muka zubama juna ido, kowannenmu zuciyarsa Na bugawa da sauri-sauri. Cikin k'asaitarnan tasa yace,  Addu'a nayi amma jan aji yahanaki amsamin da amin .

Ni dariyama ya bani wai jan aji, hakanne yasakani murmusawa kad'an ina k'ok'arin janye idona daga cikin nasa, amma saiya hanani hakan, nace,  na amsa ai, bakaji bane kawai .

 aiba kurma kika auraba .

Uhm wannan aure ana tak'ama dashi, Na fad'a a raina, a fili kuma nace,  a zuciya Na amsa .

 k'arya haramun, banji wannan sak'onba a tawa zuciyar .

Da mamaki Na waro idanu waje ina fad'in  ban fahimceka ba .

Lips d'insa yad'an ciza da hak'ora yana matsoda fuskarsa dab da tawa, gashi ya sark'eni da idanu nakasa matsawa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyata, muryarsa k'asa-k'asa tamkar mai rad'a yace,  zuciyoyi aminan juna sukan kar6i sak'on juna alokacinda d'aya ya aikashi ga d'aya, karki jahilci kanki har yanzu akwai sauran dama .....

Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice.

Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nakasa fassara zantukansa da ma'anarsu.

Tsawon mintunan dahar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahankali Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa, ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace  wasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutu .

Ya d'ago kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'ina, ya juya zuwa cikin gida.

Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki.

A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmama juna.

Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa.

Ni kad'ai Na amsa, Galadima hannu kawai ya d'aga musu.

Momma tace,  kuje ku huta mana .

mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta.







&&&&&&&





Da daddare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne dan haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ago ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa.

Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na shago mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai.

*_Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal._*



Saida yakuma maimaita maganar kusan sau uku a ransa, kafin ya kalli Munaya da dukkan hankalinta ke kan Novel,

 Friend! .

Ya kirata a nutse.

Da  na'am Na amsa ina kallonsa, saikuma Na janye saboda wandon jikinsa baiko rufe masa cinyaba, sai k'aramar riga mara hannu.

Yace,  mikika fahimta ga zancen abokinki na shago? .

 abokina? waye abokina? .

Tasowa yayi dagashi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon, nima saina tashi zaune sosai.

Ya zauna ta gefe tareda ajiye mug d'in hannunsa a drowa d'in gefen gadon, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannu ya mik'amin alamar nazo.

Ban musa masaba Na matso, ya kamoni ya sakani a jikinsa, dan tsakkiyar k'afafunsa ya sakani, saina zame Na kwanta na d'ora kaina a cinyarsa, (dama wajen lak'ewa nake nema>�*�).

Ya kar6i buk d'in hannuna ya ajiye gefe, ya d'ora hannunsa a saman cikina.

Kuma maimaita masa tambayar nayi.

Ya shafa sajensa yana cije lips,  miyasa wataran kike da basarwa ..

 ni d'in? .  nafad'a ina nuna kaina da kallonsa .

Bai bani amsaba yace  ina nufin yaron d'azun .

 Oh sorry . nafad'a ina gyara kwanciyat.

Nace,  wai Vishnu?  .

Kansa ya d'aga min

 to amma wace maganace tasa? tazama abin nazari yalla6ai? .

 game .

 game! game! nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.

 okay, wai yanda yafad'i yaci game d'in? .

 Uhhm . ya fad'a a tak'aice..

Nikuma saina murmusa,  to dukda dai bansan ma'anar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafasu akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa bane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasa .

Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.

Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.

Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login