Showing 156001 words to 159000 words out of 365757 words

Chapter 53 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2759

Mi Dahiru da Naja'atu zasu ba dariya ba, suka shiga shek'ama innaro dariyar shak'iyanci. Wai kota kwanta da yunwa ne.

Zaginsu ta hau yi ta d'auki filon kujera tana dukansu.

Sai da gwaggo Safiyya ta musu magana sannan suka nutsu,  inna ina zakuje da Jafaru ne? .

Gyara zama innaro tayi tashiga bama gwaggo Safiyya labari.

Murmushi kawai gwaggo Safiyya tayi, danta gane wayo suka mata suka gudu kawai, itama sai tace  to inna ki cigaba da jiransu, k'ila dan sunga kina barcine suka jira ki tashi sannan Ku tafi.

Da wannan gwaggo Safiyya ta rufe bakin innaro ta zauna jiran su dady.





Aiki>�#�>�#�=��.







**********





Galadima daya fita kai tsaye asibiti ya nufa, su yaa hameed kawai ya iske can, dan dady ya hana matan gidan zuwa sai anjima, doctors Na complain akan suna cika wajen da yawa.

Cikin mutunta juna Galadima ya gaisa dasu yaa sabi'u sannan yashiga yaga daddy.

Yau kam Alhmdllh dan ba barci yakeba, kumbirin fuskarsa kuma yad'an sa6e kad'an, saidai baya iya magana sai dai yayta bin mutane da idanu.

Dukda bazai iya amsawa ba haka Galadima ya risinna ya gaidashi, tare da masa fatan samun lafiya sannan ya fita office d'in doctor.

Bayan sun gaisa doctor ya bama Galadima file d'in bayanan Abba dasuka tattara.

Kar6a Galadima yayi ya duba, dukda bawai ya fahimci bayanan bane, ( kusan dai rubutun doctors sai su). Suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu sannan Galadima ya fito.

Ya iske daddy ya iso, suka gaisa sannan yamasa dukkan bayanan da doctor yamasa shima. Dady ma yaji dad'in cigaban da aka samu.

Galadima yay musu sallama ya fito.



Guntun tsaki yaja saboda yanda jama'a suka wani zuba masa idanu tamkar sunga magiji, da sauri wani dogari ya bud'e masa motar ya shiga, sannan suma suka shiga.

Daga asibiti Galadima yace su wuce birnin gayu plaza.

Cike da girmamawa sarkin mita ya amsa da to.

Maida kansa yayi jikin seat ya kwanta tareda lumshe idanu ya fad'a duniyar tunani................
'<���







Barkanku da juma'a=؋�=؋�=؋�>��<���.







Musha weekend lafiya sisters�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&=��.











*_ALLAH ka gafartama iyayen mu_*=�O�<���=�-�

*_Typing=���_*







*_Haske writer's asso...._*=ء�









*_f&RAINA KAMA......f&_*

_{Kaga gayya}_







*_Bilyn Abdull Ce_*>��<���



_________________________

_Duk marubucin daya kafa alk'alaminsa bisa takarda tabbas yagama tanadar yanda labarinsa zai kasance ne, amma sai wasu wabubuwan mamaki kaga sun gaza k'arewa a social Media, ban saniba ko samunmu available ne yakesa a kullum kuke mana kallon marasa aikinyi?, ni dai nasan time d'in dana shirya labarin RAINA KAMA ban zauna tebirin shawara da kowaba a online, inkuwa hakane tayaya wasu har suke tunanin nafara sauka akan layin labarin?, to magana d'aya zanyi a wannan ga6ar, ban gina labarin Raina kama akan kwanciyar aure bane, dan haka masu maganar munaya bata da aiki saima Galadima rashin kunya saisu jira saina kai k'arshen labarin kafin su k'alubalanceni, abin dariya, (wai aikina kenan daga nasa munaya ta murgud'a baki sai ta harari Galadima da masa k'unk'uni) tunda aikina kenan babu lallai wajen 6ata lokaci karantawa, haka Na tsara labarina tun farko kuma haka zanyi, duk wanda yaga bai masaba zai fara iya rubuta nashi shima kawai. wannan abun da kukema writer's yana 6ata mana rai, bai kamata ku dinga k'alubalantar writer's ba, bayan su suke da masaniyar yanda suka shirya labaransu, idanma zakuyi saiku ringa tanadar lokaci har zuwa bayan mun kammala, hakan zaifi tasiri fiyeda katsalandan a tsakkiyar labaran mu, akoda yaushe kuzama masu kula kafin Ku k'alubalanci mutum>�7�<���
@&._

*Ba akan kaina kawai nayi wannan bayaninba, harda sauran writers da yawa da akema makamancin hakan koma fiye da nawa.=�E�<���*



________________https://2gnblog.blogspot.com/_____________





~Book 2~ =�I�<���1� 0� �'1� 1�



https://2gnblog.blogspot.com/



...................Koda motocin suka tsaya sarkin mota ya bud'e masa k'ofa yakai tsawon lokaci baiko motsaba, saboda tsantsar tunani da zuciyarsa ta lula, aduk sanda zuciya take cikin matsanancin matsi gangar jiki ma gazawar karfin ikon jini dana 6argo sukan mata k'aranci, shi kansa yasan yanada buk'atar mataimaki a kan wannan lamarin, amma k'arancin rik'on amana Na d'an Adam ne yake yawan gargad'arsa da taka masa birki, ba kowane zai fahimci ma'anar nok'ewar tasaba, sai mutum daya tsinci kansa a makamancin halin da yake ciki.........

 Ranka ya dad'e mun iso . Sarkin mota yasake fad'a cikin taraddadi da taka tsantsan.

A hankali Galadima ya bud'e idanunsa da suka koma launin jaa saboda damuwa a kan sarkin mota, batareda yace uffanba ya ziro k'afarsa k'asa yana cije lips da had'iye wani kududun damuwa a mak'oshi.



Tunda ya fito ma'aikatan wajen suketa masa sannu da zuwa, dan tunda ya shigo k'asar sai yanzu ne zai shiga cikin plaza d'in.

Hannu kawai yake iya d'aga musu, amma bakinsa yay masa nauyi, kallo d'aya kuma zaka masa ka nazarci damuwa da buk'atar hutun dake tartare da kuzarinsa.

A cikin plaza d'in ma bata sauyaba, d'aga hannu agaresu shine yazama linzamin amsa gaisuwar dasuke masa.

Da hannu yayma d'aya daga dogaransa nuni da amso masa key.

Da sauri dogarin ya amsa yana mai nufar sashen da zai kaishi office d'in Saleem mai kula da CCTV camera's.

Sai dai kafinma yakai ga k'arasawar suka had'u da saleem, Wanda tun shigowar motocin Galadima ya gansa.

Keys d'in ya damk'ama dogarin, sannan ya k'araso domin mik'a gaisuwa ga ogansa na wajen aiki kuma magajin garinsa.

Shima d'in dai hannu Galadima ya d'aga masa, hakan kuma ya saka Saleem fahimtar akwai damuwa kenan.

Koda aka bud'e ya shiga saiyayma dogaransa nuni da suje kawai, sannan ya maida idanunsa ya lumshe tareda kwanciya jikin kujerar yana lilawa a hankali.

Shi kansa baisan tsawon lokacin daya d'auka a hakanba, amma tabbas yasan yashiga kudin nazari mai zurfin gaske. Knocking d'in k'ofar da akayi yasakashi bud'ar baki da k'yar ya bada izin a shigo.

Nuren daya shigo ya maida k'ofar ya kulle, kafin ya ida takowa cikin office d'in, idonsa nakan d'an uwannasa.

Zama yay a d'aya daga kujerun dake fuskantar Galadima,  brother what happen? .

 Northing . Galadima ya fad'a batare da ya bud'e idonsa ba.

Shiru kawai Nuren yayi shima, ya d'akko laptop a briefcase d'in daya shigo da ita, kunnawa yay, kusan mintuna biyu ya d'ago ya kalli Galadima, sai kuma ya maida kansa ga laptop d'in.  Sameer nasan kaga cigiyar da akeyi takowacce kafar yad'a labarai ta k'asarnan akan d'iyar minister, sannan jami'an tsaro tsaye suke akan binciken inda take. yakamata musan abinyi kafin lokaci ya k'ure mana .

Guntun murmushi Galadima yayi, batareda ya bud'e idanunsa ba yace  Nuren indai har babu wata waya datake aiki inda kakai yarinyarnan, kuma ka cire sim card d'in phone nata a lokacin daka d'auketa, to babu wata hanya dawani jami'in tsaro zai ganota, dama hanya d'ayace da kuskure zai basu damar bibiyarta, na d'aya lokacin daka d'auketa yazam wayarta na aiki, tabbas zasubi ta wannan hanyar su gano har iya inda ka kashe wayar, hanya ta biyu itace ka kashe wayarta baka cire sim card d'in ta ba daga phone nata, koda wayar a kashe take zasu bibiyeta ta hanyar =��� su ganota ya tashi zaune sosai yana bud'e idanunsa akan Nuren,  wannan hanyoyin biyu kawai ke garesu saikuma idan da camera tare da ita, idan duk babu wannan basuda wata hanya, ka kwantar da hankalinka my brother, komaina da tsarinsa right? .

Murmushi Nuren yayi, kafin ya salute d'in Galadima yana fad'in  I thrust to you my dear broth .

Shima galadima salute d'in Nuren d'in yayi yana murmushi.

Komawa yay ya sake kwanciya jikin kujerar,  yanzu inaga time d'in turama minister Massage yayi? .

Cikin zaro idanu Nuren yace  baka kallon hakan a matsayin ganganci kuwa? .

Baki Galadima yad'an ta6e yana crossing k'afarsa, cikeda izzarsa yace  sai idan nabama wani damar hakan ai .

Nuren baice komaiba, dan yagama sanin hatsabibancin Galadima wajen iya sarrafa Computer, dan haka ya bar wannan zancen ya d'akko wani.  yauwa to maganar Malam Saminu fa? Kasan yana hannunmu fa har yanzu? .

 wannan barsa saiya kuma magantuwa, dan da alama yasan wani Abu, saidai akwai abinda ya sakashi za6ar 6oyewa. ni yanzu damuwar 6atan Muftahu yafi damuna, nasaka camera's jikin mutane 10 danake iya zargi a masarauta amma banga alamun da hannun koda mutum d'aya ba, hakan ya tabbatar min da gaske Muftahu na bibiyar lamarina, sai dai bansan dalilinsa ba, ko kuma waye sakashi? .

Nuren ya jinjina kansa,  brother aini da Harun dama mun dad'e da zargin Muftahu, Kaine kawai kake masa kallon mutumin kirki daman .

Lips kawai Galadima ya cije, amma baice uffanba, Nuren yaci gaba da 'yan danne dannensa a laptop d'in, zuwa wasu mintuna batareda ya d'agoba yace,  maganar Sirikinka fa? .

Shiru Galadima ya masa, saida ya mula dan kansa sannan ya murmusa tareda maida idonsa ya lumshe,  a daren jiya nagama da wannan matsalar, sim card d'insa 3, akwai Contact 300 da 38, mtn yanada mutum 172, ya fara saka credit a layin shekaru 15 kenan, ranar 3/6/2005, glo 107, ya fara amfani dashi shekaru 8 kenan, wad'annan sune Sim card d'insa da yake mu'amulla da kowa a ciki, kuma anfi saninsa da su, akwai 6oyayyen layinsa Na mtn shima, yafara aiki dashi shekaru 13 kenan, kuma mutane 59 ne kawai acikinsa, sannan ba kowane yasan layinba, dan dukkan family nashi basu San da zamansa ba, ita kanta mahaifiyar su Munaya batasan anyi saving number a phone nata ba, suma da suka kirata basusan da number a wayarta ba, dan baita6a kiranta da shiba, akwai matakan tsaro dake tattare da Layin, hakanne ya tabbatar min da akwai abinda yake 6oyewa a Sim card d'in, dan sai time to time yake amfani da shi, kiran matarsa da sukayi da layin wannan shine kuskuren farko da suka tafka da Sameer ya samu hanyar musu takun sauro. zan fara aiki akan layin na shigesu ta hanyar da basu zataba .

Jinjina kai kawai Nuren yakeyi dan mamaki, Galadima da banne, kamar yanda basirarsa take daban, ya sauke ajiyar zuciya yana kama hannun Galadima da idonsa ke a lumshe har yanzun, cikin karsashi yace  lallai kai RAINA KAMA ne Sameer .

Murmushi kawai Galadima yayi, amma baice uffanba.



Knocking akayi, Nuren ya kalli k'ofar yana bada izinin a shigo, Sauban ya shigo da sallama, su duka idonsu a kansa, Nuren yace  lafiya kuwa? .

Zama Sauban yayi yana sauke Numfashi da k'yar, cikin magana d'ai-d'ai da alamar a birkice yake yace,  wlhy Yaya binmu aka ringayi da wata bak'ar Jeep, da k'yar mukasha wlhy, ni dai yau zanbar k'asarnan gaskiya . Sauban ya fad'a tamkar zaiyi kuka .

Gani kawai sukai Galadima yana dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya tsagaita.

Nuren da Sauban suka tsaya kawai suna kallonsa.

Tashi yayi tsaye yana takawa cikin izzar k'asaita, ya dafa bango yana lek'en waje ta window d'in office d'in, yakai wasu adadin lokuta a wajen, sai kuma ya juyo yana kallon Nuren d'in da Sauban da suma suka zuba masa idanu.

 my dear brother! daka tsaya sun kamaka ai, tabbas da wannan shine kuskuren da zasuyi Wanda bazasu ta6a mantawa da waye Muhammad Sameer Saifudden ba a tarihin rayuwarsu. Waya gaya maka kana yawo cikin 9ja ne batareda idon Sameer ba a kanka? .

Sauban ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin daya jik'a fuskarsa,  wlhy yaa Sam daka fad'amin da bazan tsorata ba .

Daga Galadima har Nuren dariya suka kwashe da shi, Nuren ya dafa kafad'ar Sauban yana fad'in  matsoracin banza .

 uhm-uhm yaa Nuren bazaka ganeba wlhy, tsoro halak ne fa ..

Galadima dai baice komaiba ya koma ya zauna yana murmushi.







&)))*(((&)))*(((&)))*(((&)))*(((&





Ganin har anyi sallar Magriba babu baba k'arami balle Dady ya saka Innaro d'aukar gyale ta fito, lokacin gwaggo Safiyya tana salla, shiyyasa batasan innaro ta fitaba, habiba da Naja'atu dake tsakar gida suna tattare kaya saboda hadari na farkon damina dayake nuna alamar zai zubda ruwa. suka kalli juna, Naja'atu tace  yaya habiba tsohuwarnan fa bata da dama wlhy .

Dariya habiba tayi,  ai kad'anma kika gani Naja'atu, yanzu dai zataje ta tadama baiwar ALLAH hankali .

 to ALLAH ya k'yauta .  cewar Naja'atu tana rik'e ha6a .



Lokacin da Innaro ta shigo gidan d'akin Innarsu Munaya ta nufa kai tsaye, sai dai ta iskeshi rufe, kwala kiran sunanta ta shigayi cikin masifa,  Ai'sha!! Ai'sha!! Nasan kina jina, wlhy ki fito kafin yau d'innan igiyar aurenki ta tsinke .

Mamansu yaa Hameed da gwaggon Haleematu ne suka fito, mamansu yaa hameed tace  aiko tafita fa inna, dan gab da magribar nan naga Fadeel ya shigo sun fita, bansan mike faruwa ba dai .

 yaza'ayi kusan mike faruwa tunda anyi k'ulle-k'ullen munafunci, lallai jafaru, wai yau da kaine za'a muzantani hannun mak'iyana, to nikuma naga ta yanda Ai'sha zataje wata k'asa jiyyar Auwalu da raina ........ haka taita zuba banbamin masifa matan gida na saurarenta, daga daddy har baba k'arami suna gidan amma sukak'i fitowa. Jarabar Innaro ta saka kowa na gidan fahimtar mi ake ciki, nanfa hassada da bak'in ciki suka kume zukatansu, dukda kuwa sunsan tafiyar bata dad'i baceba, maman fauziyyace kawai hakan yamata dad'i, koba komai inna ta huta da cin zarafin Innaro koyayane.



Sai da Gwaggo Safiyya ta shigo tama Innaro magana sannan ta tafi gida, su matan gidanma sai yanzu suka San da zuwa gwaggo Safiyya d'in.

Amma sunso ace innarsu munaya na gida Innaro tayi wannan rashin mutuncin.





Hummm=��.







****************************





Bayan fitowar su Galadima daga birnin gayu, sun wuce gidane, Nuren kuma yakoma hotel d'in daya sauka.

Galadima kawai ne ya shiga sashensu, amma Sauban 6angaren mai martaba ya nufa neman yarima Mahfuz.



Munaya na zaune a falon farko tareda sabbin kuyanginta guda uku, (dan bata amince su shiga falonta ba, saita gama tantance su sannan) ba wani hira sukeyiba, d'ayace a cikinsu ke sak'a shine abin ya birge Munaya take kallo, tana kwance cikin doguwar kujera ne, yayinda su kuma su ke zaune a k'asan lallausan carpet d'in falon.

Dogarai biyune suka fara shigowa hannunsu d'auke da ledoji, sai kuma mai gayya mai aiki Galadima.

Da sauri bayin suka mik'e tsaye, saida ya ida shigowa sannan suka d'urk'ushe a k'asa suna kwasar gaisuwa.

A la66ansa ya amsa yana d'aga musu hannu, yayinda idanunsa ke kan munaya da itama ke satar kallonsa

Duk d'insu kowa janyewa yayi, yayinda bayin da dogaran suka fice bayan sunkai ledojin falon Galadima.

Baice da ita uffanba yafara takawa zai shige, tamkar mai tsoron fad'a tace,  sannu da zuwa .

Ysayawa yayi cak, sannan ya juyo da kansa tamkar mai ciwon wuya ya kalleta, bata yarda sun kuma had'a idoba takuma fad'in  nagode sosai .

 for what? .  ya fad'a cikin isa .

Shiru munaya tayi, ta kasa cewa komai.

Shima bai sake cewa komai ba ya taka ya shige abinsa.

Harara munaya ta raka bayansa da shi, sai kuma ta sauke numfashi tana tashi itama, bedroom d'inta ta koma, a saman sofa ta zauna tana dafe kai, sosai take buk'atar zuwa sake duba mahaifinta, amma ta kula Galadima bashida niyyar cemata taje, kai itako wannan wane irin abune haka? shi dama gidan Sarautar haka yake bakada 'yancin kanka?, komai saida k'a'ida. tun d'azu kuma take kiran number inna bata d'agaba, tadai kira baba k'arami da daddy sun gaisa ta tambayi jikin Abba, shine ma har suke kuma sanar mata k'ok'arin da galadiman keyi. tabbas hakan da yayi yasata jin farin ciki, koba komai tasan shi adaline, ko anan gaba ragamar shugabanci ta riskesa zaiyima


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login