Showing 129001 words to 132000 words out of 365757 words

Chapter 44 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1468

ubangiji ya halicceka dominta bazakayiba, ya had'iye wani Abu mai d'acin gaske a mak'oshinsa. sannan yashiga k'ak'aro murmushin dole ga sauran hadimansa dake gida basuje tarbarsaba. daka kallesu kasan suna cikin tsantsar farincikin ganinsa, dan sunyi kewarsa, shima hakance agaresa. bayan sun gama gaggaisawa ya tambayesu lafiyarsu sannan yashige ciki.

Ko ina k'al yake tamkar yanda yake buk'atar ganinsa, (hadimansa nada k'ok'arin tsaftace sashensa koda baya k'asar).

Zama yay bisa kujera yana fad'in  ya ALLAH! Alhmdllh .

Dogarin daya shigo masa da jakka yakuma masa sannu da zuwa sannan yafice.

Yakai mintuna 5 a wajen zaune, sai k'ullawa da kwancewa kawai yakeyi, ga gajiyar zaman jirgi na nuk'urk'usarsa data rashin isashen barci dabasa samu shida Munaya. da k'yar dai yamik'e zuwa bedroom d'in, komai need sai k'amshin mayen turarensa da air fresheners mai sanyin dad'i ke tashi, ya ajiye jikkarsa a kan gadon sannan yafara zame kayansa danya samu ya watsa ruwa.



Ya d'an jima a bayin sannan ya fito d'aure da towel, yana tsane fuskarsa zuwa kai dawani. wardrobe yabud'e ya d'akko boxes kawai yasaka, sannan ya saka jallabiya, sallolin da suka riskesa a hanya ya rama, yana idarwa yacire jallabiyar, matsawa yay jikin mirror ya fesa turare kad'an ya hau gadonsa da yay missing. harya kwanta yatashi zaune, briefcase d'in dayazo da ita ya bud'e, ya Ciro wayoyinsa tareda layinkansa na Nigeria duk ya saka, sannan ya ijiye wayoyin, insha ALLAH zuwa lokacin da zai tashi yana fata komai ya dai-daita.

Addu'ar barci yayi ya gyara kwanciya, amma sai barci yace bai gadaba, tunanin ahalinsa daya baro wata k'asa ya dabaibaye zuciyarsa, wata kewarsu ke tsikarar zuciyarsa, yanzu yasan Abie yayi barci, hakama Momma watak'il ta kwanta, dan macece mai yawan k'iyamull laili, duk da a asibiti takan kwana hakan baya hanata kusanta kanta ga mahaliccinta, Aunty Mimi da Samha ma yasan sunyu barci, Sauban ne dai dakamar wahala ace ya kwanta, ya juya kwanciyar sa yana murmushi, zuciyarsa tace  to matar contract fa? . ya d'age kafad'a da ta6e bakinsa kad'an, saikuma yasaki k'aramar dariya, daren jiyane kawai ya fad'o masa a rai, yau kuma koyaya ta yini ta kwana? (danba time d'inmu d'aya da India ba), a fili yace,  ALLAH yasa yau dai babu zazza6in, my Friend kin cika taurin kai, dakin yarda nakaiki asibiti zanfi samun nutsuwa, oh god>�&�<���
B& .  ya k'are maganar da dafe kai .

Shima yajima baiyi barciba, sai can dare yaja da nisa sannan ya saceshi.





Da asubahi da k'yar ya iya tashi, alwala yay yafita massalaci, bayan an idar da salla yafito suka had'u da Sarki da jama'a keta zubewa suna kwasar gaisuwa.

Sarki yayi mamakin ganinsa, dan har saida fuskarsa ta nuna hakan, murmushi kawai Galadima yayi yana rissinar da kansa k'asa.

Sarki baice masa komaiba yanufi sashensa, sai Galadima yabi bayansa, dogarai kuma suka take musu baya, bayan sun gaida Galadima d'in.



A hamshak'in falon mai martaba na farko suka yada zango, Sarki na zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu, Galadima na k'asa kusada k'afafunsa. Kukun Sarki ne suka shigo shida jakadiyya bayan sunyi sallama..

K'aramin tire suka ajiye dake d'auke da butar shayi, sai mug da wani k'aramin bowl mai k'yau anzuba sukari, sai jug k'arami shima an zuba tataccen lemon tsami, saikuma Zuma shima a k'aramin bowl.

Kuku da jakadiyya suka zube gaban mai martaba suna kwasar gaisuwa, sannan suka gaida Galadima shima da masa barka da zuwa.

Cikeda kulawa ya masa musu, har kuku ya durk'usa zai had'ama mai martaba shayin Galadima ya dakatar dashi, tareda masa nuni dayaje abinsa.

Kuku ya rissinar da kai alamar girmamawa sannan suka fice shida jakadiyya suka basu waje.

Galadima ya had'ama Mai martaba shayi da ruwan lemon tsami kamar yanda yasan yana sha a kowacce Safiya, (ada mahaifinsa yasani da wannan al'adar, dan awajensa Sarki jalaludden ya koya). cikeda girmamawa ya mik'ama mai martaba mug d'in, kar6a yayi yana masa murmushi, sannan yace  kaifa? .

Girgiza kai Galadima yayi, yace  a'a Abba, wannan sai ku .

Mai martaba yay murmushinsu na manya sannan yace  Saukar yaushe Sameer? .

Galadima yad'an shafa wuyansa, cikin tsantseni yace,  da daddare Abbah, wani business ne ya kawoni, inaga insha ALLAH zamu bud'e company anan Nigeria saboda muma matasanmu su Mora daga guminmu .

Murmushi mai martaba yayi, ya kur6i shayinsa sannan yace  tunani mai k'yau yarona, ALLAH yasaka hannu a lamarin. ya jikin d'an uwana dasu auntyna Zeenah? .

 jikin Abie Alhmdllh Abba, dan bayan tahowarku sauk'i yakuma samuwa gaskiya, Momma kam suma lafiyarsu lau .

 to Masha ALLAH, tareda iyalin naka kazo kenan? .

 a'a Abba, ni kad'ai nazo, saina kammala abinda nazoyi itama idan zan dawo zamu dawo tare .

 to ALLAH ya tabbatar .

 Amin Abba, bara naje nad'an kimtsa mu gaisa da jama'a, dan zan d'an fita .

 ok, ALLAH yayi Albarka .

 amin Abba, a huta lafiya .

Hannu kawai mai martaba ya d'aga masa, Galadima kuma yafita.



Babu inda ya Shiga, ya koma sashensa domin yayi shiri. saida ya had'a coffee da kansa kamar yanda ya saba idan yazo k'asar, ya zauna yasha danba abincin kowa yakeci a masarautarba, ko Ummu hasheem bayacin abincinta kota kawo, duk da kuma kulawa datake nuna masa fiye da kowa a gidan, gimbiya zulfah uwargidan sarkima tanada k'ok'arin aika masa abincin inhar yazo, amma ko kallon kulolin ma bayayi, saidai bayinsa su cinye.



Yafito wanka yana tsane jikinsa wayarsa tayi k'ara alamar shigowar sak'o, wayar ya d'auka danya duba ko company ne, dan yana fatan ace komai ya daidaita ne, yanason kiran su Momma yaji Yaya jikin mahaifinsa.

Ganin number ce sai abin yabashi mamaki, bud'e sak'on yayi kawai azatonsa ko Nuren ne.



_Gargad'i!! tabbas sirikinka ya tsira a wanan karon, amma ka tabbatar masa next time bazamu barsaba, saimun raba ruhinsa da gangar jikinsa!!!!.................._
'<���

























*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu=�-�>��<��� '<���_*

*_Typing=���_*







*_Haske writer's asso...._*=ء�









*_f&RAINA KAMA......f&_*

_{Kaga gayya}_







*_Bilyn Abdull Ce_*>��<���







~Book 2~ =�I�<���5�





..............Bayan an idar da salla Galadima yace wanne office yakamata su fara zuwa?, mtn ko glo?.

Shiru Nuren yay yana tunani, zuwa can ya kalli Galadima  Sameer mizai hana mubari sai zuwa gobe, kasamu kaje kad'an kwanta ka huta, kaga yanda idonka yay jazur kuwa, ga jijiyan dukta tashi .

Lumshe idanu Galadima yayi yana furzar da huci mai zafi a bakinsa,  Nuren muje kawai, kona kwanta bazan samu nutsuwa ba, kaga fa yanda suka jigata bawan ALLAHn nan .

 hakane, amma karka damu muje kai dai kawai .

Galadima bai musaba, suka jera shida Nuren zuwa wajen mota, bayan anbud'e musu sun shiga sai Nuren yacema Sarkin mota suje hotel d'in daya sauka.

Galadima yanajinsu amma baice uffanba, yayi shiru kawai yana kallon jama'a ta glass.

Koda suka isa hotel d'in sai Nuren yace su sarkin mota suje abinsu, zuwa anjima zai kirasu su maida Galadima d'in gida.

Cikin girmamawa sarkin mota ya amsa da to, yamusu sallama suka tafi.



Koda suka isa d'akin da Nuren ya sauka Galadima cire rigar shaddar yayi ya kwanta dagashi sai dogon wandon da vest, kwanciyar mintuna 5 kacal barci yay gaba dashi. Sosai tausayinsa yakama Nuren, yanason d'an 'yar uwar mahaifinsa sosai, (Nuriddeen d'ane ga Abubakar yayan Momma, babban d'an Sarki Abdul'fatah daya gaji sunan Sarki Abubakar kakansu Galadima, mahaifin Nuren ayanzu haka shine mai jiran gado a masarautar su momma, Nuren d'ansane na biyu, akwai yayansa Ballo, shid'in sa'an Galadima ne, kusanma tare akayi goyonsu, amma Galadima ya girmesa da watanni 7 a duniya, kunga d'an uwansane na jini kenan, ta 6angaren mahaifiya=�L�<���).



Galadima ya jima yana barci, dan kiran sallar la'asarne ya tadashi ma, wanka yasake yi, ya kar6i kayan Nuren ya sanya, k'ananun kayane amma sun masa k'yau sosai, Nuren nata tsokanarsa, wai kayan sun masa k'yau, inhar Munaya ta gansa bazata ganeshi ba.

Harara ya zubama Nuren, sannan yanemi hanyar fita,  malam idan kagama surutun saika taho muje .

 sorry sarkin gagara badau mai jiran gado .

tsaki Galadima yayi kawai yafice abinsa, shifa haushin mai jiran gado d'innan yakeji idan aka ambata masa, sadai nemi mai jiran gadonsu amma bashiba, mtsoww!!.



Wata mota dake fake a harabar hotel d'in suka nufa, Nuren ya zauna a mazaunin driver, yayinda Galadima ya zauna gefensa.

A hankali Nuren ke tuk'in suna 'yar hirarsu jefi-jefi, dayake kowanne akwai nutsuwa basuda yawan hayaniya, dan shima Nuren d'in bashida surutu.

Tafiya mai d'an nisa ta kaisu wani k'auye, bawani babban gari baneba can. Galadima ya kalli Nuren yana hararsa,  wai Nuren bazaka saida gidannan ba dai ko? .

Murmushi Nuren yayi, yad'an gyara zamansa yana kallon Galadima, saikuma ya maida ga hanya.  brother kenan, ai yanzu ba abinda kuke tunanin nake aikatawa ba a gidan, wlhy babu ruwana da 'yar kowa yanzun .

 Humm Nuridden! nasan inhar kana tareda Muzaffar bazaka ta6a daina neman mataba, nidai bazan gaji da gaya maka gaskiya ba, inhar aure kakeso kawai kayi aure, bazaka gane llar zina ba saika auri yarinyar da wani yagama Sani, saika haifi yara kuma, Nuren! Ba cika baki nakeba, bakuma nafi k'arfin ALLAH ya jarabceniba, amma dana aikata zina ka ganni nan gamma a d'auramin aure da mata hud'u a rana d'aya, please and please d'an uwana, ka canja tun Kannada damar hakan, dukkanin ahalinmu basa son wannan d'abi'ar taka wlhy .

Nuren ya jinjina masa kai yana cije la66a,  na gode d'an uwana, insha ALLAH nabari har abada, kuma kwannan zakaji maganar aurena ta tashi, wlhy tun wancan lokacin da abunnan yafaru ban sake mu'amulla da kowacce maceba, idan najima zan takura saina fara azumi .

 tom ALLAH yacigaba da gadinmu muda zuciyoyinmu, amma Auren shine tafi cancanta dakai, dan wani lokacin da mutum yakai azumin ma zakaga komai yadawo, kaga Auren shine cikakkiyar mafita kawai .

 gaskiyane wlhy, ALLAH dai ya k'ara shiryamu .  Nuren yafad'a yana horn a k'ofar gate d'in katafaren gidan gonarsa dayake kiwo .

An bud'e musu gate d'in suka shiga, ma'aikatan sai murnar ganinsa sukeyi, tsayawa yay da motar batare da sun fitoba, sukaita zuwa gaishesu, bawani Sanin Galadima sukayi sosaiba, tunda bawani zuwa wajen ya keyiba, Nuren zai fad'a musu wanene, amma Galadima yamasa nuni da karya fad'a, hakkane yasakashi 6ame bakinsa.







******************************





Ran mama Fulani a 6ace yake kallon manyan jikokin nata maza guda uku tayi, cikin isarta da k'asaitarta tafara kiran sunayensu,  Talba! Wanbai! Matawalle!, kunsan dalilina Na taraku anan kuwa? .

A tare suka girgiza mata kai kawai.

Takuma gyara zamanta cikin tsantsar mulki da izza, tace,  nakula mahaifinku har zuwa yanzu baison ciwonku ba, shi dole yanaso ace masa adalin Sarki, shiyyasa kullum yake fifita d'an wani bisa Ku da ALLAH ya bashi, Matawalle shekarunka dana Galadima kusan d'ayane, amma mahaifinku nagani Galadima yay aure bai ta6a nuna damuwarsa akan kai kayiba balle sauran 'yan uwanka, to yanzu matar Galadima cikine da ita, kuma tabbas ta haifi namiji kuda sarautar gagara badau saidai kallo .

A razane Talba da wambai suka zaro idanu waje a zabure, matawalle kuwa murmushi kawai yayi yana girgiza kai da mamakin wannan kakar tasu mai shegen son kanta.

Wambai yace,  haba Granny miyasa kike fad'ar wannan maganar, yakamata bakinki ya fad'i alkairi mana, shi dan uban cikin basai mun bari an haifesa ba, koshi uban cikin dayake tak'ama yana jiran gado bai isa yayi mulkiba balle cikin da babu tabbas d'in haifosa, ni wlhy kinma 6atamin rai .

Talba yaja tsuka shima yana harare-harare,  Granny ya akayi kikasan tanama da cikin to? wannan sarkin girman kai d'inne zai iyama mace ciki? .

Harara mama Fulani ta zubama Talba,  to uban matanbaya, azatonka zai zuba mata idone yana kallonta kamar hoto ko television a gida? ince kwana nan 4 kenan dabaro inda suke .

Wambai yace  amma shine bakiyi maganarba sai yau Granny? .

 to ubana koyamin yanda zanyi .

 ALLAH yabaki hak'uri .  cewar wambai yana k'unk'uni k'asa-k'asa .

Matawalle dabaice uffanba tunda aka fara maganar yay guntun murmushi, muryarsa a tausashe yace,  Ranki ya dad'e ni banga amfanin wannan maganarba, ALLAH shine ya azurta Galadima da samun ciki a jikin matarsa, wannan kuma abun farin cikinmu ne amatsayinmu Na 'yan uwansa, shi dai mulki Na ALLAH ne, shike badawa ga Wanda yaso akuma lokacin da yaso, bamuda tabbacin tsawancin ran ganin gobenmu ma balle maganar gadar sarautar cikinma daba'a San miza a haifaba, please musama zukatanmu sallama kodan mutuwa, nifa banga wani dalili dazamu ke saka kammu a wahala akan mulkin da ubangijine kawai madawwami a mulkinsa, nikam kunga tafiyata, ki gafarceni inada uzuri .

Tunda matawalle yafara maganar Mama Fulani da Talba da wambai ido suka zuba masa, harya fice ba'a samu mai iya tanka masaba. haka yake shi, babu ruwansa da bak'in mugun abun masarautar, da zuciya d'aya yakeson d'an uwansa, shi bama wani zaman k'asar ma yakeba sosai.

Wani wawan tsaki Talba yaja, yabi bayan Matawalle da harara yana fad'in  lusari kawai, inkai bakason sarautar mu ai munaso, shifa wannan ko sarautar ya gada wlhy lusarin Sarki mai lasisi za'ayi anan, duk wannan wahalar akansa akeyinta danya zama magajin Abba amma shashashan nan baya gani .

 mtsoww!! bar banza d'an uwa, idan zai bamu matsala kai basai ka zama magajin Abban ba, nifa harma tunani nake, anya matawalle jinin gidannan ne?..........

 kai ya isa haka, banason rashin tauna magana, Ku k'yalesa zaima dawo hanyane, miye mafita yanzun? .

 mafita d'ayace Granny a 6arar da shegen cikin kawai, kuma ma ai Galadiman yazo jiya .

Da sauri mama Fulani ta tashi zaune daga kishin gid'ar datayi,  wambai kana nufin Sameer na a masarautar nan? .

 kwarai ma kuwa, da safe nagansa zaishiga mota a k'ofar sashensa, yanata faman d'aurema mutane wannan shegiyar fuskar tashi da yakejin tafi ta kowa k'yawun gani .

Wani k'asaitaccen murmushi mama Fulani tayi tana fad'in  lallai yaronnan ya isa, kuje kawai, bayan nagama tsara komai zan nemeku .

atare suka mik'e suna fad'in  ahuta lafiya ranki ya dad'e sarauniyar gagara badau .

Murmushi tama jikokin nata tana gyad'a musu kai.







____((____(((&)))____))____





Galadima da Nuren sun shiga ainahin matsakaicin gidan Nuren dake a gidan gonarsa Na kiwo, sosai ya tsara cikin gidan, dan ananne yake holewa da 'yammatansa a watannin baya, sai dai yanzu kam alhmdllh yabari gaskiya, dan sai lokaci-lokaci yake d'an ta6awa, fatansa ma yabari gaba d'aya, dama ta silar abokai ya koya>�&�<���
@&.

Galadima ya zauna saman kujerar guda d'aya yana sauke numfashi, har yanzu zuciyarsa tak'i nutsuwa waje d'aya, halin da yaga Abban Munaya ya dank'are masa zuciya.

Cikin ma'aikatan wajen yay sallama daga waje, Nuren yabashi izinin shigowa, kayan marmarine yahad'o ya kawo musu bayan ya tsaftacesu, a saman center table d'in ya ajiye, sannan yakona yaciro musu ruwa a freight d'in dake falon da cups Na glass.

Bayan fitarsa Galadima ya kalli Nuren d'in,  Brother wai miyasa ka kawoni nan ne? .

 cinikin kanka nayi .  cewar Nuren yana harar Galadima .

 Wani k'asaitaccen murmushi Galadima ya saki, yakai hannu yana shafa sajensa zuwa gemu, cikin d'age kafad'a da la6e baki yace 


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login