Showing 201001 words to 204000 words out of 365757 words

Chapter 68 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1492

yasaka hannu yana rufe bakinsa.

Haushi ya kamani na d'auki filon dana kwanta na jefa masa. da sauri ya cafe yana cigaba da dariyarsa, hakan yasa najawo na kujerar ina cigaba da kai masa duka yana karewa da wancan. daga k'arshe sakkowa yay yahad'a nida filon ya rik'e yana fad'in  sorry sorry na bari, ba 'yar tsuntsuwa ba giwar mata .

Hararsa nayi nafara kukan shagwa6a kuma.

dariya Yakuma sakawa yana fad'in  toni bansan mikikeso nace mikiba kuma? .

 ni banaso duka .

 to shikenan nabari, yanzu dai yaza'ayi Ring yaje yatsan Abbanmu to? .  yay maganar yana d'ora kaina jikin kafad'arsa .

 saika fad'amin sirrin sannan zan fad'a nima .

Ya murmusa yana jan hancina,  kin cika wayo yarinyarnan wlhy .

K'aramar dariya nayi nace,  ai awajenka na koya .

Murmushi kawai yay baice komaiba, ya jawo wata 'yar k'aramar bag mai k'yau fara ya mik'omin.

Kar6a nayi ina tashi zaune sosai na bud'e jakkar ina fiddo kayan ciki, agogone mai masifar k'yau da tsari, na azurfa 'yar asali mai tsada, sai wani d'an akwati da ring mai k'yau na azurfa shima, an masa ado da farin stone mai garai-garai tamkar diamond, na jujjuya zoben kafin na d'ago mu kalli juna ni da Galadima, ido d'aya ya kashemin=� �.

Janye idanuna nayi nakuma maidawa ga zoben ina k'ok'arin sakashi a yatsana, saidai yamin yawa sosai, na cire ina fad'in  amma gaskiya zobenan ya had'u sosai yalla6ai .

 duk haduwarsa bai kaikiba ai .  yay maganar acikin kunnena .

Kallonsa nayi, amma saiya basar tamkar bashi yay maganar ba.

Lips na cije na d'an hararesa.

Shikuma ya ta6e baki.

Na maida kayan duk a cikin bag d'in dad'an hanzari ina rik'e cikina dayay wata wuntsulawa.

 lafiya? . ya fad'a yana rik'o hannuna.

'Dagowa nayi na kallesa da k'yar, da hannu na nuna masa cikina dake juyamin, jinake kamar numfashine zai bar jikina.

Babu shiri ya dire wayar hannunsa ya rik'oni jikinsa da k'yau.

Sosai na fara murk'ususu ina kuka da k'ank'amesa, dukya rikice, yama rasa mi zaiyi?.

Ana cikin haka saiga sallamar Aunty Mimi dataga shirun yayi yawa sun dawo ban sakkoba, saitai tunanin kobana jin dad'ine, sallama tayi Galadima ya amsa murya a rikice, hakanne yasakata shigowa batareda jiran isoba.

Da hanzarinta ta k'araso tana tambayar miya faru?. nidai kuka kawai nake ina kuma k'ank'ame Galadima.

Shine yasamu damar mata bayani sama-sama, yak'are maganar da fad'in  Aunty mutafi asibiti please, maybe haihuwa Ce? .

Da sauri tace,  badai haihuwaba Sameer, cikin dake wata takwas, kaga ina zuwa . Ta fita a hanzarce.

Babu dad'ewa sai gata tadawo da innarmu da jakadiya, dak'yar innarmu ta amince ta hawo, danma taga tsantsar rikicewar da aunty Mimi tayine. har yanzu dai kukan nake ina jikin Galadima dashima dukya koma kalar tausayi kamar zaiyi kukan.

Ganinsu a haka yasaka innarsu munaya k'ok'arin komawa da baya, dan saitaji kunya ta kamata, dukda tasan suma bada son ransuba ne. ita kanta jakadiya taji kunya. ganin innarsu munaya zata gudu Aunty Mimi tayi azamar rik'o hannunta.  please inna karki duba ta kunya, halen datake cikine abin dubawa, kowa yasan dai ba haihuwa baceba tunda da saura .

Ajiyar zuciya inna ta sauke, batare da ta motsa daga inda takeba takuma musu kallo d'aya ta d'auke kanta, tace,  inaga juyine ai, zai lafa insha ALLAH .  tana gama fad'a ta fice abinta .

Jakadiya da aunty Mimi suka kalli juna, murmushi jakadiya tayi, tace,  gaskiya ta fad'a, juyine, amma nadad'e banga uwa mai kawaiciba irinta a wannan zamanin .

Murmushin itama aunty Mimi tayi, ta maida kalonta kansu, yafara lafawa sosai, dan haka munaya tafara tsagaitawa da kukan.

Galadima yakuma k'ank'ameni a jikinsa sosai yana shafa kaina, nikam sai ajiyar zuciya nake saukewa tareda shashshekar kuka, ya manna min kisses a kaina idonsa a lumshe, danshi yama manta dasu Aunty Mimi a d'akin.

Jakadiya ma dai lalla6awa tai ta gudu, dan taga magajin gari yau sai a hankali.

Aunty Mimi ta tako inda suke ta zauna a sofa tana fad'in  sannu Munaya .

Bud'e ido Galadima yayi, harsun kad'a zuwa launin jaa, yad'an furzar da iska yana lek'a fuskarta, barci ya d'auketa. ido ya d'ago yana kallon aunty Mimi dake kallonsu cike da sha'awa, tamasa murmushin kwantar da hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana cije lips da jinjina mata kai.

Tace,  tayi barcine? .

Nanma kansa ya jinjina mata, yana gyarama Munaya kwanciya a k'irjinsa yanda zataji dad'i, yace,  Aunty Mimi amma yakamata muje asibiti aga miye matsalar? .

 karka damu my k'ani, juyine kawai, insha ALLAH babu wata damuwa. bara inje nima saida safe, idan kuma kaga dawata matsala saika kirani muje asibitin tunkan dare ya kumayi .



Bayan fitar aunty Mimi kuma k'ank'ameta yayi yanamai jin tausayinta na ratsashi, ya sumbaci goshinta, kafin ya d'auketa dukda nauyin datayi ya maidata saman gadon, yanzunma a jikinsa ya sakata, yaja bargo ya lullu6esu tareda musu addu'ar kwanciya.

Cikin barci ta farka da wata matsananciyar yunwa, k'irjin Galadima na shiga girgizawa ina kuka.

Galadima ya farka a firgice yana rik'e hannunna, ya yunk'ura da k'yar ya tashi zaune,  miya faru? .  yafad'a cikin muryar barci .

 yunwa yalla6ai, abinci xanci, kafad'a masa magana yabar halbina .

Dukda tabashi tausayi saida ya murmusa, sauka yay yafita, k'asa ya sauka zuwa kitchen, yau saiga Galadima a kitchen>�#�, rasa mizaimayi yayi, ganin yana 6ata lokacine kawai dan ba iya uwar komai yayiba saiya fice, dole yaje ya tado kukunsu.

Mai aiki da aikinsa dannan saigashi ya had'a mata Abu mai sauk'i, Galadima ya kar6a da kansa Yakoma saman.

Isketa yayi zaune tsakkiyar gado tana kuma rurus, saita k'ara bashi tausayi, ya haye gadon da abincin, da kansa yabata yana lallashi. saida tayi nak sannan ya sauka da tiren yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.

Nikam hankalinna kwance nazame na kwanta, barci ya sake kwasheni.

Mamaki yasakashi tasata gaba yana kallo, saikace wata mai aljanu, lallai duk namijin daya kasa tausayawa matarsa lokacin da ciki yake jikinta yacika mara tausayi number d'aya, babu abinda miji zai iya biyan matarsa dashi akan rainon cikinsa datayi da tarbiyyar 'ya'yansa, amma a wannan time d'in wani namijinma rashin tausayinsa ke tashi akan matar, ALLAH ya ganar dasu to.



Amin galadima=�A�=��.







**********************



Washe gari





A safiyar yau su Abba suka tashi da shirin komawa Nigeria, gaba d'aya saina tashi duk babu dad'i, jinake kamar karsu tafi, dana tuna yaune zasu barmu sai hawaye ya zubomin, inama zai amince nidai nabisu mu tafi tare?.

Agogo da zoben jiya na d'auka nafita masaukin su Abba, dan Galadima ya fita tunda sasaafe, bansan ina yajeba.

Saida nayi sallama aka bani izinin Shiga sannan na shiga, Abba na zaune a bakin gado agogo rik'e a hannunsa suna magana da innarmu dake tsaye ita kuma tana zuba sauran kayansu a k'aramin akwati.

Abba yay murmushi yana fad'in  sannu munaya kinji .

Murmushi nayi a kunyace, na dafa gadon zan durk'usa k'asa na gaidasu amma saiya dakatar dani ta hanyar rik'e hannuna,  kinga zauna, inake ina durk'uso yanzu . da taimakon Abba na zauna a kujerar dake kusada gadon, sai faman jeran sannu yakeyi, nikuma ina amsawa cikeda jin kunya. gaishesu nayi, suka tambayeni yaya jikin? na amsa da  Alhmdllh .

Jakar hannuna na mik'ama Abba, ya amsa yana fad'in  minene kuma? .

 Abba ka bud'e to .  nayi maganar a shagwa6e .

Dariya yayi yana k'ok'arin bud'ewa,  yanzu dai fitinarki k'aruwa ma tayi Munaya .

Innarmu dake ta6e baki tace,  ai bamaka san fitinarta ta zarce tadaba sai jiya, juyi kawai ta zauna tana rusama mutane kuka a gidannan, yo ke aibama asan abin fad'in dazaki bariba ranar haihuwar? ..

 babu abin fad'in dazata bari insha ALLAHU . cewar Abba yana juya agogon fuskarsa d'auke da murmushi.

Nima sai ban kula zancen Innarmu ba nace,  Abba yayi k'yau? .

 sosai kuwa Munaya .

 Abba kawo na saka maka to .

 to amma kekuwa ina kika samu kud'in sayen wannan agogon da zoben mai tsada haka? .

Murmushin nayi, nace,  Abba awani shago mukaje sayen kaya tun kwanaki dashi, daga nace agogon yamin k'yau shinefa yace na d'auka to .

 Amma munaya yayi tsada da yawa, karna sakejin irin haka, dan takurawace ai, idan kuma bashida k'arfin siyen abunfa? Karki sake kinji ko? .

 inasha ALLAHU Abba bazan sakeba, amma dan ALLAH karkace bazaka kar6i wannanba, dan shima bazaiji dad'iba .

Murmushin Abba yayi, yashiga sanya albarka a garemu da abinda ke cikina, hardama addu'ar d'orewar lafiya ga Abie shima. cikeda d'oki naita amsawa da amin, da kaina na saka masa agogon da zoben.

Daga nan muka d'an ta6a hira. Dan akwai sauran time sosai na tafiyarsu. Mun dad'e muna hira, dan ko break fast yau tare dasu na sakeyi, dama tun asuba ni yanzu nakeyin nawa>�-�, sanda kowa zai k'ara sainayi na biyu.=��

Galadima ma daya dawo ya kimtsa nan yazo ya samemu, yanda suke sakin jiki da juna shida Abba abin na bani mamaki, Galadima yakuma yima Abba bayani sosai akan yanda zaicigaba da tattalin lafiyarsa da kulawa da dukkan dokokin da sukai masa, daga nan muka cigaba dad'an ta6a hira, itadai Innarmu duk adabaibaye take, danma taga yau zasu wuce da bazata zaunaba.



Wajen 12pm mukabar gidan zuwa asibiti, a asibitine akayi dogon zama, dan godiya ta musammance tashiga tsakanin surukan guda biyu, Abba kuma yay alk'awarin kuma tsayawa wajen dagewa da addu'oi na musaman ga jikin Abie da alk'awarin kawo wasu taimakon na tsarin jiki, dan sunga fa'idar addu'a sosai.

Kowa jiyake tamkar karsu tafi, saboda shak'uwace ta musamman tashiga tsakanin wad'annan families guda biyu, zaman mutunta juna ya gudana sosai a tsakani.

Kuka na shiga rairawa lokacin danaga tafiyarfa da gaske yinta za'ayi, sai alokacin muka san ashe wai harda Sauban, zai rakasu saudiyya suyi umrah ta kwana 10, daga nan saisu wuce shikuma yadawo. na kama hannun Abba na rik'e gam nak'i saki zai hau jirgi, su Sauban suka tasani da dariya kuwa, oho ban kulasu ba, Galadima ya girgiza kaiwai yana murmushi, yarinyarnan ta6ararta tayi yawa, yafad'a yana takowa inda muke da Abba yana lallashina.

A Kallonsa Abba yayi sukayi murmushi, Abba ya zame hannunsa a hankali yajuya zuwa ga jirgi, yunk'urin binsa nayi Galadima yay azamar rik'o min hannu batareda yayi magana ba, juyowa nayi na fad'a k'irjinsa ina kuma sakin sabon kuka.

Hannu biyu ya saka ya rungumoni yana guntun murmushi.

Innarmu dake hangenmu ta cikin jirgi ta share hawayenta itama tana murmushi, banda aure waya isa ya rabaka da 'ya'yanka. Abba daya zauna kusada ita ya saka hannunta cikin nasa yana murzawa, juyowa tayi ta kallesa, yamata murmushi yana share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawa, jikin kafad'arsa ta d'ora kanta kawai.

Sauban dake kallonsu yay murmushi, lallai Aunty gimbiya 'yar gatace a gidansu.



Saida naji alamun jirgi zai tashi sannan na d'ago kaina, inaji ina gani jirgin yafara shawagi a samaniya harya shilla da iyayena.

A motama haka naita sharar hawaye, dayake dagani sai shi da Samha a motar, cankuma Aunty Mimi da Khaleel da jakadiya.

Samha tana ta bani hak'uri, amma tamkar tana zuganine, saida Galadima ya harareta yana mata alamar tamasa shiru sannan tayi shiru, shikam ko sau d'aya baicemin uffanba..

Asibiti muka koma, tunda muka shigo Momma ta taso ta rungumeni a jikinta tana lallashi.

Galadima ya jingina da bango ya hard'e hannayensa yana kallonmu, a haka sauran suka shigo suka iskemu, Abie ma kallonmu yakeyi cike da tausayina.

Saida nasamu na tsagaita da kukan sannan nacema Momma zanci abinci.

Galadima yaje kusada Abie ya zauna yana k'aramar dariya,  dama kice yunwa kikeji kika zauna kinama mutane ta6ara? .

Hararsa Momma tayi tana masa dak'uwa, hakama Abie, aunty Mimi kam saida ta rankwasheshi akai.

Gurin ya dafe yana fad'in  a'a yazaku tararmin ne kuma?, gaskiyafa na fad'a ko Samha? .

Samha tace,  Uncle nima dai ina bayan aunty gimbiya .

Idanu ya kwalalo alamar tak'aremin.

Muka had'a ido na hararaesa.

Lips d'insa ya ciza yanamin alamar zan kamakine da ido.

Na ta6e bakina nikuma. Dolenesa yatashi yanemomin abinda zanci.







&&&&&&&&&&



Tunda su Abba suka tafi lafiya tamin k'aranci, bana iya tsinanama kaina komai sai kwanciya, dukna fita hayyacina na canja kamanni, ga cikifa sai kuma bud'ewa yake yana k'ara girma. Kai kace ba halitta d'aya bane a cikinsa.

Galadima dole ya d'auki hutu a office, idan abinda yazama dolene saiyaje Office kam yakanyi shine ta yanar gizo.

Gakuma nasarar jikin Abie daketa k'ara k'yau, dan wasu sassan jikinsa suna nuna alamun fara aiki kamar yanda doctors d'insa suka sanar mana.

A kwana na 8 da tafiyarsu Innarmu ranar a asibiti na kwana, saboda jiki dai yak'i dad'i, ga masifaffen cin abinci abin babu arzik'i.





&&&&&&&



Su Abba sun gudanar da ibadar Umrah cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, ga Sauban dake nuna musu komai yanda bazasu wahala ba.

Suna cika kwanaki goma yasakasu a jirgi suka nufi k'asar haihuwa Nigeria kenan, sun rabu cikeda kewar juna suna saka masa albarka.



Sun isa Nigeria batareda sanin kowa namuba sai Yaa marwan da Galadima yakira ya sanarma yaje ya d'aukesu a airport.

Isowarsu gidanmu tazama a bazata, hakan yasaka gidan rikicewa da murna, dukda kishin daya cika matan gidan ganin innarsu munaya takoma wata d'anya shakaf saboda Hutu da canji wajen zama data samu, dandanan 'yan anguwa suka shiga shigowa taya murna dama Abba jajen ALLAH ya kiyaye gaba.

Innaro babu kunya taketa haba-haba da d'anta, kota innarsu munaya batayi, dan haushinta takeji taje ta zauna a India itako an maidota gida. (Babu mai iyama Innaro dai sai ALLAH>�&�<���
@&>�#�).



Su Ayusher da sukazo suka zage suka gyarama inna d'akinta, komai ya koma need, tamkar ba shineba ya had'a uban datti na tashin hankali.



Tafiyarsu Abba Nigeria da kwana 5 Sauban ma ya dawo India, ya iske ina asibiti, dan gado suka bani dole, babu ranar sallama ma, k'ila saina haihu.

Saidai randa mukayi waya da Munubiya nake fad'a mata tace ai gidama yakamata na dawo na haihu, itama batada lafiyar sosai.

Da to na amsa mata kawai, amma ina tunanin yanda Galadima da ahalinsa zasu amince da zuwana haihuwa Nigeria, kuma tunda 'Yar uwata ta ambata dolene hakan za'ayi, kona so koban soba kuwa.





___________________________





*_Two months ogo_*=�,�>�-�





Watanni biyu kenan da tafiyarsu Abba, tunda sukatafi kuma babu wani Abu mara k'yau kona Sosa zuciya dayay gamo dashi, harma ya koma wajen aikinsa hankali kwance.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login