Showing 234001 words to 237000 words out of 365757 words

Chapter 79 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1483

maidani.

Munkai mintuna 7 sannan ya zameni ya kwantar ya mik'e zaune, batareda ya kalleni ba ya sauka daga gadon, bathroom ya Shiga, babu dad'ewa ya fito, nidai kallonsa kawai nake da mamaki, Dan fuskarnan amatuk'ar d'aure take tamkar baisan minene dariyaba a rayuwarsa, ya shinfid'a abin salla, domin rama sallolin da suka riskesa yana barci.

6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, na tashi zaune idona akan yaran, duk sun koma barci, na tsurama Abdurraheem ido, saboda fitar numfashinsa ta banbanta dana y'an uwansa, tunani nai ko yanayin nasa barcin kenan shikuma, saboda wahalar da suka sha,

d'aukar ledar kayan da mom ta kawo nayi, na fiddasu na saka, ban jira ya idarba na fice abina.

Nayi mamakin da yanzu babu kowa, harsu Munubiya sun tafi, haushi ya kamani kamar zanyi kuka, aidai sa jira na fito mu gaisa ko? hawayen da suka zubomin a kumatu na share, namafi jin haushin Munubiya wlhy.

Sallamar da akeyi na amsa da k'yar, sannan na bada izinin shigowa, cikin bayina ne guda biyu, zubewa k'asa sukayi suna gaisheni.

Cikin girmamawa d'aya tace,  dama ance mu gani idan kin fitone .

Nace,  Hummm .



Fahinmatar iya amsar dazan iya basu kenan ya sakasu mik'ewa suka fita, zamewa nai na kwanta cikin kujerar ina cigaba da zirar da hawaye.

Kusan mintuna 5 saiga Samha ta shigo, ta durk'usa gaban kujera tana sharemin hawayena, d'ago ido nayi na kalleta, namata murmushin k'arfin hali ina tashi zaune.

Muryarta da alamun tasha kuka itama tace,  Aunty Uncle Sam na kiranki .

Kai na jinjina mata kawai, na tashi gaba d'aya na d'auki mayafi muka tafi tare.

Koda mukaje k'ofar falon bata Shigaba, nikad'ai na Shiga ita kuma ta juya ta fice daga sashen gaba d'aya.



A falo na iskeshi cikin doguwar kujera a kwance, ya kifa yaron d'aya a k'irjinsa Wanda nake k'yautata zaton Abdurraheem ne, wayace manne a kunnensa, amma a hankali yake magana koni danake tsaye cikin falon banaji, na kalli abincin da aka jere a tsakar falon ina zama a kujera.

Bai dad'eba ya kammala wayar, idonsa dake jajir har yanzu ya d'ago yad'an kalleni, jijiyar kansa dukta tashi rud'u-rud'u. saida yad'an lumshe idanu kafin ya motsa la66ansa ahankali yace,  kici abinci inji inno .

Dukda maganar taban haushi haka na danne, wato inji inno ma ba injishi ba ko?. Sakkowa nayi k'asan lallausan carpet d'in, d'aya bayan d'aya na bubbud'e kulolin da kwanikan, a rai na ina tunanin ina zamu kai wanna abincin haka?.

Tashi nayi zuwa ga show glass d'in dake falon, wadda aka jera mugs and glass cups, mug d'aya na d'akko, naje wajen wanke hannu dake a wajen dinning, Wanda babu tebirin cin abincin ba'a sakaba, bansan dalinsa nak'in sakawarba, wanko mug d'in nayi na had'o kayan tea a ciki dake a wajen show glass d'in suma, na zubo ruwan zafi daga dispenser na dawo, yana kwance yanda na barsa, yanzuma garda su lumshe idanu yanata shafa kan yaron zuwa bayansa.

Na kallesa a d'arare Dan yaune karan farko dazan aikata hakan, komi yake buk'ata yakan yi da kansa, ko ruwa wannan inhar bana manta ba bai ta6a cewa na d'auka masaba, sometimes ma sai idan yasaka Samha ko Sauban su masa Abu saini na tashi nayi idan naga rashin dacewar hakan, amma dai dakansa yace Munaya yimin kaza, gaskiya bai ta6aba. muryata na rawa nace,  bismillah .

Shiru kamar bazai bud'e idonsa ba saikuma ya bud'e d'aya yad'an kalleni ya kauda kansa. cikin k'asaitar nan tasa yace,  miyasa? .

 miyasa kuma? .  nakuma maimaita maganar ina k'ok'arin janye hannuna .

Carab ya rik'e hannun nawa, ni tsoroma ya bani, na kalli hannunsa da nawan ga mug cikeda ruwan zafi yanata turiri, kuma zafin yana ta6amin gwiwar yatsuna, idonsa a lumshe har yanzu, idona harya fara tara kwalla, nayi alk'awarin koda hannun zai toye gaba d'aya bazan tanka masaba, ai yasan abinda yake dai-dai da akasin haka.

Saida mukayi 1minute a haka kafin ya maido face d'insa inda nake yana kallona, ya d'age gira d'aya yana fad'in  da zafi ne? .

Humm lallai Galadima akwai rainin wayo, na fad'a a zuciyata, janye idona nayi daga kansa na maida kan Abdurraheem dahar yanzu yake kwance a bisa cikinsa.

Ya yamutse fuska yana sakin hannun, cikin basarwa yace,  inason jarumta .

Had'iye kukan dake k'ok'arin tahomin nayi, na ajiye Mug d'in na cigaba da zuba masa farfesu a k'aramin bowl batareda nayi koda tariba.

Tashi yay zaune yana jije lips, yayinda hannunsa ke rik'e da yaron, d'ayan kuma ya dafe saitin zuciyarsa, a wahalce yake fisgo numfashi kafin ya fesoshi, tun kuma d'azu na lura da hakan, kalmar zafi daya fad'amin na shiga fassarawa, har na fahimci da manufa ya fad'a, hakanne ya Sani murmusawa batareda na d'agoba ina zuba masa farfesun nace,  tabbas duk zafi sunansa zafi, amma akan samu banbance-banbance wajen banbancesu, wani zafin a gangar jiki muke jinsa, wani ko tawani sashen jikin ake samunsa, wani zuciya, wani rayuwarma gaba d'aya Ce ke tsintar kan a zafi, saidai babu zafi mafi rad'ad'i daya kai na Mutuwa, idan da zamuyi nazari zamu fahimci rayuwa tana a tsare ne mataki-mataki, sannan iri d'ayace ga kowanne launin halitta na mutum ko aljan ko dabba, Dan mukan tainci kanmune akusan mizani d'aya, dukda ubangiji ya banbantamu ta halitta da ayyuka da tunani ko nace kaifin basira, ko'a jinsi launi biyune, akwai namiji akwai mace, dukkan rayuwa takan farane da mafari yalla6ai na d'ago ina sake mik'a masa mug d'in tea d'in again, a mamakina a yanzu saiya kar6a, na lashi lips d'ina na k'asa ina gyara zama sosai da maida hankalina wajen juya kunun dana zuba a cup da tsokali, cikin nisawa nacigaba da fad'in,  mafarin rayuwa shine dasuwar bawa a cikin mahaifiya, mukanyi wannan rayuwarne a cikin halin su wanene mu? daga nan sai matakin haihuwa, shigowa duniya a bisa bigiren wane ahali muka kasance, dukkan ahalin daka Sani sunada matsalarsu, saidai tawasu tafi tawasu zafi, daga ranka ka iso filin gwagwarmaya wato duniya, shikenan littafinka dayazama rubutacce tun a cikin mahaifiya saiya fara aiki, mala'iku masu kula da fitar numfashi su dasa alk'alaminsu, masu kula da abinci suma haka, masu kula da ruwa ma haka, masu kula da magana ma haka, masu kula da kallo ma haka, masu kula da ji ma haka, masu kula da duk wani motsinka ma haka, tafiya, zama, kwanciya dadai sauransu, kowa ana haihuwarsa tsaftatatccene, iyaye suke fara juya akalar rayuwa, walau mai k'yau ko sa6aninta, (kaga kenan akwai hisabi tsakanin iyaye da y'ay'a ma kenan?) daga nan rayuwa zata cigaba da yad'o kamar d'an duma, tun ana maka, harka koma koya, harka fara iyawa da kanka, harma ka kware ka koyama wani, (wanne ka iya? ko ka koya? yarage ruwanka) duk Wanda kaga an masa a farko to tabbas za'a k'ara masa a k'arshe, kodai silar tsufa, ko ciwo, kokuma iftila'in rayuwa, kokuma na k'arshe shine hidimar gawarka, a dukkanin dunk'ulalliyar rayuwar da kowanne bawa yakanyi zakaga cike take da k'alubale masu zuwa da zafi kala-kala, yalla6ai kasan mike taushe wannan rad'ad'in zafin kuwa? . nayi maganar ina d'ago ido na kallesa. A mamakina sainaga ya girgiza min kansa. na murmusa ina janye idona daga kansa na maida ga kofin tea d'in ina masa alamar yasha mana.

Yamutse fuska yay irin kalar tausayinnan.

Nima sainayi kwal-kwal da ido kamar zanyi kuka, na had'e hannayena waje d'aya alamar rok'o=�O�<���..

Lips d'insa yad'an ciza kafin yafara shan tea d'in. Nayi salute nashi ina masa jinjina=�M�<���.

Basarwa yayi, nima saina kad'a ido ina tunzura baki gaba, sannan nacigaba da fad'in,  Abinda ke taushe wannan rad'ad'in zafin shine *_HAK'URI_*. hak'uri muhimmun sinadarine dake jagorantar garkuwar jiki ta kowacce launin halittar jiki na d'an Adam, walau a fili take ko a 6oye take, saidai babban makarinsa da taskar adanashi shine *_ZUCIYA!_* a duk lokacinda k'arfin zuciya ya raunana to zaka samu madarar hak'uri ta salwanta, idan zafi yanata yawa babu wannan hak'urin bugu d'aya take duk wani ma'adani na cikinta saiya tarwatse, saikaga an rasa ayyukan jiki dana ruhi, shikenan wane yazama labari. daga lokacin da rad'ad'in fitar rai ya kusanci bawa dukkan mala'ikunan da suka kasance tare dakai a randa kazo duniya saisu fara janyewa daga gareka, wani bawan kafin ranar mutuwarsa zakaga ya daina cin abinci, hakan na nufin mala'ikan dake kula da abinci ka yagama aikinsa, domin ya zagaye duniya kaf duk yawan abincin dake cikin ta babu rabonka koda kwayan gero ne, ka gama cinyewa, wani kafin ranar Mutuwa ya daina shan ruwa, aikin mala'ikan dake kula da ruwa shanka yagama k'arewa kenan, duk yawan koramu da tafkuna na duniya bakada sauran rabo na ruwa, ka shanye naka, wani kafin Mutuwa ya daina magana, mala'ikan dake kula da furucinka yagama aikinsa, babu sauran wata kalma data rage harshenka ya furta, wani kafin Mutuwa ya daina ji, mala'ikan dake kula da jinsa ya gama aikinsa, babu wata kalma data rage kunnensa zaiji, wani kafin Mutuwa ya daina gani, mala'ikan dake kula da ganinsa ya gama aikinsa, kwayar idonsa bazata sake kallon wani abuba, wani kafin Mutuwa ya daina tafiya, mala'ikan dake kula da tafiyarsa ya gama aikinsa, haka-haka wad'annan mala'ikun zasuyita ja baya suma barinka, har yarage sai mai kula da fitar numfashi kawai, daga ranar da UBANGIJI yace yana buk'atar ganinka shikenan takuma k'are, sai rundinar mala'iku su had'u su takewa kwamandan mala'ikan d'aukar rai baya, idan kai mutumin kirkine fararen mala'ikune, idan na banzane mala'iku masu azaba zasu take masa baya, sauran al'amari kuma sai Wanda ya haliccemu yasan ya zata kasance=�-�. zakasha mamaki idanfa nace maka duk wannan zafin k'aramin zafine acikin kashi-kashin na abinda ya shafi haluttu, shi wannan zafin ana kiransa zafin na za6in kai, kokuma zafi na a haka tsarin yazo, ma'ana kaine ka had'ama kanka wannan zafin, kokuma wanine ya had'a makashi. Abu na biyu shine zafi na rad'ad'in Mutuwa, dolene kowa saiya d'an d'anashi, walau kafiri ko Musulmi, saidai akwai banbance-banbance na awanne tsari ka koma ga ALLAH, ba wannan zafinne kawai ke jiran d'an Adam ba, akwai zafin na *_BARZAHU_* shi ake kira kwanciyar kabari, mika tanada, mi zaka tarar shine abin tambayar, wannan kam ALLAH ne mafi sanin wad'anda zasu d'and'ana wannan zafin (ALLAH ka datar damu=�-�) .

Akan la66a Galadima ya amsa da amin, Munaya ta share hawayenta, ta cigaba da fad'in sai zafi mai gaba d'aya, shine na makoma, *_WUTA KO ALJANNA_*, yalla6ai wad'annan jimullar zafin ga d'an Adam tilas ne, na cikin rayuwa shine zafin da zaka iya controlling nashi ta hanyar hak'uri, to Ashe bai kamata ka tasirantar da wannan zafin ya cigaba da k'onaka ba, musamman idan zakayi dubi dawasu ni'imomin da ALLAH yamaka a cikin wannan zafin, ka kasance mai yawan hak'uri saikaga kanka cikin masu yawan riba, wlhy ta wannan hanyarne kawai zaka zama mai *_NASARA_* akan mak'iya ni.......... .

Maganata ta katse saboda knocking d'in k'ofar da akayi, kallon juna mukayi ni da shi, yay wani luuu da idanunsa ya lumshesu, hakanne ya sakani bada izinin shigowa kawai batare da na jira amsa daga garesa ba.

Sarkin k'ofane ya shigo, ya zube yana gaishe mu, nice kawai na amsa, boss kam hannu kawai ya iya d'aga masa, yay mana ya jiki again, nanma nice nakuma amsa shi, cikeda girmamawa yace,  ranki ya dad'e yalla6ai harun ne ke buk'atar iso .

Saida gabana ya fad'i, na had'iye wani yawu mai kauri ina kallon galadima dayay biris damu yanata shafa kan d'ansa, bud'e idonsa jajaye yayi akan Sarkin k'ofa, ya jinjina masa kai alamar ya shigo dashi.

Kallonsa nayi tamkar zanyi magana saikuma nai shiru, a raina ina mamakin wannan munafukin dami yazo kuma?..... ban kai k'arshen zancen zucin ba Harun yay sallama, nid'ince dai na amsa cikin danne zuciya da fushina.

Ya zauna fuskarsa d'auke da murmushi.

Nima saina saki tawa ina fad'in,  barka da hantsi ranka ya dad'e .

 Barka dai gimbiyarmu, ya jikin ki dana yalla6ai? .

Na kalli Galadima dayay shiru kansan jingine da kujera ido a rufe,  da sauk'i , na fad'a ina mik'ewa na koma saman kujera, dan bazan ta6a barin falonba sainaji uwarmi ya kawosa.

Ya amsa da  masha ALLAH, ALLAH ya kiyaye gaba ya k'ara lafiya .

 humm na fad'a ina amsawa da  Amin dai .



Hankalinsa ya maida ga Galadima,  Sameer ya jikin? .

Bud'e idonsa yayi shima, ya ajiye mug d'in hannunsa a teble d'in dake gefen damarsa, batare da yace uffanba ya sauke ajiyar zuciya yana taunar lips.

Banga alamar damuwar rashin amsawar tasaba a fuskar Harun, dan yariga ya saba da halinsa.

Saidai idonsa k'uri akan Abdurraheem dake cinyar Galadima d'in yana barci, mik'ewa yay yana fad'in,  my son zo mu gaisa ko? .

Ganin haka nima nayi azamar mik'ewa nakai ga Galadima kafin shi ya isa, na d'auke Abdurraheem d'in ina fad'in  ai barcima yake ranka ya dad'e .

Ba Harun ba hatta da Galadima saida yaymin kallon mamaki, nakoyi cid'in-cid'in da fuska yandama bazaice nabama Harun d'inba.

Baki ya bud'e kamar zaice wani Abu saikuma yay shiru yana kauda kansa daga kallona, nima saina ta6e baki ina barin falon da harar Harun ta gefen ido.



Gaban Harun ya fad'i, mi yarinyarnan take nufi?......

Kafin ya lalubo amsar ya tsinkayi maganar galadima yana cewa,  sorry Harun, kasan har yanzu a tsorace take, duk wani motsinsu akan idontane .

Murmushin basarwa harun yayi, yace,  ai dolene hakan ranka ya dad'e, abinne akwai tsoratarwa, wlhy jiya tashin hankalinnan ne yasaka azababben ciwon kai rufeni, shiyyasa ko ganina ba'ayiba, yanzu police d'in ina suka samosu? .

 humm Galadima ya fad'a cikin tsananin taune lips da k'unar zuciya, ya bud'e baki a hankali zaiyi magana nida ke bayansu basu saniba nai saurin tareshi da fad'in  a hannun wasu munafukaine ranka ya dad'e, ai koni daza'a bani baiwar nan da aka kama da yaran wlhy saina tsoma kanta cikin drum d'in ruwa harsaita daina Numfashi zan barta, kafin sannan kuma nagamajin labarin Wanda ya sakata, amma shi my boss ai a station suka zauna har aka kawo yaran, badasu akaje farautarba .

Tsuramin ido Galadima yayi cikin tsagwaron mamaki, miyasa to zanzo na kasa na tsare dukkan wani motsin Harun d'in? ya kula satar yaran tana Neman ta6a tunaninta takasa banbance Wanda zata zarga, ai Harun yawuce ya 6oye masa wani sirri na sashen rayuwarsa, tun da babu abinda bai saniba na baya, saidai abinda ba'a rasaba kam, danne ransa yayi ya nuna hakane, yabari har Harun d'in ya tafi sannan yaji dalilinta.

Ina kallon Sassanyar ajiyar zuciya da Harun ya sauke a 6oye, sannan yace,  ai police d'in sun cancanci Babar k'yauta, shiyyasama na shirya musu ita, sunyi aiki irinnan jaruman masu tsaro .

 hakane wlhy ranka ya dad'e  . Na fad'a cikin murmushi.

Dukfa yanda Harun yaso bugar cikin Galadima yaji yanda abun yake, na kafa na tsare, dayayi tambaya nike bashi amsa, saiya d'auka kodan Galadima bashida lafiyarne shiyyasa bai iya amsawa, tun da tunda ya shigo baice k'ala ba, kuma yasan yanayin ciwonsa, a baya ma shikan bashi taimako, baidai tsinci komai ba yay mana sallama ya fita, da k'udirin anjima ma zai dawo ne.

A sace na raka bayansa da harara, sannan na kalli Galadima na basar, dukda kallon tuhuma dayake jifana dashi kuwa.

Wani farfesun na sake zuba masa na mik'a masa.

Batare da ya kar6aba cikin k'ank'ance idon bala'i yace,  mikikayi haka? kinsan waye Harun a wajena? .

Kaina na girgiza masa.

Yaja tagwayen tsaki yana hararata,  halan satar yaranki yafara shafar tunaninki ne? kina tunanin akwai abinda Harun zai iya gazaji daga sirrina? .

Na d'an ta6e baki ina jawo teble d'in gabansa, na d'ora bowl d'in dana zuba farfesun, baki ya bud'e kamar zaiyi magana saikuma yay shiru. nima bance uffanba na ajiye masa sannan na koma k'asa Na zauna na zuba sabon kunu nahau sha.

Kwafa yayi, yace, kinma maidani d'an iska ko? .

 Hummm na fad'a kawai, naimasa kallo d'aya  yalla6ai wani karatun akan barsane a yanda yazo, sai idan lokacin fasaarashi yayi amasa fashin bak'i, nasan darajar alak'ata dakai batakai koda rabin tsakaninka da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login