Showing 354001 words to 357000 words out of 365757 words

Chapter 119 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1456

Duk suka amsa da amin suna binsa da tafi.



Daganan sauran jama'a sukaita bayani d'ai-d'ai, taro dai bai tashiba sai kusan 3:00pm.

Cikin farin ciki Galadima ya shigomin, ko kunyar su Ahmad dake zaune da Sarkin mota ya shigo dasu bai jiba ya rungumeni, saida na ankarar dashi sanann ya sakeni yana susar gefen wuya alamar yaji kunya, yayi farin ciki da ganinsu kuwa, yaran sun shiga ransa sosai, duk da abinda yayma mahaifansu basu tsanesa ba, saima zuminci mai k'arfi daya k'ullu a tsakaninsu.

Ranar sashenmu saiya koma na matasan samarin masarautar, Dan shima Sauban nan ya kawo gayyarsa cin abinci, gasu Yassar kuma, itama Samha saiga tata gayyar, saikuma ga matasan gidanmu da y'ammata da banyi zaton ganiba, harda Zarah da Siyama, dad'i tamkar xai karni kuwa.

duk yanda Galadima yaso ke6ewa da matarsa abin ya gagara, dansu Matawalle da Nuren da suka iso dawasu samarin masarautar suma duknan suka nufo, tsakaninsa da Munaya sai dai y'ar satar kallo, dan kwalliyarta tagama narkashi.

Baniba kosu Amaturrahman sunji a jikinsa raranar, d'auka dai sun shata harsun gode ALLAH, bankuma samu damar shayar dasuba sai madara suka sha. Har dare babu wata damar samun ke6ancewa da juna.

Washe gari kuma aka gudanar da hawan salla mai k'ayatarwa, wanda a tarihin masarautar gagara badau an dad'e ba ayi irinsa ba, saboda manyan sarakuna na garuruwa daban-dabanne da Governors harda uban gayya president da senators da sukazoma Abie barka da dawowa suka halarci bikin hawan sallar.

Misalta muku k'yawun kwalliyar jarumin naku Galadima ai 6ata lokacine, ammafa komai zamm, y'ammata da yawa sun k'yasa, balle yau fuskarsa washe take da murmushi na musamman Wanda jama'a basu ta6a ganiba.

Su Abbana ma sunzo gaida Abie, sun sami k'yak'yk'yawar karramawa mai ban mamaki, wadda tasani farin ciki mai tsanani dajin k'arin k'aunar Ahalin Galadima.



**



Saida shagalin bikin salla ya lafa nasamu zuwa gidanmu da zagaya dangi, kowa yayi farin cikin ganina, musamman ma Munubiya da Innarmu, su Aiyaan da sauran jama'ar gidanmu, jikin Innaro yayi tsanani, dan harma ana shirin kaita asibiti, ciwon k'afa ya takura mata ainun.



Sati biyu dagama bikin salla tawagar masarautar su Momma sukazo daga Niger, a masarautar gagara badau suka sauka, kasancewar harda uban gayya Sarki.

Wani k'warya-k'waryar biki zuwan nasu yazama a masarautar, tareda k'ulla alak'a mai matuk'ar k'arfi wadda ada babu ita, da safe Matan suka koma gidanmu akabar Sarki da jiga-jigansa anan.

A wannan zuwane aka nemi auren Ayusher, saima Abbansu ya tak'aita musu wahala akan a d'aura auren kawai baki d'aya kowa ya huta.

Kowa yayi murna da hakan k'wai da gaske..............
'<���













ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���









BOOK 3 =�I�<���3� 1�





.................Randa sukaje gidanmu ai munsha kallo da mamaki, yau ga babban Sarki har cikin gida, dan Sarki cewa yay saiya taka har d'akunan y'an uwansa, hakan yayma Innarmu dad'i, koba komai jama'ar gidanmu zasu kuma ganin martabarta.

Aiko sun gani, dan ko rantsuwa nayi babu kaffara wasu saisunyi kukan fili bama na zuciya kawaiba. Ranar anguwarmu cika tayi mak'il da jama'a.



A wannan zuwane Innarmu ta fara taka nawa d'akin itama, dan tana zuwa gaida ahalinta masarauta saboda anan aka saukesu, dan haka Galadima yake sakawa a d'akkota duk bayan kwana 2 susha hirar zuminci, duk da Sarkine dawasu manyan y'an rakiyarsa ne kawai a masarautar, sauran mata dasu Badeerah duk suna gidanmu, wasu kuma gidansu Ayusher. Kwanansu goma ciff aka d'aura auren Yarima Issifu da amaryarsa Ayusher, wannan aure yasaka kowa farin ciki da annashuwa, anyi biki na kwanaki biyu anan muka shilla Niger kaita, a can kuma aka d'auro auren Badeerah da Yaa Fadeel, kwanakinmu Biyar anashan shagali maiban mamaki da birgewa, muka d'akko amaryar Yaa Fadeel muka dawo gida.



Koda muka dawo babu zama, dan kuwa hidimar bikin aunty salama muka shiga, Wanda yanemi had'ewa Dana Muftahu da Matawalle, zakusha mamaki idan nace Muku Samha Ce matar Muftahu=��, wannan had'i ALLAH yayishine bisa umarnin Momma, kowa kuma ya kar6a da hannu biyu yay addu'a, koda Samha taso bijirewa bisa ga soyayyar Gopal nice naita tausarta da mata nasiha harta kwantar da hankalinta.

Munsha shagali kam iya shagali, babu abinda zamucema ALLAH sai godiya dakuma bin amare da angwaye da addu'a.

Aiko wad'annan bukukuwa sai suka tada tsumin Nuren shima, yace aure shima yakeso, kai tsaye kuma ya kawo Farhat d'iyar Minister a matsayin za6insa, su Papi basuk'iba, domin nagartar mahaifiyar yarinyar ya cancanci a aureta, hakan kuwa akayi, shima aka sanya bikinsa kusa, mukasha biki kuwa cikeda nishad'i da farin ciki.





*****



Bayan kammala wad'annan bukukuwa mukajema Aunty Salamah gaisuwa, da tayata murna ta musamman ni da Munubiya, tarba tamana mai k'yau da mutuntawa, a hirar da muka gudanar nake mata tambaya gameda mitasani ga Galadima?, dan naga yaranta sun kasance yaransa na wajen aiki.

Murmushi tayi tana sakama Meenal pampas,  Babu wata alak'a tsakaninmu, Ameer k'aninane uwa d'aya uba d'aya, sanan mu y'ay'ane ga Baba Rabilu da zakiji yana fad'a, har akayi aurenki da Galadima bansan akwai alak'a tsakanin Mahaifina da shiba, duk da nasan kad'an daga cikin labarin mahaifina, sai a dalilin satar Muftahu da mukayi, ta wannan hanyarne kuma mahaifina baba Rabilu yasamu ganawa da Galadima ma, akuma wannan lokacinne duk muka San komai gameda abinda yafaru, ashema yanakan Sani ya saka Ameer aikin C.I.D, bisa tsatstsauran bincike daya dad'a yanayine ya gano Galadima yanama hukumar DSS aiki, shiyyasa yatura Ameer ga hukumar dan neman kusanci dashi, wannan shine kawai abinda na sani .

Daga ni har Munubiya munsha mamaki da girmama hukumar Ubangiji, dan shine ya sanya alak'a tsakaninmu da aunty salamah batareda sanin junaba ko wani dalili, ni dai ALLAH yariga ya k'addara nice dama matar Galadima, shiyyasa ya kulla bisaga hikimarsa wadda wasu wawaye suka kalla a matsayin nasararsu.



Satinmu biyu da zuwa gidan aunty salamah mukaje India ni da Galadima, halattar bikin Akash da Doctor Erfan Fahad, abin mamaki da al'ajab saiga Radha a matsayin matar Akash, matan Dana ta6a had'uwa dasu a shagon kayan yara na Galadima, lokacim inada cikinsu Abdurrahman, masu yara Vishnu, Ashe ita k'anwar Maman Vishnu d'ince. Aiko muka rungume juna cikin tsantsar farin ciki da annashuwa, ashema munsan juna, vishnu ya k'ara girma abinsa, sai dai bai ganeniba ma=�
�.

Ana gama bikin Akash muka nufi Kashmir bikin Dr Erfan Fahad da tashi amaryar shima, nanma mun rakwashe mun kwalla kamar babu gobe. Daga nan muka dawo India muka baje kolin soyayya, duk da ni yanzuma banajin dad'in gidan babu su Momma, sainaita k'iyasta rayuwar damukayi aciki a baya, wani nayi kuka wani dariya, Ashe 6angaren Galadima ma hakance yafaru, rayuwa kenan tsarin ubangiji.

Mune har k'auyen su Khumar, shima kuku munje nasu gida.

Saida muka kwashe kusan watanni biyu a wannan zuwa sannan muka dawo bisa samun labarin rikicewar jikin innaro.

A lokacin su Amaturrahman suna rarrafensu ko ina, harma sukan gwada mik'ewa tsaye, dan suna wata na 10 ne, danma tafiyar kamar tamusu nauyine.

Isowar dare mukayi, dan haka washe gari tunda safe muka nufi asibitin da aka kwantar na innaro.

Hankalina yatashi ganin yanda Innaro ta koma, dukta tsotse takuma tsufa. Na zauna bakin gadon ina kama hannunta da share hawaye, dukkan ahalin gidanmu mazata da mata na ma'auri suna asibitin.

Innaro ta kalleni tana murmushi k'arfin hali, da ido taima Innarmu magana akan tazo kusa da ita.

Innarmu ta share hawayen idonta ta k'araso gaban gadon ta durk'usa, hannuna innaro ta saki ta kama na Innarmu.

Ahankali ta fara fad'in,  Ai'sha ki gafarceni, nasan na aikata miki kurakurai da zalunci iri-iri, na manta da duniya bakomai bace a wajen Bawa balle kayan cikinta, idan babu mutuwa akwai tsufa, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, duk yanda ka d'auki kanka hakan kake kasancewa, ko a auren yaranan da y'ay'an alhaji halluru na zalunceki, amma nayi nadama tun a auren su da mazajensu na yanzu, y'an biyu dan ALLAH Ku yafemin kuma, amatsayinku na jikokina ban muku adalciba, son zuciyane kawai da rashin hangen nesa, yafiyarku itace babban gatana, ina kuma rok'onku kumin Afuwa domin ALLAH .

Atare ni da Munubiya da Innarmu muka had'a baki wajen fad'in, duk mun yafe miki Innaro, ALLAH ya yafe mana baki d'aya, kin Isa damune ai, kuma Bawa baya zartama k'addararsa da bitar rubutaccen littafinsa tundaga cikin uwa. ALLAH ya baki lafiya dai.

Innaro tayi murmushi mai ciwo tana hawaye, ta juya ga y'ay'anta su Abbanmu da gwaggo Safiyya suma tana Neman gafararsu. Suma duk d'urk'ushewa sukai a k'asa suna Neman tata gafarar, matan gidanmu duksai jikinsu yay sanyi, suma suka durk'usa suna Neman gafararta, ta rok'esu akan suma su canja Dan ALLAH.

Cikin awannin dabasu gaza biyuba mai afkuwa ta afku, dan kuwa ALLAHn daya bamu Innaro yau ya d'auke abarsa, ta koma garesa tafiya mai nisan zango, saiga su baba k'arami na kuka da idanunsu, mahaifiya dabance, komai mugun halin mutum idan giji tazo dolene ka saduda dajin k'aunarsa ta musamman, kuka kam mun cisa tamkar babu gobe, yau gidanmu saiyay tsitt.



Gwaggo Safiyya ta mata wanka a d'akinta, aka sallaceta a k'ofar gida da raka gawarta gidanta na gaskiya, hardasu Galadima kuwa, Wanda shima saida ya share hawaye, halayyar tsohuwar kan sakashi nishad'i haka kawai, danshi bayajin haushin masifarta, saima birgeshi da takeyi, musamman idan ta kafe akan Abu, bayan tasan gaskiyane amma tace sam ita ba hakaba.

Ranar a gida muka kwana harsu Fauziyya, washe gari aka cigaba da kar6ar gaisuwa, a kwana na biyu saiga dangin su Innarmu daga Niger, harda Ayusher dake fama da tsohon ciki.

Ranar addu'ar uku saiga su Abie da mai martaba sunzo gaisuwa suma, dasu akayi addu'ar uku ma.

Aranar duk muka koma gidajenmu cikeda kewar innaro.





***



Ranar addu'ar bakwai d'in Innaro muka samu shiga wajen baba mai kanwa ni da Galadima.

Mun iskeshi shima dai lafiyar sai a hankali, dan yanzu ko fitama bayayi, muka gaidashi cikeda girmamawa, ya amsa mana da fara'a, harda tsokanarmu da cewar,  Sai yau nake ganin ango da amarya? .

Duk murmushi mukayi cikin jin kunya.

Shima ya kuma murmusawa da fad'in,  Mi kukeson Sani y'ay'ana? .

Nace,  Baba mai kanwa abinda ALLAH ya baka ikon Sani game damu .

d'an Murmusawa yakumayi yana gyara zaman hularsa, ya nisa cikin sauke numfashi. Yace,  Da farko dai niba maye bane, bakuma muguba kamar yanda wasu sukasha fad'a tun ina yaro, saidai ina tare da wasu aljanu da bansan ta Yaya suka kasance daniba tun k'uruciya. Tun farkon zuwan kakanninki gidan Malam fharuku aljanun dake tare dani suka sanarmin da dukkan asalinsu, harkuma suka rasu da matsalolin da mahaifiyarku taita fuskanta ga marigayiyya, abinda yasa na barsu ban ta6a maganarba saboda komawarsu a wancan lokacin bashida amfani, ina tausayinsu kuma k'warai da gaske, aljanuna sunsha d'aukata su kaini har cikin masarautar su Ai'sha, kullum cikin bibiyar musu ko ansamu canji nake, amma ba'a daceba har ta samu haihuwarku. Abinda yasa lamarin Galadima ya shigo rayuwaki a labarin shine, Maharbi daya taimaki Badi a jeji ranarda ya bama Auwalu babanki abin d'aukar hoto ne. Ba mutum bane wancan maharbi, aljanine yazo masa a suffar mutane, kuma har Badi yabar wajensa shima bai saniba, wannan aljani shine ya ta6a taimakonka a India lokacinda ciwonka ya tashi ka fad'i a titi, shine kuma ya kwad'aita maka wasu zantuka akan matar dazaka aura, a lokacin shekarun su Hussaina 12 kacal a duniya=�
�, badan yasan itace matar takaba ya fad'a, saidan maka fatan hakan, dan yata6a sanarmin akwai al'amari mai k'arfi dake tattare da y'an biyun Ai'sha, kuma bisa dalilin abinda akabama Auwal abin yake, sai dai shima baisan mineneba, saidai mujura hukuncin ALLAH. tun daga wannan lokacin wannan aljani ya baza y'an uwansa aljanu suna kula da dukkan motsinka Muhammad Sameer, suma su Hussaina haka itada y'ar uwarta har suka kai adadin shekarun girma. Yafara zuwama Hassana a mafarki, amma saiya fahimci batada k'arfin zuciyar da zata iya shan gwagwarmayar rayuwa dakai, hakanne ya sakashi komawa kan Hussaina, amma ita sai aka dace, wannan shine mafarkin da kuka dingayi keda y'ar uwarki Hussaina, nikuma na cigaba da d'oraki mataki-mataki akan kar6ar Muhammad a matsayin miji, Haidar da kike gani yazo har aka saka ranar aurenku ba mutum baneba, aljanine dagashi har iyayensa da sukazo neman aurenki .

Ba k'aramar zabura nayiba, hartaso bama Galadima da baba mai kanwa dariya.

 Kinga kwantar da hankalinki, ai ko driver dayay masu Muhammad aiki akan satoki ba mutum bane ba, k'arfin jini da ALLAH yabaki kikaso fahimtar hakan kuma, daga ke har Muhammad kunsha mu'amulla da aljanu a matsayin mutane ai har lokacin da ALLAH ya k'ulla igiyar aurenku, aiko cikar taron d'aurin aurenku akwai d'unbin aljannu da suka Halarta a ciki, dukkan bayanan danai muku yanzu zan baku tabbaci, wani turaren tsinke ya d'aga lamusashshiyar katifarsa ya zaro, ya k'yarsa ashana ya kunna, dandanan hayak'i da k'amshi ya gaurasye d'akin, saiga sallama munji a k'ofar d'aki.

Matashin saurayi ya shigo, Wanda Munaya bazata ta6a mance fuskarsaba, wato Haidar, hakane ya sakata zabura ta mak'alk'ale Galadima.

Haidar yay murmushi kawai yasamu waje ya zauna, saiga kuma dattijo da Galadima yata6a had'uwa dashi a India, shima dai da kallon k'urilla ya bishi, basu fita a mamakiba saiga Driver daya ta6a d'akko Munaya lokacin dayace suyi auren Contract shima ya shigo, saikuma mabanbanta fuskoki Wanda sun had'u dasu a mabanbanta gurare, harda masu zuwama Munaya a k'awaye, saida duk suka zauna suka nutsu sannan suka gaisa da baba mai kanwa, Galadima ma dai a d'arare ya yarda yabasu hannu sukayi musabaha, nikam uwar y'an tsoro ai ina mak'ure a bayansa, ALLAH ma yasoni banzo dasu Abdurraheem ba, suna gidanmu.

Baba mai kanwa ya nuna manasu yana fad'in,  Ina fata duk kun ganesu? .

Duk muka amsa da eh a d'arare.

Dattijon daya had'u da Galadima a India ne yafara magana a nutse,  Muhammad Sameer ya bayan rabuwa da gwagwarmayar rayuwa? .

Galadima ya amsa da  Alhmdllh .

Tsoho mai sihirtaccen k'yawu zam jinin indiawa yace,  ka tuna na fad'a maka matarka Ce fitilarka? zuwa yanzu ka tabbatar? .

Galadima ya gyara zama yana Murmushi har hak'waransa na bayyana, yace,  Lallai ban mantaba kaka, saidaima nabama wasu labarin, nakuma mik'a godiya ta musamman agareku da fatan ALLAH ya had'amu daku a aljanna, ya kuma biyaku da mafificin alkairi bisaga taimako na mussaman da kuka bama rauwarmu ni da matata, duk da kasancewarmu ba jinsi d'ayaba .

Gaba d'aya suka amsa da amin, haidar ya nema izinin Galadima domin Neman afuwar Munaya. Galadima ya bashi izini.

Haidar yace,  ki gafarceni bisa ga kalmomi masu zafi dana fad'a a gareki a wancan lokacin, hakan ta farune bisa k'ok'arin janyo hankalin mijinki domin jin tausayinki, kasancewarsa mutum mai tausayi da gudun shigar wani matsala ta dalilinsa .

Munaya ta murmusa tana kallonsu. Tace,  na yafe maka wlhy, kuma komai yawuce, fatana ALLAH ya tabbatar da addu'ar mijina a garemu baki d'aya .

A tare aka amsa da amin. Mun dad'e muna tattauna abubuwa da dama, kafin daga bisani sumana sallama su tafi, Wanda bai saniba saiya d'auka da gaske mutanene, baba mai kanwa yay mana doguwar nasiha mai ratsa jiki, wadda harta d'arsa tsoro a ranmu, yakuma ja mana doguwar addu'ar. Galadima ya ajiye masa alkairi mai tsoka mukayi masa sallama muka fito, bamu dad'e a gidanmuba muka koma gida jikinmu a sanyaye da abubuwan da suka faru tsakaninmu da baba mai kanwa da su Haidar.



Kwanaki uku da faruwar haka labarin rasuwar baba mai kanwa ta riskemu, mutuwarnan itama ta girgizamu k'warai da gaske, munkuma jema iyalansa gaisu.

Manyan dake kula da matsalolin gidanmu duk Ubangiji ya d'aukesu, yau babu Innaro babu baba mai kanwa.

Zuwa yanzu kam ko ina su Amaturrahman zuwa sukeyi, sunyi wayo sosai da girma, hakama yaran Munubiya danasu Safara'u datai hak'uri takoma gidan mijinta suke zaune lafiya da kishiyarta da haihuwa yau ko gobe.

Ayusher ta haihu namiji, dan haka muka d'unguma Niger suna k'wanmu da kwarkwata, hardama y'an gidanmu Wanda wanannne zuwansu na farko, sunkuma gano abinda yafi k'arfin shirmensu kuwa, yayinda girman Innarmu yakuma yawaita a zukatansu.

Mun dawo da kwana hud'u Aunty Salamah da Badeerah matar Yaa Fadeel suka sauke, babu nisa tsakaninsu Farhat d'in Nurenma ta juye, Saiga Samha ma ta haife yaranta y'an biyu duk mata, hakama matar Matawalle. Kai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login