Showing 351001 words to 354000 words out of 365757 words

Chapter 118 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1453

Alk'yabbar dazai sa nagama feshewa da turare sannan na matsa ina kwantar masa da sajensa dayasha gyara da cumb, shikuma yana saka link d'in hannunsa.

Kusan tare muka gama, na kama hannunsa na d'aura masa agogon dabai San da shiba.

Da mamaki ya kalleni amma saina janye idona ina murmushi da fad'in  Happy salla nane nida triplets d'inka .

Rasama mi zaice yayi, sai kallon agogon da koshi da kansa iya mak'urar za6ensa kenan. Yakai hannu zai rik'oni nai baya kad'an ina girgiza masa kai, Dan nasan makomar rik'onin.

Cikin marairaice face nace,  please kabari saika dawo kawai .

Wani miskilin murmushi yayi yana cije lips.

Nima na murmusa da nuna masa Alk'yabbar.

Kansa ya girgizamin a hankali yana mai shafa agogon Dana d'aura masa da d'ayan hannunsa.  kibarta zasumin nauyi da yawa, idan zamu fita gaida Governor zan saka .

Ido d'aya na kashe masa da had'e yatsuna=�L�<���alamar yayi.

Ya murmusa shima yanamin jinjina=�M�<���.

Ban barsa ya fitaba saida namasa photo biyu, sannan na rakoshi har falon k'arshe, inda Muftahu da Matawalle ke jiransa, suma sunsha wanka mai birgewa, tamkar ka sacesu ko anguna ranar aurensu.

Galadima ya kareni da bayansa tareda min alamar na koma. Baya buk'atar su ganni kenan. Nima saina juya ciki kawai. Yayinda nake jiyosu suna masa Sheri da kod'a wankan nashi.



Na lek'a yara naga barci sukeyi, Dan haka na koma kitchen muka cigaba da aikin da fatan mu kammala akan lokaci.



Tunda matasan samarin masu d'anyen jini suka fito sai kallo ya koma sama, bayi sai zubewa suke suna gaishesu, sukam sai d'aga hannu dad'an murmushi.

Haka kawai sai Galadima yaji kewar Harun, aduk irin wannan ranar shike zuwa ya fiddoshi daga sashensa, amma yau gashi bak'in halinsa yasa a gidan yari zaiyi tasa bikin sallar dagashi har ubansa. Ya k'aunacesa saboda ALLAH ashe shid'in ba haka bane a tashi zuciyar.

Motocin da aka tanada domin su suka shiga.

Wambai da talba haushi ya kamasu, ganin wai yau d'an uwansu matawalle ne zai tafi salla tareda Galadima.

Oho, daga matawallen har Galadima basusan sunayiba.



A 6angaren Abie da mai martaba shiga sukayi iri d'aya, Abie ya fito a ainahin sarakinsa na asali, sai rama wadda kayan jikinsa suka 6oye, idan ka gansu bazaka ta6a banbanta wanene sarkin ba.

Mai martaba ya fito rik'eda hannun d'an uwansa Abie, nanfa aka fara ruwan cameras dukda dogarai na karewa ma, cikin lullu6esu da manyan riguna da musu kirari da busar algaita suka shiga mota d'aya.



Masallaci yacika mak'il da al'ummar manzon ALLAH (s.a.w), isowar Sarki da tawagarsa kawai ake jira.

A dai-dai k'ofar baya ta musamman motarda ke d'auke dasu Abie ta tsaya, mai martaba ya taimaka masa ya fita suka shige cikin massalaci.

Nan take aka d'auki kabbara bisa umarnin liman domin nuna godiya da al'ajabin hikimar ubangiji na dawowar tsohon Sarki cikin k'oshin lafiya, bayan tsahon shekaru daya d'auka baya k'asar. Duk matashin dake k'asa da shekara talatinma bai sanshiba.

Mak'iyan 6oyefa da sukaga tabbas sai tsoro ya kamasu, ashedai zancen daya karad'e gari gaskiyane, yau ga Sarki Saifudden Abubakar a gabansu ko sunaso ko basaso kuwa.



An gabatar da Kud'uba tamkar yanda addini ya tanada, mai ratsa jiki da 6argo, mai k'arama muminin kwarai imani da tsoron ALLAH.

Su Galadima suna jerin sahun farko, saidai na kusada su Abie ba.

Alhmdullah, sallar idi ta gudana bisaga farincikin kasantuwar bayin ALLAH wannan rana da ko yaro k'arami ke d'okantuwa da zuwanta, bare su Galadima da jama'ar masarautar gagara badau da farin cikin ya had'e musu biyu.

Bayan idar da salla akaja addu'a mai tsayin gaske ga Abie, sannan aka bashi microphone daga zaune yay bayani mai gamsarwa da ratsa jini da jijiyoyi Wanda yasaka mafi yawan jama'ar dake massalacin hawaye.

Hatta da Galadima k'asa kawai yayi dakai yana murmushi da share hawayensa da handkerchief.

Yau dai kam ai saida aka kai kusan 11:30 a massalaci kafin a sallami jama'a.

Yayinda manya kuma suka samu yin gaisuwa ga Abie da masa murna da addu'a.



A can kuwa jama'ar gari kowa ya gumtsi labari yatafi fesarwa, hakama y'an jarida masu zuwa kallon zahiri, kafin kace mi labari ya cigaba da shiga lungu da sak'o, hakama hotunan Abie da nasu Galadima.

Bisa ga wannan labarine su Ahmad tahowa Masarauta dukda basuda tabbacin ganin Galadima d'in.



K'arfe 12 aka shirya liyafar cin abincin a masautar, wadda har governor zai halarta, itace madadin hawa da akeyi zuwa gaida Governor.

Duk yanda Galadima yaso komawa ga iyalansa hakan ta gagara, yawan jama'a ya hanashi matsawa konan da can, kowa soyake ya nuna masa kansa a jerin masu tayasa murnar dawowar mahaifinsa cikin k'oshin lafiya.





****



Alhmdllh munsami kammala komai, Na barma su Umimi sauran aikin suka k'arasa, niko nanufi tsaftace jikina kafin mijina ya shigo, dukkan abincin da za'a fita dashi kuwa nabama su Umimi umarnin kaisa duk sashen daya dace.

Galadima daya tuna da batun abincin da Munaya keyi yad'an fita daga cikin mutane yana kiran sarkin Mota, Umarni yabashi akan zuwa birnin gayu ya kar6o drinks wajen manager, yanason kiran Munaya amma babu dama, Dan dawuyama idan ta maida layinta Na 9ja bisa waya, gashi bashida damar tsallakewa ya taho gareta.





****



Sosai Momma take samun tattali ga mama Fulani, ita abinma mamaki yabata, saida aka sakko idi sannan aka kaita sashe Na musamman da akayi aikin gyarawa da safiyar, zasu d'an zauna anan itada Abie kafin asan abinyi gameda sarautarsa dake kan d'an uwansa.

A tsorace mama Fulani take, dukda kaffa-kaffa da take dasu Momma, ko kad'an batason mulkinan yabar hannun d'anta, har yanzu burinta jikokinta su gaji masarautar gagara badau.

Amma dai taita danne zuciyarta Dan karta nuna hali.





******





Bayan mai martaba da Abie sun huta aka fara gudanar da liyafar cin abincin a babban d'akin taro Na masarautar.

Wanda yasamu halartar manyan mutane dake cikin binin, duk wani mai fad'a aji ya garzayo masarautar Dan kar ayi babushi, kokuma ya shiga black list.



Matawalle ya kalli Galadima dayak'i cin komai sai drink yake sha.  Lafiya kuwa Sameer? .

Galadima ya kallesa da alamar tambaya, amma baice komaiba.

Da hannu Matawalle ya nuna masa abincin gabansa.

Murmushi Galadima yayi yana shafa kumatunsa, cikeda k'asaitarnan tasa yace,  Bazaka gane bane d'an uwa, my mata tayi abincin salla, idan naci wannan cikina ya cika naje can kuma babu space ai sai a hanani....... . Sai yay shiru bai k'arasaba.

Mi Matawalle da Muftahu zasuyi inba dariyaba, har mutanen dake d'an gefensu suka juyo suna kallonsu.

Galadima kam murmushi kawai yayi ya maida eyeglasses d'insa a ido yana kallon inda su Abie ke zaune.



Anci ansha kowa yay mak'il cike da godiyar Ubangiji, daganan aka fara gudanar da jawabai Na godiya ga ALLAH bisaga ni'imar dawowar Abie.

Mai martaba shine ya fara, sannan Abba hayatudden.

Maganarsu ta ratsa zukatan mutane da dama, domin sun nuna k'auna mai yawa da farincikin dawowar d'an uwansu, hakan ya k'ara musu kima, dan sunture zancen nan Na mutane a zuciyarsu, wato y'an ubanci dayafi komai ruruta wutar k'iyayya a masarautunmu Na Hausa Fulani.

An buk'aci ganin Galadima shima.

Ya mik'e cikeda takun izza da zagayawar jinin Mulki a dukkan sassan jikinsa, k'asaita da kwarjinin yarinta Na d'awainiya dashi. Yanda akaita zubama su mai martaba hototuna shima hakanne. Da yawan mutane dake wajen ya burgesu, koda haushinsa kakeji kwarjininsa ya Isa jin ka k'aunacesa lokaci d'aya. Ya gyara tsayuwarsa yana wani k'asaitaccen murmushi mai tsada da nuna halin dattako, cikakkiyar sallama ya musu suka amsa, sannan yacigaba da magana yana zare eyeglasses d'insa.

Hawaye cike da idonsa yace,  A watannin da bazasu cika shekara ba Na tsaya a gabanku kamar haka ina kuka da kausasan kalamai ga dukkan mai hannu a ciwon mahaifina, a ranar d'aurin aurena hakan ta faru, nasan kuma dayawanku dake nan suna a wancan zaman, sai dai bisa ga hukuncin Ubangiji yau nine tsaye a gabanku ina kukan farinciki da tausasa harshena Na Neman afuwa, na godema Ubangiji da yaymin dukkan sutura ta rayuwa, ina fatan samun ta gaba inda yafi gidan duniya, badan nafi kowaba yaymin wad'anan ni'imomin, sai Dan hak'uri da juriya da kar6ar k'addara aduk yanda tazoma bawa, bara nabaku wani labari kad'an, Wanda yana d'aya daga cikin babbar riba dabazan manta da itaba har k'arshen numfashina. Doctor Arjun shine likita na farko daya fara duba Abie, shine kuma yacigaba da kulawa dashi har nakai wayo, shi mabiyin addinin Hindu ne, sanann daga wannan k'abila ya fito, shekarar dazan shiga jami'a sai ALLAH ya jarabcesa da ciwo rana tsaka, yanama cikin aiki a asibiti ya yanke jiki ya fad'i, y'an uwansa doctors sun bashi dukkan taimakon gaggawa harya farfad'o, a daren ranar saiya buk'aci d'aya daga cikin doctors d'in daya kira masa ni. Ina tare da Momma da Jakadiya kiran ya iso gareni, munyi mamaki kwarai da gaske, dan bamu dad'e da duboshiba, lokacin salla dayayine yasakamu baro d'akin dayake ma. Haka Na tashi natafi amsa kiransa. Awajen doctor Arjun Na iya yarensu na Hindu, tunda Na shigo saiya shiga muk'omin hannu alamar nazo garesa, nabi umarninsa Na zama kusa dashi tareda rik'e hannayensa cikin nawa, muryarsa cike da rauni yace___ .

 Sameer Kasan miyasa nace a kiraka kuwa? .

 Kaina na girgiza masa alamar a'a. yayi murmushi idonsa Na cigaba da tsiyayar da hawaye, yakuma damk'e hannuna a cikin nasa yana cigaba da fad'in___ .

 Sameer kune Muslims na farko dana ta6a mu'amulla mai tsayo dasu, daga gareku na fahimci wasu k'yawawan halaye da kullum duniya kefad'in baku dasu, lallai duk mai ambatar wannan addini da addinin y'an ta'adda ya jahilci fahimta da sanin halayyar d'an adam, kun kasance masu hak'uri wajen samu da rashi, kar6ar rayuwa a dukkan halin data zo muku, kun kasance masu yawan k'yautata zato, mutane da yawa sunsha zuwa duba mahaifinka, amma duk d'unsu ban yarda dasuba amma Ku sainaga babu wani kokwanto a Kansu, da zuciya d'aya kuke k'ar6arsu da mu'amulantarsu, dukda zukatanku sunada yak'inin dolene a samu mugaye a cikinsu, a duk daren duniya idan nashiga duba mahaifinka nakan iske mamanka tana salla ko karatun littafinku, ahankali sai wad'annan abubuwan suka fara kwad'aitamin wani abu daban, tun ina kokawar turewa harya fara zama babban 6angaren tunanina dayay tasiri mai girma a dukkan kuzarina, da farko tsoro nakeji, Dan kaf ahalinmu babu wani mabiyin addinin musulunci ko kiristanci. Amma kasan duk miye matsayar wannan labarin danake baka a yau? .

 kaina Na girgiza masa jikina a sanyaye, yayd'an murmushi da cigaba da fad'in__ .

 Inason biyan ko nawane domin Shiga addininku, a yau bana tsoron kowa yasani koya ganni a ciki, inason ribantuwa da k'yawawan halayenku .

 A lokacin kunsan miya faru? .

Jama'a suka amsa da a'a. Galadima yay murmushe da share hawayensa da Handkerchief.

 Na tsinci kaina cikin zumud'i da firgici dukda k'ananun shekaruna, Dan lokacin bazan wuce 17years ba nake tunani, hawaye Na zuba a idona nace da gaske zaka musulinta Doctor?. Cikim jinjina kai ya tabbatar min. Ban tsaya 6ata lokaciba nace doctor addinin musulunci ba'a biyan ko sisi domin kasantuwa a cikinsa, imani da ALLAH da yarda da manzonsa shine babban farashi mafi daraja a duniya. Yace to a ina zan samo imanin?. Nai dariya da fad'in ta hanyar ambaton Kalmar la'ilaha illallah muhammadurrasulullh. Yace to ya shirya. Duk da k'arancin shekarunan nawa baiyi Girman kaiba ya kar6a kalmar shahada yana mai jaddadata a harshensa har saida tari ya sark'esa, rikicewa nayi Na mik'e da nufin nemo doctor amma saiya hanani, yamin nuni dana bashi ruwa, haka nadawo na bashi ruwan, kur6arsa hud'u ya janye kansa yana fad'in___ .

 Sameer, tabbas yauce ranar tafiya koda shiri ko babu, ina rok'onka koda sau d'ayane ka gudanar da salla a kaina, sannan karka yarda wani d'an uwana ya san da musuluntata, badon komaiba sai Dan gudun tozarta ku, ka sanarma Anania ina matuk'ar k'aunarta, karta manta dani .

Daga nan ya shiga maimaita kalmar shahada yana wata irin zufa maiban tsoro, na rik'ice inata ambatar sunansa da girgizashi, sai kawai naga jikinsa ya saki. Sakinsa nai Na fita da gudu kiran doctor sai mukaci karo da Momma dataji shirun yayi yawa tabiyo sawuna. Rik'eni tayi tana tambayar lafiya?, jikina Na rawa nasanar mata abinda yafaru da Hausa. Dan nasan mawuyacine asamu maijin yaren a kusa damu, hanani kiran doctor tayi taja hannuna muka k'oma d'akin tana share hawen farin ciki Dana kewar Dr Arjun, tai addu'a mai yawa akan gawarsa sannan tace Muh'd zaka iya masa wanka?. Bak'aramin tsorata nayiba, jikina Na k'yarma nace Momma wankafa?, nidai tsoro nakeji. Ta dafa kafad'ata cikin k'aramin kwarin gwiwa tace yarona karkaji tsoro, tunfarko ubangijine ya za6eka ya k'addara Dr Arjun ta hannunka zai zama musulmi, ka daure ka cika masa wasiyyar daya barmaka ta sallatar gawarsa, Dan kasandai su ahalinsa ba irin wannan jana'izar zasuyi garesa ba, ina tare dakai kaji. Bisa Umarnin Momma da koyarwarta naima gawar Dr Arjun wanka, itakuma tana bakin k'ofa tanamin gadi, Ubangiji kuma saiya ara mana dogon lokaci harna gama na maida masa Uniform d'in asibitin a jikinsa, sannan na sallacesa ina kuka. Saida muka gama komai sannan muka fito mukabar gawarsa cikin d'akin, bamukoyi nisa da k'ofarba mukaga doctor ya shiga d'akin da hanzari, mintuna kad'an da shigarsa maganar rasuwar Dr Arjun ta fara Shiga kunnuwan Mutane. Wannan rasuwa ta matuk'ar ta6a zuciyata, har a yau d'innan da nake gabanku ina jinta, kuma ban gaza wajen yimasa addu'oin samun rahama ba .

Galadima ya share hawayensa dake zirara tamkar fanfo, ya kalli mutane yana fad'in  kakannina, iyayena, yayyena da k'annenna kunsan hikimar baku wannan labarin kuwa? .

Jiki a sanyaye, wasuma hawaye sukeyi suka amsa da a'a.

Galadima yay murmushi yana kuma share hawayensa da gyara tsayuwa,  Wannan labarin yana mana nuni muzama masu nagarta aduk inda muka tsinci kanmu, babu irin k'yawawan halaye da addininmu bai koyar damuba, amma son zuciya da burukan duniya saisu sauyamu, miyasa muke mantawa damu su waye? Ina kuma zamu koma?, dalilin ruk'o da gaskiya mahaifina ya fad'a hali mai tayar da hankali na tsawon shekaru, babu wanda ya ta6a tunanin sake ganinsa anan, amma kuma sai gashi, kunsan wane irin hali mai firgici da ciwo da muka tsinci kanmu kuwa? Mahaifiyata itace silar komawata jarumi, da taimakonta nazama jajirtacce, a halin k'uruciya har tunani nake anya kuwa tana sona? Ajiye sosayyar nan ta d'a da uwa tayi ta kutsani cikin talakawan daba yarena ba, ba addinina d'aya dasuba, ba k'asa d'aya muka fitoba, naringa wahalhalun koyon sana'oi da gwagwarmaya ta fahimtar rayu, ga karatu, ga damuwa da ciwon mahaifina, ban fahimci gata taminba saida na iya d'aukar nauyin ciwon mahaifina da hidimomin ahalina, na kammala karatuna bisa bigiren danake buri, iyaye mata wlhy kuzamto masu koyi da halayen mahaifiyata, matasa y'an uwana kuzama masu koyi da rayuwata, dukda ana ganina d'an ganta ban zauna gata yamin komaiba, saina tashi da k'afafuna da gumina na gina kaina, muzama masu k'yawawan halayya koda daraja martabar addininmu ga wad'anda basu fahimcesa ba, Dan k'yawawan hallaya da nagarta yaja hankalin Dr Arjun kwad'aituwa da addinin Islam, Yakuma mutu a cikinsa bisa amincewar ubangijin al'arshi, da mugayen hallaya mukeyi saidai doctor Arjun ya k'yamacemu dajin kuma k'yamar addininmu, son zuciyoyinmu shike maidamu bayan baya a Kullu yaumin, ba tarin dukiya ko gata ko k'yawune abin birgewaba, Nagarta, nagartar samun k'yawawan halaye da d'abi'u shi ake kira jarumta, matata ta ta6a fad'amin Hak'uri shi ake kira NASARA, saida hak'uri ake zama jarumi, sai an jure zafi ake tsintar kai a sanyi. Kusan shekarunta nawa kuwa?, ashirin, inhar mace mai k'ananun shekaru irin wannan tanada hikimar zance da nazari mai amfanar da wani irin haka miyasa tunaninmu ke d'aukar mace mai k'aramar kwakwalwane?, nabaku satar amsa kaje ka mu'amullanci matarka ta nagartacciyar hanya kaga yanda zaka amfanu da tagomashin tunaninta, kunga mata biyunan sun zamema rayuwata wata ginanniyar Katanga, mahaifiyata da kuma matata da auren shekara d'aya kacal zamu cika, kakata yayata k'anwar mahaifiyata rumface su dake kare martabata da zamana cikakken mutum, ina mai farin ciki mai tsanani da samun lafiyar mahaifina, da godiya mai yawa ga wasu ke6antattun mutane wadda gudunmawar suce silar ganina a gabanku, ALLAH ya albarkaci rayuwar ahalinsu ya cika musu burukansu na alkairi, Yakuma had'amu a aljanna gaba d'aya .




Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login