Showing 162001 words to 165000 words out of 365757 words

Chapter 55 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1505

Na iske harya shiga mota, nima aka bud'emin na shiga, handbag d'ina ta mik'omin tana fad'in  ranki ya dad'e ana buk'atar rakkiyarmu ne? .

Murmushi namata, na juya na kalli Galadima danjin mizaice, kansa ya girgiza alamar a'a.

Juyawa nima nayi na girgiza mata kai, tamana addu'a tana rufe k'ofar.

Tunda muka tafi babu wanda yace uffan, yanata latsa wayarsa.

Airport muka nufa kai tsaye.

Bayan motocin sun tsaya sarkin mota na yunk'urin fita yace  2 minutes  .

Sarikin mota yace  to ranka ya dad'e .

Ni ban fahimci mi suke nufiba, naga dai sarkin mota ya fita mukuma ba'a bud'e mana ba, sai kawai nakai hannu zan bud'e.

Hannuna ya rik'o, na juyo ina kallonsa, har Yanzu idonsa nakan waya,, ajiye wayar yayi ya juyo yana fuskantata, ina yunk'urin tambayar lafiya naji la66ana cikin bakinsa.

Ya salam, na fad'a a zuciyata, saida ya shanye janbakin la66ana tas sannan ya sakeni. yanda kukasan gunki haka na koma masa, ya buga yatsunsa biyu saitin fuskata suna bada k'arar d'as d'as yace  gargad'i, first and last dazanganshi abakinki yayin fita .

Harya fita ban iya motsawa ba, saida aka bud'e murfin 6angaren danake sannan na iya sauke numfashi, na kasa fahimtar damuwar guy d'innan kwata-kwata. fita nayi nima, yana tsaye yana jiran fitowata. a tare muka jera muna tafiya, yayinda dogaransa ke take mana baya. ya wani miskile fuska tamkar bashine yagama ta6argaza ba a mota yanzun.

Mutane sai kallonmu suke, masu gulma nayi masu nunamu nayi, ni dai duk sainaji wani iri, shima tsaki yayi danya tsani kallo.

A mamaki na duk sai naga 'yan gidanmu ma a wajen, gaggaisawa muka shigayi, muka rik'e hannun juna nida munubiya muka k'arasa inda innarmu take, gaisheta nayi, nace  su Aiyaan fa? .

 suna gida zasu zauna da mamanku mana .

 kai innarmu, ya zaki barsu wajen muguwarnan, bama gara Maman fauziyya ba komu suzo wajenmu .

Murmushi kawai innarmu tayi, tace,  ashe bazaki canjaba Munaya? .

6ata fuska nayi, ina fad'in  kai inna, duk canjawarnan danayi .

Murmushi sukayi itada Munubiya. akuma dai-dai time d'in Ambulance ta shigo airport d'in, sai mota biyu a bayanta sai motar police guda d'aya.

Gaba d'ayanmu hankalinmu saiya koma can, Galadima ya k'arasa wajen Ambulance d'in, yayinda sauran motocin biyu Sauban da Nuren baba k'arami Dady ya Shafi'u da yaa Naseer yaa hameed suka fito.



Zuwansu baifi da mintuna 15 ba aka fara kiran sunan wad'anda zasu tashi a jirgin.

Sai kuma ma'aikatan wajen mutum uku suka iso wajen Ambulance d'in aka fara k'ok'arin fidda Abba. Hankalin jama'a da yawa ya tashi a airport d'in nan saboda tausayin Abba, mukam kuka ma wasunmu sukeyi ai, muna kallo aka gungura gadon da aka d'oroshi har zuwa ga jirgin.

Suma su innarmu suka shiga itada baba k'arami da Sauban.

Rungume juna mukayi nida munubiya muma muna kuka.

Galadima bai fito cikin jirginba saida yaga komai ya dai-daita. yana fitowa babu dad'ewa jirgin ya d'aga zuwa sararin samaniya, yayinda mukuma muke binsu da addu'oin fatan alkairi da samun sauk'i.................
'<���









>�%�kutt harda na gobe nayi=�D��&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&.















*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���_*

*_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���1� 2�





...............Maman Fauziyya tamatso ta kama hannunmu ni da Munubiya tana lallashinmu, da fad'a mana mu bisa da addu'a, insha ALLAHU da k'afarsa zai dawo.



Ganin mun fara shirin tafiya na taka inda Galadima yake tsaye da Nuren suna magana, tun d'anzun ina lura dashi ya kafeni da idanu, yanzunma suna maganar amma idonsa na kaina na k'araso garesu.

Nuren daketa fara'a yace,  gimbiyarmu barka da hantsi .

Murmushi nayi sannan na gaisheshi, ya amsa yana tambayata yaya jikina?.

Nace  Alhmdllh na warke ai .

 to ALLAH ya k'ara afuwa gimbiya .  yafad'a yana matsawa gefe domin bamu waje.

Galadima dake kallona hannunsa duk biyu cikin wandon sky blue d'in shaddarsa da tsawon rigar iyakarsa rabin cinyarsa, yace,  Lafiya? .

Dakewa nima nayi, cike da jan ajina nace  k'alau. Dan ALLAH zanbi Munubiya please yalla6ai .

Janye idanunsa yayi daga kaina yana fad'in  awane farashi? .

 kamarya farashi? ciniki mukeyi? .

Hannunsa d'aya ya fiddo daga aljihu ya shafa sajensa zuwa gemu, cikin kafeni da idanu yace  kusan haka, kinsan rayuwar bani gishiri in baka manda akeyi yanzun .

Cikin son tura masa haushi nace  Ai ni bana gane Hausa cikin hausa .

 really? lallai kin fad'o kuwa, kuma saiki ce ke bahaushiyace? .

Baki na tunzura masa saboda haushin rainin wayon da yake min, gasu Munubiya kuma shirin tafiya sukeyi.

 Kinsan wannan bakin kika bari na kamashi a airport d'innan....., hummm .

Idanuna na waro,  mi kake tunanin zakayi kenan? .

 kuma turowa saina nuna miki .  yafad'a yana matsowa ..

Baya na matsa da sauri zuciyata na harbawa, anya kan Galadima d'aya kuwa?.

Kwafa yayi yana kallon agogon hannunsa yana k'ok'arin zaro waya daga aljihun gaban rigar datake ring.

Nikuma na hararesa a zuciyata ina fad'in mara kunya ai nasan zaka iya. A fili kuma nace  please yalla6ai nidai badan halina ba .

Bai bani amsaba, sai sallamar danaji yayi wayarsa akan kunne.

Jinai kawai yace,  Harun kana inane? .

Bansan wace amsa ya bashiba, naji yana fad'in  ok idan ka tashi saimu had'u . daga haka ya yanke wayar sannan ya kalleni.

 uhm mikike cewa?

Haushi tamkar zai karni nace  please mana autan Momma .

Murmushi yayi yana cije lips,  wlhy yarinyarnan kin gama rainani, ninema Autan? .

 lah nama manta ashe kaifa na tsakkiyar momma ne, karma Yaa Sauban ya jini .

 kinsan ALLAH na damk'eki a airport d'innan saikin fad'amin dawa kike .

Dariya nayi ina d'aga masa yatsu biyu,  karka damu yalla6ai zanyo maka tsarabar sweet and biscuit yeah .

Da sauri yay yunk'urin damk'o hannuna ganin zan gudu. yana rik'owa mukaji ance  hallo . A bayanmu.

Batareda ya saki hannuna ba duk muka waiga ni da shi.

Matashiyar budurwa fara k'al, kuma k'yak'yk'yawa masha ALLAH.

Dan danan ya tsuke fuska, tamkar ba shine yagama murmushiba yanzun.

Nima bansan murmushi ya gushema tawa fuskarba, baiyi magana ba, sai nice nace  lafiya kuwa? . yanda nayi maganar cikin rainin hankali yasaka yarinyar rik'e ha6a tana ta6e baki tana fad'in  ke kuma fa? .

Kamar zanyi magana saikuma Na shareta kawai, galadima Na kalla fuskata a cunkushe alamar fushi, d'ayan hannunsa ya d'agamin yana ta6e fuska alamar shifa babu ruwansa.

Na tura baki tareda juyawa zan bar wajen.

Hannuna dake cikin nasa ya kuma damk'ewa da k'yau, hakan yasani dawowa baya tamkar zan fad'a jikinsa, amma nayi jarumtar tirjewa kodan jama'ar gidanmu.

Dama ajikin wasu motoci muke, sai kawai ya fisgi hannuna muka shige tsakkiyarsu ya mannani jikin mota shikuma yamin rumfa. ban ankaraba naji bawan ALLAHnnan ya ha.......>�%�.

Jikina kawai rawa yakamayi saboda tsoro, wlhy ban ta6a tunanin da gaske yake zai iya hukunta bakin nawa a airport d'inba.

Ita kanta budurwarnan idanu ta zaro waje cikin wangale baki.

Nuren dashi kad'ai yake saitin dazai iya ganinmu saikuma wasu tsirarun mutane dake nesa damu, wad'anda ba lallaine ma su fahimci abinda akeba, kaucewa kawai yay daga wajen yana tuntsura dariya.

'Yan gidanmu sunga lokacin da Galadima yaja hannuna muka shige tsakkiyar motocin, amma basa hangomu. tsabar gulma irinta mamansu Yaa Hameed da Momy da Maman Safara'u sai suna shiga k'ok'arin son ganin mi mukeyi a wajen?=�1� su duk tunaninsu wata maganar banza nama budurwarnan yake shukamin rashin mutunci Dan duk agaban idonsu tazo wajen har rik'omin hannu da yayi, dukda basa jin mi Muke fad'a Dan muna nesa dasune.

Yaa Sabi'u dabasu lura da abinda ke faruwa ba suka Shiga musu maganar INA zasuje? suzo su ajiyesu gida sufa wajen aiki zasuje.

Ina basu saurareshiba saida sukazo saitin dazasu iya ganinmu.

A tare suka zaro idanu, Baki da hanci, duk sun shiga mamakin ganin Galadima Na kissing d'ina, ai babu shirin suka koma baya zukatansu Na tukuk'i da jifanmu da kalmar 'yan iska fitsararru.



(>�#�Yo wayace kuje gani? kazantar dabaka ganiba sunanta tsafta=��=��).





Yana Sakina kunya tasakani fad'awa k'irjinsa Na 6oye fuskata, hannayensa yasaka ya zagaye bayana yana dallama yarinyarnan wata muguwar harara data saka hanjin cikinta kad'awa, babu shirin tabar wajen tana mak'yark'yata da tunanin Galadima ko dai kurmane da gaske.



Driver d'inta dake kallon komai tun d'azun ya tuntsure da dariya yana fad'in ALLAH ya k'ara, bana fad'a miki Shiba Na wasan yara bane ba, banda jaraba kinbi kin nanik'ema bawan ALLAH daga had'uwa a jirgi, kinbi kin addabi rayuwata saina nemo miki number sa, aini nama godema ALLAH da kuma sake had'uwa ya kuma nuna miki ainahin halinsa, saida Na fad'a miki baima dad'e dayin aureba, ke gadararriya kikace aurensa bai damekiba........

Yanda ta daka masa tsawa yasakashi firgita ya russuna yana Neman afuwarta.

Cikeda masifa tace  tada mota mukoma gida .

 Amma ma'am kin manta jirginku yakusa tashi? . A tsorace yayi maganar.

Harara ta Dalla masa tace  Ubanka ne ya viyamin kud'in jirgin .

Wasu yawu masu rad'ad'i driver ya had'iye yana girgiza mata kai, ya bud'e motar ta Shiga sannan ya rufe shima ya zagaya mazauninsa suka koma Inda suka fito=��.





Nasan dai kun fahimci yarinyarnan Ce da suka zauna waje d'aya a jirgi itada Galadima randa zaizo=��>�s�.



Ganin tabar wajen Galadima yay murmushi sannan yafara k'ok'arin d'agoni daga k'irjinsa, ban yarda mun had'a idoba na bar wajen.

 Saikin dawo ya fad'a a hankali.

Kasa daurewa nayi saida Na waigo Dan tabbatar da shine yay maganar kokuwa dai wanine?. Ido muka had'a ya janye nasa cikeda basarwa yana la6e baki.

Nima harara Na watsa masa ina barin wajen.

Tunda Na taho Maman safara'u da mamansu Yaa hameed da Momy suka zubamin ido.

Nikuma fahimtar kallon k'urillar da sukemin saina canja salon tafiya da kuma had'e fuska na nufi zuwa wajen gungun yaran gidanmu masu aure dasuke hira.

Suma duk kallona sukayi, namusu murmushi ina fad'in  lallai munada cin ragunan suna kwannan nan ashe .

Dariya duk sukayi, Fiddausi tace  yariman namu shikuma da kwad'ayin naman suna yazo? .

Harara Na zuba mata ina kai mata bugu ta waske itama tana dariya, yayinda su Munubiya ke tayata.

Mun gaggaisa tareda tambayar lafiyar juna, muka d'an ta6a hira kad'an da alk'awarin duk zanje mu gaisa, suma sukace zasuzo tunda ba yanzu zan koma ba. daga nan mukai shirin tafiya, Siyama da Zarah anata mana iyayi su masu motar hawa, (dayake kowacce a motarta tazo).

Ni dai ni da Munubiya Yaa Marwan ya d'aukemu muka tafi.





____________________________



Tunda nabar wajen Nuren yazo ya tasa Galadima da tsiya, wai dama haka yake ashe?, rashin kunyar tasa har agaban surukai?.

Banza Galadima yamasa yay shigewarsa mota yabarsa yana iskancinsa.

Anan suka tafi suka barsa dayake da mota yazo shima.



Galadima na barin airport gidanmu ya nufa shima.

A lokacin 'yan gidanmu suma sun Isa gida, sunata k'ananun magana akan abinda Galadima da munaya sukayi, dan saida suka bama sauran labari, nanfa suka kacame da zancen harda k'arin k'arya akai wai ba kiss kawai sukaiba ('yan gidansu munaya annamimatu=�F�<���=��).

Itadai Maman Fauziyya batace k'alaba, saima dariya da zancen ke bata, Dady kuma bai dawo gidanba, daga nan wajen aiki ya wuce, yaran gidan ma kowa gidanta ta koma basu biyo nanba. Innaro da gwaggo Safiyya kam gida suka shige ana saukesu, dan haka basuji komaiba.



Galadima bai shiga gidan ba, saiya nemi iso gidan Innaro, Habiba ta fito tamasa jagora.

Innaro na falo tana cika da batsewa gwaggo Safiyya na lalla6ata akan ta kwantar da hankalinta.

Koda Galadima ya shigo innaro sai antaya masa harara takeyi, yana kula da ita ta gefen ido, ya murmusa yana zama saman kujera, cikeda tsokana yace  Sweet Granny Yaya dai? .

Harara innaro ta zuba masa sosai, tana fad'in mikuma kazo min nan? .

Galadima ya murmusa yana maida hankalinsa ga gwaggo Safiyya, gaisheta yayi ta amsa masa cike da kulawa, sannan ta d'ora da godiya da kwarara masa addu'ar fatan alkairi.

Yaji dad'i sosai, ya amsa cikin fara'a, sannan yace,  Granny ina furar tsufa? .

 ai bazaka shata ba  .

Nanma murmushin Galadima yayi yana mamakin wannan rikitacciyar tsohuwa. Yace  tunda bazan shaba Ashe kema kuwa bak'yaje India ba .

Zabura innaro tayi, ta maida hankalinta ga Galadima tana fad'in  da gaske kake ko shak'iyancine? .

Mi su Naja'atu zasuyi inba dariya ba, Galadima ma handkerchief ya saka ya rufe bakinsa kawai. Gwaggo Safiyya kanta saida ta dara.

Galadima ya gyara zamansa yana fad'in  karki damu Granny ninmu, insha ALLAH tare dake zamu tafi idan zamu koma .

Dad'i ya kama innaro ta shiga sakama Galadima albarka.

Shidai murmushi kawai yakeyi. saida yaga sun nutsu sannan yace yazo tafiya dasu Aiyaan ne, babu musu innaro ta mik'e da kanta zuwa gidan danta kawo masa su.

Bayan fitarta gwaggo Safiyya tabama Galadima hak'uri akan darun innaro.

 karki damu gwaggo, ai dama kowa yasan idan sunkai irin wannan age d'in saida lalla6awa, ALLAH dai yaja mana ransu .

Amin gwaggo Safiyya tafad'a cikin jin dad'i.

Tunda 'yan gidansu Munaya sukaji wai Galadima ne da kansa yazo tafiya dasu Aryaan sai zukatansu suka kuma tunzura, kowa tana ganin hakan salon munafurcine, Maman Fauziyya ta kawoma innaro su, dama suna d'akinta, dan mamansu yaa hameed suna dawowa ta d'auki jakkarsu Aiyaan ta kaimata, wai sai dai su zauna wajenta ita d'akinta babu fili.

Maman Fauziyya batace komai ba ta kar6i su Aiyaan tana jinjina bak'in hali irinnan jama'ar gidan.

Amma kuma yanzu sai gasu sune dajin haushi.

Ita dai innaro ko'a kanta ta jawo hannunsu Zainab ta d'akko jakkar kayansu suka taho.

Koda sukazo ma sai Galadima yace abar kayan nasu su kad'ai yake buk'ata. ya ajiyema Gwaggo Safiyya da innaro alkairi ya fito rik'e da hannun su Aiyaan daketa murna.

Innaro har wajen mota ta rakosu, bata komaba saida taga tafiyarsu. tana komawa gida tahau had'a kayan tafiya, wai gara ta had'a ta huta, duk randa Galadima yazo sai tafiya kawai.

Ita dai gwaggo Safiyya dariya kawai tayi, dan maganar Galadima gaskiyace, lamarin innaro yana buk'atar uziri, ta tsufa sosai, kawai dai ALLAH yabata lafiyane, dan da wuya kaga innaro na kukan wani waje namata ciwo irin na tsufa. (masifarta kam dai kunsan ance abinda kayi a k'uruciya shi kake maimaitawa lokacin tsufa, ALLAH ka azurtamu da k'yak'yk'yawar k'uruciya to>�&�<���
@&).







&&&&)(&)(&&&&





A k'ofar sabon matsakaicin gidan motocin biyu suka tsaya, cikin wad'anda suke a motar baya d'aya ya fito ya bud'e motar farko, hamshak'iyar macece


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login