Showing 159001 words to 162000 words out of 365757 words

Chapter 54 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2716

na k'asa da shi adalci.





Galadima daya shiga tun a falo yafara k'ok'arin cire navy blue d'in jacket d'insa, ya wullata saman kujera, sassauta belt d'in yayi shima amma bai cireba, ya zauna cikin tsantsar nuna gajiya yana furzo iskar bakinsa, remote ya d'auka ya kunna tv, tamkar ya saita lokaci saiga hoton d'iyar minister mai amsa sunan Farhat ana nunawa, an saka 2.5 millions ga dukkan wanda ya kawota koya bada bayanan sirri akan wanda yasan wani Abu akan 6atanta.

Wani mugun tsaki Galadima yaja a zuciyarsa yana fad'in wawaye, saiku k'ara yakai 100millions ba 2 ba, idan ubanta ya shirya kawo kansa gareni nima a shirye nake nabashi shashashar 'yarsa mai zubin ta6arya, ya kashe TV d'in kawai ya mik'e ya shige ciki.

Ko ina fes da shi, yasan baida Matsala da Sauban a 6angaren tsafta dama. kayan jikinsa ya ida cirewa ya shiga wanka.

Bayan ya fito samu yay yad'an kwanta, dan ya samu Hutu kona 2hours ne, dan yanzu akayi sallar zuhur. aiko kwanciyarsa babu dad'ewa barci yay gaba dashi.



Munaya ta jawo wayarta da nufin kuma kiran inna, amma sai taga Ashe credit d'inta yama k'are, kanta ta dafe dan haushi, zuwa can tamik'e domin bin shawarar zuciyarta. turare ta kuma fesama jikinta ta d'auki gyale ta yafa.

Ta d'an dad'e a k'ofar d'akin tana tunanin idan kuma ta shiga hasashenta bai zama gaskiyaba ya kenan?, wata zuciya tace kije abinki k'ilama wanka yake.

Da sand'a na ida shiga tamkar wata 6arauniya, sai kuma na tuna ai yanada CCTV camera, nutsuwa nayi na daidaita kaina, na koma normal saboda tsaro. Ganin babu abinda naje nema d'in a falo saina zarce bedroom ina wani ciccijewa.

Mamaki ya kamani ganinsa kwance a kan gado yana shak'ar barci hankali kwance, hakan yamin dad'i kam.

Saida nabi ko'ina na bedroom d'in da kallo, ganin babu alamar akwai camera a nan saina ida shiga, wayoyinsa biyu na ajiye gefen filon dayake kwance, rabin hannun damarsa ma nakan d'aya ya d'ora cikin barci halan?.

Dole saina hau saman gadon, dan haka na tsaya tunanin yanda zanyi, banida wata mafita dan haka nahau a hankali, kai kace wata hawainiya ce.

Cikin rintse ido da cije la66a nakai hannu zan d'auki wayar d'aya.

Caraf aka rik'emin hannu, babu Shiri na bud'e idona zuciyata nawani tsitstsinkewa.

Fisgoni yayi na fad'o jikinsa, zafin danaji ya sakani sakin k'aramar k'ara.

Ya matseni a jikinsa batare da ya kula miya aikata ba. nikam jikina sai rawa yakeyi, tsorona karya d'auka ko cutar da shi zanyi ma........ maganarsa cikin yanayin barci ta Sani kallonsa.

Kad'an ya bud'e idonsa dake jajir, alamar da gaske barci yakeyi, muryarsa a sark'e irinta barci yace,  sata kika koma? .

Baki na tunzuro ina marmar da idanu da suka cika da kwalla, nace  ALLAH ya kiyaye, arafa zanyi .

Kuma matseni yayi har saida na rik'e hannunsa,, yace  wannan ba aro bane sata ce yalla6iya, dan haka dolene ki kar6i punishment .

Jin ya ambaci punishment saina kuma rikicewa, nahau k'yarma ina rantse-rantae da matso kwallan idona.

Bai wani saurareni ba ya hau sumbatar wuyana, tureshi nafarayi amma saina gaza, dan haka na koma mintsini, shima a banza man kare=�)�.

Dukna d'auka wasa yakeyi kawai farfaganda Ce danna tsorata, amma saina tsinci ya fara sakin layi, iya yina da rok'o, yakushi, mintsini, ban samu ku6uta ba, saima salonsa yafara tasiri a kaina, nima nai luf harda k'ok'arin maida murtani. saida naji zai kama wata tashar nai azamar tsaidashi ta hanyar fad'in  please yalla6ai camera .





Maganinki ai baby=��, su Galadima akwai bak'in wayo dai>�%�=��, idan ta gaskiya za'abi ni banga abin punishment anan ba>�#�, dama yadawo 'Yar matsalarsa dai tsautsayi ya kawo mai karanbani dason banza ta fad'a tarko=��>�s�=��.



**********&********







Koda inna ta dawo saita had'ama su Aryaan kayansu, da nufin su koma wajen mamansu yaa hameed harta dawo.

Amma suka tibire akan bazasu jeba, su Uncle yace zaizo ya kaisu wajen Auntynsu.

Tun inna na lallashinsu harta kai ga mammakesu suka fara kuka, daga nan sukai barcin dole.

Bata fasa had'a kayanba, tagama tsaf ta d'auki akwatin zuwa d'akin mamansu yaa hameed.

Su Bintu kawai ta iske a falo suna kallo, Aminu ne yace  innar 'yan 2 ina zaki da daddare? .

Murmushi inna tamasa tana fad'in  kayansu Aryaan ne Aminu........

Bata gama rufe bakiba mamansu yaa hameed ta fito. ganin innarsu munubiya da kaya saita had'e fuska. Inna bata damuba tace  ga kayansu Aiyaan, saisu dawo nan da zama kafin na dawo .

 to . Kawai mamansu yaa hameed tace tana kauda kai gefe.

Ran inna ya sosu, amma sai batace komai ba ta ajiye ta fice jiki a sanyaye.

Da murnar Haneeff ya tashi zai d'au jakar yakai d'akinsu, amma sai Maman ta watsa masa harara. babu shiri ya koma ya zauna. Jakkar dai sai anan ta kwana, bata d'auka ba, bata bar 'ya'yanta sun d'auka ba saboda bak'incikin inna zataje jiyyar Abba ba itaba.





ALLAH ya k'yauta=�!�.









****************************



Dakatawa yay daga abinda yakeyi, ya bud'e idanu a hankali akan fuskata, murya k'asa-k'asa ya furta  camera? .

Kaina na d'aga masa batareda na bud'e idoba.

Bai kuma cewa komai ba ya koma ya kwanta yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips yana gyara kwanciya da sake rungumeni kawai.

Idona na bud'e a tsorace, azatona zai cigaba ne, sainaga ba haka bane.

A cikin kunnene ya furta  barci please .

Kallonsa nayi ta gefen ido sai naga idonsa a rufe, nima banida za6in daya wuce na rufe nawan, dan haka na lumshe kawai.



Ni sai barcin ya d'aukeni, amma shi ya k'auracema idonsa, mamakin furicina ya dami zuciyarsa, dama yadad'e yana zargin akwai camera a d'akin nan nasa, sai dai bawai ya tabbatar bane, kuma bai ta6a yunk'urin dubawa ba. da wad'annan tunanin ya cinye lokacin barcinsa har aka kwala kiran sallar la'asar.

Bud'e idanunsa yayi akan fuskata, yad'an tsuramin ido nawasu time's, sai yaga barcin yamin k'yau, kauda idonsa yayi cikeda basarwa, saikuma ya janyeni daga jikinsa yana yunk'urin tashi, hakanne ya sakani farkawar nima, na tashi da hanzarina ina gyara rigata, sai kuma na sauka na fice batareda nako waiwayoshi ba.

Bina yay da kallo harna fice sannan ya janye yana ta6e baki.





Ban kuma jin labarin Galadima ba har dare yayi, nafito wanka ina shirin barci ya shigo, yau dai babu laptop d'in kaddara, dagashi sai phone guda d'aya ma, yana sanye da kayan barci kalar gwaiduwar kwai masu duhu.

Zama yay a kujerar dake cikin d'akin, yayinda ni kuma na k'arasa saka hijjab d'in dana jawo, babu walwala ko alamar wasa kwata-kwata a face nashi, dan haka nima saina kama kaina.

cikin k'asaitarsa yace  muyi magana mana .

Kallonsa na d'anyi, saikuma na amsa da  ina jinka .

d'ago ido yay muka kalli juna, da ido yay min nuni da bakin gadon.

Ban musaba nazo na zauna, amma sai nayi k'asa da kaina ina wasa da zoben hannuna.

Maida kallonsa yayi ga zoben danake jujjuyawa, kusan mintuna 4 harna d'auka ya ma fasa maganar, na d'ago na kalleshi.

Ya kauda kai gefe yana fad'in,  waya fad'a miki da CCTV camera a d'akina? .

Nima ban kalleshi ba na bashi amsa a tak'aice,  bakai ka saka kayarka ba danni? .

Da mamaki ya kalleni, sai kuma ya kausasa muryarsa,  Munaayaa seriously nake miki magana! .

nad'an razana, amma saina dake, nace  kana nufin bakasan da itaba? .

 idan nasan da ita mizai sani aikata wani Abu na sirrina a d'akin .

da mamaki na kalleshi domin tabbatarwa, tsantsar gaskiya na hanga a idonsa, dan haka na danna yatsun hannuna da k'arfi suka bada sautin  k'asss!, k'asan zuciyata na tunanin minene sirrin nasa? .

Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi, nima na d'ago mukaima juna kallon ido cikin ido, dukda tsorata danai da hango masifa cikinsu ban janyeba, nafara fad'in  tabbas naga camera a falonka, tana nan saitin hotonku kaidasu momma, inda flower d'in nan take, hakanne yasani zargin kai ka saka kayarka saboda tsaro .

 hummm . kawai yafad'a yana janye idanunsa, sai kuma ya taso ya dawo inda nake zaune, ganinai kawai ya rungumoni jikinsa, na waro idanu dan mamaki, shikuma ya lumshe nasa tareda sumbatar goshina a hankali, shigar sumbarce tasakani lumshe nawa idanun nima tareda k'ank'ameshi.

Cikin kunnena ya furta  i'm proud of you my friend .

Da sauri na waro idanu ina kallonsa, saiya d'agamin gira d'aya yana wani miskilin murmushi, sannan ya tadani zaune shima ya tashi ya fita.

Baki da idanu da hanci duk na saki ina binsa da kallo, a k'asan raina ina tambayar mike damun guy d'innan ne wai?.

Banida mai bani amsa, dan haka na mik'e na cire hijjab d'in nai kwanciyata.



d'akinsa ya koma ya d'akko wani Abu kamar k'aramar ball<ر� ya ajiye saman table d'in gaban gadon, sannan ya manna wani dogon Abu a jikin 'Yar ball d'in, ya d'akko laptop d'insa ya kunna. shiru na kusan mintuna uku ya k'urama abinnan ido, zuwa can yafara wata k'aramar k'ara d'i! d'i! d'i!, sai kuma k'aramar danja ajikin abinda ya manna d'in shima tana kawo haske jaa da d'aukewa.

Murmushin takaici kawai yayi, a zuciyarsa yanama ALLAH godiya dabai ta6a kusantar Munaya a d'akin nanba. dan tabbas ga CCTV camera ya gani a d'akin, an sakatane can ta saman wardrobe, yanda ko alama hankalinsa bazai kaiba, baiyi yunk'urin cirewa ba, ya d'auki kayan aikinsa ya koma parlour, dan yaga itakuma tanan a ina take?. yanama shigowa tun'a k'ofar tsakanin bedroom da falon ya gani, baima k'arasaba ya koma ciki, kashe laptop d'in yayi ya d'auke k'aramar ball d'in ya 6oye.

Duk wannan hidimar da Galadima keyi Sauban na kwance bisa gadonsa yayi d'ai-d'ai yana kwasar barci.

Gyara masa bargo yayi saboda tasowar hadarin farkon damina da iska tafara kad'awa sanyi ya busa. daga nan ya kashe masa fitila ya fita zuwa d'akin Munaya.



Ita harma tayi barci, tana k'ank'ame da fillo saboda sanyin hadarin dake busawa, gadon ya hau tareda warware bargon ya lullu6a musu. dai-dai iska ta taso mai azabar k'arfi, a rikice Munaya ta juyo ta k'ank'amesa saboda tsorata.

Rik'eta yay sosai yana fad'in  uchh! Karki karyani .

Babu shiri munaya ta bud'e idonta, tana k'ank'ame da shi tace,  wai miyasa bazaka ke kwana naka d'akinba ne? .

 k miyasa time d'in da kikaje India kika gajemin d'akina? .

Shiru tamasa bata amsaba, amma yanajin alamar murgud'a bakinta akan k'irjinsa.

 punishment ya tabbata agareki yalla6iya .

Da sauri nace  wlhy a'a, inba hakaba zaka koma saman sofa ne, ai kaima haka kamin a d'akinka .

 uyim Madan tsiwa, to ai nima dankar ki murk'ushemin abin cikin kwan cikin barci yasani kwantawa anan? .

Zan bashi amsa aka kwad'a wata tsawa data sakamu ruk'unk'ume juna babu shiri, sai kuma ruwa ya 6alle.

Da wannan damar Galadima yay amfani wajen canja salon kwanciyar tamu, tun ina nuna banaso har salonsa ya sakani sakin layi, (=��anya munaya wannan cikin naki bashine tarkon da Galadima ya d'ana miki ba?=��).





Da asuba tashi nayi inata zum6ure-zum6ure, baice dani uffanba yashiga toilet ya tsarkake jikinsa. Bayan yafito nima na shiga.

Baki ya ta6e yana wani d'age gira d'aya tamkar ina kallonsa ya fice.



Saida nasha kukana sannan nayi wankan tsarki, narasa mike sakani biyema Galadima? insha ALLAH zan d'auki mataki (>�#�idan babu abin cikin kwan ba=��, nasan inhar yana nan babansa zaita samun bonus=��).





Bayan na idar da sallar ban koma barciba, saina gyara d'akin nayi wanka, shirin fitarma na sake yi yau, dan baba k'arami yacemin k'arfe goma na safe zuwa 11 zasu tafi.

Kammalatawa kenan ya shigo, ko kad'an banji alamar shigowarsa ba, saida na gama fesa turare ina k'ok'arin ajiyewa na hango kamar mutum tsaye a bayana.

Da sauri nayi azamar juyowa, dayake yana gab dani kad'an ya rage na fad'a masa a jiki, na dai samu nad'anyi baya na jingina da mirror ina tura baki.

Ko motsi baiyiba shikam, bai kuma janye idonsa daga kallona da yakeba.

Haushi ya kamani, nima nabi jikin nawa da kallo kozanga abin da yake kallon, ganin babu wani Abu daya faru na d'ago na kuma kallonsa,  wai yalla6ai mi kake kallone haka? .

d'an yatsansa d'aya yasaka yad'an shafi girarsa yana gyara tsayuwa,  abin cikin kwan mana .  ya fad'a cikin basarwa .

 ta gefensa na ra6a zan wuce ina fad'in  ai lokaci kad'an ya rage maka ka bar ganin nasa .

Da sauri ya rik'o hannuna, na juyo muka kalli juna, mayun idanunsa ya saka cikin nawa,  kina zaton idan nabar ganinsa kema za'a cigaba da ganinki? .

Guntun murmushi nayi ina janye idona daga cikin nasa, nace  kana zaton kasheni zakayi nima? .

 cire maganar ma zato .

Kallonsa na kuma yi, cikin yanayin da shi kansa bai ta6a zaton ina dashiba nace  saika fara shiri .

Shima a dake yace  dama a shirye nake kullum .

Na murmusa ina k'ok'arin cire hannuna daga cikin nasa, amma ya hanani damar hakan, kallonsa na kuma yi nace  ko har lokacin yayi ne? .

Fisgoni yayi na koma da baya, ya mannani jikin mirror d'in tare da maida hannuna baya ya rik'e, ya matseni da jikinsa, fuskarsa gab da tawa tamkar zai had'a bakinmu, yayinda idonsa ke cikin nawa, wani miskilin murmushin gefen baki yayi, yasaka yatsansa yana zagaya janbakin dake kan la66ana a hankali, cikin muryarnan tasa mai kama da an masa dole ya fara magana cikin karsashi  ko Ubangiji yakanyi hukuncine ga bawan daya bijirema umarninsa, koda ace zubarda wannan cikin kikayi dolene saikin kuma d'aukar wani, zubar da shi na dai-dai da haihuwar yara goma anan gidan kafin na aikaki inda shima ya tafi ya matsa la66ana da k'arfi, wani zafi ya ratsani saiga hawaye a kumatuna, murmushi yayi, yasaki la66an ya dangwali hawayen a d'an yatsansa, nunamin yay yana fad'in  lallai momcyn abin cikin kwan kin cancanta 100%, amma bayan abin cikin kwanfa akwai k'annensa, please bar kuka my dear friend .  ya k'are maganar da sumbatar la66ana sannan ya sakeni yaja baya.

Koda ya sakeni sainayi murmushi kawai, sannan na juya ina fuskantar mirror, foda na d'auka na gyara fuskata, na sake saka jambaki kad'an kamar yanda na saka d'azun.

Tsayawa yay cikeda mamakin abin da nayi na ko inkula yana kallona, mi wannan yarinyar take shiryawa ne haka?.....

Kafin ya samu amsa Na juyo gareshi, fuskata d'auke da murmushi na ra6a zan wuce sa, bina kawai yay da kallo, naje gaban wardrobe na bud'e, alk'yabba na d'akko na sanya, sannan na d'auki handbag ina kallonsa har yanzu fuskata d'auke da murmushi.

Gira ya d'agamin shima yana wani k'asaitaccen murmushi, ya juya ya fita batareda yakuma magana ba.

Yana fita na sauke ajiyar zuciya ina dafe k'irji, wlhy ni kad'ai nasan dukan da zuciyata takeyi, kad'an yarage ya ranfo a tsorace nake, kalamansa ne suka shiga dawomin cikin zuciyata, mi wannan yake nufine wai..........?

 Shin bazaki bane? .

Muryarsa ta daki dodon kunnena, da sauri na gyara yanayina na d'ago muka had'a ido, Ashe yana bakin k'ofar bai tafiba.

Bance komai ba na biyo bayansa.

A falon farko na iske kuyangina suna gaidashi, hannu kawai ya d'aga musu ya fice abinsa.

Tsayawa nayi muka gaisa, d'aya a cikinsu ta yunk'urin k'ar6ar handbag d'ina.




Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login