Showing 120001 words to 123000 words out of 365757 words

Chapter 41 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1443

da sauri suna gaishemu, hannu kawai suma ya d'aga musu muka shiga motar, suka bud'e mana gate d'in muka fice.

Tunda muka fita babu Wanda yay magana tsakanin ni da shi, yana aikin tuk'insa da sauraren redio daya kunna a motar, nikam ina lafe a kujera ciwo ya isheni, dan bana fahimtar yaren dasukeyi a redio d'in, tunda ba English baneba gaskiya.



Mun Isa wani babban shagon Islamic camix, komai zaka iya samunsa daya shafi maganin muslinci.

Abinda ya kaimu muka shigayi, yad'ebo zam-zam dayawa, sannan ya kalleni yana fad'in  saikuma mi? ?

Shiru nayi ina nazari. Dame yakamata muk'ara?, zuwa can nad'an hau duddubawa ina karanta sunayen magungunan ajikin kwalin, duk maganin danaga zai iya shafar jinnu ko sihiri, saida na d'akkoshi, (a tunanina idan mun dawo gidan zan d'auki hotunansu na turama Munubiya ta bincikamin yanda yadace ayi amfani dasu.

Duk abinda nake yana a tsaye yana kallona, saida na kammala sannan nasanar masa na gama.

Mun k'arasa wajen biyan kud'i, bayan yabiya yaran shagon d'aya ya d'aukar mana zuwa mota.



Daga nan asibitin muka nufa, mun tarar har lokacin Abie yana barci, sai gaisawa nukayi da momma da aunty Mimi, duk sunji dad'in yanda sukaga Galadima cikin nutsuwarsa. Zama yay kusada Abie yana mai tsurama masa idanu da masa addu'oi samun lafiya a zuciya, da kuma kudirar binne Wanda ya cutar masa da mahaifi da ransa idan ya kamashi a hannu.

Momma tayi farinciki da yanayin Galadima d'in cikin k'oshin lafiyarsa, dan da a dane da yanzu shima yana gadon asibitin, amma Alhmdllh yanzu gashi normal.

Mukam ni da Samha muna gefe zaune muma, ba hira mukeba, kowa yayi shirune yana tunanin duniya.

Sauban ma yana dawowa daga school shida Khaleel nan suka taho.

Bamu bar asibitinba sai dare, harda Momma muka wuce, dan yau suna buk'atar Abie ya kwana tare da ma'aikatansu.



Koda muka shigo Galadima sama ya wuce abinsa, ganin haka Momma tace natashi na naje nima na kwanta na huta hakanan.

A kunyace na mik'e domin cika umarninta.

Na iske yana cire kaya, dan haka nakoma da baya zuwa falo, saida na kintaci yagama sannan na shigo, na iskeshi yashiga wanka, nima natu6e nawa na d'aura zani nasaka hijjab tareda d'aukar kayan barcina ina jiran fitowarsa.

Bai dad'eba sosai kuwa yafito, sanye yake da bathtub fara tas, ban yarda na kalleshi ba natashi nashige nima.

Mai makon yayi shirin barci saiya kwanta a bakin gadon a haka, k'afafunsa na k'asa, ya tsurama rufin d'akin idanu alamar yatafi duniyar tunani.

Nikam ruwa mai zafi na had'a nashiga koda zanji dad'in jikina, na dad'e acikin ruwan kwance, jinakema kamar karna fito. shikansa yafara tunanin lafiya kuwa?, lokaci-lokaci yakan kalli k'ofar bayin, Amma babuni babu dalilina.

Yana shirin zuwa yamin knocking sai gani nafito kuma, janye idonsa yayi daga saitin k'ofar cikeda basarwa.

Ni bammasan yanayiba, dama nayi shirin barcina tun aciki, saina d'auki zani na d'ora a saman kayan nasaka hijjab nayi sallar shafa'i da wutiri, bayan na idar nad'akko roban zam-zam d'in d'aya na zauna nafara karatu Qur'an acikin ruwan zam-zam d'in. a hankali nake karatun cikin nutsuwa, dukda barcin dakecin idona.

Har cikin 6argonsa da jini yakejin sautin karatuna, ya lumshe idanu yanamaijin kamar mu kwana a haka inayi. mik'ewa yayi shima yayo alwala yazo yay shafa'i da witiri yay joining d'ina muka cigaba da karatun a tare.

Bamu kwanta ba saida mukayi sallar asubahi. (da yake sai zuwa 1 zasu bari ashiga wajen Abie, yau kuma babu aiki).









____((()))((*((()))*))((()))____





Yauma dai haka innarmu tadagema abbanmu saida yakira Senator Halluru agabanta, dan Zarah tana kwance babuma lafiya, ga mamansu Yaa Hameed ita kanta kallo d'aya xaka mata kagane abirkice take.

Innarmu duksai suka bata tausayi, matan gidanmu kuwa abin magana yasamu, sai gulma da dariyar gatsatsa, ita kanta Momy Hadiza ta hannun damar mamansu yaa Hameed d'in dad'i takeji, tanadai nuna damuwarta agaban mamansu Yaa hameed d'inne.

Bayan Abba sun gaisa da Senator halluri sukad'anyi barkwancinsu na abokai sannan yasakko xancen Zarah.

Hankalin Senator halluru yatashi, danshi koda wasana baisan Zarah bata nanba, yadai lura kullum Sa'eed saiyaje gida yaci abinci, shi duk zatonsa Zaran bata iya girkine saboda ciki.

Hak'uri yashiga bama Abbanmu yace wlhy shi baima saniba, amma insha ALLAH zai bincika, zuwa dare sa'eed d'in zaizo ya d'auki matarsa.

Dahaka sukai sallana da Abba kowa nakuma bama d'an uwansa hak'uri akan lamarin.

Innarmu bata buk'atar jin k'arin bayani dantaji komai, takumaji dad'i sosai.







()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()





Jikin Abie dai kam yayi tsanani a tsakaninnan, yau kwana biyar kenan lamarin sai addu'a, dan baisanma Wanda yake a kansa ba, mai martaba Sarki Abdul'fatah ma yazo shida inno matarsa, (wannan ne karon farko dana gansu ido da ido), mutanen kirki masu d'aukar kowa nasu, duk da d'ar-d'ar danai tayi haka sukaita jana ajikinsu. yanda Galadima yake zubama inno da papi shagwa6a sai abin yaso bani dariya, amma dai sun birgeni, mu a gidanmu wazaima innaro wannan ta6arar bata k'arema uwarsa tanadiba, ba kamarma mu 'yan d'akinmu.

hakama sarki jalalludden shida uwargidansa sunzo da mama Fulani.

Ranar momma har tausayi tabani, kai mama Fulani batada kirki wlhy, idan kunga yanda take shinfid'a mulki a asibitin nan. Hummm>�&�<���
@&.

Galadima ne kawai maganinta, tamasa magana ya dage ya ya6a mata bak'a shikuma.

Ba gidan suka saukaba, a hotel suka sauka, dan haka yau mun iskesu a asibitin sun rigamu zuwa.

Tunda muka shigo mama Fulani ta zubamin ido, Galadima ya gaida mai martaba da matarsa yakoma kusada Abie ya zaina.

Nima k'asa na durk'usa na gaidasu su dukansu har Momma da aunty Mimi.

Momma ta nunamin kusada ita alamar nazo na zauna kusada. banyi musuba naje na zauna, dan kallon k'urillar da Mama Fulani kemin duk sai na takura.

Tad'an ta6e baki sannan ta gyara zama idonta na kaina, tace  toke amarya halan saikin tashi haihuwa zaki koma mana? daga zuwa dubiya kuna Neman share wata 1 a india .

Gaba nane yafad'i, dan nafahimci dani take, saina rasa amsar dazan bata..

'Yan d'akin kam kowa ido ya zuba ma mama Fulani har Galadima.

Aunty Mimi ce tace,  Ranki yadad'e Kodai kina Kishine haka? Amarya ta kwance Miki fada wajen mai gidanki? .

Ajiyar zuciya Momma ta sauke a hankali, taji dad'in yanda aunty Mimi ta mayar da maganar wasa, ko nad'an batason abinda zai munana Munaya ko muzantata, dan bataso yarinyar taji kamar ita dabance a cikinsu.........

Wani munafukin murmushi mama Fulani tayi, ta kalli Galadima da zuciyarsa tafara hasala akan tsohuwar, kamar daga sama sukaji tace,  cikin namu wata nawane Galadima? ............
'<���







E me=�F�<��� mama Fulani mai gani har hanji>�&�<���
@&.













*_ALLAH ya gafarta na iyayrnmu=�-�=�O�<���_*

*_Typing=���_*







*_Haske writer's asso...._*=ء�









*_f&RAINA KAMA......f&_*

_{Kaga gayya}_







*_Bilyn Abdull Ce_*>��<���







~Book 2~ =�I�<���2�





..............Shiru Galadima ya mata, da ace babu Momma daya ya6a mata maganar da har tabar India tana mata zafi kuwa. amma duk da haka maganar ta daki zuciyarsa, bai saniba ko zancen tsohuwarnan gaskiyane.

Momma da Aunty Mimi da matar sarki kuwa kallona duk sukayi, nayi k'asa da kaina gabana Na luguden duka, saboda zancen tsohuwarnan yana son tsoratani.

Shigowar Sarki Abdul'fatah (papi) da inno matarsa da mai martaba Sarki Jalaluddeen ce ta tak'aita zancen. dan daganan kowa yasaki maganar, saidai munata juyata a zukata ni da Galadima, yayinda aunty Mimi da Momma ke fatan ALLAH yasa hakane.







_____________________________





Misalin 8:pm saiga Sa'eed yazo gidanmu, a time d'in gwaggon Haleematu da mamansu yaa Hameed suna ta hayaniyar fad'a, wai mamansu yaa Hameed ce takama gwaggon Haleematu tana kallon Zarah dake alwala a fanfo tana dariya.

Shinefa mamansu yaa Hameed tace gwaggon Haleematu taci kanta tasha bak'in ruwa, karta lashe mata jika tun yana a ciki.

Wannan kalma ta mamansu yaa Hameed itace tajawo fad'a, Dan gwaggon Haleematu tace mamansu yaa Hameed tace mata mayya bazata yardaba. Fad'a sosai sukeyi suna cin zarafin juna da gori, dama kowa kishi Na cinta a zuciya.

Matan gidanmu duk sunyo waje anrasa masu dakatar dasu sai innarmu dake cewa suyi hak'uri Dan ALLAH, darene fa.

Amma Sam sunk'i saurarenta.

Innaro dataji hayaniyar tundaga gidanta yasata d'akko fayafi tafito, kamar anjehota haka tashigo gidan.

Sa'eed da Sulaiman suna awaje a mota, duk badak'alar da akeyi daga cikin gidanmu suna jiyowa, har shigar innaro kuwa suna kallo. Dayake su Abbanmu suna masallaci.

Innaro tanata magana sunk'i saurarenta, saiyi sukema kamar zasu fara danbe.

Mamansu yaa Hameed Na k'ok'arin kwalama gwaggon Haleematu ludayin miya dake hannunta innaro takawo jiki zata kare sai a goshinta, jikake kwarrrr!.

Tako dafe goshi tafasa k'ara..

Hakan kuma yay dai-dai da shigowar su Abba gidan, su duka ukun, tunkan sushigo sukejiyo hayaniyar dama, dukansu rai a 6ace suka shigo. Dan iskancin matan nasu ya ishesu hakanan, idonsu yarufe ko ganin motar su Sa'eed basuyiba.

Ran Abba yakuma 6aci, Dan ganin duk matansa ne ma masu hayaniyar, ga abinda sukaima mahaifiyarsa akan idonsa. batareda yabi ba'asiba yace duk sufice su bar masa gida.

Ananne kowa yay tsitt, yadaka musu tsawa yana fad'in wlhy idan basu fitaba zaisa a fiddasu, ko d'akunansu bai yarda wata takomaba kuma.

Dole sai 'ya'yansu suka d'akko musu hijjabai suna kuka da bama Abban hak'uri.

Amma yak'i sauraren kowa, daddy da baba k'arami kuwa babu Wanda yay yunk'urin hanashi.

Innarmu tamatsa kusadashi tana rok'onsa karyayi haka, yazauna ya sauraresu tukunna, Hararar daya zuba matace yasata jada baya tai 6am da bakinta.

Innaro kuwa maman safara'u ce takamata ta zaunar, goshi harya fara kumbura=�F�<���.









(((+)))***(((+)))***(((+)))





Kafin mu baro asibitin nama manta da maganar mama Fulani, saboda murnar bud'e ido da Abie yayi ta d'aukema kowa hankali kuma, gaskiya ina tausayin bawan ALLAHn nan sosai.

yauma bamuyi k'asa a guywa ba wajen cigaba da addu'oin damukeyi cikin zam-zam ni da Galadima, somuke muyi na 1week sannan afara bashi.





Washe gari Alhmdllh jikin Abie yayi k'yau sosai, Dan inka gaidashi yakan maka murmushin sa Na dattako, hakan ya sanya su papi sukayi shirin tafiya da yamma.

Ni da Galadima da Sauban muka musu rakkiya, sainaji tamkar nabisu. Harda 'yar kwallata kuwa. Inno tanata tsokanata, Dan tsohuwar tashiga raina sosai.

Tunda muka d'akko hanyar dawowa asibitin nakife kaina a cinya inata hawaye, sauban ne kawai ke tsokanata, amma Galadima tamkarma baya cikin motar. hakan saiya k'ara tunzura zuciyata, nakuma k'ara k'arfin kukan nawa.



Sauban yasamu guri yay parking, da hannu Galadima yamasa alamar yaje.

Fita yay yana k'uk'uni da k'umshe dariya, wai  su boss za'ayi lallashi shine aka koroni . Saida yay nisa da motar sannan yasami damar dariyar, har yashiga wajensu Momma.

Daga Momma har Aunty Mimi kalli

onsa sukeyi,, aunty Mimi tace,  Auta lafiyarka kuwa? .

Saida ya zauna sannan yashiga kora musu bayani, dariya kawai sukayi, sunsan Sauban babu sauk'i wajen taso mutum agaba.



Tunda Sauban ya fita sai Galadima ya gyara zamansa kawai ya zubamin ido, mutum ne shi dabaya son shiga hak'in wani, ko kad'an baiso ace wane yana cikin damuwa ta dalilinsa......

Wayarsa aka kira, ya kalli wayar kafin yakai hannu ya d'auka, salamar da akayi daga can ya amsa suka gaisa.

Jin ya ambaci Nuren nagane da Wanda suka ta6a yin waya kwanakine, nad'an tsagaita da kukan ina sauraren mizasu tattauna. Galadima naji yace,

 miya farune kakeson nazo Nigeria haka da gaggawa Nuren .

 no babu wani damuwa, driver da yarinyar nanfa suna hannu, so yakamata ka shigo muyi abinda yadace ko? .

 ok babu damuwa, insha ALLAH zuwa Wednesday idan jikin Abie ya kuma lafawa zan shigo .

 O right, ALLAH ya k'ara masa lafiya, a gaishesu .

 zasuji insha ALLAH, bye .

Wayar ya ajiye a tsakkiyarmu ya maida hankalinsa kaina.



Cikin wani salo yace,  Munaaya! .

Wani Yarr naji a jikina, karo na biyu kenan danaji sunana a bakinsa, sainaji sunan nawa ya canja kamar ba shiba, danya iya sarrafa sunan a harshensa..... ganin ban d'agoba yakuma kiran sunan.

Kasa jurewa nayi nad'ago idona na kallesa, ganin ya tsareni da idanu saina janye nawa. yad'an lumshe nasa ya bud'e a kaina ya furzar da huci  kina ganin haka abokai yakamata su kasance? ni friend nakine, miyasa bazaki iya fad'amin damuwarki ba? kiyi hak'uri nasan kina buk'atar zuwa gida, last week naso maidaki Nigeria, amma sai jikin Abie Daya motsa ya dakatar dani .

Tausayi yabani, nad'ago na kallesa, mutumne shi mai sauk'in kai, saidai idan baka fahimceshi ba zaka sameshi a amurd'e, domin yanada wahalar sha'ani, hawayen dasuka ziraromin na goge, muryata na rasa nace,  kayi hak'uri ina kewar su Munubiya ne, insha ALLAH bazan sake yin kukanba amma .

Murmushi yaymin yana jinjina kai, yad'an shafa girarsa zuwa kai sannan yace,  kinada tsiwa, amma wani time d'in kinada kirki .

Bansan lokaci da dariya tazominba, nad'an dara sannan nace kaima ai hakan kake, kanada tsauri kanada sauk'i .

Yawani k'ank'ance idanu cikin wani salon kallon yace,  really? .

Gira d'aya na d'aga masa nima nace,  yaah .

Murmushi mai k'ayatarwa yayi yakwashi wayoyinsa yabud'e motar yafita batare data sake cewa komaiba.

Ganin haka nima saina fito fuskata washe da murmushi, kamar banice nagama kukan shagwa6a ba=� �.

Tunda muka shigo aunty Mimi da Momma suka zubo mana ido, Sauban kam dariyar shak'iyanci yafara k'asa-k'asa.

Momma tace,  ina kuka mak'ale haka? .

Murmushi yayi yana zama kujerar dake kusada Abie yace,  ba ko ina Momma ..

Momma tayi 'yar dariya tace,  shikenan tunda ba'aso muji .

Sauban da Aunty Mimi ma dariya sukayi, nikam kunya tasani k'asa da kaina inad'an murmushi.







__((*))__((*))__((*))__((*))__



Abba dai bai yarda su maman yaa Hameed su kwana a gidanba, a daren kowacce tanufi gidansu, yayinda baba k'arami ya d'auki innaro zuwa asibiti.

Su Sa'eed kam zare jiki sukai suka koma gida, zukatansu tab da mamakin wannan lamari.



A ranar zarah sai sashenmu ta kwana a tsohon d'akinmu ni da munubiya, saboda Aminu ya sanar mata yaga Sa'eed da mijin Siyama a k'ofar gidanmu.

Gaba d'aya saitaji yau tanajin haushin mamansu, dan daba ta tanka dariyar da gwaggon Haleematu tamata ba ai dabasuyi rigima har Abba ya korasu gidaba, dayanzu gidanta zata kwana jikin mijinta itama, wane irin abin kunyane wannan kai kana gida uwarka na gidansu itama>�&�<���
@&.







%%%%%%%%%%%%%%%





Dawowarmu kenan ni da Sauban da Samha daga zagaya gari, nagaji ovar, jikina sai ciwo yakemin, dama Yaya lafiyar giwa, saman


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login