Showing 363001 words to 365757 words out of 365757 words

Chapter 122 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1472

suke k'ok'arin dannesu, Dan matasan samarin biyu sun zama magada kwakwalwa irinta mahaifinsu Sarki Muhammad Sameer suma.

Itama Hafsat yaranta hud'u, biyu mata biyu maza, wad'anda duk suka taso a hannun Munaya, akwai zaman lafiya da k'aunar juna tsakanin Hafsat da Munaya mai birgewa, Wanda ya kawoma Sarki Muhammad Sameer kwanciyar hankali da k'yautata musu gwargwadon k'arfinsa, kamar yanda suma suke k'yautata masa da dukkan iyawarsu.



Yaran Munubiya itama 6, Dan itama 8 d'inne ta haifi biyu babu rai, Ameen yana tare dasu Abdurraheem, yayinda meenal takanyi Rabin rayuwartane a masarautar gagara badau, saboda batada k'awa wadda tawuce Amaturrahman. Inhar basa Masarauta to sunacan gidansu meenal d'in, sun zama y'an mata ababen birgewa, ita meenal tana masifar son Abdurraheem ne shikuma k'asaita da muskilanci irinna ubansa Sarki Muhammad Sameer tariga tazama jinin jikinsa, yata basar da ita kenan, wannan Abu Na cimata rai, amma aduk sanda ciwonsa zai tashi tafi kowa shiga damuwa, idan kuma taga yanda Ameen da Amaturrahman ke soyewarsu saita kumajin kanta a damuwa, shikam Abdurrahman Niger ya tsallaka, Dan d'iyar Sarki Issifa da Sarauniya Ayusher Rabi'a (Amatullah) yakeso da k'auna, ya rikice sosai, haka kawai saiyayi shiri wai yatafi yima Inna Hutu, nanko wajen Amatullah yaje.



Wannan hutune Na k'arshen shekara daya kasance duk yaran suna Nigeria, saboda bikin su Aryaan da akasha babu dad'ewa.



Sarauniya Munaya kishingid'e a kilisarta hadimanta nata hidima a gareta, matasan samarin y'ay'anta suka nemi ison shigowa gareta.

Izini ta basu, tareda sallamar dukkan Hadimanta.

Abdurraheem da Abdurrahman suka shigo, Kansu d'aya, kamanninsu d'aya, halayyace kawai ta banbantasu, Abdurraheem halin Sarki Muhammad Sameer ne gaba d'a a jininsa, yayinda Abdurrahman yazama mai irin halayyar Uncle Sauban da Abie.

Har suka zauna idonta Na kansu, sukai zama irinna k'asaita suna gaisheda mahaifiyar tasu.

Fuskar Sarauniya Munaya d'auke da Murmushi ta amsa, takai dubanta ga Abdurraheem dashi ko kad'an bashida yawan magana.

 Abdurraheem saunawa zan maka magana akan aske sumarnan ne? .

Lips d'insa ya cije (d'an gado kenan=��) yanad'an 6ata fuska.

 A gafarceni Ummu, wlhy zan Aske, jiya nafita zanje shagonki askin sai takawa yayi kirana ya Sani wani aikin, amma Ummu shima Abdurrahman kimasa magana ya yanke wannan k'umbar, ALLAH k'yank'yaminta nake.......

Harara Abdurrahman ya zuba masa, zaiyi magana Sarauniya Munaya ta katseshi tana tashi zaune,  Abdurrahman naga hannunka .

 Ummu karki yarda da gulmar yaronnan ALLAH, yatsa biyunefa . Ya k'are maganar da kuma harar Abdurraheem daya ta6e baki ya cije lips.

Sarauniya Munaya tace,  Yimani shiru, nabaku nanda dare wlhy kowa ya cire k'azantar jikinsa, ina kuma fata anje an bama Abie magungunansa? .

 Eh Ummu, Abdul-fatah ya bashi, yanzuma daga sashensu muke barci yakeyi, amma su Amaturrahman nacan sun cikama Momma kunne da surutunsu Na tsiya itada Meenal .

Murmushi Munaya tayi, Dan ita babu abinda take gani tattare da Abdurraheem sai Mijinta, shikuma Abdurrahman rashin iya R kawai ya gado shida Safah da Marwah duk basu iya R ba, to ga Saifudden nanma akwai k'asaita tsiya, d'an k'arami dashi sai mulkin tsiya, ga jarabar son girma, bawani girman jalaludden yayiba amma inkaga yanda yake basa umarni saikaci dariya, hakama yaran Hafsat.

Sarauniya Munaya tacigaba da hira da yaranta da musu nasihar tsare mutuncin Kansu kamar yanda ta saba.

Wayarta da sak'o ya shigo ta d'auka tana dubawa.

Sarkine da kansa.

Gaskiya ina buk'atar jin d'umin my mata.

Murmushi Sarauniya Munaya tayi tana kallonsu Abdurraheem da suka satar kallonta, idan kaga irin wannan murmushi ga mahaifiyarsu to akan Abbun sune kawai.

Tad'an hararesu tana fad'in  Takawa ba yana fada ba? .

 A'a yana turakarsa, Dan zamu shigo nan mukaga fitowarsa daga fada .

Nanma murmusawa Munaya tayi kawai, ta tashi zaune tana gyara zaman alk'yabbarta,  Kuje Sweetheart Na nemanku, amma Ku dawofa da wuri, kunsan yau ranace ta musamman da takawa ke zaman hira damu, karkuyi sakacin dazata wuceku, akwai sak'o a d'akina saman mirror Ku d'auka akai mata, zan kirata namata bayani .

A tare suka amsa da to Ummu.

Ta mik'e ta shiga bedroom d'inta, mintuna kusan biyar saigata ta fito tabi wata hanya da zata sadata da sashen Sarki Muhammad Sameer kai tsaye batare da kowa ya gantaba, wannan tsarinsane, Dan baya buk'atar wata jakadiya a tsakaninsa da matansa, yace suke rura munafunci a tsakanin matan Sarki.

Kallon juna Abdurraheem da Abdurrahman sukai, sukayi murmushi tareda tafawa, soyayyar iyayensu Na masifar kashesu, burinsu shine suyi koyi, tafawa sukayi sannan suka mik'e domin cika umarnin Na zuwa wajen gwaggonsu Munubiya, Dan ita kad'ai ummunsu take kira da Sweetheart.





Sarki Muhammad Sameer Na kishin gid'e a k'ayataccen falonsa dayaji kayan more rayuwa, lap-top yake sarrafawa hankalinsa kwance, sai tataccen ruwan tuffa dake ajiye a gefensa, k'amshin matarsa gimbiyarsa komansa da yajine ya sakashi d'ago k'yawawan idanunsa yana kallon k'ofa tareda amsa mata sallamarta yana zare medical eyeglasses d'in idonsa.

Tunda ta shigo ya dakata da danna lap-top d'in ya zuba mata ido kawai, cikeda tafiyar k'asaita ta isassun mata ta k'araso gareshi. Zata zauna gefe ya kamo hanunta yana tashi zaune sosai ta zauna saman cinyarsa, su duka ajiyar zuciya suka saki, ya sark'e idanunsu a waje d'aya yana mata murmushin da ita kad'ai take samun ganinsa a fuskarsa, cikin matso da fuskarsa gab da tata ya hura mata iska tafara farfar da idanu.

Lumshe idonsa yayi yana cijar lips, a hankali ya furta I love you my Queen, my Everything?  .

 i love you too my king . Munaya tafad'a a hankali itama cikeda salo.

Bashida za6in daya wuce had'e bakinsu, dukda girma ya kamasu harda manyan y'ay'a da zasu iya aurarwa soyayyarsu bata tsufaba, tun anayi a afalo harya d'auka abarsa suka shige bedroom.



Bayan wasu y'an lokuta suka fito wanka fuskarsa kowanne d'auke da murmushi, Munaya ta kalli mijinta cikeda so da k'auna.

 My king miya faru kabaro fada da wuri haka? .

Murmushi Yamata mai saka zuciya nutsuwa, ya zauna kusa da ita yana kwantota jikinsa, cikin magana rad'a yace,  kewarkice kawai, jinai bama Na fahimtar komai da ake a fadancin, sai gizo kikemin kawai, shiyyasa Na buk'aci shigowa Na huta, bagashi Na huta d'inba? . Yay maganar cikin d'age gira d'aya da kashe min ido d'aya .

Murmushi nasaki ina kuma shigewa jikinsa, nace  Anya kuwa a tarihin masarautar nan anta6a Sarki irinka? .

Murmushi Sarki Muhammad Sameer yayi yana d'ago fuskarta da sark'e idanunsa cikin nawa,  miyasa kika fad'i haka? .

Murmushi nima nayi ina shafa k'irjinsa,  Kaine Sarki Na farko dakan gana da iyalansa aduk lokacin da yaso, babu maganar jiran dare, kaine Sarki Na farko dakan ware wasu ranaku Dan zaman hira da dukkan iyalansa kawai amatsayi Na Uba ba sarkiba, lamarinka akwai k'ayatarwa yalla6ai .

Hararta yayi dajan hancina,  bazaki manta da sunannan ba ko? .

Dariya mai d'aukar hankali nayi ina fad'in,  kaida sunanka, yalla6ai Na yalla6iyarsa .

Shima dariyar yayi yana kuma rungumeni a jikinsa,  Wlhy kin zuba rashin ji sosai My mata, bak'aramar wahala nashaba lokacin auren Contract d'in nan, naga alamar tsiwarki Safah ta gado gaba d'aya, yarinyarnan batada tsoro ko kad'an, ga iya magana, tafi Marwah wayo sosai .

 Ai Marwah miskilanci da gatan da Hafsat ke musune ke d'awainiya da ita kawai, yarinyarnan miskilancinka ta gado itama, itada Abdurraheem da Saifudden da Khadeeja (d'iyar Hafsat) wlhy duk hallayarkace, rashin son hayaniya, miskilanci, k'asaita da basar da Abu tamkar bai damesuba, rashin iya r, ga salon cizar lips irin naka da Abdurraheem keyi shida auta jalaludden, nifa saidai naita kallonsu idan sunayi, Dan kai nake hangowa gaba d'aya a zamanin k'uruciya, musamman Abdurraheem  .

Sarki Muhammad Sameer yay murmushi da sumbatar goshina, a hankali yace,  my mata k'yan d'a......? .

Nace,  yagaji ubansa .

Yace  kin gama magana Sarauniyar sarakuna, time d'in barci yayi .

Bai barni nak'ara maganaba ya jani saman gadon tareda ja mana bargo mara nauyi.

Har barci ya kwashesa ni nakasa nawa, Na zuba masa idanu ina tuna abubuwa masu yawan gaske da suka faru a tsawon shekaru 25 da aurenmu, Galadimana Muhammad Sameer yanzu yazama Sarki Muhammad Sameer, mutum mai tarin k'asaita, mulki, k'yawawan halaye masu nagarta, hak'uri, kawaici, dattako, iya zama da mutane, tausayin Na k'asa da shi, k'yauta da k'ok'arin tsare gaskiya, wad'annan duk halayyarsace dake kuma k'aramin k'aunarsa da addu'ar y'ay'anmu koyi dashi, Na matsar da fuskata kad'an ina manna masa Sumba a la66a, yad'an bud'e ido yamin murmushi dakuma sanyani a jikinsa. Daga nan nima barcin yay awon gaba dani.



Sai bayan sallar la'asar sakaliya Na baro sashen Takawa, nafito sainaji sha'awar lek'a Hafsat, Dan duk yau bamuga junaba saboda tayi bak'i a yammacin jiya, tsakaninmu ma akwai k'ofar dake sadamu da juna batareda rakkiyar kuyangi ba, saidai abinda yasaka jikina sanyaya iske Hafsat a k'aramin falonta tareda bak'inta suna zugata akan zamanmu, ta mik'e tsaye karta yarda Na cigaba da mulkarta, kowa yasan nama fi sarkin mulki, Dan sai abinda nace yakeyi koda a fada, itako tazama tamkar wata sa d'akarsa.

Fushin daya tasominne yasani daka musu tsawa.

Bilyn Abdull da Hafsat suka rikice, ko kad'an basusan da zuwan Sarauniya Munaya falonba, hakama Maman kadee da Aysha DanSabo da Rano, party zarah, Ummu Basheer, khaleesat hydar, Ummi Ai'sha, Faxy fashion, Zee Bawa, zee Yabour, Ayusher Muh'd, Mamugee, Asmy b Aliyu, Silmzy, Feedohm, Bily galadanci, Safiyya Huguma, kdeey duksun rud'e, Dan dama sune bak'in Na Hafsat miss xoxo.

Hafsat ta mik'e tana nufar Sarauniya Munaya datayi fushi zata fita,  Please gimbiya ki saurareni, ko kad'an niban d'auki zugarsuba, dama jira nake su gama Na kora musu bayanin bakina .

Jin wannan magana sai Sarauniya Munaya ta tsaya cak, sannan ta juyo da baya tana danne fushinta da maye gurbinsa da murmushi.

Dawowa tayi ta zauna duk tana kallonmu, cikin sanyin murya tace,  kunason sanin yanda aikai nasamu dukkan fada da matsayi a zuciyar mijina Sarki Muhammad Sameer fiyeda kowacce mace bayan mahaifiyarsa? .

A tare suka amsa da eh.

Tai murmushi da zame hular alk'yabbarta tayi baya, sannan ta kuma gyara zama da nutsuwar maida dukkan hankalinta garemu tafara bamu labari tun daga kan harmutsi da halayyar gidansu zuwa yanzu damuke tare da ita a yanzun.

Wannan shine mak'asudin fitowar labarin RAINA KAMA ga sauran Fan's.

Gaba d'aya sai jikinmu yay sanyi, domin labarin ya girgizamu, Sarauniya Munaya ta cancanci fiyema da hakan ga Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar, babu abinda zamuce saidai binta da fatan alkairi, itama k'awarmu Hafsat miss xoxo mu bita da addu'ar samun k'auna ta musamman a zuciyar Sarki Muhammad Sameer, dukda itama Alhmdllh tana samun dukkan kulawa a garesa.

Mun bama Sarauniya Munaya hak'uri da Neman yafiyarta akan jahiltar abinda bamu saniba, lallai idan kaga mace Na mulkin gidanta karka zargeta, Dan bakowacce bace take zama Sarauniya a gidan miji bisaga bigiren kauce hanya, wata k'yawawan hallayartane suka siyamata wannan matsayin da girman da soyyar ga mijin da ahalinsa, domin ayau labarin Munaya ya tabbatar mana da haka, hardajin sha'awar kasantuwa masu koyi da k'yawawan halayyarta.

Mun yarda lallai Mahaifansu Munaya Inna da mama Rabi'a RAINA KAMA ne, Galadima, kuma a yanzu Sarki Muhammad Sameer shima RAINA KAMA ne, Munaya & Munubiya suma RAINA KAMA, Momma RAINA KAMA. Abie RAINA KAMA, kai jama'a dayawa a wannan labarin sun zama RAINA KAMA KAGA GAYYA!! =��=�M�<���

Atake a wajen tace ta yafe mana, takuma gayyacemu zuwa sashenta inda tasa aka had'a mana beta ta musamman=� �=� �, dazan Baku labarin garar arzik'i da abinda wad'anan guys d'in Na HASKE sukayi dakunsha dariya, saidai ina tsoron suburbud'a alk'ur'an>�#�>�#��&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&.





Abin kallo bai k'are manaba sai da daddare, bayan sallar isha'i kai tsaye sashen Sarauniya Munaya akayo masa rakkiya, Dan wannan rana tana cikin ranakun dayakan kasance da iyalansa ba a matsayin sarkiba, matsayin miji ga matansa, sannan uba ga y'ay'ansa.

Yanda ya zauna yana wasa da dariya dasu, kowa Na k'ok'arin fad'ar abinda ke bakinsa, yayinda matansa suka sakashi tsakkiya da yaran 12 cif, k'ananun duk suka a jikinsa kowa farincikin ganin Abbu Na tare dashi, sunci sunsha a tare, zuwa k'arfe 10 suka d'unguma sashen su Momma, acanma hirar ta gudana mai cikeda farin ciki ga wannan ahali, murmushi ya Gaza d'aukewa a fuskokinsu, kowanne yanajin tsantsar so da k'aunar junansu a cikin jininsa da ayukansa..........
'<���=��





Kamar yanda Nina k'aunarku da kewarku ta mamayeni a lokaci d'aya=�-�.





Tammat bi hamdullah.



Na godema Ubangijin al'arshi daya horemin dama da kwarin gwiwar kai wannan labari k'arshe dayay ta tafiyar hawainiya tamkar bazai k'areba=��, kuskuren danayi ALLAH ya yafemin, abinda Na fad'a dai-dai ALLAH ya taramu a ladan Baki d'aya, bakina bashida Kalmar furtawa agareku masoyana, kun nunamin d'unbin k'auna da soyayya akan wannan labari, ina rok'on ubangiji ya amfanar damu da alkairan dake cikinsa, kuskuren kuma mu watsar dashi gefe domin girman ALLAH, Dan kunsan d'an Adam azijine, Nina ina a layinsu ni bilyn Abdull, ALLAH kabamu ikon koyi da k'yak'yk'yawa, ya nisantamu daga mummuna, ALLAH yasa munada Rabin sake had'uwa a buk Na gaba.=�-�=�O�<���







ALLAH ka gafartama mahaifina, kakai rahma da Ni'ima kabarinsa, ka azurtashi da yalwatacciyar rahman tareda dukkan sauran y'an uwa musulmai da suka kwanta dama=�-�=�O�<���.







ina Neman afuwa ga dukkan Wanda Na 6atamawa a yayin rubuta wannan littafi da Sanina ko'a rashin sani, Nima Na yafema duk Wanda ya 6atamin, ALLAH ya yafe mana Baki d'aya.=�-�=�O�<���





Akwai kuskuren danayi a salon wannan labari, domin kusan Munaya ke bada labarin ga k'awayen miss xoxo, amma mantuwa kansani shiga ciki, hakan tafaru bisa d'an rikicewa bayan dawowata daga hutun azumi, ina fatan zakumin afuwa, kuma zakuga gyara anan gaba insha ALLAH, domin wani lokacin gazawama nasarace, saika Gaza kake d'aukar hanyar gyara, ALLAH ya ganar damu baki d'aya, Rufaida Umar ina godiya sosai, Dan kece kika farkar dani kafin kowa=�
�=��=��=�M�<���







Takuce sai



BILKEESA IBRAHEEM MUSA

(Bilyn Abdull=� �=�L�<���)









ALLAH ya sake had'amu da alkairinsa.=��=�O�<���







I love you wijiga-wujiga, mazga-mazga, manya-manya, irin trillions d'inan my sweet fans=��=��=��=��=��=��d'd'd'd'd'd'=��=�M�<���.





I miss you wlhy '<���=�-�





SANARWA



Yakamata y'an uwana musulmi mu farga wajen yawan binciken lafiyarmu akai-akai, Dan cutar ciwon HANTA ta yad'u a cikinmu sosai, gashi mafi yawanmu bamu saniba=�-�, sai taci k'arfinmu muke farga saboda bamuda yawan kulawa Na binciken lafiya sai ciwo ya kwantar damu, gashi anata d'aukar ciwo ta hanyoyi da dama, wlhy wani abokin mijina suna hirar yanda a yanzu idan anzo tantance matasan da aka d'auka aikin Uniforms mafi yawan matasanmu Na arewacinmu suna d'auke da ciwon basu saniba, Dan ALLAH ki lalla6i mijinki kuje a abincika lafiyarku data y'ay'anku domin sanin halin da kuke ciki, ALLAH ya cigaba da bamu lafiya yakuma tsaremu baki d'aya, ciwone mai had'arin gaske da ake kamuwa dashi harta hanyar toilet. Karmuyi sakaci domin ALLAH=�-�=�O�<���.

https://2gnblog.blogspot.com/



Ya RABBI ka gafartama kakanninmu da iyayenmu baki d'aya, yayyenmu, k'annanenmu, y'ay'anmu, k'awayenmu, mazajenmu damu kanmu=�-�=�O�<���


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login