Showing 69001 words to 72000 words out of 365757 words

Chapter 24 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1479

komai. Wannan dalilin yasaka aka yanke shawarar k'arama munubiya kayan munayar kawai, da safe za'aje a kuma jera mata su a gidanta=��.

Cikin takunsa na kasancewar cikakken namiji mai tashen k'uruciya ga jinin mulki dake yawo ajikinsa yafito, waya ce manne a kunnensa, yayinda d'ayan hannunsa ke cikin aljihun jeans d'insa, bayi da hadiman gidan sai zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa, kansa kawai yake d'aga musu yayinda yake cigaba da wayarsa da Momma wadda tana India ita batazoba.

Samha tak'araso gareshi a hanzarce,  Uncle ka tsaya mana please  .  tayi maganar a shagwa6e saboda ganin ya basar da ita tamkar baima gantaba .

d'an juyowa yayi ya kalleta sannan ya d'auke idonsa yana cigaba da Murmushin sa na k'asaita saboda addu'ar da Momma ke jero musu ta zaman lafiya da samun albarka ta har abada acikin auren daza'a d'aura a gobe. jiyake tamkar yace Momma ta dainama auren shekara d'ayannan addu'a irin haka, shifa harma tausayi suke bashi yanda suke nuna farin ciki da zumud'insu akan auren, musamman idan ya kalli yanda masarautar tagama cika tab da dangi takowanne 6angare, ga tawagar wasu masarautu dasukayo gaba tun yau, hakama 'yan siyasa ba'a magana, dan ba k'aramar gayya papi da Sarki sukaima wannan aurenba, kasancewar shine jika namiji na farko dazaiyi aure a masarautar, Wanda kuma kowa ke saka ran shine magajin sarautar masarautar.

Ita dai Samha tana tsaye tana kallonsa harya kammala wayar da Momma ya kashe.

Had'e fuskarsa yayi yana hararta,  to maganatu miya faru kuma? kike kwalan kira tundaga wata uwa duniya?, wai sai yaushene zakiyi hankali Samha? .

Baki ta tunziro gaba, idonta harya cika da gwalla  amma dai Uncle aina fara yin hankalin ko, kumafa wani Abu Nazo na nuna maka, naje Sashenka wannan sarkin k'ofar yawanice kana wajen mai martaba .

Kansa kawai ya girgiza yana kallonta, saida takai aya sannan yace  to aini inada abunyi, yanzuma ba wai sauraren naki zan zauna yiba, dan nan ba India bane, ba'a ganina available ko yaushe OK? .

Harya juya zai tafi tarik'o hannunsa tana daddaga k'afafu idonta na zubar da hawaye.

Kansa ya dafe domin sanin fitinar Samha, tace,

 please Uncle Sam 2munutes to .

Juyowa yayi tamkar zai maketa, saikuma komi ya tuna ya fasa, d'an cije lips d'insa yayi yana hararta,  ke wai wace irin fitinanniyace ne?, Uwarmi to zaki fad'amin? .

Dariya tayi tana share hawayenta dan ganin tasami nasara, wayarta ta daddana sannan ta mik'a masa.

Nanma Harar tata yayi kafin ya kar6a, itace yagani a photo da 'yammata biyu masu kama d'aya, kamarma yarinyar dasuke shirin auren contract, harya yatsina fusaka zaice suwaye? saikuma yatuna. d'an murmushi basarwa ya saki kafin ya kalli Samha da ta tsaresa da idanu.  Uncle ina aunty Munaya anan?  .

Wayar yamik'a mata yay gaba abinsa yana fad'in titsiye zakimin ma kenan? an fad'a miki bazan ganeta baneba? .

Baki ta turo tana k'unk'uni,  waikai Uncle Sam bazaka ta6a canjawa baneba? kai kenan kullum sai jan ajin tsiya, shiyya sama ALLAH yayoka jinin sarauta wlhy, Aunty Munaya kin bani da wannan mijin naki mai k'asaitar tsiya, aiko wlhy tunda kace haka saina had'a maka mugunta gobe a wajen dinner  .

Ta tuntsire da dariya saboda tuno mizata shirya masa.









&&&&&





*Rana bata k'arya........*�&<���
@&





Yau mun wayi gari safiyar d'aurin aure, gida yakuma d'inkewa da jama'ar dukda d'aurin Auren na Azhar ne bayan sakkowa masallacin juma'a.

Tun jiya banida lafiya, amma na hana su Ayusher fad'ama kowa, sai Magani suka samo min nasha, itama dai Munubiya duk sukuku take, babu abinda ke damummu sai jimamin rabuwa da juna, dan itama kusan zazza6inne ma ta kwana dashi, sai dai dayake nawa ya had'a da damuwa saina fita nuna jin jiki.

Jama'ar gidanmu dai a harmutse suka kwana, wasuma ko barcin basu sami damar yiba saboda ciwon hasada dake cin zukatansu, gashi gida d'inke da jama'ar babu damar matsawa koda nan da canne sai an gane, bare sufita neman mafitar tarwatsa Auren, waddama suke d'an samin tallafinta kwad'ayinta yasaka canja shek'a (innaro>�#�), dan jiya da suke zuba tijara shigowa tayi tamisu tas, harma tana Neman tone musu asiri gaban tawagar 'yan biki, badan gwaggo Safiyya ta lalla6a taba ba'asan inda jarabar innaro zata tsayaba kam.

Ko karyawa ban iya tashi nayiba bare aje maganar wanka, ina kwance cikin bargo sai shar6ar kuka nakeyi babu wanda yasani.

Ahaka gwaggo Safiyya tashigo kiranmu nida Munubiya, da k'yar su Ameera suka samu natashi zaune ina tangad'i, gaba d'aya nayi wujiga-wujiga dani, da taimakon Munubiya dake rik'e da hannuna muka iso gidan innaro inda su Abba suke jiranmu.

Gaba d'ayanmu ne amaren aka had'a, abin mamaki saiga innaro ta kamani ta zaunar tanamin sannu, harda lallashina wai na kwantar da hankalina.

Kowa zuba mana idanu kuwa yayi, su Fiddausi sai jan tsaki suke a zukatansu sunajin wata tsanar innaro aransu.

Itakam bama tasan sunayiba, sai nannan takeyi damu nida Munubiya.

Nasiha mai ratsa jiki da 6argo sukai mana sosai, muhimmancin aure da hak'uri, biyya da tsoron ALLAH, kare hak'in miji da k'yautatama danginsa da iyayensa, k'arfafa zaman lafiya a tsakani da rik'e sirrin miji, banda biyema k'awayen banza sukaika su baroka, musamman ma da dukanmu zamu cigaba da zuwa makaranta.

Gaba d'ayanmu kowa hawaye yakeyi, musamman mani danakejin tausayin kaina dana iyayena dabasu San auren shekara d'aya nake shirin yiba nadawo garesu.

Munci kuka sannan aka sallamomu, tunda muka dawo sai aunty salamah ta saka mu agaba dole mukayi wanka, da k'yar muka amince aka mana simple kwalliya, muka saka dakakken leshin da mama Rabi'a tasa aka d'inka mana cikin kayan biki dasuka mana itada innarmu, less d'in blue ne da fararen bet ajikinsa, sai aka nad'a mana d'an kwalima blue, munyi k'yau harma bansan yazan musalta ba, nan su Ayusher suka hau zuba mana pictures. lokacin 12 tama wuce, masallacin anguwarmu daza'a d'aura auren yagama cika dank'am da jama'a, dayake bashida nisa da k'ofar gidanmu.

Cikin gidanmu kam ai ba'a magana, dan babu masaka tsinke, sai hayaniya kakeji wani bayajin zancen wani, rabin hirar jama'a kuwa duk akan zancen lefe nane da Wanda zan aura, wad'anda suka gani suna bama wad'anda basu ganiba labari.

Su siyama dai koma ganinsu ba ayi, dan suna taya iyayensu kishi da hassada, aunty Ramla da aunty Raihana sai aunty Hauwa'u ne kawai suka shigo sukaima innarmu murna har d'akinmu, amma aunty khaleesa ko k'eyarta bamu ganiba, kuma tunda safe tazo gidan daga ita har zarah, matar yaa hameed ma mama hanata zuwa tayi, dukda tanaso tazo tama innarmu murna amma surukarta takasa ta tsare, gashi bama dad'in zaman 6angaren takejiba, saboda 'yan ubanci na dangin miji da aketa nuna mata, itama matar yaa Naseer tashigo, dan har picture mukayi da ita, amma matar yaa Shafi'u ma bata shigoba.

Hakan duk bai dameniba, dan ni yanzu basune agabana ba, damuwata tarkon dana saka kaina na auren contract shike cazan tunani a halin yanzun, Wanda ko munubiya nakasa sanarma gaskiya lamarin.





*_1:30pm_*



Masallacin yagama cika taban mamaki, tuni tawagar gidan Sarki sun iso tun bayan gama sallar juma'a, d'aurin aurene daya tara manyan mutane ta dalilin gidan sarauta, manyan sarakunan k'asarnan da 'yan siyasa, governors senators attajirai na gida dana k'etare, talakawan gari da tawagar iyaye da dangin sauran angunan, abokan su abbanmu danasu yayunmu, abokan anguna da abokan arzik'i, dangin iyayenmu mata danasu abbanmu, kowa ya hallara, bakajin komai sai kad'e-kad'e da bushe bushe irinna gidan sarauta. president da Kansa ya iso wannan waje bisa gayyatar papi, bansan yanda zan musalta muku irin cikarda anguwarmu tayiba aranar, bama zaka iya gane taka maimai inane ake d'aurin aurenba. Su Kansu masarautar su Galadima sunsha mamaki, basuyi zaton auren Na Galadima zai tara jama'a manyan mutane hakaba, dubi da yanda ba d'iyar wata hamshak'iyar masarautar zai auraba. basu San abin ba anan yakeba wai *d'uwawu yafi fuska k'yawun gani*=�J�>�%�=��=�� inji masu iya magana......................
'<���







Amin afuwa, mu had'u tomorrow danjin yanda d'aurin aurenba zai kaya�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&.





Barkanmu da dawowa=�� '<���>��<���

















*_ya ALLAH ma gafartama iyayenmu_*=�-�=�O�<���



*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 0�





.........A cikinmu Fauziyya ce babba, dan haka aka fara d'aura auren ta, daga nan sai ni da Munubiya, an fara d'aura na Hassana Auwal fharuk (munubiya) da yaa marwan Ibraheem, sannan ni Hussaina Auwal fharuk (Munaya) da Muhammad Sameer Saifudden Abubakar (Galadima), saikuma Safara'u, sai Haleematu, Fiddausice k'arshe.

Ana gama d'aurin auren busar algaitu suka fara tashi, sarkin marok'a yafara zuba kirari wa Ango Galadima sarkin gobe a masarautar gagara badau.

Maganar k'yawun da Anguna sukayi ma 6ata lokacine, kowanne yafito angonsa sak abin kallo da birgewar kowa, duk miskilancin yaa Marwan saigashi yana washe hakwara tamkar gonar audiga=��.

>�%�ance anguna basa kuka ranar aurensu, to kuwa yau saiga Galadima na share hawaye, dukda auren contract yayi nakuma shekara 1 kacal, saiyajisa wani iri daban, ya kuma zama babban mutum, tuno Abie dayayi yasaka hawaye fitowa daga idanunsa, bazai iya tuna tsawon lokacin dayayi kuka na k'arsheba, amma saigashi yau yanayi acikin d'umbin jama'a, akuma ranar d'aurin auren da ya rad'ama suna na (wucin gadi).

Papi ne yad'an bugi kafad'arsa yana murmushin jin dad'i shima, dajin wata k'aunar jikan nasa ta musamman.

Aikam masu videos da photuna ansamu abinyi, hakama masu d'auka awaya ba'a magana.



Kafin kace mi social media ta d'auka, lungu da sak'o hotunan d'auren aurenne suketa yawo, musamman da jama'a ketajin wai wadda aka bugasu a jarida yana kissing ce ya aura, wayyo ALLAH abin magana yasamu a yanar gizo, kowane polder na charts ka shiga zancen kenan dai.

Daga wajen d'aurin aure tawagar gidan su Galadima k'aton hall d'in da aka tanada domin cin abincin bak'i suka nufa, duk wani maiji da kansa zaka sameshi awajenne, Galadima har kansa yafara ciwo saboda yawan magana ta amsa gaisuwar jama'a da murna da yakeyi.

Ana tsaka da cin abincin Momma ta kirashi, dama shi ba ma abincin yakeciba, zaune kawai yake yana juya spoon a plate, wayarsa yaciro daga aljuhun gaban rigar milk d'in shaddarsa, dan tuni yacire malum-malun d'in tana hannun Harun.

Ganin Momma yasashi mik'ewa yafice daga hall d'in gaba d'aya, can waje yasamu wasu kujeru ya zauna sannan yakirata ta video call, tana d'agawa sai kawai ya fashe mata da kuka ganinta zaune kusada Abie.

daga Momma har Abie d'in sagade sukayi suna kallonsa, saida yayi mai isarsa yasaka handkerchief d'insa ya goge fuska sannan Momma tace  ho d'an nema duk murnar aurence kokuwa shagwa6a ce ta motsa? .

Tur6une fusaka yayi zai sake wani kukan Momma ta kwashe da dariya irin wadda yadad'e baiga tayiba, Abie ma murmushin sane ya fad'ad'a sosai. saida Momma tayi dariyar mai isarta sannan tace,  Muh'd kafa girma, kai yanzu babban mutumne, nan kuma da wata shekarar kazama baba, amma katasamu gaba kana kuka? .

Handkerchief yasaka yakuma goge hawayen dasuka taho masa, sannan yace  momma na barka da rana .

 Barkan ka dai angon d'iyata Munaya, ALLAH ya sanya alkairi yabada zaman lafiya yasa bad'i iyanzu munan muna shagalin sunan jikan mai martaba . tayi maganar tana kallon Abie daketa zuba murmushi, gira d'aya ta d'aga masa, shikuma ya k'yafta mata idanu.

Dariya Galadima yasaka musu, irin wannan soyayya haka summa manta dashi.

Gyaran murya yayi sannan Momma ta d'ago tana kallonsa, suka saki dariya lokaci d'aya. yayinda Abie ke tayasu da Murmushi.

Galadima ya tsagaita dariyar yana fad'in  my Abie ya jiki? .

Da idanu Abie ya amsa masa da Alhmdllh, sannan yamasa nuni da ALLAH ya Santa alkairi.

Hannu yasa yarufe fuskarsa alamar jin kunya.

Har aka kammala liyafar cin abincin yana a waje suna hira da parent d'insa, saida papi ya aiko akirasa saboda yanason nunashi wa jama'arsa da basu sanshiba, hakan yabama wasu daga cikin 'yan masarautar su haushi, sai dai basuda yanda zasuyi da wannan tsohon mai k'arfa-k'arfar tsiya da Nuna Isa.

Bayan ya Yanke call d'in yamik'e yabi bayan d'an Aiken, ya iske a hall d'in kuma papi ya had'a wani video call d'in dasu Momma, domin Abie yaga d'umbin jama'ar dasuka halarci d'aurin auren gudan jininsa.

Aiko yaji dad'i sosai harma Momma, harda hawayen farin ciki Abie yayi.

Nandai a kaita zuba masa addu'ar Neman lafiya ga mummunar addu'a ga dukkan masu hannu na shigarsa wannan halin tsawon shekaru, da idanu yake fad'ama Momma magana itakuma tana fad'a musu. Daga nan Galadima yayi jawabin daya ta6a zukatan jama'ar wajen, wasu harda share hawaye, wasu daga cikinsu dasuka San wasu abubuwan daya faru wa tsohon sarki Saifudeen kam duk sai zukatansu suka karye, musamman masu hannu aciki dasuka bada gusunmawa, jin addu'a da alwashin d'ansa Muhammad Sameer dake tabbatar da bazai bar duk mai hannu acikiba, sai dai shima amasa irin na mahaifinsa, hakanne kawai zai iya dakatar dashi.

Abie da Momma Kansu kuka sukeyi daga can suma.



Taron yatashi zukatan wasu cikeda tausayin Galadima da k'udirin taimakonsa, yayinda yasamu k'yaututtuka daga manyan k'asar.

Masu hannu aciki kuwa suntafi da nufin sake shiri akan Galadima d'in, domin aganinsu sunyi sake d'an zaki ya girma, kuma Galadima na neman zame musu *RAINA KAMA......*



https://2gnblog.blogspot.com/



&&&.&.&.&&&





Gidanmu kam tunda aka kammala d'aurin aure labari ya shigo gabana yashiga luguden daka, rungume juna mukayi ni da Munubiya muka fashe da kuka mai ban tausayi, Wanda muka saka jama'a dayawa kukan, ciki kuwa harda Innarmu da mama Rabi'a. babu wanda yace mu bari, aka barmu mukayi mai isarmu, dan kowa yasan dolene muyi irin wannan kukan na rabuwa, dan yau babu fashi dolene mu Rabun, abinda baita6a faruwa agaremuba, kullum a gado d'aya muke kwana muke tashi, kowanne aiki tare mukeyin sa, komai namu iri d'ayane, daidai da pants & bra iri d'aya muke sakawa, idan d'aya bashida lafiya saika d'auka muduka bamuda lafiyar, babu abinda ke banbantamu sai hali, amma yau gashi aure zai banbantamu, jinai inama muma mazane tamkar su Aiyaan, yanda babu mai rabamu d'in.

https://2gnblog.blogspot.com/

Haka dai wannan yinin biki akayishi a wani iri, mu cikin damuwar rabuwa, matan gidanmu cikin hassada da bak'in cikin mun fisu.

danma Su Abba sunyi dogon gargad'i akan wlhy duk wacce tasake tada finina a gidan sai dai ta k'arasa bikin a gidan su.

Wannan furucinne yasaka kowa yin likimo, sai dai fa ta ciki na ciki=�J�=��.

Hotunama da akayi na family wasu fuskar tasu tamkar kashin farar safiya=��>�t�, Innaro kam ai mune nagaban girarta a yau, sai dama-dama takeyi damu, dama komai akayi saitace an kaima Ai'sha dai ko, (=��su innaro anga banza).

Wannan abun datakeyine keta kuma hasala matan gidanmu da 'ya'yansu, itakam ko a ha6ar kallabinta, warkajaminta kawai takeyi na murnar auren jikoki.

Yayinmu mazane kawai babu ruwansu, duk suna cikin farin cikin wannan aure.





Bayan la'asar sakaliya saiga sak'o daga masarata mutane biyu d'auke da akwatina biyu wai sun kawo kayan da zansa awajen dinner ni da Munubiya, sun shirya dinner d'inne mu biyu kawai banda sauran amaren.

Wannan lamari kam ya sosa zukatan mutane da yawa, ni kaina banji dad'in hakanba gaskiya, dan banason su d'auka kamar mun banbanta da sune yanzun, gaskiya da ace inada Number Galadima dana kirashi nace a fasa wlhy, saboda muma anan gidanmu yayunmu sun shirya mana dinner d'in gaba d'ayanmu, duk da ni dama ban saka ran zuwan Galadima ba a wajen.

Gashi kuma gate pass guda 30 kacal suka kawo, alamun basa buk'atar mutane dayawa a wajen kenan, ikuma na nace inhar bada sauran 'yan uwana ba ban zuwa nima d'in.

Lallashin duniya anyi nak'i sauraren kowa, nakafe akan bazan jeba.

Matan gidanmu kam cewa sukayi munafurcine kawai.

Zancensu bai dameniba, nidai ina akan bakana bazanjeba. su Ayusher sun rasa yanda zasuyi dani, dama akwai number Galadima saisu kirasa su sanar masa halin da ake ciki.

Innarmu kam ko k'ala batace daniba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login