Showing 72001 words to 75000 words out of 365757 words

Chapter 25 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1442

yitaima tamkar batasan mi akeyiba, mama Rabi'a da Aunty Salamah sai fad'a sukemin kamar zasu dokeni, hakama innaro, sai jaraba takemin harda dungure min kai.

cikin ikon ALLAH kuwa ana cikin haka saiga kiran Samha yashigo wayata, Ayusher ta d'auka suka gaisa, azaton Samha nice, saboda muryar Ayusher ma tana kama da tamu. Tace,  Aunty gimbiya ya hidima? .

Murmushi Ayusher tayi danjin sunan nawa harya canja, tace  ba ita baceba Ayusher ce .

Cikin jimami tace Aunty gimbiyar fa? .

Labarin komai Ayusher tabata, sannan tace  dan ALLAH ko zaki had'ani da Galadima? .

Samha tace  babu damuwa bara na dubashi, duk da nasan yana tare da abokansa yanzun .

Godiya Ayusher Tamata sannan suka yanke wayar akan idan tagansa zata kira .

Masifa nahau yima Ayusher akan miyasa zatace saita fad'a masa, nidai koma miye babu inda zanje.

Banza Ayusher tamin tamkar batasan inayi da itaba ma.

Kusan muntuna 7 saiga kiran Samha yasake shigowa, Ayusher ta d'aga, maimakon taji muryar Samha saitaji ta Galadima cikin k'asaitar nan tasa da izza.

Nutsuwa Ayusher tayi sosai ta gaisheshi, sannan ta masa bayanin komai.

uffan bai ceba saida ta kai ayar zancenta, lips d'insa yad'an cija kafin yace  had'ani da ita .

A kunne Ayusher ta sakamin wayar, yayinda kowa yafice daga d'akin aka barni ni kad'ai saikace wata mayya.

Dagani har shi kowa yayi shiru, shi yanajin kansa nima hakance, kusan minti 4 yaji banida niyyar tankawa saiya yi guntun tsoki,  shin ke baki iya gaisuwa bane? .

Dukda naji ban k'yautaba saina ta6e baki, cikeda dakiya nace,  ina yini . muryata a dishe take saboda kukan danaketa sha tun jiya.

Bai amsa gaisuwarba yace  wane sak'o kika bada a bani? .

Saida na tunzuro baki sannan nace  yoni minace abaka? .

Lips d'insa ya lasa yana fad'in  nikikema wannan abun? .

Banza namasa danni bansan mina masaba kuma.

Yaja guntun tsoki,  ki kama kanki fa, karkiga auren contract mukayi, akwai sharid'd'a acikinsa, bana buk'atar ganin kowa awajen inba keda sister d'inki ba, haka na tsara, kuma babu mai canjamin ra'ayina, zuwa anjima wadda zata shiryaku zatazo, idan kin gadama karki bari a shiryaki, nikuma zakiga mi zan yi akai.. .

d'if ya katse wayar, cirota nayi daga kunnina ina dubawa tamkar zan ganoshi acikinta. naja tsaki ina fad'in  aikin banza kaje ka koyo R sannan kamin wannan ikon, nifa baka isa takani ba acikin auren contract...... 

Sauran maganar ta mak'ale a mak'oshina saboda shigowar munubiya.



Zama tayi akusa dani,  sweetheart zan iya neman alfarma a wajenki? .

Kai na d'aga mata.

Ta gyara zamanta sosai tareda kamo hannayena duka acikin nata.  inason kima mijinki biyyay kiyi yanda yakeso, yanzu hakkin bin dokarsa tarataya a kanki dole inhar bata sa6ama addini ba, kina kaucewa kuwa zaki had'u da fushin ALLAH, tunda yace haka yakeso ayi kiyarda kawai, awa nawane anyi an tashi kowa yakama gabansa .

Alk'awarin Dana mata yasani amincewa zanje tilas amma badan raina yasoba.

An tsara wad'anda zasuje, dan haka aka damk'ama kowa gate pass d'insa a hannu ya Adana. dukda wasu gani kwaf zasuje kuwa.



Bayan sallar isha'i saiga masu mana shiri sun iso, babbar magana wai d'an sanda yaga gawar soja.

Jama'a ni kaina bamma gaskata cewar nibace ballan tana Ku 'yan kallo, saika rantse kace dama can mud'in jinin sarauta ne, munyi k'yau har mun gaji, gashi dandanan akayi aka gama, har kusan 9pm muna jiransu, gidan yayi tsitt duk wad'anda zasuje dinner sun tafi, wad'anda zasu bimune kawai tare damu muna jiransu Galadima, dan shima yaa marwan d'in baikai ga isowaba.

Sai around 9:15pm sannan mukaji dirar mitoci a k'ofar gidan.

Aunty Mimi ce da kanta tashigo itada wasu bayi guda hud'u, saida ta gaisa dasu innarmu sannan aka mata iso d'akinmu, wani dad'ine ya ratsa zuciyarta, dukda batasan wacece matar k'anin nataba acikinmu, amma muntafi da imaninta, jitai inama natane wad'an nan twins, ALLAH yasa haihuwar farko na haifo musu irinmu.

Daga ni har munubiya rissinawa mukayi muka gaidata cikeda girmamawa, dan munsan a haife ta haifemu, dukda bawai sa'ar innarmu bace, ko mama Rabi'a ma ta girme mata.

Hakan damukayi yamata dad'i kuma mun birgeta, ta kama hannayenmu tana yaba k'yawun damukayi, wasu turarurruka ta fidso kala uku a bag d'inta tashiga feshemu dasu, dukda uban turaren da aunty salamah tamana wanka dasu zance, dan itama haka taita zazaga mana su d'azun, ni saima hawarmin kai sukeyi wlhy.

Wasu alk'yabbu masu azabar k'yau iri d'aya aka saka mana, takalman dake k'afarmu kansu abin kallone.

Aikam bamu fitaba saida tamana hotuna, afaloma saida aka mana muda su innarmu.



A waje muka iske motoci guda uku masu k'yau, da alama sauran motocin sun d'auki jama'a sun tafi.

Saida mukaje jikin motocin sannan aunty Mimi tayi murmushi tana kallonmu, to karnayi abin kunya, wacce ta my k'ani? wacce ta Marwan?.

K'asa mukayi da kanmu saboda kunya, saida ta kuma maimaita tambayar sannan munubiya tayi k'arfin halin nunani, kunyarmu takuma birgeta sosai, hannun munubiya ta kama tana fad'in kece babba ai, zoki fara shiga . a motar farko ta sakata, sannan tadawo takama hannuna ta sakani a ta biyu.

Rufe k'ofar tayi takoma motar bayanmu tashiga. yayinda kuyangin nan hud'u suma suka shiga motar k'arshe.

Tunda nashigo k'amshin turarensa yadaki hancina, ta gefen ido na saci kallonsa, kishin gid'e yake a kan kujerar motar tamkar yasamu gado (dan bansan yama zan musalta muku tsarin motarba nikam, ammafa komai abin kallone) k'afarsa d'aya a k'asa d'aya akan kujerar, kansa na gab dani, dan dazai zame ko motsawa dolene saiya ta6a jikina, sanye yake cikin wasu Fararen suit masu azabar k'yau, sunyi mugun fidda ainahinsa matsayin cikakken namiji mai aji da gayu, aikin danna wayarsa kawai yakeyi tamkarma baisan na shigo motarba, dan ko sau d'aya bai d'ago ya dubeniba.

Nima basarwa nayi nayi tamkar bansan dawata halitta acikin motarba bayan driver.

Shikuwa tun shigowa ta k'amshin turarena yabigi hancinsa tareda shiga magudanar jininsa, a rayuwa yana matuk'ar k'aunar k'amshi, lumshe idanunsa yayi yana lasar lips, amma jinkai da k'asaita ta hanashi d'agowa yako dubeni.



Itakam munubiya tana shiga bayan aunty Mimi tarufe k'ofar yaa marwan jawota yayi jikinsa, tareda sumbatar gefen kumatunta. ta matse jikinta waje guda saboda tsorata, muryata na rawa ta gaidashi.

Ya amsa yana wani kuma shinshina wuyanta da bata wasu kisses d'in.

Mamaki da al'ajabine suka kamata, anya kuwa wannan yaa marwan d'in nanne mai shegen muskilanci da share mutane?, kanta bai ida kwancewa ba saida taji hannunsa indama batayi zatoba, tamkar zatayi kuka tace  please yaa marwan kayi hak'uri dan ALLAH, cikin motane fa .

Rungumeta kawai yayi batareda yayi maganaba.

A wannan yanayin mukaji motocin sun tsaya.

Bayan an bud'e mana duk muka firfito, tsakanina da Galadima kuwa babu Wanda yacema wani kanzil har muka fito.

Yaa marwan da Munubiya ne agaba rik'eda hannun juna, saini da nawa d'an hayak'in Mr k'asaita abaya, harmun fara tafiya Aunty Mimi tamasa magana. banji mitace ba saboda da Indianci tayi maganar=��.

Jinai kawai wani lallausan hannu cikin nawa, dagani harshi babu shiri muka kalli juna saboda shock d'in daya jamu a time d'aya.

Shine yay azamar janye nasa idanun yana cije lips, kafin nima na janye nawa cikeda kasala da luguden zuciya.

Mamakine ya kamani lokacin da muka shigo hall d'in, inda sauran 'yan uwanmu sukene Ashe, sainaji dad'i sosai wlhy.

Nandanan mc yashiga sanar da isowarmu, tunda muka shigo kallo gaba d'aya yadawo kanmu, musamman mutane dake son ganin Galadima a yau.

Can saman hii table muka isa muma, mazaunin daya kasance namu, su Safara'u tamkar su saka ihu saboda ganin yanda muka had'u tamkar bamuba, duk sai suka raina nasu kwalliyan dukda suma sunyi matuk'ar k'yawu kuwa..

Bayan mun zauna angunan suka taso suna kawo gaisuwa wajen Galadima, fuskarsa d'auke da murmushi yake amsa musu tareda mik'a musu hannu suyi musabaha, koda sun nok'e saiya kamo hannun nasu da kansa.

Bak'in ciki tamkar yakarsu Halimatu, ganin angunansu suna kai gaisuwa wa Galadima, basusan hakan dole bane agaresu kodan kasan cewarsa d'an masarauta wandama ake da yak'inin zama sarkin gobe idan da rai, idanma badan hakan ta kasanceba ta ina suka Isa ganinsa balle ma har suyi gaisuwar Baki da baki harda musabaha. Aishi adaline ma tunda harya iya halartar taron nasu.

Yayunama duk saida sukazo suka gaisa dashi, mazan da matan, sannan mukayi hotuna, su Zarah da siyama matan 'ya'yan senator kam ai yau saikikaji tsit babu felek'e, dan mazajen nasuma ko zuwa basuyi wajenba, kamar yanda basu halarci tasu dinner d'inba lokacin aurensu.

Aunty Mimi dakanta ta kar6i microphone tabada hak'uri da neman alfarmar tafiyarmu, saboda suma mutanensu nacan suna jiran isowarmu, dama munzone domin kar6ar excuse.

Hakkane yad'an rage fushin wasu, sannan mun tafi dawasu acikin yayunmu maza.

Mun tafi kowa yana yaba tsarin namu.

Yanzuma haka muka tafi tamkar wasu kurame, saidai yanzu a zaune yake, yajingina kansa da kujera ya lumshe idanu.

Nikam gefe na maida kaina ina kallon titi.

Yanzun kam koda motocin suka tsaya bamu fitaba, sai kusan mintuna 10, Ashe lokacin harsu munubiya da yaa marwan sun shiga, saura mu kuma.

Bamu fitoba saida akayi knocking glass d'in gefensa, ahankali ya sauke glass d'in batareda ya bud'e idonsa ba, wanine yalek'o yana fad'a masa mu fito, duk bud'e mana motar akayi dagani har shi sannan muka fita.

Zagayowa yayi inda nake tsaye, a mamakina da al'ajabi sai kawai naji ya sak'alo Hannunsa a k'uguna, cikeda firgici nad'ago na kallesa, saiya sakar min harara dawani munafikin murmushi, saika rantse da ALLAH kallon soyayya yamin, nikam dukda kwarjini dayamin saida na turo baki gaba da hararsa a kaikaice, ALLAH ma yasoni baiga hararba.

Ahankali muke tafiya saboda Alk'yabbata, yayinda kuyangin ke watsa wasu flowers masu k'amshi a inda zamu taka, aunty Mimi kam da wata daban santaba suna feso mana Abu mai k'amshi.

Kai jama'a wajen taronnan fa ya had'u, k'arshen had'uwa kuwa, an k'awata wajen da kwalliyar white and Golden colors, yayinda kwalliyar jama'ar wajenma white and Golden colors ne, (suma mutanemu dasukazo wajen dama ankawo musu kaya irin kalar).

Mazan sunsha wankan white suit, takalmansu da agoguna zuwa tie duk golden, matan kuma white gown ta material sai d'ankwali golden.

Yayinda tamu shigar ta kasance golden gaba d'aya, su Galadima kuma sun saka white suit, komai nasu white ne shida yaa marwan.

Tunda muka shigo wajen ya d'auki tafi, yayinda aka saki wak'ar da aka raira domin mu. (Bara nad'an raira muku kad'an>�%�=��).



*_Alk'awari yacika munubiya alk'awari yacika.... yacika yacika munaya alk'awari yacika amarya...._*

=�D�iya nan na iya to>�t��&<���
@&



Gaba d'aya sai wani tsoro da kunya ya kamani, nafara tafiya ahankali tamkar kazar da kwai ya fashema aciki.

Bansan lokacin da Galadima ya rankwafo kainaba, dan tunanina yatafi wajen mamakin yanda suketa shiryama auren shekara 1 wad'annan bidi'oin.

Jinai kawai an d'aukeni cak, ihu kawai aka sanya awajen da uban tafi, yayinda aka kuma sakin sabon kid'a na musamman.

Runtse idanuna nayi kawai zuciyata na kai kawo tamkar zata fito waje saboda mamakin munafuncin Galadima. (Yo inba munafuci ba miye na d'aukata agaban jama'a, bayan ni da shi ko magana bata had'amuba=��).

Bai direniba sai a kujerar da aka tanada domin mu.

Anan d'inma zama yayi yasakani jikinsa, kunya da haushi duk sun cikani, wlhy badan karna kunyatashi ba dayasha mamaki. Gashi sai wani magana yakemin k'asa-k'asa kai kace ta arzik'ice, nanko duk gargad'ine wai na kama kaina karnayi abinda wani zai fahimci ba auren soyayya bane a tsakaninmu.

Baki na tunzuro gaba dan haushi, yasaka d'an yatsa ya d'alli bak'in nawa.

Naji zafi wlhy kuma.=��



Abun ALLAH wadai bai k'areba saida akazo yanka cake, bayan su munubiya sun gama nasu cikin mutunci da yaa marwan saimuma muka yanka namu, maimakon yabani kamar yanda na bashi sai kawai yasa Wanda yaciro a bakinsa, bayan yayi tamkar zai bani, harna bud'e baki zan kar6a saiya lunk'uma a baki, nanma mutane suka Sanya dariya da tafi.

Wai kawai ina hararsa saboda haushin abinda yayi sai kawai naji fuskata cikin tafin hannunsa, kafin nayi wani yink'uri ya had'e bakina danashi waje d'aya yajuyemin cake d'in daya gama narkewa da yawunsa a bakinsa.

Bai cire bakinsaba saida ya tabbatar na had'iyeshi sannan.

Ai wlhy ihun yanzun yafi na ko yaushe, abokansa harwani kirari suke masa, yayinda wasu keta d'auka a hotuna, Munubiya kanta kunshe fuska tayi a alk'yabba tana dariya, duk miskilancin yaa marwan saida ya dara shima.

Aikam saida nayi hawayen bak'in ciki, mugu kawai yabani k'azantar yaunsa nasha, wlhy badan mutaneba saina k'ak'aro amai kuwa.

Daya bani drink ko k'insha nayi, ya rankwafo kaina bakinsa saitin kunnene yace,  bakiji sharad'inaba kenan? ALLAH shima zan zuba abaki na juye miki shi a bakinki yanzunan. Ai babu shiri na kar6a kuwa.

Daga nanne Samha taje wajen mc ta kar6i microphone wai tanason saka gasa tsakanin Uncle Sam da Uncle marwan, za'a shigar damu wani d'aki, bayan mintuna biyu mu fito, kowa ya nuna matarsa, duk wanda ya canka dai-dai shine yaci gasar, shikuma zata bama k'yautar.

Galadima jiyay tamkar ya mangare Samha, sai antaya mata harara yakeyi itada Sauban, dan yasan wannan munafurcin sune suka kulloshi.

Ai kam k'in kallonsa sukayi sunata k'unshe dariya.

Dole yanda sukace d'in haka akayi, muna shiga aka gyaramin janbakina da Galadima ya tsotse, sannan aka kuma feshemu da turararurruka saboda kowance k'amshin turaren mijinta daya manne mata yabar jikinta.

Kujeru aka ajiye mana muka zauna, kowacce taci serious.

Da Galadima aka fara, gabansa sai dukan sittin-sittin yakeyi, danshi da gske ba iya gane ni zaiyiba, inba na nuna halin nawa bane.

Aiko ya nuna d'aya acikinmu, mik'ewa tayi takoma gefensa ta tsaya, amma bai ta6a ta ba, dan ba'asan wacecenba acikinmu.

Shima yaa marwan rikicewa yayi, dama mafi yawan lokuta ta halayya yake ganemu, shima dai wadda Galadima yabari ya nuna.

Bayan suma sun koma gefe aka koma kan za6in Galadima, mc yace  zamu iya Sanin wacece? .

Murmushi munubiya tayi, cikin sanyinta tace  Munubiya ce .

Juyowa Galadima yayi ya kalleta, sanyinta ma kawai ya isa tabbatar da gaskiyarta.

Nima aka tambayeni cikeda Jan aji nace  Munaya ce .

Nanama ihun akayi, cikinsu babu Wanda ya canka dai-dai, dan haka ni da Munubiya su samha suka bamu wata k'yauta dabamusan ko miye a cikiba, wai mune mukayi wining.

Daga nan aka rufe taro da addu'a aka tashi.

Har gida suka maidamu muda tawagarmu, lokacin 1:15pm.

Muna zuwa kowa makwanci kawai ya nema...............
'<���







Irin wannan dogon page haka=�(�=�F�<���, shikenan harda na gobe na had'a muku kenan=�D�.

�&<���
@&�&<���
@&



















*_Ya ALLAH ma gafartama iyayenmu_*=�O�<���=�-�

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 1�





.......Har safiyar yau jikina sai k'amshin turaren Galadima yakeyi, feena dake kwance kusa dani tace,  Mrs Galadima! k'amshin nan nakufa yayi over .

Harara Na dalla mata, tareda kai mata bugu ta kauce tana dariya, Bilkeesu ma dariyar takeyi,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login