Showing 54001 words to 57000 words out of 365757 words

Chapter 19 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1459

dariya ba kai tsaye.

Tuni an kar6i kayansa an nufi sashin inno dasu, shikuma yanufi fada, Dan yasan yanzu Sarki suna fadanci.



Cike fadar take da 'yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso yashiga da sallama, nanfa dogarai suka fara zuba masa kirari.

Hannu kawai ya d'aga musu ya rissina yana mik'a gaisuwa ga Sarki.

Sarki da fuskarsa tacika da fara'ar ganin jikan nasa ya amsa cikin lumshe idanu.

Nan dogarai suka d'au da fad'in  sarki ya amsa maka sarkin gagara badau na gobe, an gaida magajin sarki, galadiman gagara badau, ALLAH yabaka zamani irinna sarki gagara badau.

Galadima Yakuma rissinawa ya mik'a gaisuwa ga 'yan majissar sarki, suma cikeda fara'a suka amsa, kowa yasan irin tsantsar k'aunar da sarki kema jikan nasa a masarautar.



Atake anan sarki ya sallami kowa, fadanci yatashi saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu, yau yanada ganawa ta musamman da jikansa.

Haka kowa yatashi yana musu addu'ar kasancewa cikin aminci.



Tareda Galadima sarki yashiga cikin gidansa, hannunsa Na rik'e da Na Galadima, ba sabon Abu bane hakan a masarautar, duk Wanda yakwana yatashi acikinta yasan matsayin Galadima azukatan masu masarautar.

Akatafaren falon sarki suka yada zango, babu dad'ewa da shigowarsu saiga jakadiya da kuyangi uku, kowanne d'aukeda babban tire, bayan sun dire komai suka zube suna kwasar gaisuwa wa sarki, sannan suka gaida Galadima.

Jakadiya ma ta rissina ta gaida Galadima damasa barka da zuwa masarautarsu.

Bayan fitarsu Galadima yakuma risainawa a girmame ya gaida sarki kakansa.

Cike da murmushi sarki ya amsa yana kamo hannunsa,  Muhammad Sameer! kana lafiya .

 Alhmdllh ranka ya dad'e .

 Masha ALLAH, ya kabaromin Zeenah ta da jikin babanka da 'yan uwanka kuma su Haneefa? .

 Momma lafiyarta lau, hakama jikin Abie Alhmdllh, suma su aunty mimin haka .

 to Alhmdllhi, ALLAH yacigaba da jagorantar lamuranku ya albarkaci rayuwarku ta gobe da jibin jibima .

Murmushi Galadima yayi yana amsawa da amin.



Sarki da Galadima tare sukaci abinci, (tun yana k'arami dama idan yazo gidan hakance ke faruwa tsakaninsu) Sunci sun k'oshi sukayi hamdala ga ALLAH.



babu wani 6ata lokaci sarki yashiga masa bayanin kiran nasa akan maganar da Fateema (mom) tazo masa da itane jiya, shima ya zauna yayi nazari yagane hakan shine dai-dai, Galadima ya auri Munaya.

tur6une fuska Galadima yayi tamkar baisan komaiba, yace  ranka yadad'e ka gafarceni, ammafa ni bata minba ai .

Sarki yay murmushinsu Na manyan k'asaitattun masu ji da mulki,  basai tayi makaba Muhammad, domin sanda Na aurama babanka Zeenah itama bai mataba, amma saboda biyayya dakuma tausayin d'iyar 'Yar uwarta ta amince tamin biyayya, to kaima hakan nakeso gareka, ka amsamin da to kawai saimu zauna lafiya, kasan magana biyu ba halina baceba ko .

Jinjina kai Galadima yayi yana kuma tankwashe k'afarsa, cikeda girmamawa yace  ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, Na amince da za6inka, ALLAH yabani ikon rik'ewa .

Cike da tsantsar farinciki Mai martaba ya rik'o hannun Galadima,  Muhammad ALLAH shiyi maka albarka, ya tsareka dadukkan sharri, ALLAH yabama mahaifinka lafiya kaji .

 amin ranka ya dad'e, ngd sosai  .

Daga nan hira suka cigaba dayi cikin tsantsar soyayya da k'aunar juna, kowanne yanajin d'an uwansa sosaih a ransa.

Kusan atare suka yini, inno tun tana zuba idon shigowar Galadima harta hak'ura. Galadima bai shigo wajenta ba sai bayan sallar magriba.

Tundaga k'ofar sashenta hadimai keta kwasar gaisuwa, tuni labarin tahowarsa ta iske inno, hakan yasa ta k'imtsa da k'yau, ta sallami bayinta masu mata hidima.

Fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi ya k'araso falon, bai zauna ko inaba sai jikin kakarsa, oh my sweet inno I miss you so much wlhy .

Kunnensa tad'anja kad'an, cikeda tsokana tace  miskili kafi mahaukaci ban haushi, aini harna fara shirin yo bikonka daga turakar mai martaba .

Yayi 'Yar dariya yana fad'in  tuba nake ginbiyar papi .

 ja'irin kaya, bazaka canjaba dai? ya kabaro iyayen naka da 'yan uwanka? .

 kowa lafiya lau ranki ya dad'e .

 to Alhmdllhi  .

Nanma hirarce ta 6alle tsakanin kaka da jikanta, kan mace me nanma an cika masa gaba da kayan itatuwa, shikuma yana zubama inno shagwa6ar daya saba tana biye masa.



Masu jiran Galadima kuwa a airport saida sukaga kowa yagama fita ajirgi babushi sannan wani dogari yakira sarkin fada yake sanar dashi sufa basuga Galadima ba.

Sarkin fada yace  yo kunacan kuna shashanci yaza'ayi Ku gansa, shi harma sun shige cikin gida da sarki  .

'yan uwansa ya sanarmawa suka tattaro suka dawo masarautar.>�#�



Dole a nan masarautar ya kwana, washe gari ya zagaya duka sashen sauran matan sarki ya gaidasu a mutunce. suma dai sunmasa tarbar mutunci kamar yanda suka saba, duk da dai taciki Na ciki. Sannan sai sassan iyayensa yayun momma da k'annenta, dukda dai bako ina yashigaba.

Yanzunma tare sukayi karin kumallo da maimartaba, sannan suka fita fada tare, da Galadima akayi fadanci yau, yana gefen adalin kakansa.





Washe gari da safe ya tattara inasa-inasa ya cane India, yabar tsofin da kewarsa, shima yatafi yana kewarsu.





********

https://2gnblog.blogspot.com/



Gwaggo Safiyya tacigaba da samun kulawa sosai, dukda dai tanad'an jin jiki, kullum matan gidanmu sukanzo sau d'aya, muma dai makaranta tasa bama yini a asibitin, amma kullum da safe mukanzo mu kuma dawo da yamma.

Matan gidanmu kam jarabar innaro tasakasu k'ok'arin zuwa kullum, dan tace wlhy duk Wanda bata zuwa saitayi Dana sanin saninta.

Wannan furuci ya d'an tsoratasu, dan kowa agidan yasan wacece innaro, idan kaga mutuncinku ya d'ore to kana cinna mata 'yan canji ta k'ark'ashin k'asane=�J�, amma kana hanata gobe bazai hana ta karta maka rashin m ba>�#�. (Ho innaro mu ta mutunci>�8�<���
@&, ina yinki over ginbiyar Malam faruku=��=�J�)

�&<���
@&



Abin yafara tsoratani ganin har sati 1 dayin maganarmu dasu Galadima amma babuko labarinsu, tun ina saran yau gobe har na daina lissafin ma, ganin zan saka kaina a damuwa nacirema zancen a raina gaba d'aya, domin Na gama fahimtar maganar Galadima da abokinsa k'aryace, maybe ma mafarki nayi naketa shirmena kawai.

A tsaitsaye damuwa tafara ramar dani a tsaye, sai idanuwa da dogon hanci.

Tun ina daurewa har Abu yaso yaci tura, ciwon kai Dana k'irji suka fara zama abokaina.

Ranar data kama sati biyu cif saiga bak'i su Abba sunyi, babu Wanda yasan daga ina suke, kuma su Abba basuma kowa bayanin komaiba dangane da bak'in. saida sukayi kwanaki uku da zuwa sannan naji wai wanine yakawo kud'in aurena yana son abama d'ansa.

Lamarin yabama kowa mamaki, nanfa 'yan gidanmu suka hau dariyar mugunta wai kwantai dai ya tabbata kenan.

Gugar zanar dasuke tayine ya fusata innarmu, tasakama Abba kuka akan bata aminceba, yaza'ayi su d'auki aurena subama mutumin dabasu saniba, idan su sun gaji dani itafa tanason kayarta.

Lallashi duniya Abba yayi dan innarmu ta fahimta amma Sam tak'i saurararsa, wannan ne karon farko da yaga tsantsar fushinta.

Yarasa yazai mata, dan shima lamarin Na damunsa, yarasa minene yasakashi amincewa yabada auren d'iyartasa ga mutanen?, shi dai kawai tsohon yamasa kwarjinine wlhy, dan jiyay ko kad'an bazai iya musa masaba. dukda talakawane kamarsa, harma yana ganin yafisu abubuwa da yawa.



Lamarifa yayi tsamari a d'an tsakaninnan a gidanmu, dan innarmu takasa kwantar da hankalinta, hakama abbanmu, yayinda 'yan gidanmu sukejin Dad'i kamar su had'a fati.

Nikuwa uwar gayya ai ba'a magana ma, nakira number Galadima yafi sau 200 amma tak'i shiga ko sau d'aya, lokaci guda nagama fita hayyacina, 'Yar uwata kanta dukta lalace kamar itace cikin matsalar.

Innaro kam ciwon gwaggo Safiyya ne ya d'auke hankalinta, duk da dai su Abba sun mata bayanin kawo kud'in nawa, amma cikin halin ko in kula tace su basu kawai, idan sun barni agidan kuwa najawo musu abin kunyar dayafi nabaya, harma tashafi sauran kannena suk'i auruwa tamkar ni.

Wannan furuci ya Sosa zuciyar abbanmu, amma saiya danne saboda girman mahaifiya.

An sallamo gwaggo Safiyya da kwana biyu jikina ya birkice nima, dole aka kwasheni aka kai asibiti.....





*********



A 6angaren sarki kuwa bayan tafiyar Galadima da kansa yazo masarautar gagara badau, an masa tarba ta girmamawa domin shid'in babban abokine ga kakansu Galadima wato (marigayi sarki Abubakar na lll).

Mama Fulani kanta in kunga yanda take girmama sarki (Abdul'fatah idris) saikusha mamaki Ku d'auka ba itace mai ji da kanta d'innanba da tsantsar nuna sarauta(gaba da gabanta yo>�t�).

Sarki bai 6ata lokaciba ya sanar musu abinda yazo dashi, ganin tsantsar farinciki nayi ga mafi yawan jama'ar gidan, dan hukuncin sarki Abdul'fatah yamusu dai-dai, koba komai an k'ask'antar da Galadima d'in, Wanda yadace ace an sama masa d'iyar wani mashahurin sarki ya aura, kodan sarautar da ake da yak'inin shine yakama ta ya gada.

Murmushi papi yayi, saboda ganin farinciki zancensa a fuskokin wasunsu, yasan tabbas dawata manufa suke wannan farinciki, amma hakan bai damesa ba, domin shi da k'yak'yk'yawar niyya yayi. maganar sarauta kuwa sune suke ganin bazai iyaba saida wata d'iyar babban sarki, amma shi yanada yak'inin ko d'iyar shugaban talakawan duniya koda baiwace agidan Galadima ya aura sarauta ta ALLAH Ce.



Daga baya ya tsara musu yanda yakeso Neman auren ya kasance, bawai zasuje musu da rigar mulki baneba, yanason suje amatsayin talakawa domin ganin tarbar dazasu samu daga iyayen yarinyar, daganan zai gwada yak'inin tarbiyar gidan da mutuncin iyayenta.

A masarautar sarki ya kwana, washe gari sukayi shigar talakawa shida sarki jalaludden k'anin mahaifin Galadima, sai wazirin papi dana sarki, saikuma k'annen mahaifin Galadima biyu sannan aka sami tsohuwar mota suka tafi aciki bisa jagorancin wani dogari da sarki yasa yamasa binciken gidansu munaya.

Abinda basuyi zatoba shi suka samu, domin tarba ta mutunci da girmamawa suka samu dagasu Abba, duk da suna kallonsu talakawa fitik harma da yak'inin sun fisu komai.

Hakan ya burge sarki Absul'fatah (papi) shi kansa sarki jalaludden lamarin ya masa dad'i. Sun bada kud'in gaisuwar farko data biyu naira subu 30 kacal.

Sai bayan tafiyarsu sannan su Abba sukaita mamakin kansu anya mutanen bada wani siddabaru sukazo musuba? Yazama ayi basu sansuba amma suzo su kar6i auren 'yarsu? sukuma su basu babu musu kamar sun gaji da ita. (Niko nace kwarjinin sarauta suka muku abba=��=��).

Can kuma dasu sarki suka tafi sunata yabawa suma, sarki Absul'fatah dad'i dukya gama cikasa, lallai Galadima yasamu tsatson daya dad'e yana masa fata da addu'ar samu.



Momma koda papi yakira yamata bayanin bataji komaiba, saima addu'a data masa da kuma nuna farin cikinta akan lamarin, koba komai zataga auren Galadiman ta, amma saida tayi hawaye data tuna za ayi auren Galadima babu mahaifinsa, kamar yanda akayi na Haneefa (Aunty Mimi).

Data sanarma Abie saiya fad'ad'a murmuahinsa, yayinda hawaye ke zirara ta gefen idanunsa, ALLAH sarki iko da falala, tun yaronsa na shekara 5 a duniya yake a wannan halin, gashi har zaiyi aure, yagodema ALLAH da wannan jarabawa shikam.





A satin papi yaje India ma da kansa, yaduba jikin Abie dakuma maganar auren Galadima dayayi musu, nanma saida Abie yay hawaye, amma sarki Absul'fatah yayta masa nasihar yawan hak'uri da kar6ar k'addara, ya nuna masa sunada yak'inin zaici ribar can.

Abie yana son surukinsa kuma aminin mahaifinsa sosai, dan duk lokacin dazaizo dubashi da irin salon nasihar dazai masa wadda zai k'ara tasirantar da imani a zuciyarsa.

Galadima kuwa sai wani basarwa yakeyi irin shifa abin bai d'ad'ashi da k'asaba, kuma bayason abin, aurenma dole za ai masa, haka yaytaima Abie korafi yana shagwa6a.

Murmushi Abie yay tayi yana lallaahinsa da idanun.

Cikin tsokana sauban dake d'ayan gefen Abie shima yace  yaa Sam to kawai ni abani kana, kaga na huta da zuwa tad'i k'ofar gidan kowa .

Wata uwar harara Galadima ya maka masa, wadda tasaka Momma da auty Mimi da samha da jakadiya dariya, shi kansa Abie murmushine ya fad'ad'a afuskarsa.............
'<���





Wannan shine yafaru 6angaren Galadima munaya bata saniba.





Guys kuje zuwa kawai, k'ila zuwa dare kujini da bonus�&<���
@&�&<���
@&

ALLAH yabama munaya lafiya.







Barka da juma'a.=�� '<���











*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=�-�=�O�<���

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���1� 8�



https://2gnblog.blogspot.com/

..........A Asibiti gado suka bani, sunata fad'an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi 'yar k'aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?.

Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu.

Wannan karonma Mama Rabi'a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga 'yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne.

Duk suncika d'akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi'a har Munubiya babu wanda yabasu amsa.

Doctor ne yashigo yace sud'an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi'a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo.

Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara'u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d'aukar kai, saikace ba 'yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak'uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba>�#�.

Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar.

Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad'in maganinku ai, baku masu dangiba..........gabana yafad'i, saboda jin tamkar k'amshin turarensa. da sauri Na d'ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu.

Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k'ananun kaya wad'anda suka fidda ainahin k'irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala.

Mu 4 ne kawai a d'akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu.

A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud'ani.

Sauran 'yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d'in.

Annanma yayi kusan mintuna hud'u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k'arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad'a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa....... tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d'aya.

Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi.

Hannu kawai ya d'aga musu yamatso jikin gadon danake.

Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad'anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara'u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za'a kwashe.

Munubiya ce cikin k'arfin hali tace  Munaya ki tashi ana miki magana fa . daka ganta kasan a tsorace take maganar.

Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login