Showing 318001 words to 321000 words out of 365757 words

Chapter 107 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1500

damma akwai madogara Na business kala-kala da koyaya asiri zai rufu.



Yauma suna asibitin, Dr Erfan Fahad ya shiga wani aiki, Galadima ne kawai zaune a office d'in cikin k'ananun kaya, yana zaune a kujerun dake cikin office d'in daga can gefe, k'afarsa hard'e bisa teble d'in tsakkiyar kujerun, ya d'ora laptop yanata aikin Company daya zamana saita nan, harma Na Hukumarsu dake nan Nigeria, wato (DSS). Idonsa Na saye cikin medical eyeglasses mai haske, sosai yayi zurfi a aikin, alokacinne kiran Munaya ya shigo wayarsa, amma yay burus yacigaba da aikin tamkarma baijiba harta yanke, kuma kira Munaya tayi, nanma yak'i d'auka.

Bata gajiba tacigaba da damunsa, cikeda jin haushi ya kalli wayar yana jan tsaki, mamaki ya kamashi ganin Number d'in dabai saniba, baima ta6a ganiba, yanzunma harta yanke bai d'aukaba.

Idon Munaya harya fara tara kwalla.

Cikeda Damuwa takuma kira, shikuma ya d'auka cikeda k'uluwar an dameshi.

Kawai saita sakar masa kuka.

Kasa motsawa yayi, Ya kuma kasa magana, Munaya tace,  Ni zakama wulak'anci ko? Shikenan sai anjima .

Zaiyi magana k'itt ta yanke wayar. Kansa ya dafe yana fad'in  O ALLAH my mata bansan ke baceba . Kiranta yayi amma tak'i d'auka harta tsinke, saida yakuma kira sannan ta d'aga, itama tana gab da katsewar, harma ya fidda ran bazata d'agaba.

 Shikenan kin rama ko? . Ya fad'a a hankali cikin taushin murya da nuna kulawa a gareta.

Munaya ta d'an tura baki kamar tana ganinsa, amma batace komaiba.

Ya murmusa yana ajiye lap-top d'in ya sauke k'afafunsa.  Kinga bara Na kiraki video call, gara naga dai ma ya kika koma .

Bai jira cewata ba ya yanke wayar.

Dad'i sosai ya kamani da jin k'arin k'aunarsa, Wanda ban ta6a tunanin kalloma zan isheshiba shine yake damuwa idan Na damu..........

Kiran ya katsemin tunani, Na d'aga amma saina saka hannuna Na kare idona, bakina da rabin hancina kawai yake gani.

 Haba my mata please mana, ko saina miki kukane? .

bakina nad'an motsa da turashi gaba kad'an alamar eh.

 Humm kinga duk randa Na kama bakinnan zai min bayani dalla-dallane .

Cire hannuna nai babu shiri ina kallonsa, ya kashemin ido d'aya.

Nai k'asa da idona ina fad'in,  ALLAH ya shiryaka, nidai babu ruwana .

K'asaitaccen murmushinsa yayi yana gyara zamansa,  Anya kina missing d'ina kuwa? .

Fuska Na marairaice masa kalar tausayi, nace,  sosaima kuwa .

 uhmyim to inga idon .

d'an kwalina naja Na rufe fusakata ina dariya.

Yace,  Nifa wannan kunyar a ringa ajiyemin ita gefe sai ina buk'atarta, ina my children's? .

 Nayi k'yautarsu . Nayi maganar ina bud'e fuska.

 Dakin birgeni, kinga danazo tun anan saina tanajin wasu abin cikin kwan .

Share zancen nai kamar ban fahimtaba, nace,  yaushene zakazo to? .

 Kina missing d'inane? .

 Sosaima ALLAH kuwa .

Dad'i ya kamashi, cikin lumshe idanu yace,  ina tafe soon, sai kunyi kwana 5 sannan zazo nayi kwana 1 mu dawo Nigeria ki tattaro kayanki miyo gaba .

 To ALLAH ya kaimu, ya jikin Abiena? .

 Abienki nata samun kulawa Alhmdllh, muna kuma hango nasara sosai, Dan Abokina yasan aikinsa sosai  .

 Alhmdllh, ALLAH yasa iyakar wahalarce tazo, muma muga Abie d'inmu Na tafiya da k'afafunsa, yadawo k'asarsa ta haihuwa inda mak'iya basa son zamansa, bak'inciki dukya kashe shegu .

 ALLAH ya tabbatar my Queen, guntsamin mana, Yaya kuka iske Niger d'in? .

Cikin tsumud'i nace,  karkad'e kunnenka kasha labari yalla6ai .

 Na karkad'e da k'yau yalla6iya .

Cikin Nutsuwa Munaya ta shiga zayyane masa komai, tun yana al'ajabi yakoma mamaki, Yakoma tausayi, ya koma murna da nuna tsantsar farinciki.

Yace,  ALLAH Sarki innarmu, Ashe ita jinin girmace, shiyyasa ta kasance mai dattako, lallai yanzu Na fahimci ina kika kwaso halinnan naki, dama nadad'e ina tunanin anya baki shafi jinin masu sarauta ba, jan ajinki da son girma yayi yawa .

 kai ba'ace naka yayi yawaba sai nawa? .

Murmusa yay yana shafa girarsa d'aya. Yace,  toni minayi kuma? .

 Ai idan zan lissafo maka sai kud'inka sun k'are ban gamaba .

 Sheri dai zakimin kawai yalla6iya, inasu Abdurrahman wai? .

 Tab ai wad'annan inba yunwa sukejiba ganin su wahala yakemin ni kaina, ai saikazo kawai kadai sha mamaki, duk yanda zan musalta maka a yanzu hasashe kawai zakayi .

 Ina tafe insha ALLAH, koma Dan Na d'akko matata Na gudo, amma yanzu kam dole saina nema izinin shigowa .

 Meyasa? .

 Kinta6a ganin jinin mulki yashiga wata masarauta bada neman izini ba? Hakan tilas ne, yak'e-yak'en dake faruwa a masarautu yakawo wannan sharad'in, zuwa yanzu kuma yazama babbar Al'ada mai k'yau .

 Lallai, to yanzu tayaya zaka nemi izinin? .

 Zaki gani bari lokaci dai yayi. Yanzu mizan samu Na rage zafi? .

Cikin salon narkar dashi Munaya ta juya idanu tana fad'in  Mikakeso? .

 Gaba d'ayanki wlhy . Ya fad'a cikin marairaicewa.

 Indai nice dama takace ai Muhammad Sameer .

Lumshe idanunsa yayi yana cije lips, yaune ranar farko daya ta6ajin sunansa a bakinta,  Please sake fad'a naji .

 Mid'in? .  Nafad'a cikin d'an waro idanu .

Ya wani marairaicemin kamar k'aramin yaro, yana k'ank'ance idanunsa da suka sauya kala. Yace,  Sunana .

Yanda yay maganar cikin sanyi da kasala saida tsigar jikina ta tashi, kamar yanda ya buk'ata nakuma maimaita masa a kasalance.

 My Queen ina k'aunarki da yawa, zan tabbatar miki hakan randa kika dawo gareni, jinake duk duniya nafi sauran maza morewa da samun nutsatstsiyar mace mai tarin baiwa da tarbiyya, Har abada Na mallaka miki Muhammad Sameer da komai nashi, ki yi yanda kikeso dani my Heartbeat .

Kwallan farin ciki ya cikamin ido. Nace,  My king tukwiycin wannan k'yauta sai ina kusa dakai, Dan tsadarta yakai tsada, tukwiycinta mai girman darajane, kuma zan mik'ashine gamai daraja, dolene yakasance a waje mai daraja, ba Kaine kaima sauran maza zarraba, nice, ni Munaya ninaima sauran mata fintinkau wajen yin dace da samunka a matsayin miji, Uban y'ay'ana, Masoyina, cikon farincikina, I love you so more irin wadda bata k'arewa d'innan har a Aljanna....

 Na gode Uwargidana a Duniya da Aljanna, kece shugabar Matan Muhammad Sameer anan duniya, kuma kece a Aljanna insha ALLAH, ALLAH yayi miki albarka wadda bata yankewa keda gudan jinina .

Hannuna naima kisses uku Na hura masa.

Ya wani lumshe idanu yana dafe k'irjinsa alamar sak'ona ya isa.

Wata dariya mai ida kashe jiki murus nayi masa, aiko saiya zame ya kwanta kawai cikin kujerar yana kifa wayar a k'irjinsa ya lumshe ido.

Nakuma bashi wani kiss d'in mai k'arar sauti, babu shiri ya d'auki wayar da Sauri saidai kitt Na yanke kiran ina dariya.

Nima zubewa nayi a gadon k'irjinna Na dukan goma-goma, dayasan tsiyar da Na shirya masa dabai yarda dani hakaba=��>�-�.

Dariya kawai da tafi naji akaina, nai saurin bud'e ido, sainaga Ayusher, Munubiya, da Feena akaina. Hararsu nayi ina juya fuska can gefe da fad'in,  y'an sa ido, Uwarmiye aka biyoni? .

Ayusher tace,  Yo k'arshen munafurci da cika baki mukazo gani, yaudai munga abinda ake 6oye mana da cika baki . Suka kwashe da dariya suna tafawa.

Banza namusu.

Feena tace,  Aini wlhy dama tun a asibiti nace muku gayunnanfa sun d'inke, wuya tayi wuya SIRRIN ZUCIYA ya fito fili, sun gama cika bakin da jan ajin, shi k'asaita da mulki, ita jan aji, Ashe harda Mulkin bamu saniba. Kai kusamana wak'a muyi murnan K'ulluwar k'auna .

Ayusher ta saka wak'a a waya suka ko dage suna tik'ar rawa..

Dariya suka bani wlhy, nace,  y'an iska kwadaiji da munafurcinku wlhy, nan gani nan bari dai Munafuncin su innaro ..

Aiko mi zamuyi inba dariyaba gaba d'ayanmu, nikaina Innaro d'ince kawai tazomin abaki ban shiryaba.





**********



Washe gari aka gudanar da bikin tarbarmu, Wanda yay matuk'ar k'ayatar damu da sakamu farinciki, munga al'adun daba namuba, su innarmu ansha shiga ta alfarma suda su Abba, Saiga su Abbanmu da sarauta, wai tunda sune mazajensu innarmu anbasu wata sarauta domin girmamawa agaresu, hakama Yaa Marwan, dad'i tamkar zai kashemu, aiko munsha hotuna da nuniya wajen jama'a.

Gashi ni banda ma sakewa, saboda yanzu banason hayaniya mai tsanani kusa dani, da za'ayi kid'a ma sai wajen nabari tilas, dama hayaniyar mutane da surutai harta fara sakani ciwon kai.

Da Galadima ya kirama sai Munubiya ce ta kar6a, ta sanar masa halin danake ciki, duk saiya rikice, yaringa rok'on Munubiya ta kula masa dani sosai.





******



Kwanakinmu 7 da zuwa cif mukaga anata hidimomi a masarautar, kasa shiru mukai saida muka tambayi dalili, su Badeera suka sanar masa wai wani d'an Sarki ne zaizo dana k'asarmu ta Nigeria.

Mamaki ya kamani, to wanene wannan? Dan nidai ko a jiya munyi waya da gadima kuma baicemin zaizoba, hasalima yana India, tunanin bashi bane ya sakani kauda zancen araina muka cigaba da hidimominmu.

Yanzu kam a masarautar babu inda bamu saniba, Dan kulum su Badeera cikin zagayawa damu suke, har cikin gari saida muka fita sau wajen uku, gaskiya Agadaz tanada abubuwan k'ayatarwa da Tarihi, hotuna kam ai yinsu muke tamkar babu gobe.



Su Hajiya Innaro dai kam an nutsu, ni harma tausayi tafara bani wlhy, Dan haka muka rage iskancin da muke mata, yanda ake bata kulawa da girmamata kawai a masarautar ya isheta kunyar abinda ta aikata, (lallai babu Abu mafi dad'i irin ka sakama mai jifanka da sharri da tarin alkairi) wlhy har Abadan bazai sake sukuniba a gabanka saboda d'unbin kunya da nadama dazata addabi zuciyarsa, Dan kullum zai kasance cikin tsarguwa da tsangwamar kansane. Kunga dai yanda innaro ta kasance a yau.=��>�7�<���
@&



Sai wajen la'asar sakaliya labari yazo mana wai d'an Sarki nan ya iso, bushe-bushen algaitu irin nasu kawai dake tashi ya tabbatar mana da lallai yazo d'in.

Cikin mu babu Wanda ya maida hankali akan lamarin, danni kwance ma nake Na kifa Absurraheem saman cikina yana barci, Feena da Deejahma suna gefena zauna suna kallon hotunan da mukayo ayawon jiya da muka fita, su Munubiya kam Na tsakar d'akin suna hira da sauran y'ammatan, Ayusher nama Zuhuriyya kitso, Wanda anayi yana warwarewa saboda gashin akwai santsi, sai wata dabara sukeyi a k'arshen kitson.

Bayan sallar isha'i saiga mama Rabi'a ta shigo d'akin da muke, duk muka gaidata, fuskarta d'auke da Murmushi ta kalleni ina canjama Amaturrahman kayan barci dan an musu wanka.  Munaya ta shi kiyi wanka yanzunan .

Da mamaki nace,  wanka kuma mama? Lafiya kuwa? .

 Lafiya lau, kedai ta shi kiyi, bama Maryamu ta k'arasa shirya Amaturrahman d'in .

Nidai duk al'ajabi ya kasheni, ganin duk yawan y'ammatan dake d'akin ba'ace kowa yatashi yay wankaba saini, suma dai Kansu kallon mamaki sukemin ni da mama Rabi'a d'in. Hannuna ta kama muka fice zuwa wani d'akin.



Cikin bayin gidan d'aya ta had'amin ruwan wanka, dama tunda mukazo komai yimanashi akeyi. Mama Rabi'a tacemin  Kinutsu kiyi wanka mai k'yau wlhy, inba hakaba dakaina zan canja miki wani .

Mamaki kuma kasheni yayi, nadai nutsu nayi wankan fiyema da yanda take buk'ata, ga ruwa nata tashin mayataccen k'amshi, dan wannan masarauta sunsan sirrin k'amshi kam, akwanaki 7 d'inan har turare yafara zaunawa a jikinmu saboda bala'in yawan amfani dashi, motsi kad'an sai ahau tiraraki da turarurruka iri-iri.

��

Nafito Na iske Ayusher Na jirana wai zatamin kwalliya, zanyi gardama saiga mama Rabi'a ta shigi, dole Na zauna akamin simple, nikaina nasan nayi k'yau, kayan da aka bani Na sanya saida Na kallesu Na sake kallo, dan lafayarsuce ta buzaye datasha wani d'inki mai k'ayatarwa, aka d'oramin bak'ar alk'yabba tamkar ta larabawa, tasha golden d'in aiki daga sama har k'asa, a bud'e take dawasu igiyoyi biyu, can sama dakuma tsakkiya. Nidai narasa bakin magana, dan turarema har neman hawarmin kai ya fara, kai nidai a raina nafara tunanin ko tsafi za'ayi danine. Sai gulma muke da idanu ni da Ayusher, dan babu damar yi a fili ga mama Rabi'a a d'akin.

Hannuna ta kama muka fito, aka had'ani da bayi uku nabin bayana, sai ta hud'un a gabana tana mana jagora, masarautar tayi tsit babu yawan hayaniya, saboda d'an Karen sanyi da ake zubawa, kowa ya shige ciki sai d'ai-d'aiku dake kai kawo.

Wani sashe dakecan gefe shima mai k'yau muka Isa, munsha zuwa ta wajen amma bamu ta6a shiga cikiba, Baiwar tayi sallama, dukda ba'a amsaba ta shiga, mukuma muka cigaba dabin bayanta.

K'aton falone mai tarin k'awa da tsari, Wanda ke tabbatar maka a gidan sarauta kake, ganinai duksun durk'ushe k'asa, Na bisu da kallon mamaki sannan Na kalli inda suke fuskanta...................
'<���













ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���











=ء�HASKE WRITERS ASSO....





f&RAINA KAMA...!!f&

(Kaga gayya)





Bilyn Abdull ce>��<���





BOOK 3 =�I�<���2� 4�





.................A hakimce yake kishingid'e saman lallausan dardumar data k'awata k'yawun falon, Rabin jikinsa duk akan tum-tum, gabansa da butar shayi ta buzayen asali, gakuma mitsi-mitsin kofuna saman wani k'yak'yk'yawan tire k'arami, gefe Bowl ne Na glass cikeda kayan itatuwa, saikuma kwanika 4 dake rufe Wanda bansan minene a cikiba, gefensa yaransa ne duka ukun kwance duk nad'e cikin showals, yanda nake binsa da kallon mamaki haka shima yake bina da kallon mamakin canjawa da k'ayatarwar da shigar ta k'aramin.

Sudai bayinnan sun lalla6a tuni sun fice abinsu.

Cikin d'age gira ya sakarmin Murmushi yana min nuni da hannu wai nazo gareshi.

Tamkar mai tsoron a kamata tana satar naman miya haka nake tafiya garesa, dan kallon da yakemin ba k'aramin haddasamin kasala da sanyin jiki yayiba.

Na k'arasa gabansa ina zama a kasalance, zaman danayi ya kalla, ya min jinjina irinta saraki=�M�<���.

Kallon kaina nayi nima, dan banga minayi ba dahar za'amin wannan jinjinar.

Cikeda k'asaitarnan tasa yace,  Kallon fa? .

Ajiyar zuciya Na sauke, dan narasa bakin magana, ya tashi zaune sosai yana janye tum-tum d'in dake a tsakkiyarmu, ya matso jikina sosai yana wani shinshinata da lumshe idanu, murya a sark'e yace,  Amaryar Muhammad Sameer wannan k'amshin yayifa 100% .

Yanda yay maganar a dokin wuyana saida tsigar jikina ta tashi, cikin magana d'ai-d'ai nace,  Wai dama Kaine d'an Sarki da aketama wannan shirin? .

Murmushi ya saki, ya matsar da bakinsa saitin kunnena a wani salo yace,  koban cancantaba ne? .

Kaina Na girgiza masa alamar a'a.

Ya kuma shigewa jikina sosai,  Wai miya kashe bakin tsiwarne haka yau? .

 Mamaki mana .

 To miye abin mamakin? Ni d'in ko zuwan nawa? .

Nace,  Duka .

Wani miskilin murmushi ya saki, ya lalubo hannuna dake 6oye cikin alk'yabbar ya saka nashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login