Showing 324001 words to 327000 words out of 365757 words

Chapter 109 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1536

inaga hakanne yasaka Galadima d'an sakewa yaci abincin, dukda bama wani Na kirki yaciba, Dana nuna damuwa saiya kalleni.

 Karfa ki damu, inhar ina mura banajin dad'in komai, haka take wahal dani .

Cikeda tausayawa Na masa sannu, nima duk saina kasa cin abincin.

Spoon d'in hannuna ya kar6a, da kansa ya koma bani abaki, dukda marairaice masan da nayi akan Na k'oshi bai saurareniba, baikumayi maganaba, saida ya tabbatar Na k'oshi da gaske sannan ya barni.



Kowa yaci ya k'oshi yay nak Alhmdllh, muka fito da ledojin kayan mak'ulashen da Yaa Marwan shima ya saima kowa, dan kud'in abincin Galadima ya biya.



Dagananfa muka damk'i hanya babu sanya, dan burinmu mu Isa Nigeria a yau, wancan zuwanma dan bamusan inda muka dosa bane.

Aikam dai tafiya tayi riba, dan salla kawai muka tsaya mukayi, Azuhur da la'asar muka had'a muka kuma damk'ar Hanya, bayan magrib muka shigo Nigeria, nanma mun tsaya munyi sallar Magrib da isha'i, daganan muka cigaba, abinci ma sai saya akayi kowa yaci a hanya.

Yanzunma dai Galadima baici Na kirkiba, dan bayajin dad'in bakinsa, da gaske Mura batai masa da wasa kam, dam duk bashida wani sukuni.

Sai wajen 2am muka shiga namu garin, zuwa lokacin kowa yayi ligif, ga gari tsitt, sai motoci jefi-jefi Na matafiya irinmu, saikuma manyan motoci masu d'aukar kaya.

Gidanmu aka nufa, saida aka fara saukemu harsu mama Rabi'a anan, Fadeel Yaa Marwan da Abbansu ne kawai aka nufi gida dasu su kam, shima Galadima masarauta aka juya dashi, sama-sama mukayi sallama Na fita, tausayinsa Na cin zuciyata, yana buk'atar kulawar matarshi matuk'a, amma ya zanyi.



Duk y'an gidanmu sunyi barci, sai tsirarune suka fito y'anson ganin dami mukazo?. To babuma abinda aka fitar daga mota, kowa dagashi sai handbag d'insa ya fita.

Koda muka shiga kowa wajen kwanciya ya nema, dukda sashen namu yad'anyi k'ura, amma bamu damuba, Inda zamu kwanta kawai muka karkad'e.



*******



Galadima yana shiga gida ruwan zafi ya had'a yay wanka, kozai sami sauk'in ciwon da jikinsa ke masa, yad'anji dama-dama kam, ya nema kayan barci masu kauri ya saka, dan muma dai nand'in cikin sanyin ake, gadonsa ya haye, ya shige bargo yana sauke numfashi da k'yar, babu dad'ewa barci yay awon gaba dashi.





Washe gari



Bamu tashiba sai kusan 12, su innarmu ne kawai suka tashi da wuri, y'an gidanmu anata shigowa musu sannu da zuwa, kowacce jikinta saiya fara zanyi, dan yanda muka dawo 6ul-6ul damu kad'ay ya Isa basu amsar muna cikin k'oshin lafiya, kuma inda mukaje wajene mai daraja.

Duk wadda ta fita saita nufi gidan Innaro da nufin mata sannu da zuwa, ammafa dason jiyo gulma.



Tab hajiya Innaro mai abin mamaki, zama tayi tiryan-turyan tana basu labarin garar arzik'i da wacece Inna. Ta rik'e ha6a tana tafa hannaye da fad'in  Yo Niko koda naji wannan halin dattako Na Ai'sha, Ashe jinin sarautace , shiyyasa duk shirmenkunan bata shigarsa, maganama saitaso ta kula maiyinta, duk shirme ya rufe mana idanu bamu fahimtaba, lallai yau naga tushen arzik'i Na gaskiya ba hayeba, nayarda da masu iya magana dakance duk Wanda yace shine to bashi bane wlhy..... .

Innaro dai taita zuba musu labari babu k'ak'k'autawa, sukam sun kume motsin kirki summa kasa, a yanda su inna suka dawo kawai ya Isa ya tabbatar musu da gaskiyar innaro d'in.



Tunaninsu bai kuma birkicewa ba saida aka shiga fiddo tsaraba daga motocin da muka dawo dasu, kowacce saita shige d'aki ta koma lek'e ta window itada y'ay'anta>�#�.

Zarah da siyama da har yanzu suna gida, a sanyaye suka shigo gaida su inna, duksun rame sunyi duhu, dan kowacce tana son mijinta, amma gidajensu sun gagaresu komawa, dan bayan tafiyar su Munubiya saiga takardun saki daga mazajensu su duka.

Duk munyi mamakin yanda sukai laushi da fita hayyacinsu, amma bamuce komaiba, muka tarbesu kamar yanda muka saba a ko yaushe. Nidai wlhy duksai tausayinsa yama kamani.

Su Ayusher sukai shirin tafiya gida, iya abinda zasu iya d'auka suka had'a Yaa Marwan yazo ya kwashesu..

Suna tafiya nima sai hankalina ya koma ga mijina, waya Na d'auka Na kirashi dan naji Yaya jikinsa, harta yanke bai d'agaba, nakuma kira dai...



Galadima Na kwance zazza6i ya rufeshi, tunda yay sallar Asubahi yakoma yakuma k'udundunewa a bargo, cikin barci yaji wayarsa Na ring, kasama motsawa yay balle ya d'auka harta tsinke kiran yakuma shigowa, hannunsa ya tura k'ark'ashin filon da k'yar ya jawo wayar, yabud'e ido kenan ta katse, harzai ajiye saikuma yaga my mata, kiranta yay yamaida idonsa ya rufe yana saka wayar a kunne batareda yayi maganaba.

A sanyaye Munaya tace,  Yalla6ai are you okey? .

 My Queen! . Ya kira sunana a hankali ba tareda ya amsa tambayar dana masaba.

Sautin muryarsa kawai ya tabbatar min da lallai bashida lafiya har yanzu, rikicewa nai nacigaba da jera masa tambayoyi, babu wadda ya iya amsamin saida yaga nak'i inyi shiru yace,  relax dear, zan samu sauk'i karki damu .

Hawayen da suke zubamin Na share, Na tabbata abinda zai kwantar da Galadima ligif haka ba k'arami bane, inhar yazam ba ciwonsaba to lallai abin ya girmama.

K'arasowa innarmu tayi da sauri cikin d'akin d'auke da Amaturrahman dake kuka, dukta rikice ta shiga tambayata lafiya?.

Dole Na yanke wayar ina duk'ar dakai da saurin goge hawayena. Nace,  Innarmu shine baida lafiya har yanzun .

 Ya salam, murardai? .

Kaina Na d'aga mata. Amaturrahman ta d'oramin a cinya tana mik'ewa.  To ai bakiga ta zamaba kuwa, bara Na sanarma abbanku .

Ban iya cewa komaiba Na fara shayar da Amaturrahman ina share hawaye.

Bansan miya faruba kawai naga Munubiya ta shigo tana had'a kaya, da tambayata ya jikin nasa?.

Na amsa mata ne kawai cewar da sauk'i amma badan inada tabbacin hakanba.

Itace take sanarmin wai Su Abba sunce muma mu shirya kawai mu koma d'akunanmu tunda andawo lafiya, zaman wankan ya Isa kawai...............
'<���













ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���







=ء�HASKE WRITERS ASSO....





f&RAINA KAMA...!!f&

(Kaga gayya)





Bilyn Abdull ce>��<���





BOOK 3 =�I�<���2� 5�





.................Da mamaki Na kalli Munubiya ina kwantar da Amaturrahman. Nace,  Komawafa Munu? .

Tsayawa tayi daga shirya kayan da take tana kallona da mamaki,  Ban ganeba, bakison komawar ne? Dakikemin wannan banzar tambayar? .

Baki Na zum6ura ina fad'in  Nikam dai bazan koma haka siddan ba, sai inhar yazo ya warwarema iyayena komai gameda tubalin daya k'ulla aurenmu a farko, yakuma basu hak'uri .

Kasa magana Munubiya tayi, saima ta zauna a bakin gadon, ita batasan wajen ubanwa Munaya ta d'akko halin taurin kai ba wlhy, ita tama rasa mizata ce mata.

Nima d'auke kaina nayi gefe Dan ina kan bakana, ina tausayinsa Dan koba komai ya k'yautatamin a lokacin da nima banida lafiya, kuma ta silata yake kwance yanzu, to ammafa hakan bazai zama yasha a banzaba, kenan ma anan gaba wasu zasu iya aikata hakan ga kowacce mace?.



Laraba dataji komai dake faruwa tana niyyar shigowa saita koma da baya gabanta Na fad'uwa, ita bataga laifin Munaya ba, dan wannan shine martaba da sanin ciwon kai, kuma wannan ya tabbatar mata da ba kwad'ayine yasata zama da shiba, amma bata fatan abinda zai girgid'a wannan Auren komai k'ank'antarsa waya ta d'auka ta kira Mom ta sanar mata komai, hankalin mom ya tashi, danba ta wanann hanyar takeson Munaya ta hora Galadima ba, bakuma taso iyayenta su Sani, suma sunada burin d'aukar mata mataki itada Momma, Dan bazasu bar wannan gangancin Na Galadima ya wuce a banzaba.. Momma ta kira tace Dan ALLAH ta kira Munaya tabata hak'uri akan ta koma, Dan babu mai kula da Galadima d'in, insha ALLAHU daga baya wannan maganar za'ayita.

Momma ma duksai ta damu, dan har cikin ranta tana k'aunar Munaya, bazataso wata matsala ta tasoba bayan hankalinta ya kwanta akan zamansu.



Munaya suna tare da Munubiya har yanzu a d'aki, ta balbaleta da masifa kamar ta daketa, Munubiya tanada hak'uri, shiyyasa idan tana masifa dolene kasan takai k'arshen 6acin rai, Munaya saita zuba mata ido kawai takasa cewa uffan, ana cikin hakane kira ya shigo wayar Munaya.

Harzata share saikuma ta d'au tana dubawa, ganin Momma tai saurin d'agawa tana share hawayen da suka zubo mata. Cikeda girmamawa kamar yanda ta saba ta gaisheta.

Daga can Momma ta amsa cikin kulawa itama, face,  Kun dawo lafiya d'iyata? .

 Alhmdllh Momma ya jikin Abie .

 Jiki kan Alhmdllh d'iyata, dama Abbanki ne ya kirani akan zaki koma, saboda Muh'd babu lafiya, da farko dai nayi tunanin cewa a barki harsai yazo yafad'a musu laifin daya aikata agaresu, saikuma nayi wani tunani daga baya, kiyi hak'uri ki koma yaud'in Dan ALLAH, saboda Mura bataima Muh'd da sauk'i, namiki alk'awarin zan d'auki mataki da kaina, zan sanar masa Ku tahoma gobe idan ALLAH ya kaimu kinji .

Bazan iyama Momma musuba har abada, Dan nasan bazata cutar daniba, saidai kuma nayi mamakin dama tasan auren Contract mukayine?.......

Katsemin tunani tayi da fad'in  d'iyata idan kinga zaki cutu abari kawai, bazan ta6a bari Muh'd ya cutar dakeba wai danni Na haifesa wlhy .

 A'a Momma Na amince .

Daga can Momma ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in,  Alhmdllh, d'iyata nagode sosai, ALLAH yay miki albarka kinji .

Idona cike da kwalla Na amsa da amin.

Tace Na gaida mata kowa ta Yanke wayar.



Munubiya dukda ta fahimci dawa Munaya tayi waya batace da ita uffanba, tacigaba da had'a musu kaya kawai.

Ciwonsa ne yasani Na danne zuciyata Na amince, dakuma Kimar mahaifiyarsa danake gani, Dan sun nunamin dukkan k'aunar da inhar Na bitilcemusu banma kaina adalciba nima.

yinin ranar gaba d'aya a hidimar shirin komawa mukayisa, ga gajiyar tafiya Na nuk'urk'usarmu, amma ya muka iya, da yamma dole su mama Rabi'a suka dawo domin mana rakiya.





A gurguje please>�(�=��.







******



Abin mamaki sai gamu da rusar kuka ni da Munubiya, saikace wasu sabbin amare, bayan nasiha da Abba da baba k'arami, daddy sukai mana Na ajiye musu keys d'in motocinsu, da farko sunce bazasu kar6aba Na sanya musu kuka.

Innaro tahau musu fad'a babu k'yau maida hannun k'yauta baya ai, wannan aikin shaid'anne.

Albarka dai munshata kam, yayinda zukatan matan gidanmu yakusa babbakewa saboda bak'ar hassadarsu, kowa son samunshi ace d'ansane yayi.

Laraba ma harda hawayen sabo, dan bak'aramar girmamawa aka mata a gidannanba, har abada bazata ta6a mantawa da dattako irinna inna ba.

Kaf matan gidanmu dasu aka tafi, innarmu da Innaro kawai aka bari, amma hardasu Siyama.

Ni suka fara rakawa, ALLAH ya somu muka iske Muftahu yadawo daga yawonsa zai shiga masarautar, da taimakonsa muka shiga, yayi mamakin dawowata, dan Galadima ya sanar masa muna Niger, shi baisan yadawoba ma, hasalima babu Wanda yasan Galadima ya dawo masarautar, tunda ko salla bai fitaba, sai hadimansa kawai.

Ba sashenmu akai kainiba, Muftahu ya sanar musu sai an fara kaini wajen mama Fulani sannan, haka al'adar masarautar take.

Aikam dai hakan akayi.

Tarba ta mutunci mama Fulani tasa akaima dangina, tana nandai yanda kuka Santa da mulkinnan nata da izza, amma ni a yanzu tunda Na fahimci ita ba muguwa bace sai salon nata yake k'ayatar dani.

An min dukkan yanda al'adar masaurat ta tanadar, sannan mama Fulani dakanta tamin rakkiya sashena tareda bayi da dangina, ko ina k'al tamkar muna nan.

Bayan fitar mama Fulani y'an gidanmu suka kuma shishshiga suna kallo gida wai, dan ranar suna da suka fara zuwa basu sami wannan damarba saboda idon mutane, nidai batasu nakeba, hankalina nakan mijina, burina naje naga halin da yake ciki.

Munubiya takuma min nasiha da bani wasu dabaru, tunda su sinzama tsoffin hannu, muko yanzune zamuyi zaman auren tsaftatacce, takuma nunamin nabi komai a hankali, tasan yayi kuskure amma bata hanyar tonama kanmu asiri zan nuna masa kuskurensa ba, kodan matsalar gidanmu ai saina duba, ni macece inada damar juya komai cikin sauk'i, nama iya zama dashi a lokacinda yake ik'irarin auren yarjejeniya bare kuma yanzu daya furta yana sona da bakinsa.

Naji dad'in shawarwarinta, nakuma fahimceta sosai, Naimata godiya kuma, da alk'awarin amfani da shawararta insha ALLAH.

Hakama mama Rabi'a tak'aramin nasiha da gargad'i mai yawa akan karsuji karsu gani, Na tsare musu mutuncinsu, Dan kowa da tarbiyyar gidansu yake ado.

Itama na amsa mata da insha ALLAH zan kiyaye.

A y'an gidanmu kam Maman Fauziyya Ce kawai tamin fad'a, amma sauran babu wadda tace nayi mai k'yau ko mummuna, wannan ba matsalarsu baceba, nima ban damuba, Dan wad'anda suka Isa dani sunmin kuma ya wadatar. yayinda zasu tafi rungume juna mukayi da Siyama da Munubiya, Zarah muna hawaye, jimuke tamkar karmu rabu.

Dan wlhy yanzu nikam tausayi suke bani, koma miye dai iyayen su mata da k'addara Ce taja musu.

Inaji ina gani suka tafi suka barni da kewa, danma laraba Na nan.

Suna wucewa laraba ta kalleni, cikin dabarunsu Na tsoffi tace,  koyaya jikin magajin garin? .

Kaina a k'asa nace,  inaga barci yake iya .

Tayi murmushi, Dan kunyar Munaya da kawaicinta Na burgeta, yanda idon yaran yanzu ke a bud'e da rashin kunya a halinyanzu, da watace tuni tanufi d'akin mijin.

tace,  yakamata to kiduba koya tashi, da saiki samu kayan k'amshi ki dafasu, insha ALLAH yasha Na kwana biyu sai murar ta barshi .

Godiya Na mata sannan Na mik'e a kunyace Na fita.

A falon dazai sadani da sashensa naci karo da Muftahu, barka da zuwa yakuma yimin muka kuma gaisawa amutunce.

Yace,  Boss d'in Na ciki kuwa? Dan sarkin k'ofa yace yayi sallama Dan nemamin iso yaji shiru .

Nace,  Ai bashida lafiyane, maybe ma barci yakeyi, mura ke damunsa, amma bara Na duba ka shigo .

Cikeda tausayawa Muftahu yake fad'in  Kai aikam mura Na wahal dashi sosai Idan ta damk'esa, shiyyasa bayason zuwa Nigeria lokaci irin wannan Na sanyi, aini banga ta shigaba, bara naje muzo da doctor jalal daganan nasamo muku abinda zakuci, yanzu haka yinin yau baici komaiba .

Godiya namasa ya juya ya fita, nikuma na nufi k'ofar falonsa.

Tun a falon na tabbatar mai d'akin babu lafiya, Dan komai a kashe yake har AC, Wanda inhar yana gidan AC yini yake yana aiki, koda uake akwai sanyi yanzu, shi ko damunsa bayayi ma, Na k'arasa k'ofar Bedroom d'in, harna kai hannu zanyi knocking kuma saina fasa, tura k'ofar nayi a hankali da sallama Na shiga, d'akin dund'um da duhu gashi bansan ina makunnar fitilar take bama ni, tsaye nayi ina tunanin mafita, na komane ko nayi magan...?



Galadima dake kwance yau yini guda cikin halin ciwon kai da zazza6i, salla Ce kawai ke tadashi, abincima da k'yar ya had'a shayi yasha bayan sallar la'asar, tunda ta shigo yana jinta, saidai baisan wanene ba, shi a tunaninsa ma wanine yazo cutar dashi, jin anyi shiru ankuma k'i magana ya mik'a hannunsa da k'yar ya kunna fitilar dake dirowar gefen gadon.

Baya nad'anyi kad'an danni tsoratama nayi, harma na fara zaton kobaya d'akin, sai kuma na nutsu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login