Showing 312001 words to 315000 words out of 365757 words

Chapter 105 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1431

Dakatar dashi papi yay ta hanyar kiran sunansa.

Galadima ya amsa masa da k'yar.

 Kayi hak'uri Muhammad kaji, ALLAH yana tare da masu hak'uri, Hayatudden ya sanarmin komai, ALLAH yabasu lafiya, ba shari'ar duniya bace kawai shari'a, akwai babba wadda babban alk'ali zaima kowa, koba komai ALLAH ya kunyatasu tun a duniya, kowa yasan misuka aikata, kuma ka dak'ilesu suda masu burin aikata irin nasu, ka ringa tunawa akwai tonon asirin dayafi wannan, harma abinda yafi wannan da suka aikata akwai babbar kotu mai cikeda d'unbin jama'a da babban alk'ali a gaba, banason kabar wannan abin yayma zuciyarka tasiri haryakai ga kadaka k'asa, sannan karna kumajin kayi kuka, ka kwantar da hankalinka muci gaba da musu addu'a, insha ALLAH gobe zan shigo garin .

Gyad'a kai Galadima yayi tamkar yana gabansa, papi yakuma kwantar masa da hankali da nasiha mai ratsa jiki, saida ya tabbatar hankalinsa ya kwanta sannan ya barsa....



Ya jingina da kujerar yanamai lumshe idanu, wata nutsuwa ta musamman Na ratsa jinin jikinsa da zuciyarsa, knocking glass d'in da akayi ya sakashi bud'e idanu a hankali, ganin sarkin motane saiya sauke glass d'in k'asa, cikin girmamawa sarkin mota ya mik'o masa gorar ruwa.

Bai musaba ya kar6a yana gyad'a masa kai alamar ya gode.

Sosai yasha ruwan kuwa, wata nutsuwa takuma saukar masa, ya kuma d'aukar kamar 5minutes ya fito daga motar, ya koma cikin asibitin, yanson ganawa da doctor d'in, idan yaji bai gamsu da aikinsaba dolene yasan mai yuwuwa.



Yana shigowa su Ahmad suka k'araso gareshi suna gaidashi da jajanta masa.

Cikin k'arfin hali yace,  baku tafi gida bane? .

Sarkin mota dake tsaye kusa dasu yace,  Ranka ya dad'e ai Ahmad shine ya taimakeni nakawo camera d'in kotu d'azun .

Da mamaki Galadima ya kalli Ahmad yana nunashi da d'an yatsa alamar kaid'in?.

Murmushi Ahmad yayi yana gyara tsayuwa. yace,  Uncle bayan fitowa daga kotune za'a hutunnan sai naji wani yaron su Abbana yana waya akan atare su Aunty a kar6a Camera d'in, dan basa buk'atar ta k'araso Court d'in, to hakan danaji shine Na k'arasa garesa Na bigi cikinsa akan zancen .

 nake cemasa zamuje ni da su Ahakam muma a kwato Camera d'in damu, so hakan dayaji saiya d'auka da gaske tare nake dasu, shine yabani key d'in mashin. Ina ajiye driver d'inka, sai mukazo asibiti ni da Yassar muka sanarma da Uncle d'ina, shine ya bimu da Ambulance har wajen da abun ya faru muka d'akkosu .

Galadima ya kamo hannun Ahmad ya rungumesa, yayma su Yassar dake kallonsu alamar suma suzo, cike da farin ciki suma duk sukazo jikinsa.







__________

https://2gnblog.blogspot.com/



Hankalin mai martaba a matuk'ar tashe yake, jin wai dan kawai yayi mulki wasu suka bada gudunmawa domin durk'usar da d'an uwansa,  hazbinallahu wa ni'imal wakil wannan wace iriyar masiface hakan?.

Sai safa da marwa yakeyi a bedroom d'insa, idanunsa Na kwarar da hawayen tausayin d'an uwansa da Galadima, ALLAH Sarki mahaifiyarsa, yadad'e yana zarginta akan ciwon d'an uwansa, Ashe babu hannunta a ciki, son zuciyar mahaifinta ne, Wanda a yanzu haka tsufa ya kamashi sosai. Waya ya d'auka ya kira Abba hayatuddeen danyaji wane hali d'an d'an uwansa yake cikine? Dan yayi tsumayen shigowarsu masarautar amma yaji shiru.

Bugu biyu Abba Hayatudden ya d'aga. Mai martaba ya tambayeshi suna inane?.

Abba hayatudden ya amsa masa da vewar gasu a cikin asibiti, Dan mutanen su Alhaji Mansur sun saka an tare matar galadima a hanya itada Nuridden yayin kawo Camera Court.

Kasa magana mai martaba yayi, saboda jin kuma wani sabon zaluncin, Wanda suka aikata baya baima ishesuba kenan.

Abba Hayatudden ma bai kuma cewa komaiba saboda yasan ran yayan nasa ya 6aci.



Mama Fulani kanta yau cikin damuwa take, bata ta6a tunanin mahaifinta zai iya aikata hakanba, dukda tsantsar son datake da burin y'ay'anta suyi mulki bazataso duk'usar da Saifudden akan hakanba, shekaru 26 bawan ALLAH Na kwance yana jiyya tamkar gawa, banbancinsa da gawar fitar numfashi, wannan wane irin son zuciyane su jinin sarauta sukeyi? Shikenan saboda sarauta sai aita halaka juna?  Ni Marawuyya wannan wane irin burine mai cutar da imani.......





Lallai zato zunubine koda ya zama gaskiya=�"�, kiyi hak'uri mama Fulani munata zarginki Ashe ba haka bane>��>�&�<���
@&.







.............................&





A gidansu Munaya ma hankalinsu a matuk'ar tashe yake, gasu Abdurraheem nata kuka, dan tunda Munaya tabar gidan suke kuka, kukansu ya tada hankalin Munubiya dasu Inna sosai, lokacin da aka harbi Munaya bak'aramar fad'uwa gaban Munubiya tayiba, ta mik'e a zabure tana dafe k'irji, number Munaya tashiga nema, dan taji a jikinta wani mummunan abu ya faru da y'ar uwarta.



Lokacin da labarin abinda ya faru da Munayar ya iso garesu mafi yawan jama'ar gidan saida suka koka, Dady kuma ya hana kowa zuwa asibitin, saisu mazan kawai sukai shirin zuwa, gashi basusan wane asibitin bane.



__________



Iyalan su waziri hankalinsu a matuk'ar tashe yake, hakama su Alhaji Sageer, ga duniya tanata ALLAH wadai dasu, gaba d'aya yau kowacce kafar yad'a labarai da social media maganar kenan, su kansu sauran manyan kowa ya shiga hankalinsa, dan lamarin yayi matuk'ar girgozasu, suna yabama basirar Galadima matuk'a, gashi yabi ta hanyar da babu Wanda yata6a zaton zata 6ille masa yayi nasara, inhar za'a iya samun irinsa a yau, to lallai wataran za'a samo Wanda ya fisa ma.





....................&



Yanda masarautar su Galadima take a harmutse gameda wannan lamari haka tasu papi ma ta gama harmutsewa, dan lamarin ba'a cewa komai, cin amanar da waziransu sukayi yayi matuk'ar girgiza masarautun, bakajin komai sai gutsiri tsomar bayi da dogarai, harma da manyan gidan ba'a barsu a bayaba.

Tashin hankalin da papi da inno suke ciki ba'a magana, ga Sauban ya tasasu gaba yanata kukan son zuwa yaga halin da Munaya da Nuren suke ciki, harma da yayansa.



Dukda an hana fad'ama Su Momma amma saida labarin yakai musu, aranar aka nemama Aunty Mimi ticket d'in tahowa Nigeria, Samha nata kuka itada Khaleel zasu biyota, amma bata sauraresuba, dan hankalinta a matuk'ar tashe yake.



............................&





Doctor da kansa ya fito yayma Galadima iso cikin office nashi, bayan sun zauna doctor ya kalli Galadima cikin alamun damuwa, yace,  ranka ya dad'e da farko dai ina mai baka hak'uri akan zaluncinsu mijin y'ar uwata, ALLAH yay maka babban samako da sayya agaresu .

Murmuahi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.

Doctor ya kuma gyara zama yana fad'in  Alhmdllh jikin namijin babu wata babbar matsala, yanzuma mun saka masa alurar barcine cikin ruwan danya huta sosai yasamu nutsuwa, daya farka Normal zaku gansa. Ita kuma akwai harbi da akai mata a hannu, amma Alhadullh mun samu nasarar cire harsashin, tafin hannunta kuma shima anji mata ciwo, dan yatsunta Na tsakkiyama duk sun samu karaya, amma shima an gyarashi, maganar gaskiya ranka ya dad'e bazan 6oye makaba, tasamu buguwa akai, dan ALLAH ne ya tak'aita batasamu wata babbar Matsala a brain ba, saidai ahalin yanzu dukkan wani motsi mai k'arar sauti bama buk'atarsa kusa da ita, insha ALLAH inhar za'a kiyaye cikin kwanaki kad'an komai zai iya dai-daita, takuma dawo normal kamarma komai bai faruba, zamu bata dukkan kulawar daya dace da izinin Ubangiji. daganan har kwanaki uku zuwa hud'u zata kasance a halin barci, dan hakanne kawai zai girmama nutsuwar da muke buk'atar ta samu d'in, kai kad'aine kuma zaka ringa shiga d'akin .

Galadima ya lumshe idonsa tausayin Munaya da yaransu Na kuma mamaye jinin jikinsa da kowanne ga6a, da k'yar ya iya bud'e baki yace,  Doctor! Kana ganin zaku bata dukkan kulawa?. Sannan tanada yara jinjirai, yaya kenan za'ayi? .

Insha ALLAH ALLAH ranka ya dad'e, dan munada kayan aiki a asibitin mu, dakuma kwararrun likitocin da zasu iya aiki a kowacce k'asa, maganar yara inaga inhar akwai mai kulawa dasu acigaba da basu madara har ALLAH yasa ta farfad'o, saboda mu yanzu matsalarmu kawai shine motsin dazai iya farkar da ita ko wanda zaiyi tasiri cikin brain nata .

Gyad'a kai kawai Galadima yayi, yabama doctor hannu sukayi musabaha, daganan ya fito.



Kuma ficewa yayi daga cikin asibitin, Sarkin mota yay saurin biyo bayansa, da hannu yamasa alamar yashiga mota suje.

Dukda sarkin mota baisan inda suka nufaba haka ya amsa cikin girmamawa.

Saida suka fara tafiya ya sanar masa inda zasuje.

yana nufi gidansu Munaya dan yaga halin da yaransa suke ciki.



Munubiya da kanta ta fito masa dasu itada Ayusher, tausayin su ya kamashi matuk'a, musamman ma Munubiya, dan tayi wujiga-wujiga.

Cikin k'arfin hali yace,  kiyi hak'uri Sister, muyi musu addu'a ita kad'ai suke buk'ata a wajenmu, yanzu yaza'ayi dasu Amaturrahman? Dan nakula kamarma yunwa sukeji? .  yay maganar yana kallon yaran da sukayi barcin wahala bayan sun gama shan kuka .

Share hawaye Munubiya tayi. tace,  Yakamata a nemo musu madara, idan kuma Na shayar dasu to shikenan .

Galadima ya jinjina kansa yana fad'in  Bamusan hikimar da ALLAH ya 6oyeba a gaba, karmuyi ganganci, bara kawai a nemo madarar, dan dolene su kwana anan, ita ba'ason mata hayaniya yanzun, maybe ma harnan da wasu kwanaki, saboda ta bugu a kanta, kuskuren kwakwkwaran motsi zai iya shafar brain nata .

Munubiya takuma fashewa da kukan tausayin y'ar uwarta, hakama Ayusher, shi kansa Galadima dauriya kawai yakeyi, danma ya 6oye idanunsa cikin eyeglasses shiyyasa basa ganin nasa tsantsar damuwar.

Muftahu ya kira ya sanar masa a samoma su Abdurraheem Madarar da zasu ringa sha.



Daga nan gidan yabaro akan cewar Muftahu zai kawo, yakuma rok'esu akan Abdurraheem, dan ba'ason yacika yawan kuka.







A gurguje please=��=��



_________



BAYAN KWANAKI UKU

https://2gnblog.blogspot.com/

A kwanaki ukunnan fad'ar tashin hankalin da bayin ALLAH suke ciki 6ata lokacine, musamman ma Galadima da har wata uwar rama yayi lokaci d'aya, hakama Munubiya da innarsu, Nuren dai ya farka tun washe garin faruwar lamarin, kuma jikinsa Alhmdllh yanata murmurewa, saidai tausayin d'an uwansa daya addabi ransa.

Ko abinci Galadima bayasonci, sai Aunty Mimi ta turkesa tana bashi abaki, shima baifi yay lauma biyarba yace ya k'oshi. tayi-tayi kuma ya kafe, garama idan tea ne, shima sai an had'a da lallashi, babu abinda ke addabar ransa irin damuwar Munaya da yaransa, sukansu duksun rame, danma suna samun tsantsar kulawane ta kowanne fanni.

Papi yazo ya dubasu, hakama su mom da iyayen su Nuren d'in da y'an uwansa, mai martaba ma da daddare yazo cikin 6adda kama ya dubasu.

Mama Fulani ma kullum saitazo, a matan Sarki gimbiya Zulfah Ce kawai batazoba, Dan kunyama ta hanata walwala gaba d'aya a masarautar, Mai martaba kuwa ya hanata hanyar ganinsa gaba d'aya itada y'ay'anta, sai matawalle kawai daya nuna damuwa akan abinda kakansu da mahaifiyarsu suka bada gudunmawa wajen aikatawa wan mahaifinsa, sanan yay ALLAH wadai akan son zuciyarsu, koda yaushe yana tare da Galadima da Muftahu a asibitin, da wata buk'ata ta taso kafin Galadima yayi shi yayita.



A koda yaushe Momma cikin kira take taji yaya jikinsu Munaya, koda wasa ba'a sanarma Abie komaiba, Dan ana ganin cigaba da haske game da jikinsa sosai, ba'a fatan wani abinda zai maido da hannun agogo baya game da ciwon nasa.

Addu'oi kam sosai aka duk'ufa yinsu game da Munaya, wadda har yanzu Galadima ne kawai keda alhakin shiga ya dubata, shima sau d'aya a rana kawai, yau dai duk ake saka ran farkowarta, Dan an dakata damata dukkan wata allura dake sakata barci, saidai kuma har dare babu wani bayani.

Zasu tayar da hankalinsu doctor yace suyi hak'uri, maybe zuwa dare ko safiyar gobe ta farka d'in, danba a sume takeba, barcine kawai da sune suka sakata ta hanyar mata allurar.

Badan hankalin nasu ya kwantaba sukai shirun, har lokacin barinsu asibitin yayi babu wani bayani game da farkawar tata.



Washe gari.





Duk dai yanda akaso farkawar Munaya a ranar sai a washe garine ALLAH ya amince da hakan, Alhmdllh anci nasarar farkawar tata yanda ake buk'ata, saidai ciwukan jikinta a halin yanzu.

Saida doctors suka gama dukkan kai kawonsu naganin komai ya ida daidaita sannan aka bama Galadima damar shiga.



Tamkar mai sand'a haka ya shiga d'akin, tana kwance amma idonta biyu, sai dai a lumshe suke, an kuma cire mata bandejin da aka zagaye mata fuska, sai kad'an aka bari inda ciwon yake.

Durk'usawa yay a gaban gadon, ya kamo hannunta Na haggu dakeda lafiya ya saka nashi ciki, a hankali ta bud'e idanunta saboda jin tattausan hannunsa cikin nata, ga k'amshin turarensa daya mamaye d'akin Wanda ya tabbatar mata da shid'inne, tana shak'a a hankali.

Idonta ta saka cikin nasa, kowanne yakasa koda kwakwkwaran motsi tsawon mintuna 2, a hankali Galadima ya bud'e baki tamkar mai rad'a ko gudun wani ya jisu yace,  Munaayaa I love you, I really love you, I love you more and more my Heartbeat..

Lumshe idanu Munaya tayi, wasu hawaye suka gangaro daga cikin idanu zuwa gefen kunnuwanta, zuciyarta sai wani irin bugawa take da sauri-sauri, ta kuma damk'e hannunsa cikin nata tana maijin tsigar jikinta Na tashi, jininta sai yamutsawa yake a kowanne 6angare. Kuma bud'e idon tayi a kansa, suka sakarma juna lallausan murmushi ga hawaye Na zuba a idonta har yanzu, shima kwalla sun tarar masa a cikin ido sun saka idon wani k'yalli Na musamman daya kuma sakama munaya wata kasala da tsantsar k'aunarsa, ya lumshe idanunsa alamar tabbatar da abinda ya fad'a mata har cikin ransane ba iya fatar bakiba.

Itama hawayen ta kuma matsowa, ta bud'e baki da k'yar tana cigaba da kwararo hawaye. Tace,  i love you too yalla6ai, I love you so much... .  takai k'arshen maganar wani kukan Na kwace mata.

Hannunta dake rik'e cikin nasa ya sumbata yanamai jin farin ciki, yace,  ki kasance dani Munaya, ki kasance dani har k'arshen rayuwata, ke Katanga tace, haskena ce, farinciki nace, duniyata ce, duk duniya kece mace ta farko bayan mahaifiyata da y'ar uwata danakema so Na musamman, please karki barni uwar y'ay'ana, karki gujeni komai rintsi, nima namiki alk'awarin kasantuwar mu tare har k'arshen numfashi, ki rayu dani, ki mutu dani bugun zuciyata, kamar yanda nima burina kenan a gareki tsawon lokaci .

Lallai yau daba'a halin ciwo takeba har rawa sai tayi, Wanda bata ta6a tsammani ko tunanin zaisotaba shine yake furta wad'annan dad'ad'an kalamin agareta, shine yake rok'onta ta kasance dashi har k'arshen rayuwarsa?, shine yake kiranta katangarsa?, harskensa, bugun zuciyarsa? Koda a yau tabar duniya ta ribantu da nasarorin masu yawan da wahalar k'ididdiga wajen lissafi.

Galadima dake share mata hawaye da hannayensa ya duk'a ya manna mata kiss a goshi da saman la66a.

Ta kuma bud'e idonta da suke jajur akansa, murmushi suka kuma sakarma juna, ya girgiza mata kansa alamar tabar kukan, idanunta ta lumshe alamar amsawa.

Shikam ya tsura mata idanu ko k'yaftawa bayayi, y'ar ramar da tayi saiya k'ara mata k'yau da k'uruciya, ya shafa k'ananun kitson dake kanta ta kuma bud'e ido tana kallonsa.

Cikin d'age gira d'aya yace,  baki tambayi ina yaraba? .

Lallausan murmushi ta kuma sakar masa, ta kwanto hannunsa dake sark'e da nata saitin bakinta ta sumbata, sannan ta d'orasa a saman k'irjinta.

Tausayinta ya kamashi sosai, domin jikinta akwai zafi har yanzu, ga abincinsu sunyi matuk'ar cika, Wanda zazza6in nata yanada nasaba da rashinsu gareta, dukda akwai Na zafin ciwo.

Hakan da tayi shima saiya fahimci mitake nufi, kuma duk'owa yay ya sumbaci goshinta, zaiyi magana doctor ya shigo.

Shiru Galadima yay ya juyo yana kallonsa, itama Munaya daga kwancen take kallon doctor ta k'asan ido.

Doctor dake gulma da zuciyarsa yana fad'in lallai ya yarda, duk sarautar Sarki a gaban matarsa bawane, matarce ke zama sarauniya..... (Ga naku Matan kwarai sarakin duniya=�M�<���=�L�<���=��)

Galadima ya katse tunaninsa ta hanyar buga yatsunsa biyu suka bada sautin d'as-d'as.

Doctor ya dawo hayyacinsa a kunyace. Yace,  sorry ranka ya dad'e, dama Nurse zata goge mata jikine da kuma gasa mata, Dan tasamu sauk'in nauyin da yay mata .

Murmusawa Galadima yay, ya zare hannunsa daga cikin Na Munaya yana mik'ewa tsaye, hannayensa ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login