Showing 231001 words to 234000 words out of 365757 words

Chapter 78 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1484

matan Sarki da sauransu Galadima babu wani bayani, zuwa yanzu ma wasu sun fara tunanin kodai yama mutu ana 6oyewane kawai.

Wajen 8:00am Dr Yaseen Ali Modibbo babban likitan zuciya da akeji dashi ya iso, bisa kiran da Dr jalal ya masa yafad'a masa, dan abubuwan da sukaima Galadima bai farfad'oba Akash yakuma sanarma likitansa, shine yace tofa gaskiya Kodai asamo ainahin likitan zuciya ko kuma su taho dashi kafin cikar awanni 12, idan ba haka ba komai zai iya faruwa.

A k'iyasin da sukayi cikin awanni 12 bazasu Isa india ba, tunda duk tsiya sai an samu jirgi mai tafiya, sannan ma kafin komai ya biyo baya. Hakkane yasaka Dr jalal kiran Dr Yaseen Ali Modibbo d'in, cikin amincin ALLAH kuma ya amsa zaizo d'in, saikuwa gashi ya iso.

Canjama Galadima d'aki akayi, dukkan kayan aikin da Dr Yaseen yazo dasu aka shigo dasu, rufe d'akin sukayi suka duk'ufa su uku kansa suna taimakon Dr Yaseen d'in.

Sun jigata kwarai da gaske kafin zuciyar Galadima tafara bugawa k'asa-k'asa, sai numfashinsa yafara fisga yana k'ok'arin fita. Duk ajiyar zuciya suka sauke. Suka cigaba da aikinsu, ana sakama Galadima wani abu a k'irji kamar dutsin guga, saiya girgiza sannan a cire, akuma maidawa. Basu barsa ba saida yasaki wata ajiyar zuciya mai matuk'ar sauti, harsu mai Martaban dake falo saida suka jiyosa kuwa.

Wannan ne yasaka zukatan doctors d'in uku sanyaya, Dr Yaseen da Dr jalal suka had'a baki wajen fad'in  Alhamdulillah! .



Numfashin Galadima ya dawo dai-dai, amma sun masa allurar barci danya samu nutsuwa.

Yaranma an kawosu ne Dr Yaseen ya kuma bincikawa, shima dai yace suna da ransu, amma Abdurraheem yanada ciwon zuciya shima, shiyyasa yafi sauran y'an uwansa jigata, ALLAH nema dai yay rabon yanada sauran numgashi, amma allurar tamasa k'arfin da zata iya dakatar da bugun zuciyarsa. Suma dai sun kuma samun taimako, musamman ma dai Abdurraheem da tausayinsa ya kama mutane da yawa a wajen.





*_2:00pm_*



Zuwa wannan lokacin Munubiya da mama Rabi'a da Ayusher Feena duk sunzo masarautar, Hakama baba k'arami da daddy, dan an sanar musu samo yaran da halin da galadima yake ciki.

Amma saboda kara irinta Abba da innarsu Munaya sai suka bar su Baba k'arami da maman Fauziyya da mamansu yaa Hameed, maman Safara'u suka taho, sai innaro da gwaggo Safiyya.

Ba'a barin wani bak'on fuska shigowa masarautar a yau, amma su sai mai Martaban yasa aka shigo dasu, basu samu ganin ko d'aya a cikin su Munaya ba, saidai Munubiya da aka shigar d'akin galadima inda Munaya ke kwance, Sauran kuma sun shiga ayarin y'an zaman jigum-jigum da jiran tsammani.



Har zuwa wannan lokacin Galadima da Munaya babu Wanda ya farka, Amaturrahman da Abdurrahman dai sun farfad'o, sai dai suna kuka ko fita bayayi.

Wanka laraba ta musu aka gasa musu jikinsu sosai, yau dai dole aka nemo madarar da Galadima bayason susha d'in, ita aka dama aka basu sukasha, aiko sun shata sosai dan yunwa sukeji, bayin ALLAH, rabonsu da abinci tun jiya da rana kusan I war haka d'in.

Tausayinsu ya kama Munubiya dake basu madarar, tana yi tana sharar hawaye, da da farko nono inno tace ta basu, sai papi yace,  a'a kar ayi wannan gangancin, dan ba'asan abinda ALLAH zaiyiba wataran, ko akwai k'addarar aure a tsakanin yaransu, kar azo ayi Dana sani a watarar da baza'a iya maido wannan ranarba balle a gogo 6arnar da akayi .

Kowa ya gamsu da wannan magana, dan haka Muftahu yafita suka nemo madara shi da Saleem.

Shine aka basu.





Baiwar da aka kami da mutumin kuma suna hannun police, kuma kowa yaji cewar tana cikin bayin gidan wad'an da aka aminta dasuma sosai, saidai ba'asan ta wane sashe bace.

Wannan Abu ya tsurar da zukatan Sauran bayin, dan dolene ya shafesu.



Hankalin Uwargidan Sarki Sarauniya Zulfah (mahaifiyar su matawalle) a tashe yake, amma dayake ta iya takunta bazaka ta6a fahimtar haka ba, saima nuna tsantsar damuwarta akan lamarin da tayi fiye da sauran matan Sarki. dama kuma tafi nuna kulawarta ga Galadima kowa yasan wannan, shiyyasa babu Wanda yakawo wani Abu game da ita, saima wasu daban ake zargin.



Munaya da Galadima sun farfad'o ne kusan time d'aya, amma Galadima ya riga Munaya, dama allurar awanni 4 kacal aka masa, da Sunan ALLAH a bakinsa ya farka, sannan yafara kiran yaransa d'aya bayan d'aya yana fad'in karsu tafi su barsa..

Rik'eshi Dr Yaseen yayi yana fad'in  ka kwantar da hankalinka ranka ya dad'e, dan zuciyarka tana cikin yanayin jiran k'iris ne, inamaka albishir da cewar yaranka suna raye, yanzu nan zakagansu insha ALLAH ..

Galadima ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kallon Dr Yaseen, ya lumshe idonsa a hankali sannan ya bud'e, hanunsa ya d'ora akan saitin zuciyarsa saboda wajen yamasa matuk'ar nauyi.

Ana haka Dr jalal ya shigo d'auke da yaran biyu, dan Abdurraheem shi yanan a d'akin kusa dashi bai farfad'o ba.

Tunda Galadima yaga yaran sa suna a raye saiya kuma rungumesu a k'irjinsa da Dr jalal ya d'ora masa, wasu hawaye masu zafi suka gangara gefen kunnensa.

Dr Yaseen yaji dad'in kukan da Galadima d'in yakeyi, dan zai rage masa rad'ad'in da yakeji da nauyin zuciyar, hakan ya nuna aikinsu zaiyi k'yau insha ALLAH.

Galadima ya dad'e rungume da yaran, saidaga baya ya farga babu guda d'aya.

A hankali ya bud'e baki yana fad'in,  ina d'ayan? .

Murmushi Dr Yaseen yayi, yace,  gashi a gefenka yana barci shima .

Juyawa Galadima yay ya kallesa, ganin d'an cikin yaron Na motsi alamar fitar numfaahi sai dad'i ya kuma ratsashi, ya lumshe idonsa yana yun k'urawa zai tashi zaune, taimaka masa. Dr Yaseen yayi, yatashi rik'e da yaransa, kwantar dasu yayi sannan ya matsa ga Abdurraheem hannunsa dafe da k'irjinsa har yanzu, rankwafawa yay kan yaron ya sumbaci goshinsa da kumatunsa, sannan ya shafa kansa la66ansa suna motsawa alamun yana masa addu'ar fatan samun lafiya a garesa shima.



A 6angaren Munaya Itama tana farkawa da kuka ta farka, tana kiran yaranta, itadai afad'a mata idan sun mutu kawai saita hak'ura.

Rungumeta Munubaya tayi tana lallashi da mata albishir d'in dawowar yaran garesu, hakan yasaka Munaya d'agowa da sauri tana kallon Munubiya,  Sweetheart da gaske kikeyi? .

 da gaske nakeyi Sweetheart, yanzu haka suna tare da mahaifinsu .

Dad'i ya ratsa Munaya, ta kuma k'ank'ame Munubiya suka rungume juna suna kuka da dariya lokaci d'aya.

Hakan kuma saiya sanya su inno kukan tausayinsu da sha'awar wannan k'aunar juna nasu.

Saboda su mai Martaban sun shiga wajen Galadima sai akace ita Munaya tayi wanka kozataji k'arfi kafin su fito.

Bata musaba ta amince, ruwa mai zafi laraba ta had'a mata, tashiga wankan. Tanayi tana kukan farin ciki. bata cuci kantaba tayi wanka sosai ta gasa jikinta.

Kafin ta fito an gyara d'akin tsaf, sai k'amshin daddad'an turaren d'aki yakeyi, babu kowa duk sun fice.



Su mai Martaban suna tare da Galadima, sunyi farin cikin tashinsa, hakama yaran. sunkuma yima Abdurraheem addu'ar tashi shima. Sun d'an jima a d'akin, dan har saida aka shigo dasu Dady da baba k'arami, Yaa marwan, Yaa Hameed suma suka gaidashi da masa jajen ALLAH ya kiyaye gaba sannan suka fita gaba d'aya.

Daga nan manyan irinsu mama Fulani, inno matana Sarki da sauran su duk suka shigo suma, harda su innaro da akaita kuka.

Galadima dai Kansa kawai yake iya d'agawa, idonsa a lumshe. Baya buk'atar kallon kowa a cikinsu.

Su inno duk tausayinsa ya kamasu.

Innaro aka share hawaye tace,  barka da arzik'i kaji, ALLAH ya kiyaye gaba, ya shiga tsakanin nagari da mugu, ya tona asirin duk makirin dake cikin wannan satar yara .

Duk da amin suka amsa. Galadima ma yace amin akan la66ansa. sai tunani yake ina Munaya take?, dan hankalinsa yafara tashi da rashin gilmawarta, musamman daya tuna a halin daya tafi itama ya barta.

Yadai kasa daurewa ya bud'e baki da k'yar yace,  Mom ina Munaya wai? .

Saida mom ta matso da kunnenta sannan tajishi, tasan yana lafiya ma ya aka k'are da k'asaitar magana balle yanzun. Murmushi tayi, tace,  tana d'aki, itama sai yanzu ta farka, dan dole aka sake mata allurar barci bayan tafiyarka, waccan bata dad'eba ta saketa .

Tausayin Munaya ya kuma kamashi, ya jinjina kai yana yunk'urawa zaune sosai. Cikin yamutse fuska yace,  Mom nima yakamata nayi wanka Na rama sallolin dake kaina .

Mom tace,  to bara a kira su Muftahu su kamaka  .

Kansa ya girgiza mata da mata alamar, zai iya da kansa.

Mom tace,  Alhmdllh . Rigarsa ya jawo yasaka, dan da dagashi sai best. d'aukar Abdurrahman da Amaturrahman yayi ya fito, yabar mom tana gadin Abduraheem dabai farko ba. babu kowa a falonsa Dan duk sun fice.

Da k'afa ya turo k'ofar, Munaya Na zaune a bakin gadon rik'e da mansa zata shafa amma dukta kasa, burinta taga halinda Galadima da yaranta suke ciki kawaine damuwarta, gashi har yanzu babu Wanda yazo yakirata akan su papi sun fita. bud'e k'ofar ya sakani d'ago ido. Zummbur na mik'e tsaye ganin Galadima rungume da yaran, ai yau nama manta dawata kunyar towel na d'aura, hawaye suka shiga zarya tsakanin idona da kumatu, Galadima ya tako a hankali zuwa gareni idonsa a kaina. Da sauri namatso garesa nima, nahad'ashi shi da yaran na rungume ina sakin kuka mai k'aramin sauti.

Shiru yay kawai ya zubama gashinta ido yana tausaya mata daga ita har yaran, ansakasu a yak'in dabasu San mafariba, ya godema ALLAH da yarannan sunada sauran numfashi a duniya. Da baisan yanda zaiyi da munaya ba. Ganin kukan nata zaiyi yawa ya bud'e baki da k'yar yace,  ya isa mana .

d'ago idanu nayi na kallesa, cikin muryarta data dishe saboda kuka nace,  Nagode yalla6ai, dasun mutu nima mutuwa zanyi .

Murmushin gefen baki yayi, cikin d'age gira d'aya yace,  dama ana sonmu haka? .

Sai yanzu kunya ta kamani, nai k'asa dakai ina kallon k'afafunmu.

Bai sake cewa komaiba ya ra6a ta gefena yaje ya shimfid'e yaran akan gado.

bathroom ya nufa yana cire rigar jikinsa, nidai Na k'arasa gadon Na rungume yaran ina sumbatarsu, wani dad'i da tsantsar farin ciki Na ratsani, Na d'aukesu Na fara shayar dasu ko zasu rage nauyin da sukamin, aikam kamar jira sukeyi suka kama sha. Hannun rigar namijin Na d'aga saboda tanan muke gane shaidarsu, ganin Abdurrahman ne saina fara tunanin ina Abdurraheem shikuma?, hankalina yaso tashi amma saina daure ina jiran Galadima ya fito naji daga garesa.

Galadima dake kallonta bata saniba ya d'an cije lips, ya tabbatar yanzu tana son yaransa, amma baisan miyasa take ignoring d'insu ba idan yana waje? Kokuwa tsabar jan ajinne oho?.

Har Lokacin daya fito wankan tana shayar dasu, ta shafa kan wannan ta shafa Na wannan, sosai suka birgeshi itada yaran, jin kamar motsi yasakani kallon wajen, da sauri na janye yaran daga bakin nono naja towel d'in na rufe abinna ina turo baki gaba.

Baki ya ta6e yashiga takowa inda muke, ya rankwafo kaina ruwan fuskarsa yana d'iso min a jikina, a kasalance yace,  wane darene jemage bai ganiba malama, tunkan su sha ni........ .

Da sauri na saka hannu na toshe masa baki.

Zama yayi yana janye hannunna, cikin waro idanu yace,  to mikike tunanin zan fad'a? lallai kinfi k'arfina, niba can Na dosaba to .

Sosai naji kunya, na sauke yaran a kan gadon na sakko, zuciyata cikeda mamakin sa, ya d'aure fuska yana basarwa yayta sakin magana kuma kamar bashi yayiba.

Ficewata nayi bayan na d'auki bathrobe d'insa na d'ora akan towel d'in jikinna.

Wani kallo ya bita dashi yana ta6e baki, kafin ya maida ga yaransa daketa kalle-kalle, ya shafa kumatunsu sannan ya mik'e zuciyarsa na tunanin su Momma, addu'arsa d'aya kar wani ya sanar musu.



Kasa fitar nayi saboda jin kamar da mutane a falon da zanbi ya sadani da 6angarena.

Badan nasoba tilas Na dawo baya.

Galadima dake gaban mirror yana shafa mai yana kallonta ta ciki, amma sai yayi biris tamkar bai gantan ba.

Komawa nayi na zauna a bakin gado ina tunanin mafitar yanda zan samu kaya, da jin haushin sharenin da yayi.

Ana haka mukaji knocking, saida ya kalli Computer d'in yaga Mom Ce d'auke da Abduraheem sannan ya mik'e yana amsawa..

Zuwa yay ya bud'e mata, bata shigoba ta mik'a masa yaron da har anmasa wanka Ashe, ta mik'a masa kaya a leda tace na Munaya ne.

Galadima yace,  mom ya tashine? .

 ya tashi, tunma fitowarka babu dad'ewa, harma an masa wanka .

Sumbatar kumatun yaron yay yanama mom sannu



Idonsa akan yaron yana kuma sumbatar goshinsa cikin lumshe idanu ya k'araso inda nake dana zuba musu idanu cikeda sha'awa.

Kusa dani ya zauna ya d'ora minshi akan cinya. nima rungume kayana nayi na sumbaci goshinsa, inason bashi abinci amma inajin kunyar Galadima, gashi ya zubamin ido yak'i tashi.

Lura da hakan dayay ya sakashi yin miskilin murmushi ya mik'e yabar wajen.

d'an hararan bayansa nayi ina fad'in mugunta dai babu k'yau a kan la66ana..................
'<���







 Hummm fans nasan kwace wai ina Harun ne?>��, kumuje zuwa dai danjin ina ya shige haka? Ita kuma sarauniya Zulfah (uwar gidan Sarki mike matsalarta)?.=�(�=��

















*_Ya Rabbi ka gafarta ma iyayenmu_*=�-�=�O�<���

*_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���2� 8�





............A yanda Na kula har yanzu bayajin dad'in jikinsa, dan komai a d'an wahalce yakeyinsa, koda ya fiddo kayan daga wardrobe saiya dawo bakin gadon ya zauna ya dafe Kansa, kallonsa nayi cikin damuwa nima, Na cire Abdurraheem Na kwantar, sannan Na mik'e zuwa garesa, durk'usawa nayi Na d'ora hannayena akan gwiwarsa,  yalla6ai lafiya? .

Shiru yamin kusan minti 1, harna fidda ran samun amsa ma na yunk'ura na mik'e da nufin barin masa d'akinma duka.

Hannuna ya rik'o, na juyo na kallesa, har yanzu yana yanda yake baiko d'ago motsa ba.

Na cije lips ina had'iye kukan dakeson zubomin, rayuwar nan tasa bana sonta wlhy, ni y'ar dangi Ce, nariga natashi gidan yawa, dukda gidanmu bahagon gidane mukanyi hira koyayane, amma shifa magana ma idan bai ra'ayiba wahala take masa, Abu na damunsa a rai amma bazai iya fiddashi yaji sauk'iba, Momma ta had'ani da aiki, a watannin baya kad'an kamar yafara canjawa, amma gashi yakuma birkicewa yanzu, tayaya Momma take tunanin zan iya canja Galadima? murd'ad'd'en mutumne shi mai wahalar sha'ani, ga tsantsar mulki da k'asaita da suka zama jinin jikinsa, s.........

Tunanina ya katse lokacin danaji an jawoni, nai firgigit saboda fad'awa danayi jikinsa, shikuma yay baya ya fad'a kan gadon, kad'an ya rage mu danne Amaturrahman, yad'an kauce kad'an yana sauke ajiyar zuciya.

Uffan bai ceminba ya maida idonsa ya lumshe.

Mamakin wannan lamari ya kamani, hannu yasaka ya kwantar da kaina a k'irjinsa yana d'an buga bayana da d'ayan hannun, zanyi magana ya d'ora yatsunsa hannunsa uku na tsakkiya akan bakin alamar nayi shiru. banida za6in daya wuce yin shirun, nabisa yanda yakeso.



Yanayin da zuciyarsa ke bugawa sai yabani tsoro, na saka hannuna na danne wajen sannan na d'ora kaina bisa hannun, ajiyar zuciya yayi yana cizar lips..

Tsawon mintuna 3 muna a haka, har knocking d'in k'ofa akayi amma baiko motsaba bai barni na motsaba, na yunk'ura zan tashi ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login