Showing 96001 words to 99000 words out of 365757 words

Chapter 33 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1501

na tashi zaune na gaidata cikin girmamawa.

Ita kuma ta amsa cikeda fara'a.

Kallon Galadima tayi dayake tsaye yana kallonmu,  ranka ya dad'a kozaka bamu wajene .

Murmushi yad'anyi yana fad'in babu damuwa.

Yana fita matar ta zauna kusa dani a bakin gadon, fuskarta d'auke da murmushi tace,  sunana doctor Hafsat Abu, friend d'in Galadima ce tun a primary school .

Murmushi nayi mata na yak'e kawai.

Takuma gyara zamanta tana kallona, please dear karkiji nauyina, ki fad'amin matsalarki kai tsaye, dan ba'a wasa da wannan matsalar, takan zama babban Abu anan gaba ga d'iya mace .

Kai na jinjina mata ina hawaye, sannan nace  inajin zafin wajen sosai .

 ok kozaki iya kwanciya nagani .

Ido na waro waje a tsorace, sai kuma nayi k'asa da kaina saboda kunya.

Tayi murmushi tana kama hannuna,  karkiji kunya akan lafiyarki dear, please ki daure kinji .

Kai kawai na gyad'a mata sannan na kwanta, babu yanda zanyi dole na yarda ta duba, kanta kawai ta girgiza da mamakin Galadima, saikace Wanda ya kusanceni da k'arfin tuwo?, ai wannan kam da wani doctor d'inne saiya yima Galadima fad'ama wlhy, dan ko kad'an bai bini a hankaliba, amma ciwon daya jimin bazai zama mai cutarwa ba insha ALLAH.

da kanta yanzu ta had'amin ruwan zafi tazuba wasu magani, sannan ta taimakamin har zuwa bayin ta nunamin yanda zanyi. ban cutar da kainaba na nutsu nayi komai yanda tace, dukda inajin zafi kuwa, bayan nafito saina sameta zaune ta gyara gadon tsaf, gakuma abinci a ajiye, da alama Galadima ne ya kawo, tsareni tayi da lallashi naci abincin ma yanzun, sannan tabani magunguna nasha, ta kalleni da murmushi,  ALLAH yak'ara lafiya gimbiyarmu, indai zaki cigaba da kulawa kamar yanda na nuna miki insha ALLAH nan da 2days zaki dawo normal, ga drugs d'inan saikina sha, shima wannan cream d'in kina matsi dashi awajen a koda yaushe .

Kaina na jinjina mata sannan nace  nagode Aunty .

Sallama tamin tafice.



A falo ta iske Galadima, bayan tamasa bayanin yanda yakamata a kula dani saita kallesa cikin tsokana,  ranka ya dad'e kafayi 6arna gaskiya, Shifa wajenan ba a nuna masa k'arfi, please a kiyaye .

Murmushi kawai yayi baice mata komaiba.

rakiya yamata tareda mata alkairi sannan yadawo.

A kwancen data barni ya iskeni, zama yayi gefen gadon yad'an kalleni ya janye idonsa  yaya kikeji yanzun? .

Baki na turo masa, amma ban tankaba. shima bai damu da amsawar tawaba, ya basar kawai ya d'akko wata maganar.

 nasan babu abinda zan fad'a ki yarda dani tabbas, sai dai zankuma maimaita miki SAMEER BAYA ZALUNCI, koda wasa ban ta6a kawo zan aikata hakan agarekiba har kibar k'ark'ashin kulawata, bansan miya shiga kainaba a jiya .

Kallonsa nayi ina hawaye da takaicin maganarsa, nace  bakasan miya Shiga kankaba ka d'auki fresh milk kabani? bayan kasan mika zuba .

Shima kansa ya d'ago yana kallona, cikeda k'asaitarsa yace  ban fahinceki ba, mikike nufi? dan ina son na kusance ki sainayi amfani da wani abu? da hakan naso daret zanzo gareki tunda nasan nabiya sadaki ai, tunda ba tsoranki zanjiba ko? .

 dama ai bazaka fahimceni ba tunda Kasan ka aikata ai, kuma ai alk'awarin zama tamkar abokai kamin ba irin wannan ba , na had'e hannuna alamar roko=�O�<��� ina kuka nace  dan girman ALLAH ina rok'onka kabani Sakina a yau natafi gidanmu, wlhy nafasa auren Contract d'in, koma waye yayi abun ni na yafe masama, kawai ka sallameni .

Yama rasa mizai cemin shi, ajiyar zuciya yad'an sauke, kafin ya cije lips nashi,  shikenan, zan miki yanda kikeso, amma kibari ki warke, bai kamata ki koma gida ahakaba .  yana gama fad'ar haka yatashi yafice batareda yaji amsa taba.

Duk da naso yabani sakina a yau, amma zanyi hak'uri na warke d'in kwana nawane.







******



Yinin yau haka mukayishi duk zukatanmu babu dad'i, Galadima kam ai ciwon mara saiya nemi dawo masa sabo, jiyayi kawai yana sake buk'atar kasancewa dani, haka yayta dannewa har zuwa dare, dan bazai kuma yarda yin gangancin nanba. ganin yana neman mutuwa yay shiri a gaggauce yafito domin zuwa hospital.

Tunda yafito suke zubewa gaisheshi, hannuna kawai yake iya d'aga musu, dan kallo d'aya zaka masa ka tabbatar yanada damuwa, da sauri sarkin mota yazo yabud'e masa ya shiga, suma dogaran dakan bisa idan zai fita sai duk suka taso.

Tundaga fitarsu gidan Muftahu na kallonsu, yad'an murmusa kawai abinsa. (=�D�wlhy Reader's suka kamaka zaka gane bakada wayo=�!�)



Shi kad'ai yasan azabar dayakeji a jikinsa, yana kwance cikin kujerar ne sai faman cije lips yakeyi.

Tunkan sarkin mota ya tambayama ya sanar masa asibitin da zasuje.

Sarkin mota ya amsa cike da girmamawa da tausayin shugabansa, dama shi tunda yaga yafito ya fahimci akwai matsala.

Tun amota yakira wata number yana tambayarsa ko yana asibiti?. Dr Jalal ya amsa da eh yana nan.

Yanke wayar yayi kawai baisake cewa komaiba. Dr jalal yabi wayar da kallo yana mamakin Galadima da halinsa, kiransa yakuma yi shi dan bai fahimci inda maganar tasa ta dosaba. sai dai harta yanke bai d'aukaba, yana k'ok'arin sake kira yaji ana Knocking d'in k'ofar.

Amsawa yay da yes tareda izinin shigowa.

Wani dogari ya bud'ema Galadima k'ofar yashiga, da hanzari Dr Jalal yamik'e yana murmushi da masa welcome.

Hannu kawai ya iya d'aga masa ya zauna kujerar gaban decks d'in.

Shima Dr jalal saiya zauna,  ranka ya dad'e lafiya dai ko? .

Saida yaja wasu Seconds sannan yafara ma Dr jalal bayanin damuwarsa, ya sanar masa mararsa namasa ciwo tun jiya, kuma ada bata masa kamar hakan.

Shiru Dr jalal yay yana nazarin maganar tasa, saida yakai aya sannan yace  ranka yadad'e kokasha pills ne? .

Kallonsa Galadima yayi,  pills kuma? wane irin tambaya kakemin haka? .

 afuwa ranka ya dad'e, matsalar taka tayi kama da wanda yasha tablet ne, mikaci na k'arshe jiya? .

cikeda nazarin maganar Jalal yace  fresh milk ne last abinda nasha jiya da daddare .

 to amma bayan shi kafara jin matsalar? .

 kusan haka gaskiya .

Dr jalal dai shiru yayi, dan ya tabbatar wannan aikin desire tablets ne, amma koya fad'a dawuya Galadima ya yarda, sai kawai yashare ya had'a masa drugs da injection yamasa, yace yad'an kwanta na kamar 20 minutes a office d'in. bai musa masaba ya shiga inda jalal kan huta idan yaso, saiya kwanta kawai, dan shima bazai iya tafiyarba, d'akin ma da taimakon jalal d'in yashigo.

Ni bansan hidimar da akeyiba, dan rabona dashi tun bayan munyi maganar saki, abinci ma tun Wanda doctor tabanine a cikina, sai kusan 8 Samha takawo min kayan fruits dawani Abu mai dad'i daban san mineneba=��.

Ta zauna mund'anyi hira kafin tafice. a bakin ta nakejin wai jibi Friday zasu koma India.

Na danci abinda takawo nasha magani nayi kwanciyata cikeda kewar 'Yar uwata dana kanyi akowanne dare.



Galadima kam bai dawo ba sai kusan 1pm, yana shigowa sashensa yawuce yay shirin barci ya kwanta, Alhmdllh zuwa yanzu yaji k'arfin jikinsa, sai dai zuciyarsa nata cud'a masa tunanin ina yasamo pills? dan shima yafara yarda da maganar jalal, musamman idan ya tuno furucin Munaya na d'azun da safe.

To kenan wani ya zuba masa bai saniba? to amma wazai zarga shikam? duk wad'anda suka shigo wajensa a jiya amintattun sane, Sauban, Samha, Harun, Muftahu, duk sun shigo wajensa a jiya, amma Muftahu shine last shigowa, shiru yay yana nazari, can kuma saiya cije lips d'insa ya lumshe idanu yana shafa gurin Dana cijesa.

A haka barci ya kwasheshi.





&&&&







Munubiya tashiga damuwa sosai akan rashin jina a waya, takira number ta yafi sau goma amma switch up, gashi yaa Marwan ya hanata kiran number dana kirasu a ranar, yace wai number Galadima ce bai kamata su damesa ba.

Haka taci kukanta a yinin ranar, saikace mara lafiya haka ta yini, zuwan su Ayusher ne ma yad'an sanyaya ranta har suka janye mata hankali da yawan tunani, a ranar gidan suka yini cir, sunsha hira da labarina, kowacce tana missing d'ina.

Sunce suna son zuwa amma an hanasu, wai gidan danake ba gidan da ake zuwa any how bane ba, babu yanda suka iya haka suka hak'ura.







*********





A gidanmu ma yau sukayi niyyar kawo min akwatinana da abinda ba'a rasaba, amma ankira wayata akashe, wannan yasa Abba yace abarni akaima su fauziyya nasu. ni daga baya idan an sameni akai min nawa d'in.

Duk inda akaje da innaro ake zuwa, kowacce ta taima gidanta kallon kwaf kenan, sotake taga gidan wacce tafi acikin sauran 'yan uwana.

ALLAH ya taimaki munubiya lokacin dasukaje gidanta yaa Marwan yana gidan, hakama su Ayusher.

Fita yayi yasiyo musu abubuwa yakawo, sannan suka zuba musu girkin da sukayi, babu ko kunya suka mik'e kafafu suka ci abinsu, to dama gidan Fauziyya ne kawai suka samu sukaci abinci, su Safara'u kam casukai basu fara girkiba, dan ita haleematu ma ruwa wannan bata basuba, banda innarmu akaje, dayake kowacce idan za'aje gidan 'yarta banda ita ake zuwa.

Zasu taho kuma yaa Marwan yabasu kud'in mota, dukda kuwa a mortar Dady yaa Anas ya kaisu.

Tunda suka dawo gida aka shiga labarin yanda aka iske gidan kowa, nanfa wad'anda gidan 'ya'yansu ba'a samu wani abun kuzo aganiba sai suka fusata, kunsan dai halin jama'ar gidan namu>�#�, wannan Abu saida yakawo rikici, fad'a sosai sukasha abinsu, itadai innarmu k'ala bata ceba, saima ta maida hankalinta ga girkin dare datakeyi, ga innaro sai habaici takeyi, saida gwaggo Safiyya tazo da k'yar ta lalla6ata tafita.

Matan anguwa makwafta kam sun masa kunne suna saurare da kwasar dariya, dan lamarin gidanmu yazama kamar na 'yan wasan kwaikwayo.

Duk tsiyar dasukeyi dady yana gidan yana jinsu, amma ko lek'owa bai yiba, danshi bashida hayaniya ko kad'an, balle daya fahimci abin yashafi 'yan bani na iya d'in gidan ne, dariya kawai yayi yace ALLAH ya k'yauta. kad'anma kenan ai, bakuga komaiba tunda yanzu kuka fara aurarwar, kuma har yanzu da sauran 6ur6ushin amarci ga yaran harsu Aunty khaleesa kam dake cikin watanni na hud'u da auren.





&&&&&





Alhmdllh yanzu kam naji dad'in jikina, dan ko ciwonma banaji, sai shirye-shiyen kayana nakeyi dan yau nakeson tuna masa batun sakina, tun shekaran jiya rabona da ganinsa, harma na d'auka baya gidan sai d'azun da safe Samha take cemin ai tare suka fita itada Uncle Sam da Sauban birnin gayu da asibiti zagayen marasa lafiya, sune har Asibitin mahaukata, tace duk atsorace take ALLAH yasa kartayi mafarki.

Ni dariya ma tabani yanda take bani labarin kamar a firgice take.

Komai nagama had'ashi tsaf, Galadima kawai nake jira, amma abin haushin har kusan 4pm babu labarinsa, gani nayi zan zauna jiran gawon shanu, dan haka na mik'e zuwa sashensa.

Nayi sallama yafi 7 amma babu amsa, sai kawai natura na shiga, a zatona rainin wayonsane da mulkin ya motsa, babu kowa a falon sai wani k'amshi dake tashi na musamman, ko ina kuma need a gyare,, a yanda naga yanayin falon kamar babu kowa a sashen gaskiya, dan komai akashe yake har AC, dawuya kuma yana nan kaga AC n sa a kashe, duk da haka saina d'an zauna ina k'arema ko ina kallo, kai kace yau nafara shigowa, hotunansa da bana gajiya da kallo naketa kallo yanzun ma, idona nacikin zageye-zagaye saina hango wani k'aramin frame na photo, bana ganin mutanen jiki sosai dan haka namik'e tsaye, ga hoton na isa, yana a kusurwar d'akinne ta gabas, saman wani d'an katako da aka k'awata wajen, bayan foton akwai flower babba mai k'yau, sai aka jigina hoton jikin flower d'in.

K'yak'yk'yawan mutum ne ajiki Wanda kallo d'aya zaka masa ka hango tsantsar kamaninsa da Galadima, saikuma mace a gefensa itama masha ALLAH, Galadima kuma yana satar kamanninsa da ita, musamman idonsa ha6arsa dawasu abubuwa, saikuma wadda nake k'yautatama zaton aunty Mimi Ce kusada matar, shima namijin ina tunanin Galadima ne, yana cinyar mutumin, bazai wuce 5 to 6 years ba a picture d'in, Anty Mimi kuma bata wuce 10 ba, sai tsohon ciki ajikin matar, dukda ban saniba sainayi tunanin iyayensane, duk cikin kayan sarauta suke.

Samha ta fad'amin iyayensa suna india, Abbansa bashida lafiya, ban wani tambayeta komaiba, iyanan naji kawai.

Hoton na maida na ijiye ina murmushi, sun birgeni gaskiya sosai, flower d'in nabi da kallo, itama tamin k'au, gawani k'amshi mai dad'i datakeyi, kuma nalura da dare kamar tana wuta haka. Hannuna na kai na ta6a ganye d'aya ajiki, sainaji Ashe ta roba Ce ma, mamaki ya kamani, banyi zaton ta roba bace wlhy, dan tayi k'yau.

Har zan bar wajen, kamar ance na d'aga kaina saman p.o.p d'in ta jikin kusurwar sainaga tamkar CCTV camera, amma bakowa zai iya fahimtar hakanba, domin ansata cikin tsantsar kulawa, gabanane yafad'i, nayi azamar kauda idona tamkar ba ita nake kalloba, saina d'an gyara zaman flower d'in kawai nabar wajen zuciyata na tsitstsinkewa, toshi miye nawani saka CCTV camera a falonsa?, komawa nayi na zauna, zuciyata nawasu tunane-tunane daban.

Sai lokacin tunanin koma bayanan yazomin, abinda Nagano ya hanani lek'a bedroom d'insa, dan nasan zai iya ganin komai ta CCTV camera d'insa.

��

Sai kawai natashi na fice nakoma nawa d'akin.............
'<���







Hum masu karatu kuna zaton Galadima bai fahimci Muftahu namasa zagon k'asaba kuwa>��?. kuduba yanda ya shashantar da binciken ya akayi yasha desire tabs a fresh milk>��.



To koma dai miye kumuje zuwa, ai masu iya magana kance *Karshen alewa k'asa*=�D�=�N�<���.





Humm ya kuke ganin sakin da Munaya ta nema? Shin zata samu? kokuwa zai bita bazai bayarba>��?.



Kumuje zuwa dai a page nagaba my guys>�s��&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&

















*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=�-�=�O�<���

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 7�





...........A gajiye yadawo gidan, daga masarautar su papi yake, dan shine yamasa kiran gaggawa a daren jiya, yau tunda safe ya tafi, dan jirgin 7am yasamu, shine sai yanzu yake dawowa.

Saman kujera ya zube yana furzo iska, sarkin mota daya biyoshi dawasu kaya ya ajiye, yana niyyar fita yajiyo maganar Galadima d'in. tsayawa yayi yajuyo yana kallonsa.

idonsa a rufe yace,  kunnamin AC  .

 to ranka ya dad'e . sarkin mota yafad'a yana risinar da kai alamun girmamawa.



Ya dad'e zaune a wajen idonsa a rufe, jin ana kiran salla a masallacin masarautar yasashi mik'ewa da k'yar yanufi bedroom d'insa. makunnar fitilar ya laluba, haske ya gauraye d'akin, komai normal kamar yanda yabarsa. anutse yafara zame sky blue d'in shaddar jikinsa. wanka yashiga, bai 6ata lokaci sosai ba yafito, jikinsa ya goge tsaf yajawo jallabiya fara tas mai dogon hannu yasaka, tamasa k'yau sosai, yad'an fesa turare yafita da hanzari jin za'a tada sallar magrib.



Nagaji da jiransa har zuwa magrib, bansan hawaye sun fara bin kumatuna ba, ahaka nayi sallar magrib, nayi alk'awarin ko yanzu yazo yabani sakina a gidanmu zan kwana, bayan na idar yau ko doguwar addu'a banyiba nadawo kan sofa na zauna tareda rabga tagumi na zubama akwatina idanu.

A wannan yanayin yashigo ya sameni, cikeda mamaki yake bin akwatin gabana da kallo, shi yama manta dawani maganar saki da mukayi.

Ban San ya shigoba saida yad'an bubbuga hanun sofa d'in, firgigit nayi ina kallonsa, bansan murmushi ya su6uce minba da ambatar Alhmdllh.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login