Showing 219001 words to 222000 words out of 365757 words

Chapter 74 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1520

cije lips nashi yayi yana janye idonsa.

Ya sauke k'afafunsa yana d'ora laptop d'in saman kujerar, ya d'auki ruwan gabansa yana sha da maida hankali garesu. jin hirar tasu ta y'ammata ce sai ya zuba musu ido kawai bai saka bakiba, dan shi dama ba'a wannan hirar dashi tun can da, suma duk sunsan haka, shiyyasa ko suna shirmensu basa sakoshi.

Ganin zasu saka masa cinwon kai saboda hayaniyarsu Na Neman yin yawa saiya mik'e d'auke da Laptop d'insa.

Duk kallonsa sukayi, Zayyan yace,  ina zuwa daddyn Triple's? .

K'aramin tsaki yaja, da k'yar ya bud'e baki yace,  zaku samin ciwon kaine, zanje nad'an huta kafin time yayi . ya k'are maganar da kallon agogon hannunsa.

Matawalle yay murmushi yana salute nashi, shima murmushin ya masa yana kaimasa rankwashi, ya kauce gefe yana murmushi, (dayake shima bai cika hayaniya ba).

Wuce warsa yay cikin takun nan nasa Na izza da k'asaita, da sauri wasu yaran masarautar dasuka had'a tasu dabar agefe biyu aciki suka taso suka k'ar6i laptop d'in hannunsa saboda girmamawa, ya mik'a musu yana murmushi, yana gaba suna binsa a baya, sai zuba masa surutu suke akan shagalin daza'a sha yau, shidai murmushi kawai yake musu babu magana, basu damuba, dan kowa yasan halin galadima a masarautar nan, haihuwar nan ma wasu da yawa zasu iya cewa sunga hak'oransa a waje. duk inda suka gitta ana kwasar gaisuwa, bayi kam zubewa suke domin girmamawa a garesa.

Har sashensa suka masa rakkiya, sarkin mota ya kar6a laptop d'in ya k'arasa masa da ita zuwa ciki..

Baibi ta ainahin k'ofar da zata kaishi babban falonsu ba, saiyabi wata k'aramar k'ofa da kai tsaye nasa sashen zai shige basai mata y'an suna sun gansa ba.

A falo ya iske Sauban kwance yana barci, da alama yagama yawonsa ne gajiya ta makesa, da kallo Galadima ya bisa, amma dan ya tabbatar da lafiyarsa saiya d'ora yatsunsa biyu a wuyan Sauban d'in, babu zafi, ya maida goshinsa saiyaji zafi sosai, Galadima ya girgiza kai, yasan dama ba lafiyace zata saka Sauban barci a irin wannan lokacin ba ana wannan hidimar.

Bai tasheshi ba ya shige cikin bedroom, zama yay a bakin gadon yana cire bottom d'in rigar guda uku, ya huro isaka daga bakinsa yana zamewa ya kwanta batareda ya cire rigarba, zuciyarsa tana ta jujjuya mi Muftahu yake nufi ne? wace magana zasu tattauna?. waya ya jawo da nufin kiransa, sai kuma ya fasa, jefar da wayar yayi yamik'e yana ida cire kayan gaba d'aya. ya shige wanka.

ya ja adadin wasu mintuna masu tsayi kafin ya fito sanye da bathrobe fara sol, sai k'aramin towel a hannunsa yana goge fuskarsa zuwa wuyansa.

Yana tsaye gaban mirror zai fara shafa mai ya jiyo ana knocking d'in k'ofar falonsa, Computer d'in daya ajiye wadda yake kallon kowane 6angare na sashen daga cctvs cameras d'in daya zagaye ko ina, tun zuwan dayayi Na k'arshe ya saka akayi masa wannan aikin, sannan ya d'auki mataki akan waccan cctv d'in da Munaya tamasa hannunka mai sanda da ita.

Sarkin k'ofa ya gani, sai kuma Muftahu daga can waje alamar yana jiran iso ne.

Guntun tsaki Galadima yayi, ya fito zuwa falo, Sauban dake barci ko motsi baiyiba balle yasan ana knocking d'in. yana daga tsaye yabama sarkin k'ofa izinin shigowa.

Cikin girmamawa yace,  ranka yadad'e yalla6ai Muftahu ne ke Neman iso .

Da hannu Galadima ya masa nuni da ya shigo.

Sarkin k'ofa ya amsa da to sannan ya fice.

Komawa Galadima yay ciki yacigaba da shafa mansa, saida ya gama tsaf sannan ya zira jallabiya Brown ya fito.

A falo ya iske Muftahu zaune yana control d'in television da remote.

Galadima ya zauna a kujera mai zaman mutum d'aya, sai wani d'aure fuska yake.

Muftahu bai wani damuba, dan yariga ya saba da wannan ai.

Kallonsa Galadima yayi cikin lumshe ido yana fad'in  Mike faruwane? .

Ajiye remote d'in Muftahu yayi, ya kalli Sauban dake barci.

d'an ta6e baki Galadima yayi, yace,  karka damu, kayi maganarka kai tsaye kawai .

Cikin jinjina kai Muftahu yace,  Ok, babu abinda ke faruwa saidai shirin faruwar kam, Ranka ya dad'e bamuda isashen lokacin wata magana mai tsawo yanzu, saidai ga wannan takardar ka duba, so yanzu wannan ne akan ga6a, shine yakamata mu d'au mataki akansa, daga baya komi kenan namaka alk'awarin warware makashi, fatana dai ka fahimci wannan d'in saboda had'arinsa .

Kar6ar takardar Galadima yayi, ya d'auki medical glasses d'insa daya ajiye a teble glass d'in dake gefen haggunsa ya saka, duba takardar yay a tsanake, cikin wani yanayi dake nuna tsantsar tashin hanki yace,  Muftahu wannan maganar gaskiya ce kokuwa? karkamin wasa da hankali a wannan karon dan bazan d'aga maka k'afa ba a wannan ga6ar alwashi nane .

Murmushi Muftahu yayi, ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in  Nabaka wannan damar, inhar kayi gamo da sa6anin hakan karka barni da numfashi ranka ya dad'e .

Wani shegen Murmushi Galadima yayi, yamik'e d'auke da takardar ya koma bedroom batare da kuma kallon Muftahu ba.

Tausayin Galadima ya kama Muftahu, mik'ewa yay shima ya fice.



Jefar da takardar Galadima yayi akan gado yana taune lips nashi tamkar zai huhhudashi, wata irin suya zuciyarsa ke masa, lallai dolene ya jinjinama Munaya, dan ta taka rawa wajen shagaltar dashi wanene shi? minene burinsa?, ganin tunani bazai masaba yatashi jikinsa Na rawa yafara wasu had'e-had'en abubuwa, waya ya d'auka ya kira Ayusher, ta d'aga cikin hanzari tana mik'ama Munaya dake shayar da Amaturrahman data tashi daga barci tana kuka.

Kallonta tayi da mamaki tace,  wace Ayusher?....... .

Galadima ya katseta da fad'in  ki kawomin kayanda su Abdurraheem zasu saka . iyakar maganar da yay kenan ya yanke wayar yana cigaba da latse-latse, zuwa can kuma ya ajiye ya mik'e yana cire jallabiyar jikinsa.



Baki sake Munaya tabi wayar da kallo, mike damun galadima haka? Muryarshi irin wadda tasan asalin galadima ce, hakan na nufin akwai matsala kenan? to mine zaiyi da kayan da yara zasu saka?. batada mai bata wad'an nan amsoshin dan haka ta mike tana ajiye Amaturrahman d'in, aiko ta fashe da kuka an cireta bata k'oshiba, tsaki Munaya tayi tana fad'in  ai saikiyi tayi, ku matsala ubanku matsala mutum yarasa wazai kama.

Ayusher da Aunty Salamah suka kalli juna suna gumtse dariya.

Gyale taja ta lullu6a, dama tasaka doguwar rigar matirial kafin dai time ya k'arasa. ganin zata wuce yarinya na kuka Auntu Salamah tace,  dawo ki d'auketa mana, idan kinje can saiki bata nonon .

Tamkar Munaya zata saka kuka haka ta dawo ta kwashi Amaturrahman ta fice tana k'unk'uni.

A falo ta iske Sauban Na barci, wucewa tayi cikin bedroom d'in kanta tsaye, amma saida tayi sallama ya bata izinin shiga.

Tun da ta shigo taga yanayin da yake sai gabanta ya dad'i, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki ta mik'a masa ledar data zubo kayan sannan ta zauna a kunyace saboda yanayin da yake babu kaya.

Ba tare da ya kalleta ba ya hau Fiddo kayan, ya zubesu saman gado yana d'aukar hotonsu a waya, yay latse-latse nawasu mintuna kafin yasaka wayar a kunne.

 Saleem ka dubamin kalar kayannan, koda basu kaisu tsadaba, yanzunan kataho ka kawominsu .

Bataji mi Saleem yafad'a daga canba.

Muryarta a raunane tace,  yalla6ai mike faruwa wai? .

Jajayen idanunsa ya d'ago ya kalleta, k'ala baice mataba ya mik'e ya d'akko wani k'aramin box ya dawo ya zauna, ita duk saima kunya takuma kamata, saboda dagashi sai boxer, amma taga ko a kwalar rigarsa bai damuba, hidimar gabansa kawai yakeyi.

Kwantar da Amaturrahman tayi kusa dashi ta tashi zuwa wardrobe d'insa, k'aramar t-shirt ta d'akko, tazo ta mik'a masa.

Ya d'ago ido yana zuba mata harara, dukda ta tsorata saita daure tace,  please mana yalla6ai . tayi maganar muryarta a raunane.

Saida yayi k'aramin tsaki kafin ya amsa ya saka, wani abu da batasan minene ba taga yana mak'alawa jikin kayan yaran, saida yagama tsaf sannan ya maidasu a ledar, kallon Amaturrahman dake k'yalla y'an idanu zata fara k'aramin kuka yayi, ya shafa kumatunta batare da ya d'auketa ba.

Laptop d'in sa ya jawo ya saka eye glasses d'insa, ya kalli Munaya yamata alama da ido akan tazo.

Babu musu ta taso zuwa kusa dashi ta zauna.

Laptop d'in ya d'ora mata akan cinya yace,  wanene SD a cikin su? .

Nutsuwa Munaya tayi tana kallon hotunan, cikin waro ido tace,  kai ga Fu'ad ai .

Da mamaki Galadima yace,  Fu'ad!? .

 eh wlhy yalla6ai, Wanda ya kaimu birnin gayu plaza ranar da abunnan ya faru .

Kar6a laptop d'in Galadima yayi yakuma kallon hoton da k'yau yana taunar lips, kuma mik'a mata yayi batare da yace komaiba. itama batace dashiba tacigaba da bin hotunan da kallo sannu a hankali. Harta kai k'arshensu babu SD. ta kalleshi cikin damuwa,  yalla6ai babushi fa anan gaskiya .

Kansa ya jinjina mata yana kar6ar laptop d'in, cigaba yay da danne danne, itadai Munaya tana kallonsa.

Kuma d'agowa yay ya kalli Munaya,  duba annan kuma fa .

Kallon hotunan ta shigayi, canko saiga hoton SD, tace,  Alhmdllh gashi anan .

Kallon hoton Galadima yayi, da mamaki yace,  kinsan wanene wannan kuwa? .

 Ah! yalla6ai SD ne mana .

 Munaya kin tabbata wannan ne kika gani a wajen Abba? .

 Wlhy shine yalla6ai, bazan ta6a manta fuskarsa ba ai komai dad'ewa. balle acikin abinda bai rufa 2years ba, amma kasanshi ne? .

Bai iya cemata komaiba, sai zuciyarsa dake wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata fad'o, mamaki ya hanashi motsin kirkirma, Alhaji Shehu Darma shine SD kenan, babban Amini kuma d'an uwa ga Mahaifin su Samha, innalillahi, ya abubuwa keneman koma masa rikid'ar hawainiya haka?, wannan fa Fu'ad d'in d'ane ga yayar Uwargidan Sarki mahaifiyarsu Matawalle, cikin cije lips ya buga hannunsa akan gadon yana fad'in  Kai!!!! miyasa hakane? miyasa duk Wanda Na yarda dashi shike fara bayyana a maicin dunduniyata?!! miyasa rayuwa tazomin da irin wannan rikicin ne?, oh God!! .  ya k'are maganar cikin matsanancin k'araji, tareda runtse hannayensa waje d'aya.

Tsoro ya kama Munaya, ganin yanda duk ya rikice kamanninsa suka canja, idonsa yayi matuk'a jajur, jijiyoyinsa da gashin jikinsa duk sun mimmmik'e, ga Amaturrahman data tsorata lokacin daya buga gadon, d'aukarta tayi tahau jijjigawa.



Sauban ma a firgice ya tashi, ya hau waige-waige, ganin babu kowa a falon saiya nufo hanyar bedroom d'in Galadima, tabbas muryarsa yaji a yanayin da ba'aso. harzai murd'a k'ofar saiya fasa saboda jin kamar muryar Munaya tana magana.



Tunda tasamu Amaturrahman tayi shiru sai ta d'auki towel d'insa ta goyata, ta matsa kusadashi a tsorace, hannunta ta d'ora akan nasa daya dafe mirror, ko motsi baiyiba balle ya kalleta.

Murya a d'arare kuma a sanyaye tace,  please yalla6ai, fushi baisa a samu sauk'i saidai ya k'ara zafi, kaine kasha gayamin wani karatun baya buk'atar fassara ko dogon nazari, akan barsane kawai a yanda yazo, dukda bansan tushen matsalarba zan iya bada gudunmawa wajen kama bakin zarenta, kayi hak'uri ka kwantar da hankalinka, ita fahimta fuskace, ba fushinka ko tsantsar damuwa ne abin buk'atarba yanzu, d'ana tarkon dazai fara kamo maka hannun mak'iya shine jarumta, ka danne kuma ka daure, ni dama Dan banida ikon hana walimar nanne kawai, amma inaji a jikina akwai lauje cikin nad'i, saidai wad'anda suka nad'a d'inne bamuda ilimin saninsu sai ALLAH yaso Samar damu, amma ai duniya makarantace, idan su a can suka yini kaikuma saika nuna musu kwana kayi, lokuta da dama fushinka ke lalata maka aiki, dan inhar kana cikin fushi dukkan aikinka tafiyar hawainiya yake, wannan lagon naka suka samu suke wasa da hankalinka, koda ace wani ya salwanta cikin yarannan karka d'aga hankalinka, ALLAH n daya baka yafika sanin hikimar k'addara hakan, duk lokacinda kaga Matsaloli sun raunana, buk'atu kan kuma kan yalwata ne, kasa a ranka wannan wata damace tazo gareka, ai duk lokacin da aka rasa kwallo a cikin wasa, ba wasan ake dainawa ba, wata kwallon ake jehowa a cikin fili .

Duk maganar da takeyi ko motsawa baiyiba, baikuma juyo ya kalleta ba, saidai alamu sun nuna yana saurarenta, ta janye hannunta ta juya zata fita tana hawaye.

Cak ta tsaya saboda rik'o hannunta da yayi, kusan minti 1 suna a haka, ta waigo ta kallesa, har yanzu yana a yanda yake, kallon hannunsa daya ruk'o nata tayi.

Bai kalletan ba kuma bai saki hannunba yace,  Lallai ina shaidama dukkan Wanda ya maida rayuwata data ahalina magijin kallonsa, zan tsiyayar masa da idanun, sannan zan kacaccala rayuwarsa Na binnesa da ransa . ya mik'e tsaye sosai tareda juyowa ya jawo hannunta ta fad'o jikinsa, saurin dafe Amaturrahman dake bayanta tayi da d'ayan hannun. Ya saka idonsa dasuka firgitata cikin nata, fuskarsa dab da tata yace,  kedai kibama yaranki kariya kawai, dan sune fitilar zuciyar mijinki .. sakin hannunta yay ya zagayeta yabar wajen.

Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo, yayinda zuciyarta keta kuma maimaita maganar tasa, _yaranta, kuma mijinta?_ mi yake nufi to?, amsar itace bata saniba.

Jitai kawai ya saka mata ledar kayansu Abdurraheem a cikin hannu, baice k'alaba yabar wajen zuwa gaban wardrobe d'insa yafara fiddo had'add'iyar Shadda gizna ash colour, sai maik'o take da d'aukar idonu.

Ganin ya shareta yana cigaba da hidimarsa itama saita juya ta fice.

Tunda Sauban yaji motsin kama handle d'in k'ofar yabar wajen da sauri.



Fitarta babu dad'ewa Saleem ya kawo kayanda Galadima ya umarcesa.





__________________________





Munaya Na komawa Aunty Salamah tahau shiryata, dukda taga a yanayin data dawo bata tambayeta daliliba, saida tagama gyara mata fuska tana gyara mata gashi Munaya tafara fad'a mata iya abinda taga ya dace kawai Aunty Salamahr ta iya Sani, sauran kuma sirrinta ne ita da mijinta.

Murmushi Aunty Salamah tayi, tace,  dukda banida tabbacin faruwar wani Abu dagani har Munubiya dama mun shirya hanyoyin d'aukar matakai saboda tsaro, kowa baisan dalilin Munubiya na dagewa akan ki dawo gida ki haihuba, amma ita tasan dalilinta, ba son zuciya ya sakata yin hakanba, Ubangiji Na kallon kowa kuma zaiyi maganin komai, tun a shekaran jiya Saleem yazo mungama tsara komai dama, kuma ya tabbatar min Muftahu yasan komai dan yaga alamar shima tsaye yake da k'afafunsa, inaga yau dai shine yabama Galadima satar amsa, kuma hakan da yayi shine dai-dai, saboda duk abinda zai faru a yau d'innan shi Galadima zai fara zargi .

Munaya tace,  hakane Aunty Salamah, shiyyasa wlhy Muftahu yafara bani tausayi, ALLAH ya kawo ranarda zai wankesa ayi walk'iya aga kowa dai .

Amin ya rabbi gimbiyar Galadima Sameer, ku kwantar da hankalinku, komai kam ya taho gangarar zuwa k'arshe, dan alamomi suna nuna haka .

 nima inajin haka a jikina Aunty Salamah .

Da wannan hirar aka gama gyaran kan tahau shiri cikin less d'inta Ash colour irin kamar kayan da Galadima zai saka kenan.

Hummm masha ALLAH, maganar k'yawun da Munaya tayima 6ata lokacine, amma tayi k'yau.

Yaranma tsaf aka gama shiryasu, abin kamar ka sacesu ka gudu, sunyi fes.



Kowa yagama hada-hadar shiri, ana fitowa daga sallar La'asar za'a fara kwasar mutane zuwa hall d'in da aka tanada.



*_4:00pm_*



Dukkan mai ruwa da tsaki akan wannan taro ya hallara a gaban motocin da za'a kwashi jama'a, ana fitowa daga salla kuwa aka fara tafiya.



Munaya dai tana d'aki bata fitoba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login