Showing 93001 words to 96000 words out of 365757 words

Chapter 32 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1493

iyawa saboda jigata, zan iya danganta abinda Galadima yayimin da fyad'e, dan baya cikin hayyacinsa ko kad'an, kamar yanda nima nawa ya gushe daga farko nabashi gudunmawa. (Nasan duk mai hankali ya k'iyasta a yanda Galadima ya zomin zai tabbatar dolene na jigata d'in=�-�).

Tunda yasamu nutsuwa yana gefena a kwance kawai, a hankali memory d'in brain nasa ke tariyo masa abinda ya aikata tamkar a mafarki, ya bud'e idonsa da hanzari akaina, domin kuma gaskata abinda yafarun, shin da gaskene ya aikata?  innalilahi yashiga maimaitawa dan ganina kwance a gefensa ina hawaye, daganin yanda nake a kwancen ina fidda numfashi d'ai-d'ai kasan nagama jigata, yabi d'akin da kallo cikin tsantsar takaici, yaushema shikam yazo d'akinnan?  Hasbinallahu wa ni'imal wakil. mike faruwa danine ni Sameer? wace k'addarace kuma ta kutsoma rayuwata? yanzu nan ni Muhammad Sameer ne da wannan d'anyan aikin? miya samu tunanina haka?.......

Tunaninsa ya tsaya cak lokacin daya jiyo dasashshiyar muryata ina kiran innarmu da Munubiya, muryata a raunane, runtse idanunsa yayi tareda mik'ewa zaune da k'yar, dan jikinsa gaba d'aya yayi week, ga wani masifaffen ciwo da kansa keyi. da k'yar ya iya kuma bud'e idanunsa a kaina, babu shiri yakuma runtsewa saboda tsorata da ganin yanda yamin, hawaye kawai yaji suna neman zubowa a face nashi saboda shi mutum ne mai tausayi, bayason yaga ancutar dawani bare kuma shi da Kansa ya aikata, jarumtar had'iyesu yayi tareda kuma bud'ewa, yazubama fuskata ido batareda ya iya cemin uffanba, yama rasa ta inane zai fara shikam, mizai fad'amin kuma a yanzu Na yarda dashi? mizai cemin shikuwa?.

Innarmu dana sake ambata murya a sark'e yasakashi saurin kallona, baisan yarik'o hannuna ba ya rumtse anasa, la66ansa sai motsawa suke amma yagaza yin magana, shi yanzu ma baisan wane irin taimako zai baniba, bai ta6a irin hirarnan dawani abokiba balle yace yasan ya zaiyi, bai ta6a aikata zinaba, zai iya rantsuwa da Ubangijin daya haliccesa bai ta6a ta6a jikin wadda ba muharramarsa ba, sai ita Munayar daya d'auketa randa yasa a sato masa ita. Kuma ko muharramar tasa bazai wuce yarik'e hannun taba shima ba kowaba wlhy, inhar kacire Samha Momma Aunty Mimi ko Mom, sukad'aine mata Muharramsa da zaice yanada shak'uwa ta musamman dasu, amma shi ko yaran masarautar nan bama kowacce zai iya ambatarta da sunanta dai-daiba.....

Rashin ya cika da tashin hankali, kukan danakeyine yasakashi waigen phone nashi, baiga komaiba, tunawa yayi ba d'akinsa baneba nan, ya saki hannuna ya sakko agadon bayan ya suturta jikinsa, jikinsa gaba d'aya ya mutu, ahaka da sand'a yakai falonsa, wayarsa dake a saman kujera ya d'auka, to inama zai dosa shikam? wazai kira akan wannan abin kunyar daya aikata? tunanin bincike a network ne ya fad'o masa a rai, maybe yasamu bakin zaren, Google yashiga yay d'an rubutu yahau Searching, amamakinsa kam saigashi sun bashi, saiya kuma wata tambayar, nanma yasamu amsa dai-dai,  Alhmdllh yafad'a yana mik'ewa rik'e da wayar.

Inda yabarni ya iskeni, Toilet yawuce kai tsaye, yayinda nabishi da kallon tsana, nikad'ai nasan minakeji akansa, ayanda nakeji ko wuk'a aka bani zan iya fidda masa hanji waje, tabbas yanzu nakuma yarda banida wayo, yanda tun farko Na yarda da maganar wai auren yarjejeniya mukayi da Wanda yafi k'arfin ajina da matsayina, inma banda wauta irin tawa tayaya mutum kamar Galadima zai nemi kulla aure dani?, Na manta namiji zai iya komai domin cikar burinsa, k'ilama *AUREN 'DAN'DANE* yayi dani, ai sainaji wani kuka ya tokaremin mak'oshi, har ina neman shid'ewa.

Kamar yanda yaga sunsa ya had'a ruwa mai zafi-zafi, sannan yafito, ficewa yakumayi, babu dad'ewa sosai yadawo yakuma shigewa toilet d'in, ni dai idonama Na rufe gaba d'aya, dan bana k'aunar ganinsa.

Jinai kawai an kama hannuna ana k'ok'arin tadani zaune, wata azaba naji har cikin kwalwar kaina, saina fashe dawani marayan kuka Wanda yasakashi saurin sakina nakoma Na kwanta.

Runtse idonsa yayi saboda jin addu'ar danake jero masa ta neman sakayya ga ALLAH tsakanina dashi, wani bai ta6a masa makaman ciyar addu'ar nanba, amma gashi matarsa ta sunnah tana masa, duk da yasan hak'in sane ya k'ar6a agareta hakan bai hanashi jin bak'in cikiba, dan aganinsa inada hujjar masa addu'ar da tafi wannan muni, tunda Bahaka mukayi dashiba.

Cikin tsantsar damuwa ya d'aukeni zuwa bayin, yayinda nikuma nake kuka ina fad'in ya saukeni, duk da a hankali nake maganar yana jina.



Ba k'aramin daga mukayi dashiba wajen taimakona, harda cizonsa nayi a damtsen hannunasa, aiko yacizu wlhy, dan hakwarana saida suka huda lallausar fatarsa, (to dama ba wahala tasaniba fatar) amma a mamakina sainaga ko gezau baiyiba, kuma Na tabbata yaji zafin cizonnan, saidai bansan dalilinsa Na daurewaba, da k'yar ya samu nayi wankan tsarki kuwa, dan saida yakusa makeni ma dan haushi sannan nayi, harya dawo dani d'akin ban daina jera masa ALLAH ya isaba a fili da kiransa mugu azzalumi.

Duk da kalamaina suna sukar zuciyarsa haka yadake yanuna tamkarma baya jina.

Bashida maganin dasuka rubuta akan matsalata, sai dai yanada Wanda zai iya taimaka min kafin zuwa Safiya ya nemo wancan.

Haka yakawo min maganin da tea wai nasha, harara kawai Na zuba masa Na maida kaina Na kwanta batareda nako motsaba balle yayi zaton zan tashi.

Shima baice komaiba yakamani ya tayar, hannunsa da k'irjinsa nashiga bugu, ina kuma kaimasa cizo, amma k'arfin ba d'ayaba, bai barniba saida ya tadani, sannan ya wani ci uban Magani fusakarsa amatuk'ar murtuke, yace  kinsan ALLAH koki kar6a kokuma....humm .

Yanda yay maganar kuma sai tsoro ya kamani, Na watsa masa harara kafin nabud'e bakin, da kansa yabani shayin, sannan yabani magani. mugun Ashe harda Na barci, cikin mintuna k'alilan barci yay awon gaba dani.

Sai lokacin ya samu damar sauke ajiyar zuciyarsa tareda dafe kansa dake tsananin sara masa. Duk yanda yaso yayi tunanin ya akayi hakan tafaru yakasa, saboda matsanancin ciwon da kansa kemasa, dole yamik'e zuwa d'akinsa, shima ruwan mai zafi yay wanka dashi sannan ya tsarkake jikinsa ya fito, Magani yasha ya haye gado ya kwanta shima, yasan bazan farkaba a nan kusa.

Maganin barcin da shima yashane yasaka barci suresa shima.





&&&&&(())&&&&&







Tun daga shigar Muftahu wajen Galadima har zuwa sanda ya zuba Abu cikin milk d'in Galadima lokacin daya Shiga bedroom d'insa d'aukar Abu suna kallo, har ya girgiza ya ajiye kwalin da sauri inda ya d'auka, fitowar Galadima zamansa da files d'in daya bama Muftahu Na masu buk'atar taimako a asibiti da aka kawo masa zai biya, har shigowar Munaya falon Galadima da fitar Muftahu, zamanta da kar6ar wayarsa zuwa fitarta itama, yanda Galadima yafara fita hayyacinsa har dawowar Munaya sashen takawo masa wayarsa, fitarta dakuma bin bayanta dayayi, hankalinsu ne yad'an tashi ganin yadad'e bai dawoba, gakuma a yanayin daya fita.

Hakanne yasaka aka turo wasu mata biyu da kayan fruits wai sukawoma Galadima domin suyi CID d'in yana ina?.

Sai dai sarkin k'ofa kuma yace saiya musu iso, kamar yasani saiya rufe k'ofar ta ciki sannan yanufi sashen Galadima d'in, yayi sallama tafi sau 15 amma babu amsa, ya tabbata da yana kusa daya amsa, komawa yayi yace musu ai yamayi barci, su koma dashi kawai, babu magiyar dabasu masaba yak'i bud'e musu, dan yarigada yasan komai Na kitumurmurar gidan, sannan yasan Galadima bayacin abincin kowa a masarautar, ko ankawo su yake bamawa, idan kaga yaci abincin dawani yadafa a masarautar to tabbas aunty Mimi tana k'asar, sunzo tare kotazo ta iskeshi. dan haka yahanasu shiga, harma yad'an tsargu da tunanin kawai wani Abu a k'asa ganin sun jajurce dason shigar.

Ransu a 6ace sukabar wajen, inda aka aikisu suka koma, sun Isar da abinda yafaru.

Hakan kuma yakuma tada hankalin masu Aiken nasu, domin an ruguza musu plan d'insu kenan...........
'<���







>��hummmm.s����&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&











_ko Yaya za'a kwashe tsakanin Galadima da Munaya da safe kuma>�#�>�-�, Munaya team amin afuwa>�s�=�O�<���ku kora da wanan<�~�<�z�<�{�>�B�<�w�>�C�<�x�<�y�=��=��._

<���<���





*_Masu karatu nasan kowa yamatsu yasan tarihin masarautar su Galadima, insha ALLAH zakuji, inason muzo ga6ar daya kamata kuji d'inne insha ALLAH, saura k'iris=��=�L�<���._*









Barkanmu da dawowa=�� '<���.













*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=�-�

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 6�





..........Da kuka na farka, duk da naji dad'in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi nayi zuwa toilet danna d'auro alwala, na tuna labarin da wata k'awarmu ta ta6a bamu akan yanda taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d'an zafi na had'a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad'i, amma inajina kamar ba a dai-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa masallaci shima.

Koda na idar kwanciya nayi saman abin sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tunano abinda yafaru a jiya tamkar a films ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d'inan dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d'in ma, da dai na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa dasu innaro yafimin....



Tun d'azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan mawa, bayason zalunci ko kad'an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa tilas yace  tashi zaune muyi magana .

 baza na masa, a zuciyata nace bazan tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad'amin na yarda, azzalumi, dama abinda ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d'iyar talakawa banida k'arfin gogayya da kai, tabbas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan zalincin dakami.........

A fili kuma nace,  kagama zalintata kazo kanamin mazurai da mulki, ank'i tashin . a hankali nake maganar banyi tunanin yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin

 k!!!!! .

Yafad'a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara maganar ya rumtse idanu saboda yanda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya, ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad'a yace,  Niba azzalumi baneba, zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na auroki! tun jiya kike fad'an magana amma na shareki, ni sa'an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?.........

Zumbur namik'e zaune, duk da azabar da k'asana kemin, na kallesa ido cikin ido ina zubda kwalla nace,  bakada abin fad'a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina 'Yar talaka bana d'aukar raini wlhy, mina maka ne? miye had'ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala'i, tunda na had'u da kai ban kuma samun nishad'iba, wlhy bazan yafe makab.......

Jikake bamm! ya make bakina da bayan hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe? .

Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala'in tsoronsa daya kuma shigata, maganar ma a tsorace dama nayita, Dan tsabar bala'i na hango cikin idonsa Dana kallesa.

Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru

Ganin bazan sauraresan ba da gaske saiya tashi ya fice yabarmin d'akin.

Nakuma 6arkewa da kuka.



Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe kansa daya koma masa ciwo k'asa-k'asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha'awar ne wai? dan bai ta6a jin makamancin feelings irin na jiya ba, da sauri yamik'e yanufi sashensa, a falo ya tsaya, ya d'auki kwalin hollandia fresh milk d'in jiya yana dubawa, shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa yake?. to amma ai ba yaune yafara shan fresh milk ba a gidannan balle yace kuma shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d'aya tunaninsa ya kulle, dama shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakoma ya kwanta, ko azkar yakasayi yau, babu dad'ewa barci yakuma kwasheshi anan.



Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba da ita a wajen.

Har Samha suka kawo abinci duk barci suka Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad'an daga aikinsa ya mammaketa a safiyarnan.

Su duka sai wajajen 12 suka farka, kowanne yatashi da damuwarsa.

Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad'ai ya isa na daina jin zafinnan irin haka, balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon k'asana yabar zafin saima zugi yake k'arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi nakeji sosai.

Yanda nake takawar ina hawayene yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda yamin jiya. bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..

 Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone? .

Wata uwar harara dataso bashi dariya na zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna na fisge, ya d'aure fuska shima yana hararata,  k! Wlhy kinutsu kafin na canja miki kamanni .

 yo kammani na yaushe kuma zaka canja min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka amma sai zalunci taf zuciyarka .

Idonsa ya runtse dan bayason Kalmar zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad'in  wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai kashe miki ni .

Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina kuka saigashi yadawo da wayarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar datake sakani wannan kukan da complain d'in zafin, yasan koya tambayeni ba fad'a masa zanyiba..

Da turanci suka gaisa, amma da zaiyi tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.

Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda yake nuna masa yanzun ba.

Galadima ya gyara zamansa sosai yace  to ai na sanar maka fyad'e akama yarinyar fa .

Akash yace  zata iya kai shekara nawa yarinyar? .

'Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye yana fad'in  Maybe 19years ko 20 kawai .

 ai bama yarinya baceba can sosai, inaga taji ciwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan my man, please ka kwatarma yarinyar hak'k'inta wajen azzalumin nan .

lips d'insa kawai ya cije maganar Akash na sukar zuciyarsa, da Akash yasan shine yay aika-aikar dabai ce hakaba. sallama sukayi ya yanke wayar, saikuma yafara tunanin doctor d'in dazai nemo ya dubani, dan bashida damar fita dani a gidan yanzun.

Can doctor Hafsat ta fad'o masa a rai, ita kad'ai zai iya aminta tasan matsalarsa, dan ya yarda da ita sosai, yasan zata masa k'yak'yk'yawar fahimta.

Kiranta yayi bayan sun gaisa cikin mutunci ya fad'a mata matsalar ta yanda zai iya, dukda ya 6oye mata wacece keda matsalar ta fahimcesa, d'an murmushi kawai tayi tana girgiza kai da tausayin yarinyarnan data shiga hannun Galadima, duk abinda zata buk'ata tagama had'ashi sannan ta fito, matsalar gidansu data Sani yasakata yin shiri tamkar ba doctor ba.

Shiru d'akin yayi, sai kukana dayake fita a hankali, shikam ya zubamin idanu yana kallona k'asan ido, zaune yake k'afa d'aya akan d'aya, ya jingina da kujera, saika rantse idonsa a rufe yake, amma yana kallonane ahaka.

Bayan doctor Hafsat tazo k'ofar fada saita kirashi, dan baza'a barta kai tsaye tashigaba.

Ina kallonsa ya fice bayan ya yanke wayar daban San dawa yakeyinta ba.

Kusan mintun 20 saigasu sunshigo dawata mace, ba yarinya baceba can gaskiya, zasu iya zama sa'anni da Galadima d'in, dan haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login