Showing 360001 words to 363000 words out of 365757 words

Chapter 121 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1458

na miye ba a masarautar, dama kusan kwanaki uku kenan bak'i nata sauka, ni dai harna kasa hak'uri na tambayi Galadima, yace, wlhy shima bai saniba.



Ana sakkowa daga massalaci sallar juma'a aka hana Galadima shigowa gida, papi ya umarcesa da zuwa ya zauna inda aka tanada dominsa.

Mamaki ya kamasa ganin gurin dank'am da jama'a, addu'a kawai aka gudanar papi yabada umarnin fara abinda ya tara mutane, daga baya koma mikenan jawabi zai biyo baya.

An umarci Galadima da tasowa zuwa saman daddumar dasu Abie da manyan sarakuna ke zaune, ya zauna a tsakkiya shidai zuciyarsa na faman tsitstsinkewa da bugun mamaki.



Turaki ya mik'e a tsanake zuwa gaban mai martaba Sarki Jalaludden Abubakar, yay gaisuwa tare da risinawa sannan ya zare rawanim dake kansa, gaba d'aga wajen aka d'auki kabbara, Abie yay k'asa da kansa yana share hawaye, shidai dan anfi k'arfinsane kawai, amma daba yanke wannan hukuncinba wlhy.



tuni bugun zuciyar Galadima ya k'aru ganin Turaki ya nufo garesa, zaiyi maganar papi yay masa alamar yay shiru>�+�.

Dole ya maida bakinsa ya tsuke yana had'iyar yawu da k'yar.

Tsohon Sarki Jalaludden ya taso da taimakonsa Turaki ya cire hular saman kan Galadima aka d'ora masa sabuwa dal, sannan aka fara nad'a masa rawani akai, jikin Galadima sai tsuma yakeyi, ya kafe papi da Abie da ido ko k'yaftawa bayayi, shikad'ai yasan a halin dayake ciki, zufa sai tsatstsafo masa take a kowacce mahudar gashi dake a jikinsa.

Tsaf aka gama nad'a masa rawani jama'ar wajen suka d'auki kabbara, yayinda za'a saka masa alk'yabba sai dogarai suka baza riguna ana masa kirari.

Galadima yay k'asa dakai idonsa na kwararar hawaye lokacin da kunuwansa ke jiyo masa jawabai daga bakin sank'ira.



 ALLAH ya d'auki rawani ya maida bisa kan matashi kuma adali tsohon Galadima a yau yazama Sarkin wannan masarauta ta gagara badau bisaga adalcin tsohon Sarki mai murabus a yau, masarautar gagara badau tayi sabuwar amarya, a halin yanzu Mai martaba Muhammad Sameer Saifudden Abubakar shine Sarkin wannan adalar masarauta, ALLAH ya tayashi rik'o, yabashi ikon koyi da k'yawawan halaye irinna manyan wannan gida .



Tuni waje ya harmutse da surutai, kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Galadima kam saida papi ya rungumesa a jikinsa sannan yafara samun nutsuwa, yayinda aka kawo Matawalle shima aka zaunar aka nad'a masa rawanin wazirci, shine zai zama wazirin d'an uwansa Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar.

Ai tuni guri ya rinca6e, babu maijin zancen wani, kafafen yad'a labarai da social media duksun d'auka, masu murna nayi masu bak'in cikin nayi, (kusan shigabanci, dolene kasamu masoya da mak'iya=�-�).



Mama Fulani da labarin ya Isar mata zarewa tayi, sai surutai take Wanda ba kowa ke fahimtaba, Gimbiya zulfah kuwa yanke jiki tayi ta fad'i wanwar, koda aka zuba mata ruwa ta farfad'o saita kama aman jini zuciyarta yariga ya buga.

Ba'a katse su papi daga abinda sukeba aka nemo doctor dazai dubata, saidai bata d'auki wani dogon lokaci ba tare ga garinku nan.



Haka duniya take, lokacin da wani ke zuwa sannan wani ke ficewa, hakanne ga gimbiya Zulfah, tatafi a randa Galadima ya zama Sarkin gagara badau.>�4�<���=��=��=�M�<���



Ni kaina da labarin zaman mijina Sarki yau babu zato ya zomin saina rikice, na rud'e, ganin lamarin nake tamkar tatsuniya ko mafarki, ga ciki, nama rasa murna zanyo ko kuka.

Ban fita a wannan magaginba saiga zancen halin da gimbiya zulfah take itada mama Fulani, saikuma ga abinda ya girgiza kowa shine mutuwarta.





***



Koda aka buk'aci jawabi daga bakin Galadima kasawa yayi, shifa ganima yake a mafarki komai ke faruwa, shima Matawalle ya kasa cewa komai, sai zirar da hawaye kawai sukeyi Wanda hakan ya birge kowa da bada mamaki.

Abubuwa sun rinca6e fiye da yanda bakwa zato a masarautar gagara badau, bayan an sallaci gawar gimbiya zulfah aka kaita makawancinta na gaskiya y'ay'anta na kuka da y'an uwanta.



Kiri-k'iri ganin mijina ya gagareni har dare, Abdurraheem sakin k'ulafucin Uba sai kuka yake yak'iyin barci, su Amaturrahman da sukayi nasu na lallashesu sai suka kwanta, dan sunsaba da yayi sallar isha'i yana tare dasu, amma yau shiru babu amo babu labari.

Nikam sainaji abin yana cizon zuciyata, indai wannan mulki zaisa mijina yin nesa dani bana farin ciki, saigani da kuka rurus.



Sai misalin 12pm Sarki Muhammad Sameer yasamu rakkiyar zuwa sashenmu.

Ina zaune afalo nayi tagumi naji alamar mutum tsaye a kaina.

A firgice na d'ago kaina ganin mijina saina mik'e a firgice tare da fad'awa jikinsa na saki kuka.

Shima rungumeni yayi sosai yana sakin nasa kukan, sannan ya d'aukeni cak zuwa cikin bedroom d'in ya ajiyeni a saman gadon, kuma rungume juna mukayi muna cigaba da kukan mu.

Tsawon lokaci muna haka, sannan yafara dakatar da nashi yana lallashina.  Munaya kinga abinda su papi sukaimin ko, ni dai banason sarautarnan, amma sunk'i saurarena, wlhy banaso munaya, banaso nidai .... Yakuma fashewa da kuka.

Tausayinsa saiya kuma kamani, nakuma rungumesa tsam a jikina, abinda kaga ya saka Galadima kuka aiba k'arami beneba kuwa. Daure zuciyata nayi na shiga lallashinsa.

Na kuma rungume sa sosai cikin nutsuwa ina fad'in,  Mijina ba komai ne ake tuntu6e dashi bisa shiryawa kaiba, wani abun tunkan kasan tuwarmu gudan tsoka rubutaccene a littafin k'addararmu, babu wani d'an Adam da alk'alamin k'addararsa ke a tafin hannunsa, gudun zuciya yafi na k'afafu sauri, idone kawai ke iya banbance fari da bak'i, baki kuwa d'and'ano kawai yake tantancewa, aikin kunne kuwa jine kawai da banbance k'arar sauti, baka tunanin duk mutum mai baiwa ALLAH ke ba damar banbancewar? Irinku kune kuka cancanci mulkin al'umma, domin kuwa bashine burinku ko damuwarkuba, kune zaku iya adalci da tausayin na k'asa daku, ka amince dayin wannan sadaukarwar ga iyayenka da al'ummarka, domin samun damar k'ar6ar sakamakonka wajen adalin Sarki mai tarin rahma da jin k'ai. Zuciya da tunani duk mallakar gangar jikice, haka gudanar jini da motsin ga6o6i, su papi sune sukasan tayaya ka cancanta kaida d'an uwanka, har suka d'auki wannan nauyin suka d'ora muku, Ku kar6i yau d'unku da hannu biyu, domin jiyanku tazama labari, Ku hidimtawa gobenku domin Ku ribantu da jibinku, wannan shine kawai masalaha mai k'ayatarwa ga mu ahalinku, masu ganin baka kaiba saisu ajiye makamansu su tabbatar da ka kai d'in, kazama RAINA KAMA mijina, kosu amince, ko karsu amince kaine RAINA KAMA .

Tsam ya rungumeni yana fad'in  kece RAINA KAMA munaya, domin a dalilinki ne suke ganin nayi feeling, har ake ambaton ni da sarauta har Abadan, su ganin auren talaka shine k'ask'anci, shine ke nufin ka koma k'asa, a yak'ininsu saika auri y'ar wani mashahurin Sarki ne darajarka ke a idonsu, sun manta ba talaucine ya rarrabe tsakaninmu ba, Wanda yafi wani bautar ALLAH shine mafifici a cikin bayi, su Papi sun tabbatar min kina d'aya daga cikin manufofinsu na bani Sarauta, sunason tabbatarma duniya da mai sarauta zai iya auren d'iyar talakawa, basai y'ar mai mulki irinsaba, sunason duniya tasan shima talaka akwai baiwa da darajar da ALLAH yamasa fiye da mai mulki, sunason duniya tasan ba mai mulki bane mafi k'ololuwar daraja a cikin bayi, kowanne Bawa da tarin daraja da baiwar da ALLAH ya masa, kinga kuwa kece RAINA KAMA my heartbeat, ko ni kin zamemin RAINA KAMA balle su da suke tunani ba daidaiba .

Kasa magana nayi, muka rungume juna tsam cikeda so da k'auna.



An cigaba da gudanar da gagarumin biki na wannan nad'in sarauta, kwanaki 5 cif akayi anayi, danma mutuwar gimbiya zulfah ya rage armashin bikin.



bayan lafawar komai da sati biyu mukaje India Galadima ya maida dukkan harkokinsa nacan ga Sauban daya zama tilas ya d'auki matarsa su koma can, dole kuma ya ajiye aikinsa duk da sonsa da yake, su Vijay zasu cigaba da kulawa da komai, idanma suna buk'atarsa zai cigaba da kawo shawarwari.

Mun dawo da kwanaki biyu aka gama kammala aikin Company d'insu na nan Nigeria, Wanda dole su Vijay sukazo suka aiwatar da komai, zuba masa kaya da d'aukar ma'aikata da dukkan abinda yakamata ayi.



Wata d'aya cif a tsakani aka basa umarnin shirya fara gudanar da mulki, Shiga fada da nad'e-nad'en sarautu da zaiyi, dakuma Neman matar aure dazai k'ara.>�&�<���
@&



Wannanfa Abu ya tayarmin da hankali sosai, ga cikina ya tsufa, aiko na birkice masa naita kuka, kai wlhy kishiya da ciwo, duk dauriyarka saikaji babu dad'i, musamman idan kana son mijinka kuma.

ALLAH Sarki Momma Uwa ta gari, itace taita kwantarmin da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya, hakama Galadima yayta lallashina da nunamin muhimmancin lafiyata kodan tsohon cikin dake jikina, itama Munubiya da Innarmu haka, nima da naga mijina da kowa na son ganin kwanciyar hankalina saina kwantar d'in, na kar6a k'addarata da hannu biyu.

Da farko d'iyar Mom akace ya aura, bankuma San yanda akayi ya zameba yace yabani wuk'a da nama na za6o masa dukkan wadda tamin, koya take wlhy zai aura shikuma.

Kusan sati biyu daya bani sainaita nazari da hasashen wazan za6a masan, haka kawai matashiyar budurwa Hafsat da muka ta6a had'uwa a jirgi ta fad'omin a rai, lokacin inada cikinsu Amaturrahman, tamin wani taimako da Galadima ya yaba mata sosai, Wanda harna kamashi yana satar kallonta, amma a time d'in saiya basar kamar yanda halayyar tasa take, Nima sai banja maganarba, mukan gaisa da Hafsat miss xoxo time to time, amma mun dad'e bamu had'uba, inagama tun taron sunan su Abdurrahman da tazo.

Muna zaune dashi na lalubo hotonta da mukayi ranar suna tare na nuna masa.

 My king wannan ta makane? .

Kar6ar Hoton yay yana kallo, yay wata irin zabura yana ajiye hoton gefe da hararata,  Kina zargin ina sontane komi? .

Murmushi nayi ina d'auke hoton, nace,  yanayinka da amsarka kawai ta wadatar dani ranka ya dad'e, danason ma kanason miss xoxo da tuni na had'a wannan alak'ar wlhy, ALLAH yabamu zaman lafiya .

Duk yanda yaso bijirewa da nuna ba haka bane ban sauraresaba, na nunama Momma photo aka shiga binciken miss xoxo. A cikin sati biyu aka gama komai, duk da itama ta nunamin bata aminceba.

Duk da kishi na cina haka na jajirce tsakanin borensu, babu 6ata lokaci akasha biki.

Da kaina namata rakkiya d'akin mijinta a maimakon rakkiyar jakadiya da har yau bai za6aba., nai k'ok'arin danne kishina nai mana addu'ar zaman lafiya. Na dawo d'aki ina kuka da rungume y'ay'ana, akuma asubahin farko na farka da nak'uda. Wadda har aka wuce dani asibiti Sarki Muhammad Sameer bai fitoba, yanacan yana lallashin amaryarsa daya maida cikakkiyar mace a daren jiya.

Na sauka lafiya na haifi d'a namiji mai kama dani sak, sai daga baya labari ke kaiwa kunnen Sarki Muhammad Sameer, ya rikice da murna, gashi babu damar binmu a asibiti, dole ya hak'ura har muka dawo.



Fad'an farin cikin samun wannan haihuwa ga Sarki 6ata lokacine, hakama su Abie da tsohon Sarki da a yanzu suka koma daga gefe suna koyama yaransu dabarun mulki.

Washe garin suna kuma Sarki Muhammad Sameer ya zauna a fada, tare da yin wasu nad'e-nad'e, hardasu Badi a ciki, sarkin mota da Sarki k'ofa sunce iya wuya suna tare dashi.

Haihuwar danayi Ce ta d'auke hankalina daga damuwar kishin mijina da wata, duk da bana nuna kishin dama a fuska balle Hafsat ta fahimta, dan Alhmdllh tarbiyyarta tasa muke zaune lafiya, saima k'ok'arin jan yarana da take a jikinta, yarona yaci suna Abdul-fatah, papi kenan, daga Hafsat kuma Sarki Muhammad Sameer yace ya tsaya, mata biyu sun ishesa, ALLAH yamusu zaman lafiya.



Rayuwa ta cigaba da gudana cikin nasarori, wajen saloon d'ina nata ha6aka, da kud'in shigarsa na d'auke kaso mafi tsoka na nauyin gidanmu, mahaifina ma yasamu sarauta da Sarki Muhammad Sameer ya nad'ashi, hakan yamin dad'i sosai.

Munubiya itace mai kula da ladies mirror, office d'inma ita ke zamansa time to time, danni banida wannan damar a yanzu, fitarma sai wadda ta zama tilas nakeyi.





Sarki Muhammad Sameer nada watanni takwas akan mulki ALLAH yayma mama Fulani rasuwa, tsakaninta da papi wata 1, wannan rasuwa biyu ta matuk'ar girgizamu, dan Sarki Muhammad Sameer kusan zarewa yayi akan mutuwar papi, yabasa gudunmawa mai yawa a rayuwarsa, wadda mantata abune mai matuk'ar wahala a garesa, mai makon babansu Nuren ya hau mulkin, sai yasa aka nad'a Nuren d'in. Sarki Nureddin ALLAH ya tayaku ruk'o baki d'aya.



Babu dad'e da nad'im Sarki Nureddin akasha shagalin bikin Saleem da Feena, bikin dayay armashi sosai, dan itace last mace dasu innarmu zasu aurar, saura y'an k'ananun y'ay'ansu Aryaan, Aiyaan da Ahmad, Wanda a yanzu sun zama samari masha ALLAH, dan duk suna sa2 a secondary school, jirama Sarki Muhammad Sameer yake su kammala ya had'asu da Khaleel su wuce karatu.



A yau kuma Munubiya ta kawo mana ciyara da y'ay'anta Meenal, Ameen da k'aramar Ai'sha muna ce mata Islam. Munsha hira sosai, taita mamakin yanda nake zuba mulkina, yo matar Sarki uwar gida wasace=��=�M�<���>�8�<���
@&>�8�<���
@&.









BAYAN WASU SHEKARU



Rayuwa ta shud'a ababen dariya Dana kuka sun faru iri-iri, an haifi wasu wasu sun rasu, hak'urin zama Na yau da kullum, wataran a 6ata ma koka 6atama wani.

Zuwa yanzu kam munyi rashin wasu daga cikin iyaye y'an uwa zuwa kakanni, ALLAH yayma Abbanmu rasuwa shida wasu matan gidanmu biyu, inno ma haka, yayinda innarmu ta gama takaba sai danginsu sukazo suka tattarata zuwa k'asarta ta haihuwa, muna kuka tanayi hakama jama'ar gidanmu da y'an anguwa, Dan bamason tafiyar tata, amma hakan gatane a gareta komawa cikin ahalinta, a gagara badauma kam mun rasa da yawa, tsohon Sarki jalaludden Abubakar ALLAH ya masa rasuwa sakamakon ciwon hanta, wadda ya dad'e da ita a jiki Ashe, wannan ma shine dalilinsa na dagewa akan Abie ya kar6a mulki. Saida rayuwa tazo gangara yake sanar ma Abie d'in Wanda shima zuwa yanzu girma ya kamashi sosai, Dan yatsufa komai ma sai an masa, danma ALLAH yabashi gwarzuwar mata Momma, dukda itama girman ya kamata bata gajiyawa da hidimarsa.



Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar, adalin Sarki da talakawa ke alfahari da mulkinsa, musamman ma matasa da akullum cikin bin hanyoyin inganta rayuwarsu yake, suna zaune lafiya shida wazirinsa kuma d'an uwansa, babu wani y'an ubanci ko k'iyayyar juna, k'yawawan zukatansu sun sakasu kawo canji mai yawa a wannan masarauta, da farko su Talba ne sukaso kawo musu hargitsi, tunda suka fahimci haka sai aka sakasu barin k'asar tilas suda iyalansu, tun daga nan masarauta tadawo dai-dai.

6angaren Harun ma ya fito tun lokacin daya cika shekaru goma, amma bisaga karamci Na adalin Sarki Muhammad Sameer saiyasa aka kawosa fada, yay masa hidima mai yawa, wadda ta sakashi kuka da gurfana gaban Sarki Muhammad Sameer Neman gafara da nadama akan abinda ya aikata, Muftahu da ayanzu yake rik'e da sarautar matawalle yay murmushi yanama Sarki Muhammad Sameer magana da ido akan ya yafe masa tunda yayi laushi, Sarki Muhammad Sameer ya jinjina kansa yana murmushin nan nasa Na k'asaita da cizar lips.

Yafewar da Sarki yamasa Ce tabashi damar Neman gafara ga Uwargida Sarauniya Munaya itama, babu wani ja'inja tace ta yafe, ba'a barsa ya zauna masarauta ba, anmasa hidima mai yawa da aure aka sakashi komawa wata k'asa, Dan bawai kowa ya gamsu da tuban nasaba, ayanzu kuma Sarki da wazirinsa basa buk'atar duk wani mai ru6a66iyar zuciya a kusa dasu.



Sarauniya Munaya uwargidan sarki mai fad'a aji a wannan masarauta, jarumar mace mai nagartacciyar zuciya, hamshak'iya wadda ayanzu tazama babbar mace jerin manyan mata sahun faro wajen dattako da mulki dama dukiyar itada y'ar uwarta Munubiya.

A yanzu yaranta takwas a duniya, Amaturrahman, Abdurrahman, Abdurraheem, Abdul-fatah, Ai'sha, Zeenah, Saifudden, jalaludden Auta kenan, Ai'sha da Zeenah da suke kira da Safah da marwah tagwayene, bayan haihuwar Abdul-fatah tayisu suma, daga nan sai mai sunan Abie, dakuma auta takwaran tsohon Sarki babansu matawalle konace waziri, ayanzu kam duk sunzama manya, musamman su Amaturrahman da suke manya duk suna a jami'a, suna k'asar India tareda uncle d'insu Sauban da ayanzu shima yazama babban mutum, yazama babban d'an kasuwa bisaga jagorancin dukiyar d'an uwansa, yayinda su Aiyaan da Khaleel, Aryaan, Ahmad ke taimaka masa, kaga matasan samari abokan juna kenan, kansu ahad'e yake su hud'unnan, sune yanzu duniya ke yayi take son gani a fanin na'ura mai kwakwalwa wato Computer, Wanda ayanzu Abdurraheem da Abdurrahman


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login