Showing 90001 words to 93000 words out of 365757 words

Chapter 31 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1476

da yinin washe gari , kullum dai Samha kan kawomin abinci tareda kuyangin Aunty Mimi.





&&&&





Bayan sallar isha'i damuwa da rashin jin innarmu da Munubiya ya gallabi zuciyata, jinai bazan iya daurewa ba, dan haka na yanke shawarar zuwa na rok'esa ya aramin charger kona samu nayi charge wayata, duk da ma banida isashen credit aciki. na d'au turare nad'an fesa kad'an sannan nazura dogon hijjabi nafita zuciyata na d'ar-d'ar.

Na dad'e k'ofar falon tsaye ina tunanin yanda zan shiga, daurewa nayi nai Knocking, wata murya naji ta amsa sa6anin tasa, akace  waye? .

Saida gabana yad'an fad'i, cikin rumtse idanu nace  nice .

Galadima dake kwance cikin kujera idonsa a lumshe yana sauraren Muftahu yabud'e idonsa da sauri.

Shikam muftahu cewa yayi  bismillah ranki ya dad'e, ki shigo .

Na tura k'ofar ahankali na shigo da wata sabuwar sallamar, Muftahu ne kawai ya amsa cikin washe baki, (yayinda k'asan zuciyarsa ke wata iriyar murna ganin shirinsa zai tafi dai-dai kenan). Galadima kam idanu kawai ya zubamin cikeda mamakin miya kawoni?.

Gaisawa mukayi da Muftahu cikin mutunci. saiya mik'e yana fad'in  ranka ya dad'e nikam na wuce, zuwa Safiya zamu k'arasa maganar kawai .

Kansa kawai ya d'agama Muftahu n.

Muftahu ya kalleni yace  gimbiya mu kwana lafiya .

Na murmusa sannan na amsa da  to ALLAH ya tashemu lafiya .



Koda Muftahu yafita sainayi tsaye nakasa magana ganin ya zubamin idanu, ganin banida niyyar magana saiya nunamin kujera alamar na zauna. shima yana tashi zaune sosai.

Ban musaba na zauna.

 miya faru? .  yafad'a yana zuba Hollandia fresh milk a glass cup d'in gabansa .

d'agowa nayi nad'an kallesa, dai-dai yasaka kofin a bakinsa zai sha, janye idanuna nayi ina kuma had'e fuska. aransa yace kai wannan yarinya akwai jan ajin tsiya.

Saida naja wasu seconds sannan nace charger zaka aramin please, nabaro tawa a gida, gashi inason waya da munubiya da innarmu.

Crossing kafarsa yayi yana cigaba da shan free milk nashi tamkar bai jini ba, harna fidda tsammanin zai tanka min, sainaji yace,  ina wayar? . yay maganar da mik'omin hannu alamar na bashi

Mik'ewa nayi na kai masa wayar ina tunanin mizaiyi da ita?.

Koda ya kar6a saiya mik'omin cup d'in hannunsa bayan yak'ara fresh milk d'in a ciki.

Na girgiza masa kai alamar na k'oshi.

wani kallo ya watsamin daya sani kar6ar dole. nadawo mazaunina na zauna, inata rik'on cup d'in amma nakasa sha, haka kawai naji hankalina bai kwanta da fresh milk d'in ba, bawai zargin yazuba wani Abu nakeba, haka kawai dai banjin sha.

Shikuma ya basar dani yanata juya wayar kawai a hannusa, basan miyake kalloba ajikinta.

Kallona yayi yace,  kin rik'e Number su? .

 eh nafad'a batareda na kallesa ba.

Wayarsa ya d'auka guda d'aya ya had'omin da tawan ya mik'omin,  kije kuyi wayar kawai, da safe sai a nemo miki charger d'in .

Na tashi naje na kar6o tareda cewa  nagode najuya nafice da cup d'in fresh milk d'in a hannu na.

Bina yayi da kallo harna fice, ya sauke ajiyar zuciyata kafin ya cije lips nashi domin jin mararsa tad'an rik'e masa kad'an.



Koda naje d'akina saina kasa ajiye fresh milk d'in, haka kawai naji kuma sha'awar nasha, nako d'aga cup d'in na shanye tas sannan na zauna ina juya wayar tasa datamin k'yau, saina tuno wayarsa daya barmin ranar idi, na ta6e bakina kawai nafara saka number innarmu..............
'<���







Hummm mi zai biyo baya bayan shan fresh milk kuma?. da zuwan muftahu?.>�%�



Wannan amsar sai ranar Monday>�+�. naso yimuku wannan weekend d'in amma munada biki gsky.=��=؃�<���





*_hhhh naji k'orafinku sister's, ammafa ko pages biyu nakeyi ba isarku zaiyiba=��, wlhy bama nida time d'in yin typing 2pages a rana, saboda inada aure, akwai nauye-nauye a kaina nima, masu kuma so nagama kafin azumi suma ina basu hak'uri, bazai yuwu nagama kafin azuminba, dan azumin kad'an ya rage, kuma banason datse labarin nan kamar yanda nayi a SIYASA KO KABILANCI, zanbi a hankali na gama, wlhy nafiku son nagama nima Na huta, Dan dana fara buk zai fara cizona a zuciya nima, so kawai nake naga nagama=��, karku manta ko tarihin masarautar su Galadima sameer har yanzu bamu saniba, Dan haka zamuyi, iya inda muka tsaya saimu cigaba bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya, Dan kamar yaune ai.=��=�L�<���._*



Ngd sosai da soyayyar dakuke nunama buk d'innan, ina sonku nima har cikin raina, ina fata zaku fahimceni=��=�L�<���.



d'd'd'd'd'd'd'

�&<���
@&



















*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���_*

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 5�







..........Bugu biyu ta d'auka, jinayi tamkar anmin bishara da aljanna dan dad'i, lokacin danaji muryar innarmu tayi sallama cikin sanyinta sai kawai na Sanya mata kuka.

Ita kuma daga can batasan wayeba, a sanyaye tace  baiwar ALLAH ko bawan ALLAH lafiya kuwa? .

Murmushi nayi, gakuma hawaye na kwaranya, nace  innarmu nice fa .

Cikeda d'okantuwa tace,  Munaya kece? ya kuke? .

Murmushi nayi mai sauti, nace  innarmu ina yini? inasu Aryaan? Wlhy ina missing d'inku innarmu, ALLAH kamar na dawo gida . na k'are maganar da sakin kuka.

Kallon juna sukayi da Abbanmu, da yake girkin tane tana d'akinsa, sukama juna murmushi, Abba yace,  haba dai munaya ta jaruma ce da kuka haka? Ina aka ta6a kai mutum gidan miji yayi sha'awar dawowa gida inbada yawoba? .

 wayyo Abbanmu I miss u so much kaima wlhy .

Dariya suka sanyamin shida innarmu, Abba yace,  yo ga sakaran yarinya, miyeto na kukan hakan? Yaya mijin naki da jama'ar gidan? .

 komai lafiya lau Abba, sai kewarku, musamman ma Munubiya, ALLAH ina kewarta Abba, dan ALLAH kace ya kaini na ganta .

Yanzu kam dai su Abba sosai sukemin dariya, saikuma suka shiga tsokanata, tun ina kukan harna ware nima ina dariya, munyi hira sosai, kafin Abba yace  saida safe hakanan, karda ki k'are masa kud'in, ki gaidashi .

Cikeda farinciki namusu sallama, da cewa zankirama gobe.

Na yanke wayar ina murmushi, Munubiya na kira itama, cikin sa'a tashiga kuwa. tana kwance jikin yaa Marwan yana d'an rage zafisa>�+�, wayar tafara ring, shine yamik'o mata, ta amsa tana kallon number, irin Special number d'in Nance, wadda zaka ganta a tsare. (>�+�bara na Baku, amma banda matan aure 07000000000=��)�&<���
@&�&<���
@&.



Saida ta kalli yaa marwan ya d'aga mata kai alamar tayi picking sannan ta d'aga.

Muryar Munaya dataji yasata mik'ewa zaune zumbur cikeda d'oki.

Kowa yay kewar d'an uwansa, dan haka ko gaisuwa bamu tsaya yiba muka shiga fad'ama juna yanda mukai missing. muka 6alle hira kamar zamu ga juna tacikin wayar..

Mun d'au tsawon lokaci munayi kafin yaa Marwan yasamu dole yin sallama, wayar ya kar6a ya jawo matarsa ya rungume, zatayi magana ya d'ora yatsansa a bakinta alamar tayi shiru tareda yanke wayar ko sallamar arzik'i bamuyiba.

Inajin sukur-sukur d'insu ta wayar, dan haka na tuntsure da dariya ina fad'in oni su yaa marwan Ashe dai ashe?....=��>�-�.

Number Fauziyya na gwada itama akashe, nace lallai amarci yayi dad'i kenan?, itama Ayusher na kira number busy, 'Yar tara, nasan tanacan itada khamees ana soyewa.

Feena ma wayarta Switch up, nad'anyi tsok'i na ajiye wayar Na tashi domin yin shirin barci, dan yau ina cikin farin ciki, tunda naji muryar families d'ina.



Tun bayan fitar Munaya kam Galadima yafara jin canji a jikinsa, a hankali yakejin wani feelings na bijiro masa, kamar wasa abufa yafara tsamari, tun yana basarwa har mamaki yafara kamashi, shin wai mike faruwa ne dashi haka? bazaice baya sha'awa ba, yanayi sosai, dan wani time d'inma saiyasha tablets, ko allurar kwantar da sha'awan, amma baita6a jin irin na yauba, k'arfin sha'awarsa yasashi katange kansa daga dukkan abinda zai iya zurmasa ga halaka har yazama hanyar tsanin aikata zina. duk da jiya yad'ansha wahala saboda abinda yafaru tsakaninsa da yarinyar can duk da shi yayine badan yaji wani abuba, amma Abu yaso zamar masa Matsala a yinin gaba d'aya, sai dai tunda yaje yay allura sai nutsuwa tazo masa.

Dauriyarsa ce take Neman zuwa k'arshe, sai kawai jikinsa yafara rawa, da bin bango yashiga bedroom d'insa, drowan gefen gadomsa yabud'e yad'iba drugs kusan uku ya watsa a baki, ruwa ya d'auka frigate ya korasu suka wuce.

Humm abanza wai man kare, maimakon yaji sauk'i saima abin ya k'aru. yadawo falo saman doguwar kujera Yakuma kwanciya bayan ya kashe AC n gaba d'aya, Dan k'ara dulmiyar dashi yakeyi.



Nima d'in agareni kusan hakane, kad'an-kad'an nafara jin tsigar jikina Na tashi.

Kamar wasa ina wanka sai Abu yafara shan kaina, abinda bansan ma'anarsa ba yafara bin jinin jikina da 6argo, na lumshe idona ina hango abunda yafaru tsakani na d'azun da Galadima, duk dani wahala ma nasha, wani feelings na tashin hankali yafara bijiromin, idanuna harsun sauya kamanni, da k'yar nayi wanka nafito, ko towel d'in ban cireba na saka hijjab Na d'au wayarsa Na fita, koda nayi sallama a k'ofar falonsa banji ya amsa ba, nayi har sau uku shiru kakeji, shikam yana kwance yana jina, amma bakinsa yakasa koda motsawa barema ya amsa min, saima muryata dake sakashin jin wani zirrr, duk sanda nayi sallamar sautin muryata na motsawa da tsigar jikinsa ne, gaba d'aya gashin jikinsa ya tashi.

Jin shirun yayi yawa natura k'ofar kawai Na Shiga abuna, azatona ko barci ya d'aukesa kokuma bai jiniba.

Ganinsa kwance saman doguwar kujera yasa gabana d'an fad'i, gawani iri dana kuma ji jikina yayi, dagashi sai boxer da vest, hannunsa d'aya dafe da mararsa, d'ayan kuma dafe da kansa, kauda kaina nayi daga kallonsa saboda tsorata da ganinsa a ainahinsa, gaskiya ba k'aramin namiji bane guy d'innan, duk kunya ta isheni, ban ta6a ganin namiji ba a haka, yo samarin gidanmu basa zama haka. duk tunanina barci yakeyi, na ajiye wayar saman cikinsa a hankali, kamar yanda naga d'ayar a ajiye, caraf ya rik'e hannuna da hannunsa daya dafe kansa, tsoro yakamani lokacin daya bud'e idonsa yana kallona, jazur idon yake abin tsoro. Muryarsa a matuk'ar sanyin daban ta6a Sanin yana da shiba yace  mi zakiyi? . idanu na nad'an waro waje cikin tsarguwa nace,  mi zanyi kuma? wayarkace fa na ajiye maka . ajiyar zuciya yad'an sauke, ya zuba min idanu batareda yasakimin hannunba. Gaba d'aya jikina yakuma rikicemin, jima nake tamkar Na fad'a kansa saboda abinda nakeji, ganin karna aikata abinda zanzo ina nadama saina zare hannuna dad'an k'arfi, jikinshi babu kuzarin kirki, danhaka yasaki hannun kawai, nikuma na juya nafice daga d'akin da saurina.

Lips d'insa ya cije da matuk'ar k'arfi kamar zai huda, Yakuma dafe mararsa datayi tamkar zata fashe masa, kai bazai iya daurewaba, domin zai iya mutuwa wlhy, ganin yarinyarnan kuma Yakuma birkita tunaninsa. idonsa yarigada yarufe, ya manta matsayin Auren Nasu, duk da gargad'in da wani sashen zuciyarsa yake masa akan alk'awarin daya d'auka, burinsa kawai ya sauke wannan nauyin kozai samu nutsuwa, da k'yar yamik'e ya fice zuwa d'akina.



Nikam INA zuwa na zube saman gado bayan Na zare hijjab d'in, dagani sai towel, marata data d'aure tamkar zata fashe na rik'e da hannu biyu Ina hawaye, wai wannan wace iriyar masiface ne?, nashiga uku ni Munaya, mike shirin faruwa dani ne?..

 innalillahi kawai nake iya karantawa saboda tashin hankali, jikina harwani rawa yakeyi, ko kad'an bansan Galadima ya shigo d'akinba, dan nafad'a wata duniya ta daban, babu zato kawai naji mutum yafad'o jikina yana sauke numfashi wani na k'orar wani, wata wawiyar runguma yamin tareda matseni ajikinsa gam, kai kace cikinsa zai maidani.

Humm maimakon na turesa sai nima nakuma k'ank'amesa, banyi k'asa a guywaba wajen maida masa murtani abinda yakemin..

Daga ni harshi kowa yafita hankalinsa, dan idonmu yarufe bamusan mi Muke aikatawa bama.

Hankalina bai nemi dawowa ba saida naji Galadima na neman kasheni, duk da inajin lokacin dayake jero addu'a amma ban dawo dai-daiba, nayi nisan da banajin kira kam, saida mai gayya mai aiki ke shirin faruwane na farga.

Ina yayi Nisan da bazaiji kiranaba balle kuka da magiyata akan karya cutar dani, yatuna alk'awarin daya d'auka please, baimasan inayiba, duka, cizo, yakushi, babu kalar da ban masa ba, amma bawan ALLAH nan saida yamin biji-biji, dukkan fushinsa na shekarun baya saida ya fanshe a wannan daren.

Nayi kuka harma ba'a jin sautin fitarsa, a jama'ar gidanmu kuwa ai mutum d'ai-d'aine ban kiraba, duk tsanar innaro danayi ranar saida nakirata ta taimakeni (>�#�Munaya anga idi=��).





&&&*&*&*&&&





A can kuwa muftahu Na fita sukaci karo da Harun, kallon-kallo akama juna, cikeda tsantsar mamaki Harun yace,  wai Muftahu mikake shiryawa ne? .

Kallon rainin hankali muftahun yamasa, yagyara tsayuwarsa yana wani murmushin da bakowa zai iya fassara Shiba,  ban fahimci tambayar takaba, amma mikake nufi? .

Harun ya d'an hararesa,  Muftahu karka rainamin wayo, tabbas nasan ni da kai duk abokan Galadima ne, bayan zumunta dake a tsakaninmu, amma shige masan dakake fiye da kowa a wannan tsakanin yana bani mamaki .

Muftahu ya ta6e baki yana wani basarwa, kafin ya kalli Harun a wani yanayi,  Harun kana sakamin idone kenan a al'amurana? humm bazance ka bariba to, kacigaba, ni da kai d'an halak ka fasa, idan kaga dama ka kunna wutar jefani bayan kaga abinda zanyin, wannan ba damuwata baceba, inar Na cimma burina right? .

yana gama fad'ar haka yabar wajen kawai. Yayinda Harun yabishi da kallo kawai tamkar wani soko, a zuciyarsa yana tunanin mi Muftahu ke shiryawa ne akan Galadima? tun kwanaki yakeson fargar da Galadima illar kusanta Muftahu a jikinsa, amma abin kamar wani tsafi, da Zarar sun ke6ance da Galadima to saikaga Muftahu a wajen, saikace mai gani har hanji, kenan yakamata yasake shiri akan Muftahu?.

Da wannan tunanin shima yashige mota yabar gidan, saikuma Galadima ya fad'o ransa, waya ya d'auka ya kirashi, amma saiyaji Number busy, hakanne yad'an sakashi nutsuwa, a tunaninsa ko Galadima yana wayane dasu Momma. (A time d'in Munaya Na waya da phone d'in Galadima).





&&&* * & * *&&&



Yanda ta tashi a firgice haka shima ya tashi, jikinsa ya jawota ya rungume saboda waige-waige da takeyi tana kwala kiran sunan MUNAYA!.

jinta a jikinsa saita d'an sami nutsuwa, cikin kuka tace,  yaa marwan mike faruwa da 'yar uwata ne?, nayi mafarkinta cikin mawuyacin hali tana kuka da kiran sunana Nazo Na ceceta .

 sorry baby, ki kwantar da hankalinki mafarki ai ba gaskiya baneba, maybe shaid'anune kawai suka taswuranta hakan a gareki, amma ba d'anzun kuka gama wayaba? kofa awa 5 ma ba'ayiba da gama wayar taku? .

 hakane yaa marwan, amma acikin awa 3 wani Abu bazai iya faruwa ba? ka kiramin ita please naji? .

 no kiyi hak'uri, dare yayi gaskiya, babu yanda za'ayi mu kirata a wannan time d'in, k'arfe 1 fa ta wuce, 2 ma saura, karkuma ki manta tanada miji itama yanzu. Muyi addu'a ALLAH yasa alkairine, da safe saiki kirata ko? .

Cikin share kwalla ta d'aga masa kanta, a hankali ya kwantar da ita a jikinsa bayan shima ya kwanta, yad'an furzo huci kafin yakai hannu yana shafa kanta tareda sumbatar goshinta yacigaba da bubbuga bayanta a hankali, kowa yana yin adu'a, ahaka barci ya kwashesu, duk da sun dad'e basu koma ba, musamman ma Munubiya da mafarkin yak'i barin ranta, Dan takasa yadda Munaya Na cikin k'oshin lafiya gaskiya, ka wai dai dan batada yanda zatayine ta hak'ura.





*****&&&*&&&****





Hawaye kawai nake iya zirarwa, amma kwakwkwaran numfashi bana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login