Showing 48001 words to 51000 words out of 365757 words

Chapter 17 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1473

tsit.







&&&&



Gaba d'aya a kwanaki biyunan banida wani sukuni, tunanin maganar yak'i barin zuciyata, a kowacce dak'ik'a zuciyata tunzurani takeyi akan Na amince kawai, dan banida wata mafita sai wannan, ni kaina inason sanin Wanda ya aikata mana wannan abun, sannan bana fata sauran 'yan uwana suyi aure su barni a gidannan, hakan ba k'aramin tozarci zai zamarminba, ga Munubiya tadage akan innarmu ta sanarma Abba itama ad'aga bikinta har saina samu miji nima ahad'a ni da ita, na nuna mata 6acin raina akan maganar amma abanza, tanuna Sam ita tana a kan bakanta, nikuma harga ALLAH ba zanso hakan ta kasanceba.

Ita kanta innarmu nakula danne zuciyata kawai takeyi akan fasa aurena, amma tana cikin matsananciyar damuwa.

Yanzu yazanyi kenan? Na amince ko karna amince? gashi ya gargad'eni akan kadda Na nemi shawarar kowa, ni kaina nama kasa sanarma koda Munubiya, kuma kullum cikin tanbayata take mike damuna? duk da ita zatonta akan maganar Haidar ne har yanzu nake cikin damuwar.



Yau dai kwanaki biyu kenan da faruwar abin, har yanzu kuma nakasa tsayawa a matsaya d'aya.

Kusan tashin hantsi muna tsakar gida a baranda muduka 'yan matan gidan, kowa da hidimar dayakeyi, sai wasu daga cikin k'annenmu dake wasa agefenmu, iyayenmu kuma Na daga can k'arshen barandar suma kowa da hidimarta, innarmu ce kawai babu tana gidan mama Rabi'a taje duba feena da jikinta yad'an motsa.



Tsayuwar mota mukaji a k'ofar gida, yara suka tafi da gudu dansuga wanene? azatonsu cikin su Dady ne.

Mintuna baifi 10 ba saigasu suna shigowa da ledoji, saikuma ga Zarah tashigo cikin kwalliyar kece raini, tana taku d'ai-d'ai, daka ganta kaga mai yaron ciki, cikeda muran muka hau mata sannu dazuwa, itako saiwani ciccijewa take tana kuma Jan kai, ita adole matar manya.

Abin kallo bai k'areba saida mamansu yaa Hameed ta iso da d'an gudu ta rungume Zarah a jikinta, duk mukai galala muna kallon wannan sabon salo.

 masha ALLAHU Zarah sarkin haske, kinganki kuwa, da anganki anga matar manya yarinyata, kai ai aure Ni'ima ce babba, duk wacce ALLAH yabama 'yarta miji matan gidannan ta godema ALLAH, Dan wlhy yana sonta .

Caraf Momy Hadiza ta kar6e da fad'in  wlhy kuwa Yaya, ai babu babban bak'inciki irin kanada gandamemiyar budurwa a d'aki tayi kwantai takasa auruwa, aimu sai godiyar ubangiji wlhy, babu ta inda ni'ima bata saukar manaba, Zarah zoki zauna ki huta kinji 'yar albarka .

Maman safara'u da gwaggon haleema da maman su Fiddausi suka kwashe da dariya.

Kowa yasan damu ake wannan gugar zanar, amma sai mukayi murmushi kawai bamuce komaiba, maman fauziyya ma batace komaiba, nama godema ALLAH da innarmu bata nan balle ranta ya 6aci.



Tsam namik'e nabar wajen zuciyata Na suya, Na danne kukan dake shirin tahomin...

Maman Safara'u tace,  to yanzu ke bazaki iya danne zuciyarki ba saikin nuna hasaadarki a filin ALLAH?, to Ashe ranar auren 'yan uwanki mutuwa kuwa zakiyi?, dan kina gani za'a d'auke kowacce abarki agidan.

Wani k'arfine yazomin a zuciyata, Na had'iye kukana, najuyo ina kallonta ido cikin ido, wani murmushin takaici nasaki, sannan nace  maman Safara'u ke uwace agareni, sannan innarmu takoya mana tarbiyyar girmama kowacce mace agidannan, badan hakaba dana fad'a miki maganar dabazaki ta6a mantawaba, kuma ba hassadar tasani tashiba kamar yanda tunaninki yabaki, natashine Na d'aukama Zarah ruwansha, naga tashawo rana kuma babu Wanda yayi yink'urin bata .

Ina gama fad'ar haka nabar wajen. tsit banji kowa yasake maganar ba, bansan miyasa ba, maganar tawace tasakasu yin shiru kokuwa oho.

Ina shiga falonmu Na fashe da kuka, anzo ga6ar da kawai zan amince da buk'atar Galadima, insha ALLAHU aranar datake fad'ar za'a tafi abarni, aranar nima zanbar gidan, Na gwammace nayi auren shekara d'ayan nafito.

Tunanin tawace hanya zanbi Na fad'ar musu Na amince na farayi, dan basu bani number ko wata hanyaba dazan iya nemansu, gashi kuma bazan iya gane gidan dasuka kainiba.

Tunawa dawata farar takarda nayi, wadda nagani a bag d'in dana fita da ita a ranar, kuma nasan ni bani Na ajiyeba.

Da Sauri Na d'auki bag d'in na zazage, saiga takardar tafad'o, na d'auka na bud'e, Number wayace ajiki kawai.

Jikina har rawa takeyi na d'auki wayata na kwafe number, sai kuma nakasa kira, na fara zagaye d'akin.

Motsi naji kamar na tafiya, da Sauri na shige bathroom d'inmu dan nasan Munubiya ce.

fanfo na kunna yanda zata d'auka wanka nakeyi.

Sha warar tura massage kawai na yanke. dan haka na rubuta



*_ na amince inhar bazai zama ka wulak'anta rayuwa taba ._*



Haka kawai natura masa na cire kayana nafara wankan gaskiya...........
'<���







�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&time d'in wasa yafara.>�8�<���
@&











*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=�O�<���=�-�

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���1� 7�





.........Cikeda girmamawa yace,  Ranka ya dad'e barka da dare? .

 barkan ka dai Muhammad. dama kashigo k'asar kenan? .

Gabansa yad'an fad'i, danshifa yama manta mai martaba baisan yazo k'asarba, dakiyar dole ya aro yace,  wlhy kuwa nashigo d'azun yin wani aiki, amma gobema idan ALLAH ya kaimu zan koma .

 tofa, gobe gobe? kuma gashi inason ganinka a goben .

d'an jimm yayi, irin tamkar baisan komaiba, cikeda shakku yace,  ranka ya dad'e lafiya dai ko? .

 lafiya k'alau, wata muhimmiyar magana nakeson muyine .

 to shikenan, zanshigo insha ALLAH  .

 to madalla saina ganka .



Dafe kai Galadima yayi yana mamakin kansa, anya kuwa baima kansa d'aurin gorobo? koda yake idanfa yayi hak'uri shekara 1 ne ko 2 kacal, inma komai yafito kafin cikar shekarar zai sawwak'a matane, yad'an murmusa sannan yakoma ya kwanta abinsa cikeda tunani barkatai.







&&&&&





Rashin reply d'in Galadima ya dameni, haka dai naita danne zuciyata dankar innarmu da Munubiya su fahimta, nacigaba da harkokina tamkar banida wata damuwa a zuciya, saima sallar dare damuka fara dagewa da tashi nida Munubiya, gakuma azumin damuka tashi dashi yau litinin.

Duk da innarmu ta fahimci inada damuwa batacemin uffanba, saidai tausayina na damun zuciyarta, tana dannewane kawai.

Munubiya kam tsaf tagama fahimta ta, amma itama saita nuna bata fahimci komaiba, taje tasamu innarmu da maganar son a d'aga bikinta again.

 munubiya ba wannan yakamata muyiba, addu'a yakamata muyima 'Yar uwarki, idan da rabo saikiga ALLAH ya kawo mata miji a cikin watanni 2nan dasuka rage kinji. nima nasan tana acikin damuwa, amma tana dannewa a zuciyarta saboda farin cikinmu. addu'ar dazamu mata itace tsantsar k'aunarta a garemu .

 shikenan innarmu, insha ALLAH zamu kuma dagewa da fad'ama ALLAH, itama ALLAH ya kawo mata ta hanyar da batayi zatoba, ya sakanka mata fiyeda sadaukarwar datayi, innarmu nasan sadaukarwar da 'Yar uwata tayine yasakata a wannan halin, ta sadaukar da farincikinta saboda ni, mizanyi na biyata nikam .

Murmushi innarmu tayi, tace,  addu'a .









&&&&&



Washe gari yatashi ya shirin tafiya masarautar su Momma, Harun yakira yace ya nema masa ticket.

Cikeda mamaki Harun yace,  yaushe kashigo k'asar Galadima? .

K'aramin tsaki yaja, dan shifa yama manta Harun baisan da zuwansa ba, Link d'in hannun rigar milk d'in shaddarsa yake k'okarin sakawa, cikeda dakiya yace,  jiya nazo da daddare, kuma inagama yau zan koma .

 tofa, amma baka cikin masarauta? .

 no a hotel Na sauka .

 ok barato a nema ticket d'in, sai muzo mu d'aukeka .

 karka damu harun, banason kowa yasan nazoma, muhad'u dakai kawai a airport  .

Koda suka yanke wayar sai yaja tsaki, gaba d'aya yakoma mak'aryaci, abinda yatsana arayuwarsa fiye da komai kenan (k'arya) amma sai gashi shi yana zundumata,  Astagafurullh yashiga maimaitawa a zuciyarsa.

Tsaf yafito cikin shadda milk color (nakula yana k'aunar milk) d'inkin rigar 3quarter, harda su hula, yayi k'yau sosai, yafito ainahin sa na cikakken bahaushe kuma basarake, ya fesa turaraensa Na kullum, komai nasa dayazo dashi ya had'a a waje d'aya. sannan yakashe kayan wutar bedroom d'in.

Afalo ya iske Muftahu zaune yana jiransa, yad'anyi mamaki amma sai bai nunaba, yabashi hannu suka gaisa.

Muftahu yace,  zaka dawo ta nan kenan? ..

Kai Galadima yad'aga alamar a'a, sannan yanufi kayan wutar falon yafara kashewa. saida yagama komai sannan ya kalli Muftahu alamar suje.

Murmushi kawai Muftahu yayi, danya lura yau miskilawanne aka.



Sun isa airport, lokacin shima harun harya je, mamakine ya kama harun Dan ganin Galadima tare da Muftahu, shima yanzu yana mamakin yanda Muftahu ke kuma kusanta kanshi da Galadima, baice komaiba yabashi hannu suka gaisa kamar yanda yabama Galadima.

Harun yanason suyi magana da Galadima amma ga Muftahu a wajen, sai kawai yashare akan sayi a waya kawai.

Basu wani dad'e a airport d'inba jirgin su Galadima yatashi.







&&&&





Yau hankalin kowa a tashe yake agidanmu saboda gwaggo Safiyya da aka kawo batada lafiya, dayake ba'anan kusa damu take aureba, tanacan wani gari daban, tun lokacin bikinsu yaa Hameed tamasu Abba complain akan batajin dad'i, amma kunsan maza darashin d'aukar Abu serious, sai basu maida hankalinsuba.

Ita kuma kunya tahanata kuma musu maganar, har aka gama biki ta tafi, ashe baiwar ALLAH ciwo nata cin jikinta babu Wanda yasani, tun tanayi a tsitsaye har takai ga kwanciya, yaranta sun kaita asibiti amma basuga wani canjiba, hakanne yasa suka maidota gida, Dan aganinsu dai su Abba sunfi mahaifinsu k'arfi.

Aiko suna isowa babu 6ata lokaci aka wuce da ita asibiti.

Dan danan aka fara bata taimakon gaggawa.

Muda innarmu ne kawai da innaro a asibitin, amma matan gidanmu babu wace tabimu, kusan mudasu baba k'arami muketa shiga da fita a asibitin dan ganin komai ya dai-daita.

Kusan yamma saigasu Safara'u lokacin ma gwaggo Safiyya tana barci, yaranta duksunyi jigum-jigum da innaro saboda tashin hankalin dasuke ciki.

Har dare ba'abar kowa yashiga wajen taba, sai su Dady kawai, ganin dare yayi akace mu muje gida kawai.

Haka muka tafi akabar innaro da aunty habiba d'iyar gwaggo safiyyar ta uku, itama tayi aure amma tafito, yanzu zawarci takeyi. saikuma yaa Anas da aka barmusu saboda ko wani Abu zai taso.









&&&





Tunda yafito daga jirgi ya hango tawagar masarautar kakannin nasa, yasan tarbarsa sukazoyi, inhar zaishigo haka sukeyo gayyar tarbarsa, saikace wani bak'o daban, gefe yayi da fuskarsa dankarsu gansa, sashen motocin da akan d'auka drop ya nufa, duk manyan motocine da aka tanada dama domin irinsu, d'aya yabud'e da Kansa yashige da sauri, alamar yayma driver d'in suje.

Tacikin glass yake kallonsu yana murmushi, yanda suketa d'aga kai nason hangosa, suna fita daga airport d'in ya kwantar da kansa ajikin seat ya lumshe idanunsa yana tunanin wane hukunci mai martaba zai yanke akan maganar, shin ya amincene? Kokuwa?.

Driver yace,  oga ina muka nufa? .

Bai bud'e idonsaba kuma bai d'agoba, yace  gidan sarki .

Ta madubi driver n ya kallesa,  yalla6ai ko kaine ma dai akazo tarba daga masarauta? .

Murmushi kawai yayi batareda yace komaiba.

Jin bai amsaba sai driver yakama bakinsa ya tauke shima.

Ganin shine yasa dogarai suka bari aka shigar dashi har cikin masarauta, tunda yafito bayi da hadimai keta zubewa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai yake d'aga musu, fuskarsa ad'an sake take, bai d'aureba baikumayi murmushi ko dariya ba kai tsaye.

Tuni an kar6i kayansa an nufi sashin inno dasu, shikuma yanufi fada, Dan yasan yanzu Sarki suna fadanci.



Cike fadar take da 'yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso yashiga da sallama, nanfa dogarai suka fara zuba masa kirari.

Hannu kawai ya d'aga musu ya rissina yana mik'a gaisuwa ga Sarki.

Sarki da fuskarsa tacika da fara'ar ganin jikan nasa ya amsa cikin lumshe idanu.

Nan dogarai suka d'au da fad'in  sarki ya amsa maka sarkin gagara badau na gobe, an gaida magajin sarki, galadiman gagara badau, ALLAH yabaka zamani irinna sarki gagara badau.

Galadima Yakuma rissinawa ya mik'a gaisuwa ga 'yan majissar sarki, suma cikeda fara'a suka amsa, kowa yasan irin tsantsar k'aunar da sarki kema jikan nasa a masarautar.



Atake anan sarki ya sallami kowa, fadanci yatashi saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu, yau yanada ganawa ta musamman da jikansa.

Haka kowa yatashi yana musu addu'ar kasancewa cikin aminci.



Tareda Galadima sarki yashiga cikin gidansa, hannunsa Na rik'e da Na Galadima, ba sabon Abu bane hakan a masarautar, duk Wanda yakwana yatashi acikinta yasan matsayin Galadima azukatan masu masarautar.

Akatafaren falon sarki suka yada zango, babu dad'ewa da shigowarsu saiga jakadiya da kuyangi uku, kowanne d'aukeda babban tire, bayan sun dire komai suka zube suna kwasar gaisuwa wa sarki, sannan suka gaida Galadima.

Jakadiya ma ta rissina ta gaida Galadima damasa barka da zuwa masarautarsu.

Bayan fitarsu Galadima yakuma risainawa a girmame ya gaida sarki kakansa.

Cike da murmushi sarki ya amsa yana kamo hannunsa,  Muhammad Sameer! kana lafiya .

 Alhmdllh ranka ya dad'e .

 Masha ALLAH, ya kabaromin Zeenah ta da jikin babanka da 'yan uwanka kuma su Haneefa? .

 Momma lafiyarta lau, hakama jikin Abie Alhmdllh, suma su aunty mimin haka .

 to Alhmdllhi, ALLAH yacigaba da jagorantar lamuranku ya albarkaci rayuwarku ta gobe da jibin jibima .

Murmushi Galadima yayi yana amsawa da amin.



Sarki da Galadima tare sukaci abinci, (tun yana k'arami dama idan yazo gidan hakance ke faruwa tsakaninsu) Sunci sun k'oshi sukayi hamdala ga ALLAH.



babu wani 6ata lokaci sarki yashiga masa bayanin kiran nasa akan maganar da Fateema (mom) tazo masa da itane jiya, shima ya zauna yayi nazari yagane hakan shine dai-dai, Galadima ya auri Munaya.

tur6une fuska Galadima yayi tamkar baisan komaiba, yace  ranka yadad'e ka gafarceni, ammafa ni bata minba ai .

Sarki yay murmushinsu Na manyan k'asaitattun masu ji da mulki,  basai tayi makaba Muhammad, domin sanda Na aurama babanka Zeenah itama bai mataba, amma saboda biyayya dakuma tausayin d'iyar 'Yar uwarta ta amince tamin biyayya, to kaima hakan nakeso gareka, ka amsamin da to kawai saimu zauna lafiya, kasan magana biyu ba halina baceba ko .

Jinjina kai Galadima yayi yana kuma tankwashe k'afarsa, cikeda girmamawa yace  ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, Na amince da za6inka, ALLAH yabani ikon rik'ewa .

Cike da tsantsar farinciki Mai martaba ya rik'o hannun Galadima,  Muhammad ALLAH shiyi maka albarka, ya tsareka dadukkan sharri, ALLAH yabama mahaifinka lafiya kaji .

 amin ranka ya dad'e, ngd sosai  .

Daga nan hira suka cigaba dayi cikin tsantsar soyayya da k'aunar juna, kowanne yanajin d'an uwansa sosaih a ransa.

Kusan atare suka yini, inno tun tana zuba idon shigowar Galadima harta hak'ura. Galadima bai shigo wajenta ba sai bayan sallar magriba.

Tundaga k'ofar sashenta hadimai keta kwasar gaisuwa, tuni labarin tahowarsa ta iske inno, hakan yasa ta k'imtsa da k'yau, ta sallami bayinta masu mata hidima.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login