Showing 210001 words to 213000 words out of 365757 words

Chapter 71 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1435

sannu da zuwa ga y'an uku a masarautar k'arfe 8pm, wannan yasa ba'a jimaba aka barsu suka shige Dan Munaya tasamu ta huta.



Mamaki ya kama Munaya ganin an cika mata gado da tarkacen Teddy's, wannan abun haushi da yawa yake, kuzo Ku kama jera d'iyan aljanu agado kawai.

Sudai su mom suka jasu gefe aka kwantar da yaran, itama zama tayi abakin gadon tana dafe kai.

Aunty Mimi tace,  lafiya dai k'anwa? .

 wlhy kaina ke ciwo aunty mimi .

Sannu suka shiga yimata, mom tace,  bara laraba tazo ayi wanka kisamu kici abinci saiki sha magani ..

Munaya ta amsa da  to tana d'an kwanciya a bakin gadon.





*********



Laraba amintacciyar baiwar inno tama Munaya cikakken wanka da babu algus acikinsa, itako sai raki takeyi da zille-zille. a haka dai aka gama wannan wanka, lokacin da suka fito sun iske yaranma Mom tamusu da kanta, ana tsaka da shafesu da mai itada Aunty Mimi.

Munaya dake d'aure da zani ta rufo babban towel a jikinta ta zauna a bakin gadon tana jingina da fuskar gadon, k'asa-k'asa take kallon yaran da mamakin anya kuwa itace wai ta haifesu? koda yake ba'a jayayya da ikon ALLAH ai, tanajin k'aunar yaranta a har cikin jininta, hakama Na y'ar uwarta, amma data tuna zasu rabu kwana kusa sai hawaye suka cika mata ido.

A dai-dai wannan time d'inne Galadima yay sallama, hannunsa d'auke da Leda fara.

Aunty mimi da mom dake sakama yaran kayan sanyi suka d'ago duk suka kallesa suna amsa masa sallamar.

Idonsa akan Munaya datai masa kallo d'aya ta d'auke ido, murmushi yayi kawai ya zauna a bakin gadon yanama su mom sannu.

Cikin tsokana mom tace,  aikin kud'i nikam nakeyi, musamman akan kishiya sa haushi, bar saurin godemin , tai maganar tana dungure d'an hancin macen dake hannunta.

Murmushi kawai Galadima yayi, sai Aunty Mimi CE ke bama mom amsa da  habawa Mom, dukfa kishinki keda Momma kwayi Ku gama, itafa wannan sarauniyar saita za6a ta darje ehe .

Mom tai dariya tana mik'ama Galadima ita,  yo da wannan nanannen hancinne zata za6a ta darje d'in? maji magani dai ai .

Galadima ya lumshe ido yana manna yarinyar da k'irjinsa, k'aunarta Na rsatsashi, ya sumbaci goshinta sannan ya bud'e idonsa, kwantar da ita yayi akan cinyarsa ya bud'e ledar yana fiddo dabino mai k'yau da tsafta, a bakinsa ya saka ya tauna, kafin ya d'ora bakin nasa akan na yarinyar ya zuba mata, da farko yamutse fuska ta shigayi, taji bak'on abu a bakinta, saikuma a hankali tafara motsa d'an bakin, galadima dai yana kallonta da murmushi, dadai taji zak'i saita mamule abinta.

Mom tace,  oh su madan kamila kenan, anji zak'i .

Dariya duk sukayi, ya d'auketa yamata kiran sallar hud'uba a kunnenta sanan ya ajiyeta a gefe yana fad'in  ALLAH ya rayaki akan sunnah da tafarkin gaskiya .

Su mom suka amsa masa da amin.

Kallon Munaya daketa shafa manta kamarma batasan dasu a d'akinba yayi, yanda taketa wani basarwa shi mamaki tabashi, baiyi zaton hakanba gaskiya, cayake zata nuna tsantsar farincikinta akan yaran?. janye idanunsa yayi ya kar6i d'ayan yaron.

Shima haka ya tauna dabino ya bashi, sannan yamasa hud'uba da addu'a ya kwantar dashi. Kar6ar d'ayan ma yayi, Wanda bai cika kuzariba, yad'an masa kallon wasu mintuna yana tatta6a jikin yaron, sai kuma ya kalli mom da Aunty Mimi da suma kallonsa sukeyi.

Mom tace  Yaya dai Sameer? ..

K'aramar ajiyar zuciya yayi yana shafa sumar yaron,  mom yaronnan kamar baida kuzarin sauran 'yan uwansa .

 nima na lura da gakan Sameer, amma maybe yanayinsa kenan, kasan kowa da yanayin da ALLAH yake yinsa ai .

 hakane . ya fad'a cikin sauke ajiyar zuciya, sannan ya d'auki dabino shima yamasa tamkar sauran y'an uwansa, yaron yadad'e bai shanye dabinon ba, daga Bayama saiya fara kuka mara sauti.

Rungumesa Galadima yayi yana hura masa k'aramar iska a kunne da d'an jijigashi, sai kuwa yayi shiru, shima hud'uba yamasa, ya kwantar dashi kusada y'an uwansa amma sai yaron yakuma Sanya kuka, gashi muryarsa bata fita da k'yau.

d'aukarsa ya kumayi yana murmushi da fad'in  oh little Sameer what happen? .

Mom tace,  shagwa6a ce mana .

Dariya Aunty Mimi tayi, yayinda Galadima da Munaya suka murmusa, Dan duk abinda ke faruwa tana allonsu ta gefen ido, amma ta basar kamar bata d'akin.



Fita Aunty Mimi da Mom sukayi suka barmusu d'akin.

tuni 6angaren ya rikice da k'amshin girki, dan cikin kuyangin da su mom sukazo dasune suke tsara girki wa maijego dasu kansu.

Tashi Galadima yayi d'auke da yaron a jikinsa ya nufi inda Munaya take zaune, tun d'azun tagama shafa man amma tak'i tashi ta saka kaya.

Zama yay kusada ita sosai jikinsa har yana gogar nata.

Da sauri ta yunk'ura zata mik'e, ya saka hannu d'aya ya ruk'ota yana maidata.

Kallonsa tayi fuska a cunkushe kamar zata fasa kuka, idanunsa ya saka acikin nata yanda bazata iya janyewa ba, aiko duk k'ok'arinta nason ta janye d'in ta kasa, sai cika sukayi da kwalla, dan yana ganin k'yallin ruwan hawayen.

Yad'an murmusa yana lumshe ido da bud'ewa a kanta. muryarsa cikeda k'asaita da sanyi yace,  kekuma salon taki murnar kenan? .

Had'iye kukan dake Neman kufce mata Wanda itama batasan dalilinsa ba tayi, tayi murmushin takaici tana janye idanunta daga cikin nasa, muryarta a sark'e cikin sanyin rauni tace,  Ina tayaka murnar sosai yalla6ai .

Lips nashi yad'an cije, ya lalla6a ya ajiye yaron da barci ya d'auka gefen y'an uwansa, Munaya duk tana kallonsa.

Kuma matsawa yay jikinta sosai ya jawota jikinsa, batayi yunk'urin hanashiba, kamar yanda bata hana hawayenta zubaba. Ya saka tattausan hannunsa yana share mata hawayen,  Friend dukda bansan miya sakaki kukaba ina mai baki hak'uri, wannan ranar bana buk'atar damuwar kowa sai farinciki, musamman ma daga gareki, ina rok'onki alfarmar fansar wannan damuwar taki da farinciki akan kowanne farashi, komai tsadarsa kuwa . ya k'are maganar da sumbatar sumar kanta.

Murmushi tayi, ta d'ago daga jikinsa idonta akan yaran dake jere reras abin sha'awa. Shima d'in su yake kallo.

 bana cikin kowacce damuwa da kake tunani yalla6ai, kawai dai... sai tayi shiru.

Kallonsa ya maido gareta, yace,  kawai dai mi yalla6iya? .  ya k'are maganar cike da tsokana .

Ta murmusa tana mik'ewa tsaye, wardrobe ta nufa ta fiddo sabbin kayanta cikin na lefe, bata kuma kallonsa ba ta wuce bathroom domin saka kayan.

Binta yay da kallo harta shige, yasaki miskilin murmushi yana kwantawa kusada yaran, a fili ya furta  yarinya nasan matsalarki . yay maganar yana sumbatar kuncin na kusa da shi, sauran kuma ya shafa Kansu.

A haka Munaya ta fito ta iskeshi, ya ta6a wannan ya ta6a wancan, kallo d'aya tamasu ta d'auke kanta.

Sallamar da akayi a bakin k'ofar ya saka Munaya amsawa da bada izinin shigowa.

Laraba tashigo d'auke da tire babba.

Da sauri Munaya ta nufeta ta kar6a, Dan dattijuwace sosai, sannu ta mata tana fad'in  iya aida wanine ya kawo .

'Yar dariya laraba tayi, tace,  dole na kula da amanar uwar gijiyata ai ranki ya dad'e .

Munaya da Galadima suka kalli juna suna murmushi, Dan sunsan inno take nufi.

Laraba ta juya zata Fifa saboda ganin Galadima na nan.

Kiranta yay ta juyo, yace,  zokiyi aikinki kar Inno taga ta rame tace baki rik'e amanaba, nima yarana abincinsu suke buk'ata .

Hararsa Munaya tayi, yay Biris kamar bai gantaba, saima d'an yatsansa daya saka cikin hannun yaron, shiko ya rik'e gam tamkar yasan minene.



Laraba tace Munaya ta zauna ga abinci taci..

Yamutsa fuska Munaya tayi, kamar zatayi kuka tace,  wlhy iya bakina banajin d'and'anon koda yawuna ma .



 hakane ai saidai hak'uri ranki ya dad'e, dama wasu idan sun haihu sukanyi k'am baki, amma a hankali zai canja .

Badan munaya tasoba ta zauna, laraba tabata kunu mai k'yau da aka dama don ita, sai k'amshin kayan yaji yakeyi, sai farfesu.

Kallon abincin kawai Munaya keyi, amma ko kad'an batajin sha'awar ci, ta tuna kwanakin baya da idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi wajen son ci, hikimar ubangiji daban ce, ta d'ago ido suka kalli juna itada Galadima dake kallonta tun d'azu, a zuciyarsa yana tuna kwanaki uku rak dasuka shige, yanda ta maida abinci, murmushi yamata ta d'auke idonta ta maida ga abincin.

A haka Mom ta shigo ta iskesu, zama tayi tana fad'in  yanaga bakici komaiba? .

Idon Munaya cike da kwalla tace,  ALLAH mom banajin d'and'ano .

Zama mom tai kusada ita, tace laraba taje itama ta karya. Kunun ta d'auka ta tsiyaya a Kofi ta d'iba mata farfesun,  kar6a maza runtse ido ki shanye kunun nan d'iyata .

Kunyar Mom ta sakata k'ar6a tana had'iye kwallarta, tafara sha badan tanajin dad'inba, sai dan tsatstsareta da ido da Galadima yayi shida Mom. ahaka dai tasamu tasha yafi rabi, dama yunwar takeji, dad'in bakinne kawai bataji, shima farfesun tad'anci, dandanan tafara zufa. tace,

 Mom dan ALLAH bara na kunna AC .

 a ina? .  galadima ya fad'a yana tashi zaune da sauri .

Ita mom ma dariya ya bata, yawani had'e fuska yana harar Munaya,  malama babu wani AC da zaki sakama mutane anan, kina ganin yara duk da mura sukazo duniya saboda rashin jin maganarki.....

Mom ta katseshi da fad'in  ai bama zai yuwuba, itada ke jego ko fankace a d'akinnan ai saidai kallo kuma, yanzu ruwan sha ma sai mai zafi .

Galadima ya sakko daga gadon yana fad'in  hakan ai shine dai-dai wlhy, remote d'in AC d'in ya d'auka a lokan gefen gadon ya masa yanda bazata iya control d'insa bama gaba d'aya, sannan yafice abinsa yana murmushin mugunta.

Mom ta girgiza kai kawai, a ranta tana mamaki canjawar Sameer......

Maganarsa ce ta katse mata tunani, harya fita ya dawo baya,  mom ga maganinta nan tasha, kuma yaranan yunwa sukeji .  yak'are maganar cikin marairaicewa .

Dakuwa mom tamasa,  Sameer kaci kidanku, wai yaushe kama fetsare hakane ban saniba? .

Fita yayi yana dariya, ta kirashi da sauri. Kuma dawowa yayi, tace,  kasandai Doctor tace a nemi madara, naga kuma bama kada niyyar hakan .

Gaba d'aya fara'ar fuskarsa ta d'auke, yad'an shafi girarsa da d'anyatsa d'aya yana fad'in  Mom wai wace madara ga abincinsu?, ALLAH dai ai shiya haliccesu, kuma shine zai wadatasu da abincin nasu, amma kawai sai a kama wani danna musu wata madara? dan ALLAH mu ajiye zancen madarar nan ma gefe mom .

Numfashi mom ta sauke, tasan murd'ad'd'en halin Galadima da dagewa akan ra'ayinsa, cikin kwantar da murya tace,  na yarda da maganarka, amma ita za'a tausaya mawa, shayar da yara uku bafa abune mai sauk'iba Sameer, wasuma d'ayane idan suna da fargabar shayarwa kaga duksun k'are sun lalace, koda dai sau d'ayane sai a ringa basu madarar a rana, tunda ALLAH dai baya hanaka yanda zakayi bane .

Tashi Munaya tayi tana hawaye, taje ta hau gadon kawai tayi kwanciyarta, ta kula Galadima yacika son kansa, tanaga saita tuna masa da matsayin auren nasu da alfarmar yarda ta haifa masa y'ay'an dayake neman nuna mata mulki a kansu, aidai abin shayarwar a jikinta yake, sai kuma yanda taso tayi da kayanta, dolene ta takama wannan homar tasa birki.

Daga Mom har Galadima da kallo suka bita, yaja guntun tsaki yana juyawa zai fita.

Mom tace,  zaka siyo d'in? .

A k'ufule yace,  zan duba . Yay ficewarsa. shifa ya lura yarinyarnan ma batason yarannan, shin bak'in ciki take ALLAH yamasa k'yautar abinda kud'i baya sayane ko me? ALLAH zaiyi maganinta kuwa.





>�#�>�#�ho Galadima, uwa ta ta6a k'in d'antane>�&�<���
@&.







&&&&&&&&&&&&





Mama Fulani dai yau tagaza gane kanta, duk yanda taso danne zuciyarta tayi murnar koda ganin idone ta kasa, shiyyasa ko zuwa wajen tarbarsu batayiba.

Takuma hana dukkanin bayinta da kuyangi shiga inda take.



Abinda bata saniba idon Galadima fes yake akan dukkan Wanda ya tayashi murna da samun k'yautar ALLAH, wad'anda bama su fitoba sun shiga black lists, kuma d'aya bayan d'aya saiya kartama kowa rashin m acikinsu.







&&&&&&&&&



Innaro kuwa dai saita hau tsiya dataji labarin su Munaya kowa mijinta ya d'auketa zuwa gidanta, tahau zazzaga masifa anmata ba daidaiba, babu Wanda ya kulata, dan masu zugatan suma hassada ta ishesu, basuda kuzarin taya 6era 6ari=��..

Haka tagama jarabarta takoma gida tana huci, Abba yasha dariya, danshi lamarin mahaifiyar tasu yanzu kallon rikicin tsufa kawai yake masa, inba rikicin tsufaba miye abin tada jijiyar wuya anan? Sunada damar hana yaran komawa gidajen mazajen sune?.

Shikam baba k'arami ma lokacin da take jarabar zuwa yay ya ra6a ta gefenta ya fice daga gidan.





Ai lamarin innaro sai ita>�#�>�&�<���
@&.





******************



A 6angaren Munubiya ma Alhmdllh, dukkan wata kulawa mama rabi'a tana tsaye akan 'yarta da jikokinta, sai zuba mata gata akeyi da k'yak'yk'yawar kulawa mai ban sha'awa.





Suruka ta gari dadi alkur'an=؃�<���=؃�<���=��=��.







&&&&&&&&&&&&



Mom dai da k'yar suka lalla6a Munaya itada Aunty Mimi ta amince ta shayar da yaran, suna sha tana kukan zafi kuma=�9�, sunsan zataji zafi tunda Na farkone, ga yaran a buk'ace suke dama, amma kukan datake yawuce Na zafi kad'ai, (basusan harda haushi Galadima bane=��>�-�).

Mom data fahimci hakan saita fara lallashin da nuna mata muhimmanci hak'uri, su maza komai zasu iyayi akan y'ay'ansu, musamman ma shi da yake tsaka da d'okinsu yanzu, karma tabari irin wad'annam abubuwan su dameta, shima yafad'ane kawai amma zai sayo madaran .

Itadai Munaya kai kawai take d'agawa amma batace uffanba, dan tagama Sanin Galadima da halinsa Na kafiyar tsiya da dagiya akan ra'ayinsa.

Bayan duk sunsha sun k'oshi Aunty Mimi tace ta kwanta ta huta kafin time d'in walimar yayi. ALLAH ya taimaketa maganin yasata barci kuwa, yaran Na gefenta suma suna nasu barcin, kowa cikinsa ya cika kenan=��.



Ajiyar zuciya Aunty Mimi ta sauke tana murmushi, tace,  Mom d'an nan naki bazai canja ba dai ashe? lamarin Sameer saishi wlhy, koda bayaso susha madarar saiya fad'a da harshe mai dad'i ba fad'aba .

 Humm, kibari kawai, nifa harna fara murnar ya canja, Ashe yana nan yanda nasan kayana, yarinyar tanada hak'uri kuma wlhy, dan zama da mai halin Sameer saika daure, muma iyayen idan mun k'ureshi ba iya mana kawaici yakeba .

Aunty Mimi tayi dariya,  papi ne mai tankwarashi kobai soba ai, idan yak'i bari abasu madaran dashi kawai za'a had'ashi, komin wadatar nono shayar da yara uku ba sauk'i ne dashiba, balle ita farin Shiga ma ..

Mom tace,  hakanma shine kawai mafita ai .





***************************



*_8:15pm_*



Liyafar cin abinci tafara gudana a babban d'akin taro Na masarautar gagara badau, Munaya da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login