Showing 327001 words to 330000 words out of 365757 words

Chapter 110 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1519

waje d'aya ina kallonsa, yana cikin bargo ya lullu6e har kansa, janye bargon dake lullu6e da fuskarsa yayi yana kallona ta cikin d'an hasken fitilar.

Idanu ya zuba mata cikeda mamakin yaushe tazo gidan? Ya ciro hannunsa daga bargon yana min alamar nazo.

A hankali na cigaba da takawa, zuciyata cike da d'unbin tausayinsa, koba komai ta sanadina ciwon ya sameshi, na zauna a bakin gadon idona a kansa, hannuna ya kamo cikin nasa dakeda zafi alamar zazza6ine ma a jikinsa. Ina had'iye kukan daya tahomin nace,  Sannu, ya jikin? .

Idanunsa ya lumshe da cije lips.

Na kama bargon zan yaye yakuma rik'e d'ayan hannun yana girgizamin kai, ahankali yace,  Sanyi .

Sannu na kuma masa, sannan na zare hannuna zan mik'e, amma saiya rik'oni da sauri, jiyowa nai ina kallonsa.

Ahankali Yace,  Ina zakije? .

Badan ina kallon la66ansa ba dabama zan fahimci miyace d'inba, Dan banjiba.

Dawowa nayi na zauna, nad'an matsa hannunsa,  zan had'a maka ruwane kasamu kad'anyi wanka, kaci abinci kuma .

 Zan daiyi wankan kawai? .

 Abincin fa? .

Kansa ya girgizamin alamar a'a.

Kamar zanyi magana saikuma na fasa, tashi nayi na shiga toilet, dukda babu wani datti dai sai naga yakamata na wanke, na cire mayafin jikina na tsaftaceshi, na saka air freshener sannan na had'a masa ruwa mai d'an zafi ba canba dai, yanda zai masa dad'i.

Zaune na iskeshi a bakin gadon ya dafe kansa, kallo d'aya namasa na d'auke kai, Dan dagashi sai boxer.

 Ga ruwan na had'a .

'Dago idonsa yay ya kalleni yana sauke hannunsa daya dafe kai, yanda tawani k'asa dakai kamar tana gaban surukinta, yad'an murmusa danshi kunyar nan tata birgeshi take.

Duk saina takura da kallon dayakemin, gashi kunyar motsawa nake daga wajen, Dan sket d'in jikina ya kamani sosai, maganarsa Ce ta katsemin tunani.

Na d'ago ido naimasa kallon fisha na janye ina fad'in  Towel? .

 Uhumm . Kawai yace yana cigaba da kallonta.

Ahankali na dunga tafiya saikace wata mai tatata, Dan inaji a jikina kallona yakeyi har yanzu, saida na d'akko gyalena dake jikin k'ofar bayi na yafa sannan na d'akko towel d'in.

Duk abinda takeyi idosa na kanta, towel d'in da hannunna ya had'a ya rik'e, na kallesa fuska a marairaice ina f'ad'in,  karfa ruwan ya huce yalla6ai .

Ya zubamin jajayen idonsa ga jijiyoyin kansa sunyi rad'a-rad'a, baice komaiba ya zare towel d'in ya yafa a jikinsa yana mik'ewa da k'yar, saiya kuma bani tausayi, Dan na lura k'arfin haline kawai yakeyi.

Bedsheets d'in saman gadon Na cire bayan Na kunna fitilar d'akin ya gauraye da haske, Na bud'e wardrobe d'in kayansa Na d'akko wani bedsheets d'in Na shinfid'a, Na share d'akin, banyi morping ba tunda darene, nasaka turare sanann Na fita.



Yauce rana ta farko dana shigo kitchen da nufin dafama miji abu, sainakejin karsashi da alfaharin nimafa yanzu matar aurece tamkar kowacce mace, natashi daga matar Contract yanzu, wasu hawayen jin dad'i suka zubomin, nasa bakin mayafin Na share, a kayan da mukazo dasu Na ciri kayan k'amshi, ina d'auraye tukunya laraba ta shigo, juyowa nai ina kallonta.

Tace,  ya jikin nashi? .

Ajiyar zuciya nad'an sauke. Nace,  da sauk'i iya, amma kwance Na iskeshi rijib ga zazza6i, zan dafa masa ruwan zafinne da d'an abinda zaici .

 ALLAH ya k'ara sauk'i, dama mura bata masa da sauk'i, dan yasha zuwa can yanayi kota sameshi a can, namiki karambani Na dafa ruwan zafin gashinan .

 Nagode iya, wlhy babu wani karbani, taimako dai, mun saki aiki ga gajiyar tafiya .

Dariya tayi tana gyara tsayuwa. Tace,  Aini gajiyarnan kam ta gudu, ras nakejina, kunedai dayake ba wahalar kuka saniba koyaya kuka motsa sai jiki yayta ciwo .

Nima dariya nad'anyi, ina cigaba da had'a komai akan k'aramin tire.

Laraba tace,  To yanzu Yaya za'ayi kenan da abinci? Kinga dai ba'a barshi da yunwa ba? .

Nace,  Iya ga Muftahu can ya tafi samo masa abincin .

Tace,  To shikenan hakanma yayi .

'Daukar tiren nayi natafi kai masa.



Har yanzu bai fitoba, mamakin dad'ewarsa ta kamani, ajiye tiren nayi a k'aramin table glass d'in dake gaban gadon nima Na zauna ina tsumayen fitowarsa. Kusan mintuna 3 da zamana saigashi ya fito.

Ban kallesa bama gudun karnaga abinda yafi k'arfina, kaina a k'asa ina wasa da stones d'in jikin mayafina.

Shikam tunda ya fito idonsa Na kanta, ya zauna kusa da ita yana tsane ruwan fuskarsa zuwa kai da towel.

Kallonsa nayi kad'an, ganin bathrobe ce a jikinsa saina samu nutsuwa.

Da hannu yay min nuni da mansa, na mik'e Na d'akko, amma saiyak'i kar6a.

Nad'anyi shiru da tunanin miyake nufi?...

Katsemin tunani yayi da fad'in  Manma nizam shafa? . A hankali yayi maganar, kuma fuska babu walwala.

Ni mamakima yabani, amma to da banzo ba waye yake shafa masa?, bance komaiba na zauna kusa dashi ina zuba man atafin hannuna da mutsukashi, kunya tasa narasa dama ina zan fara?.

Lura da hakan dayayi saiya mik'amin hannu kawai, banida za6in daya wuce cika umarninsa, anutse na shafa masa man dan banida yanda zanyi.

Kaya na d'auka masa marasa nauyi, ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi ya saka, nidai kauda idona nayi gefe harya gama.

Natashi na had'a masa tea d'in da ruwan kayan k'amshinan, yana zaune akan sofa ya zubamin ido saikace wata television, dana mik'a masa mug d'in saiya had'a harda hannuna ya rik'e, da ido namasa alamar da zafifa cikin marairaicewa.

Shima saiya min nasa salon da ido alamar da gaske.

Nakuma narke fuska tamkar zanyi kuka, zame mug d'in yayi yana wani miskilin murmushi.

Ya d'ora cup d'in akan bakinsa yana kallon yanda take tatta6a tafin hannunta, a ransa yace hajiyar tsiwa kenan, andawo koya kuma zamu kwashe?.

Tea d'in yamasa dad'i, Dan saiya tuna masa da inno, itace kan masa wannan had'in inhar yana mura, yanasha yana kallona a k'asan ido, saika rantse kuma ba kallon nawa yakeba, amma ni inaji a jikina.

Knocking k'ofar da akaine ya sashi kallon cctv, ganin Muftahu da Dr jalal sai ya juyo ya kalleni da alamar tuhuma. Uffan bance da shiba, na mik'e da nufin fita na bud'e musu saiya dakatar dani ta hanyar d'agamin hannu.

Komawa nayi na zauna, shikuma ya mik'e rik'e da mug d'in ya fita.

Ajiyar zuciya nad'an sauke ina binsa da kallo.



Saida ya zauna cikin kujera sannan yabama su Muftahu izinin ahigowa.

Duk suka zauna suna masa sannu, ya amsa musu cikin d'aga kai da basu hannu sukayi musabaha.

Magunguna Dr jalal ya bashi na mura. Sannan ya buk'aci yimasa allura, amma saiya nuna bayaso.

Cikin dafe kai yace,  bar Allurarnan Jalal, bara nasha maganin kawai .

Murmushi Dr jalal yayi, Dan yasan dama Galadima bayason allura. Basu wani dad'eba sukai masa sallama suka fita.

Fitarsu dana gani yasani fitowa falon, kallonsa nayi ina zama, shima idonsa a kaina, da hannu ya nunamin ledojin da Muftahu ya ajiye.

Bance komaiba na bud'e, d'aukar d'aya nayi na fita, na kaima laraba dakema su Abdurraheem shirin barci.

Cikin tsokana tacemin  kodai murufe d'akinmu kawai .

Dariya nayi na fita ina fad'in  kai iya yanzufa zan dawo .

Inajiyo dariyarta daga falo. Nidai nashiga kitchen na d'auki plate da spoon na koma wajensa.

Farfesun kifi na zuba masa, dan zaifi masa sauk'in ci, da farko ma cayay bazaiciba, saida naita rok'onsa harda kwalla sannan ya amince nabashi da kaina, yad'anci babu laifi, nabashi drugs d'in da Dr jalal yabashi .

Koda yagama sha saiya jingina jikinsa da kujerar yay shiru, yad'anji dad'in jikinsa kam ba laifi, falon saiya d'auki shiru, muna a hakane kiran Momma ya shigo wayarsa.

Yabud'e idanu yana d'aukar wayar, yay picking, gaisawa sukayi, bansan mitace da shiba daga can najidai ya amsa da  Insha ALLAH goben muna hanya . A hankali yake maganar saboda kansa, bama su dad'eba ya yanke wayar ya mik'e, hannu ya mik'omin alamar na kama.

Banyi musuba na saka hannuna cikin nashi ya mik'ar dani, bedroom d'in muka koma, ya zaunar dani bakin gadon sannan ya cire kayan jikinsa, ya hau gadon ya kwanta.

Nidai k'in kallonsa nayi, saida ya kwanta sannan ya kirayi sunana a hankali can k'asan mak'oshi, kallonsa nayi.

Yace,  Please mammatsamin jikina kozai rage ciwon da yakemin .

Tausayi yabani, dan haka banyi musuba na hau gadon sosai nafara masa tausa a nutse, idonsa ya lumshe yanamai jin dad'in tausar, ahankali drugs d'in dayasha yafara cin k'arfinsa, barci mai nauyi yay a won gaba dashi, saida na tabbatar barcin yayi nisa sannan naja bargon na kuma lullu6a masa har saman kafad'a, nai masa addu'a na mik'e Na lalla6a na fita a d'akin bayan na kashe masa fitila.



Koda na koma d'aki laraba har tayi barci, nima shirin kwanciyar nayi kawai na kwanta, cikeda kewar y'an uwana da jiya iyanzu duk muna a tare=��.





********



Iyayen Su Munaya maza sunyi farin ciki da labarin da Abba yabasu akan dangin inna, dan suna tausayinsu sosai, innaro ta tarasu duka tasa aka kira mata inna, harda hawayenta tana Neman gafararta bisa ga abinda tamata tsawon shekaru.

 Kiyafemin Ai'sha, dan lallai son zuciya ya rufe idona ruf, banason ara6i y'ay'ana koni saboda abin duniya, nata k'ask'antar dake agaban wad'anda duk kin rigasu zuwa gidan, wlhy wani lokacin su mero ne suke zugani, dan ALLAH kiyi hak'uri, nasan dai da wuya ki yafemin ma..... .

Da Sauri inna tace,  Wlhy na yafe miki nikam, dama ban ta6a rik'eki a raina ba, dan matsayin uwa mahaifiya nake kallonki, inhar bazan iya musawa mahaifiyata magana ba ko jin zafinta to lallai kema baki cancanci na musa mikiba, ni dukanku ma na yafe muku wlhy, ALLAH ya kare gaba, yakuma yafe mana baki d'aya .

Su Abba duk suna amsa da amin, kowanne yanajin dad'i har cikin ransa, lallai idan kaga halin girma to daga tsatson d'an masu girma ya fito, duk cin kashin da innro tama innarsu Munaya hakan baisa ta gagara yafe mataba, ya rabbi kabamu k'yak'yk'yawar zuciya gaba d'aya.

Masu samun fawar cin zarafin inna a wajen innaro duk sai suka nutsu suma, dan yanzu kam babu dama.

Haka su inna sukaita rabon tsaraba akaita rabo, har gidajen iyayen su Maman safara'u duk saida aka kai, kafin kacemi labarin tushen inna yabaje anguwa, mutane sai mamaki da al'ajabin hikimar ubangiji sukeyi, lallai Maman biyu tazamema matan gidansu RAINA KAMA, su sunata hura hanci y'ay'an wasune, da mata gorin rashin dangi Ashe gaba da gabanta, aifa matan anguwa suka dinga shigowa mata murna da sannu da zuwa.



Matan gidansu Munaya bak'inciki tamkar zai karsu, saidai babu damar koda yin tari, saidai kukan zuci da bak'incikin hassada mai cinye farin cikin Bawa.





******





Washe gari Galadima yatashi dad'an dama-dama, dan babu zazza6in sai ciwon kai, shima bamai tsananiba irin na jiyaba.

Da safen yake sanarmin nayi shiri wai zamu koma, mamaki ya kamani, wannan wace irin tafiyace haka babu shiri, bayanma naji yanata kukan rashin kud'i a tsakaninnan, saidai banida damar Musawa, dan inason zuwa naga jikin Abie nima.



Da yake tafiyar saida yamma, tashin hantsi muka shiga cikin gida gaida mutane, fada Ce kawai bamujeba, sai yaran aka kai can, kowa yana yaba k'yawu da girman da yaran suka k'ara, gimbiya zulfa dai bata yarda mun gantaba, wai batada lafiya tana kwance.

Bamuce komaiba muka fito, mun iske Galadima yana fada, dan haka muka cigaba da shirye-shiye, sai a waya na kikkira mutane mukayi bankwana, naso had'uwa da Aunty Salamah dan inason ta warwaremin wasu tambayoyi, to amma hakan bata samuba, ko gidansu baba mai k'anwa ban lek'aba, kuma wlhy naso hakan matuk'a, to amma ga ayanda tafiyar tazo babu shiri.



K'arfe 2:00 mukabar masarautar gagara badau zuwa masarautar su papi, tarba akai mana ta mutunci, ina mamakin yanda suke matuk'ar k'aunar Galadima, Sauban tamkar zaiyi rawa dan dad'i, ammafa yayi 6ul-6ul dashi alamar yanashan gata, dukda lokacinmu k'urarrene munsha fira, inno tsohuwar mutunci, yanda take jana ajiki abin ba'a magana.

Galadima ma tunda suka gaisa da papi da mutane saiya shige cikin d'akin inno ya kwanta, dan bayason yawan hayaniya, saida akayi magrib muka baro masarautar cikeda d'unbin alkairin wad'annan bayin ALLAH, alkairi sosai Galadima yay ma laraba, harda hawayenta nima haka, dan munyi sabo sosai, bansan miyasa Galadima baice mutafi har itaba, kokuwa matsalar kud'ice oho, lallai na yarda sabo Turken wawa, shi akema kuka ba mutuwaba. Nuren ya d'auke mu.

Mun biya gidan Mom, itama dai haka tasha hidima damu, saidai akwai yarinyarta ta biyu nakula tun a wancan zuwan bata yina, dan ko gaisheni bama yi takeba, tata yatsine-yatsine kenan, a wancan zuwan abin yad'an dameni, amma yau ko a jikina, dan abinda na lura dashi son Galadima takeyi, dan haka na watsar da lamarinta ko kallo bata isheniba, babu mai takani na zauna, babu ruwana da arzik'inka ko ahalinka, ka mutuntani nima na mutuntaka saimu zauna lafiya.

Wanda takeyi donshi d'inma ko kallo bata isheshiba, dan baya sakar musu fuska, duk shakkarsa sukeyi har babban wan nasu gaba d'aya, dan ko sauban ya girmeshi balle Galadima.

Bamu bar gidanba saida time d'in tashin jirginmu ya matso, dan tacan zamu wuce, dukansu gidan sukai mana rakkiya har airport, har saida sukaga tashin jirginmu.





******



Abin ya had'emin da yawa kam, ga yara ga babansu daba lafiya, sauk'inama basuda yawan rigima, Abdurraheem ne dai idan yaji ya takura babu zaman lafiya, Alhmdllh ALLAH dai ya taimakemu mun Isa lafiya, Khumar da Samha, aunty Mimi sukazo tararmu, bama tamu sukeba ta yaran sukeyi, ganin haka Galadima yaja hannuna muka shige mota, saida suka gama murnarsu sannan suka shigo, aunty Mimi na fad'in,  Oh shine kuka shige mota? .

Galadima yabata amsa da cewa,  Tunda batamu akeba mizamu zaunayi .

Dariya ta sanya da fad'in  yau naga kishi, to kuma dai sannunku badan halinkuba .

Murmushi nayi ina gaisheta, Samha ta mak'alk'aleni.

Haka dai muka k'arasa gida.

Momma da jakadiya duk suna a harabar gidan da sauran hadimai mazan da mata. Kowa burinsa yaga yaran. Momma dai Nita rungume tanamin oyoyo. Kunya dukta kamani, ina k'aunar wannan baiwa har cikin raina wlhy.

Galadima kam jingina yay da mota kawai yana kallonsu cikeda jin dad'in yanda kowa ke farin cikin dawowar iyalansa.

Saida muka shiga ciki sannan Momma kecewa  Ina uban gayyar wai? .

Galadima dake shigowa a k'arshe yace,  gani a anan, naga batani akeba Momma shiyyasa naja gefe .

Duk dariya mukayi, yayinda bayin sukai k'asa da kai duk suna k'umshe tasu, dan babu damar yi.



An shiga gaishe-gaishe damana sannu da zuwa, hadiman gidan duk suka fice aka barmu mu kad'ai.

Momma duk tana rungume da jikokinta wad'anda suke rikid'ewa ruwa biyu, kamannin Galadima da Munaya, Khaleel ma yabi ya mamuk'e mata.



Galadima ya mik'e ya haye sama, danya d'an watsa ruwa, gashima magrib tagabato anan.

Momma harda hawayenta najin dad'i da farin ciki.



Tofa lamari ya canja salo, a wannan karon dai maimakon Momma tace nabi mijina saitace na shiga d'akinta nayi wanka na huta, aunty Mimi kuma ta kwashi yaran da taimakon Samha zata musu wanka.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login