Showing 132001 words to 135000 words out of 365757 words

Chapter 45 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1476

baka kai girman saida kainaba yaro .

 uyim! Haka kace ko? .  cewar Nuren yana kallon galadima .

 kaima kasan hakanne ai .

Mik'ewa Nuren yayi yashiga wani d'aki yana dariya, mintuna 4kacal saigashi tare da wani dattijo.

Galadima da yake kishingid'e yad'ago ido yana kallon Nuren da dattijon, amma baice komaiba yacigaba da latsa wayarsa hankali kwance.

Dattijo direban Alhaji balala ya zube k'asa yana kwasar gaisuwa ga Galadima.

Galadima shi mutumne mai mutunta Wanda ya girmesa, dan haka Yakuma d'ago kai yana kallon dattijon, fuskarsa ba'a d'aureba ba'a sakeba, cikin muryarnan tasa ta isar masu mulki da k'asaita yace  no baba zauna da k'yau, kabar durk'usamin banaso .

Dattijo yace,  ai girmanka ne ranka ya dad'e .

Murmushi kawai Galadima yayi, ya ajiye wayar hannunsa yatashi zaune sosai, ruwa ya d'auka ya zuba a cup sannan ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallon dattijo.

 bawan ALLAH minene sunanka? .

Jikin dattijo Na rawa yace  Barau ranka ya dad'e .

 humyim baba barau, koka sanni? .

 sosaima ranka ya dad'e, wanene zaice bai sankaba a wannan nahiyar .

Galadima ya wani lumshe idanu yana cije lips nashi, ya bud'e idanun akan Mal barau da duk yake a tsure, sosai kwarjinin Galadima da cikar haibarsa suka rikita dukkan tunaninsa da kwarin guywarsa.

Galadima ya katse masa tunani da fad'in,  Baba barau nasan akwai tambayoyi taf bakinka a gareni, saidai bazan baka amsar ko guda d'ayaba, zan baka dama da sharad'i, Na farko shine kanada damar fad'amin gaskiyar abinda kasani idan Na tambayeka, nikuma nabarka ka tafi salin alin, Na biyu inada sharad'in ka d'aukarmin alk'awarin komai zai fito abakinka ya zamto gaskiyar abinda Na tambayeka, idan kamin k'arya koka yaudareni kuma.... Humm .  yak'are maganar da cije lips nashi batare da ya k'arasaba .

Hakan yasaka jinin Malam barau rawa, yana karkarwa yace,  insha ALLAHU ranka ya dad'e zaka sameni yanda duk kake buk'ata .

Nuren yace,  good daka fahimci hakan .



Galadima bai sake cewa komaiba yacigaba da latsa wayarsa.



Nuren ya kalli Malam barau yace,  malam barau kasan wanene tsohon Sarki? .

 eh kwarai ranka ya dad'e Na sanshi, shine yake jinya a India yanzu haka aiko .

 shin minene alak'ar uban gidanka da tsohon Sarki? .

A rikice Malam barau yace  ranka ya dad'e miyasa zakamin wannan tambayar? Ku gafarceni, kuyi wata amma ba wannanan ba dan ALLAH .

Galadima ya d'ago idanu ya zubama Malam barau su, jiyay zuciyarsa tana Neman fara hasala, har zaiyi maganar sai kuma miya tuna yay shiru ya had'iyeta, maida kansa yayi yacigaba da latsa wayarsa.

Nuren ya bud'e k'aramar drowa dake jikin center table d'in falon, saiga bindiga 'Yar k'arama ta bayyana, Malam barau ya waro idanu waje yana kallon yanda Nuren ke d'ura Bullets a cikin bindigar.

Galadima duk yana kallon Nuren ta gefen ido amma baice masa uffanba, saida Nuren ya gama sannan ya tashi ya koma kujerar kusada Malam barau, cikin d'aure face yace,  nasan dai tsoron mutuwa ko rasa aiki zai hanaka bamu amsar tambayarmu, to tabbas in baka fad'anba zan fasa kwalwar kanka da wannan gun d'in, kuma ko k'arar fitar bullet d'inta baza'ajiba ballema asan an kasheka, akuma cikin falonnan zan binne gawarka wlhy!! .

Jikin Malam barau Na 6ari yarik'e wandonsa, dan har fitsari yafara fito masa kad'an, yace,  ranka ya dad'e mi kuke son sanine? .



Galadima dake latsa wayarsa hankali kwance, batareda ya d'agoba yace, 20 ga watan Yuli miya faru a masarautar gagara badau .

 ranka ya dad'e wlhy bansan komaiba, amma tabbas ogana yafito ransa a 6ace daga wajen meeting d'in dasukayi da Sarki shida abokansa. daga hakan bansan komaiba wlhy kaji Na rantse maka .

Idanu Galadima ya d'ago ya zubama Malam barau, yace,  malam Saminu kafadda!. koba shine ainahin sunanka ba? Na sanar da kai karkamin k'arya, dan tunkan nakawoka nan nasan komai daya shafeka, amma a tashin farko kamin k'aryar sunanka Malam barau, humm abin dariya, inason mutum mai gardama dason ku6tar da kai. Malam Saminu shiga tarkon Muhammad Sameer ba abune mai sauk'iba, ina aiki da kwakwalwa, kamar yanda gangar jiki take aiki da zuciya, karka yarda a maganarka ta gaba k'arya ta shigo, idan hakan ta kasance saina binneka da ranka, wannan tabbatacciyar maganar Muhammad Sameer Saifuddeen ce .  ya k'are maganar da mik'ewa tsaye yana had'a yatsunsa biyu ya buga a saitin fuskar Malam Saminu, suka bada sautin d'as! d'ass!, sannan ya ra6a ta gefensa yafice .



Nuren ya girgiza kansa,  dattijo kayi kuskure kwarai da gaske, Galadima ya wuce dukkan tunaninka, tashi mu koma inda ka fito, a yanzu kam bazai ta6a saurarenka ba sai kuma wani karon .

Hawaye Malam Saminu yafarayi yana bama Nuren hak'uri,  yalla6ai dan girman ALLAH ka kirashi, wlhy zan fad'a yanzu, wlhy nagaji da zaman kurkukunnan, nasan hankalin iyalaina da mai gidana a tashe take, ka taimakeni .

K'ala Nuren baice masaba, ya dannashi a d'akin ya maida ya kulle sannan yabi bayan Galadima.







&):(&):(&):(&)(&):(&):(&):(&):(&





Tunda suka tafi babu Wanda yay maganar, saida suka shigo cikin gari sosai.

Nuren yace,  dattijonnan nakula zaiyi taurin kai gaskiya .

Murmushi Galadima yayi yana kuma lafewa cikin seat, idonsa a lumshe batareda ya bud'eba yace,  mu wuce asibiti .

Amsawa da to kawai Nuren yayi.



Sun isa asibiti suka iske duk 'yan gidanmu suna nan, saisu Munubiya da Dady yace su tafi gidajensu hakanan, tundama ba bari ake aga Abban ba basuga amfanin zaman nasuba, gashi mafi yawansu duk da tsohon ciki, sai kuma Munubiya da Fauziyya da Haleematu dake fama da laulayi.

Haka ba dan sun soba kowacce takama hanyar gidanta, wadda mijinta kuma yace ta jirasa ta zauna jiransa.

Suma su innarmu Yaa Anas ya kwashesu ya maida gida.



Lokacin da su Galadima suka shigo asibitin mafi yawansu duk sun wuce, sai mazan kawaine a asibitin.

Dan haka Galadima yasamu gaisawa da Munubiya dake jiran yaa marwan yazo d'aukarta.

Munubiya ta tambayi 'Yar uwarta fa?, gaban Galadima yafad'i, danshi yama manta su Munaya suna hanya, guntun murmushi yayma Munubiya yace insha ALLAH suna hanya itama, maybe su iso cikin darene kokuma da asuba .

 ALLAH ya kawosu lafiya .  cewar Munubiya tana sharar hawaye .



Tabama Galadima tausayi sosai, haka ya k'arasa wajen doctor domin kumajin ko ansamu wani cigaba a jikin abban..

Doctor yamasa bayanin duk an gyara karayar jikin Abba, hakama sauran ciwukan suna samun kulawa, kuma bugun zuciyarsa ta daidaita bakamar jiya zuwa safiyar yauba.

Galadima ya jinjina kai, tareda sake jaddadama doctor gargad'in kulawa da Abba d'in sosai.

Yad'an jima a asibitin sannan su sarkin mota sukazo d'aukarsa, Nuren kuma daga nan hotel d'in daya sauka yanufa. ya sauka hotel ne saboda basa buk'atar wani a masarautar su Galadima yasan da Nuren d'in.



___________________________



Wajen misalin 2:30 na dare su Munaya suka sauka, Sauban yayta wayge-wayge ko an zo d'aukarsu, amma baiga alamun wani mai alak'a da masarautaba, ya kalli Munaya yana dariyar tsokana,  Aunty gimbiya Honey d'inki ya manta damu, bai aiko d'aukarmu ba, kuma inatsoron mu shiga motar haya azo a kwamushemu, kinsan yanzun kasuwancin kidnapping shine keda tsada a 9ja .

Duk da Munaya tana tare da damuwa hakan bai hanata yin dariyaba, tace,  kai yaa Sauban bakada dama, ina zamu samu waya mu kirashi to? .

Kafin Sauban yabata amsa sukaji magana a bayansu.

 to maganannu, saikuzo mu wuce, wannan surutun nakuma bayasa ayi kidnapping d'in naku ba .

Gaba d'ayansu juyowa sukai suna kallonsa, Galadima ne sanye cikin wando fari 3quarter da riga t-shirt pink mai gajeren hannu. harya kwanta suka fad'o masa a rai, babu shiri yazari mukullan mota yafito, bai tada kowaba a dogaransa saboda kasada irin tasa ya fito zuwa airport, isowarsa baifi da 17minutes ba jirginsu Munaya ya sauka, tunda suka fara fitowa daga jirgin idonsu a kansa, har tsayuwarsu da waige-waigen dasukeyi na son ganin Wanda yazo d'aukarsu yana kallonsu. shagala yay da kallon Munaya, wadda sai a yanzune yaga k'ibar da Samha ke fad'in tayi, ta murje tayi 6ul-6ul da ita, har wani haske yaga ta k'ara masa, saboda hasken daya haske ko'ina a cikin airport d'in. yadad'e tsaye a bayansu, duk gulmarsa da Sauban yayi akan kunnensa ne.



Sauban ya k'araso da sauri ya rungume d'an uwansa, dukda jiyane kawai suka rabu saiyaji yayi kewarsa.

Galadima yad'an daki bayansa yana fad'in  k'aton banza, ka girma bakasan ka girma ba .

d'agowa Sauban yayi daga jikin Galadima yana dariya, yayinda Munaya da Galadima suka had'a idanu, gira d'aya ya d'aga mata, itakuma tayi guntun murmushi tana kauda idonta gefe. (A ranta tace d'an duniya).

Juyawa yayi batare da yak'ara magana ba, Munaya da Sauban sukabi bayansa, Sauban ya shiga baya, badan Munaya tasoba tashiga gaba kusada Galadima da zaiyi driving nasu, wannan ne karon farko da zataga tuk'insa a k'asarsa.

Saida yatada motar suka fita daga airport d'in sannan a hankali kamar bataso tace,  yalla6ai mun sameku lafiya? .

Juyowa yayi kad'an ya kalleta ya maida kansa ga titi, saida yaja numfashi sannan yace,  kunzo lafiya my Friend? .

Kallonsa kawai tayi kad'an ta girgiza kai, a zuciyarta tace su Friend anji jiki, zanbika a hakan kodan samun yanda nakeso a kanka, danna cika alk'awarin danama mahaifiyarka insha ALLAH.

jin batace komaiba yakuma fad'in  ko gajiyar tafiyarce? .

 kusan haka yalla6ai .

Yace,  to sannu yalla6iya .

Ba Munaya ba har Sauban saida yayi dariya da wannan suna, daganan motar ta d'auki shiru, har suka Isa masarautar.



Muftahu dake binsu abaya ya sauke ajiyar zuciya, sannan shima ya shigo masarautar, tunda Galadima ya fito daga sashensa akan idonsane, Dan haka yay saurin bin bayansa da mota shima Dan yaga inda zaije. (Humm Muftahu=��).



Sosai Munaya kejin barci da farinciki, yau gata tadawo k'asarta ta haihuwa, sun shiga sashen komai need tagansa, sai k'amshi dake tashi kamar kullum.

d'akinta ta shige, Sauban da Galadima suka nufi nasa. Sauban ya zube a kujera yana kiran  wash! .

Galadima ya d'an hararesa,  amma idan yawonkane aibaka gajiya .

 yaya wlhy bazaka ganeba, nidai kawai bani wajen kwana na kwanta wlhy .

 Saidai ka kwana anan falo kuwa, kafin da safe a gyara sashenku ka koma can .

6ata fuska Sauban yayi,  haba Yaya da gatana na kwana saman kujera, kadai katafi d'akin Aunty gimbiya ka kwana gaskiya kabani gadonka .

Galadima zaiyi magana Sauban yatashi da gudu ya shige bedroom d'insa ya saka key.

Da sauri Galadima yace,  zan 6ata maka rai fa Sauban .

Ina, baima sauraresa ba, dafe kai Galadima yayi kawai, wlhy baisan lokacin da Sauban yafara rainashiba, kodan yaga tsawonsu kusan d'aya yanzu?. babu yanda ya iya dole yafita zuwa d'akin Munaya>�+�.................
'<���









Ho Sauban aikinka yay k'yau>�#�, su Galadima dole a tafi=��, ba ruwana karya jini>�-��&<���
@&



Readers kuma kuyi dariya a hankali fa>�+�=��.





Barkanku da juma'a=�K�<���.





Musha weekend lafiya sisters=��=�K�<����&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&.

















*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu=�-�>��<��� '<���_*

AWESOME WRITER'S ASSO..<���



(palace of excitation and pleasant writer's)



INA TARE DA ITA!

=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�

(bansan ita bace)

=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�=�>�



Story & written by mmn fareesa



Wannan page din nakune INA TARE DA ITA fans club gsky naji dadi sosai da comments dinku na jiya dan yafi na kowa=�;�=�;�



NOT EDITED



<��69&70



Kafin tayi mgn taga get man yabudewa yah Suleiman get ya cinno hancin motarsa ....wani irin bugawa kirjinta yyi sbd tunawa datayi da warning d'in da yah Suleiman yyi mata game da maganar Abbas din agabanshi...

Shikuwa Abbas kallon ta yake yanata zuba surutunsa har yalura tana duniyar tunani"fuskarsa ya matsa gab da tata yahura mata iskar bakinsa....adede nan Yah Suleiman dakeyin parking idanunsa suka hasko masa baby da wani gab da juna dan saiyaga kamar kissing d'in ta zaiyi..

Wani mugun burki yaja,yana huci yafito azafafe ko murfin motar be rufeba yanufi gunsu.

Wani irin zafi da k'una yakeji azuciyar sa afili yace gsky yarinyar nan ta rainani ,amma zanyi maganinta dg shi har ita,yafad'a idanunsa sunyi jajir zuciyarsa nace masa ko shine ABBAS?"

Azafafe yakoma mota yaciro bindigarsa yanufo gunsu...



Baby kuwa tunda ta ga yadoso gurunsu atsorace ta kalli Abbas daketa tambayar ta tunanin me take haka?"

Murya na rawa sbd tsoro tace pls yah Abbas kabar gidan nan yanxun ga yah Suleiman nan kuma wlh zai iya maka illa dan zafin zuciya ne da shi"

D'agowa Abbas yyi yahango jarimi ,sadauki ingarman namiji cikin kakinsa na sodoji. yanufosu sai kuma yaga yajuya gun motarsa.

Da sauri yace wanene shi ?"meye matsayinsa agunki? da kika tsorata dan yaganmu tare da ke matsayina na Wanda zaki aura.....maganar ta mak'alemasa ganin yah Suleiman din yasake nufosu da bindiga ahannunsa.

Salati baby tayi sai hawaye shar afuskarta ta San lallai yau me kwatar Abbas gunsa sai ALLAH .



Shikuwa yah Suleiman wani mugun kallo yake jifarsu da shi yana ganin duk Dan sbd Abbas din ko waye take zubda hawayenta sbd shi bata sonsa aidama be manceba tace bata sonsa Abbas take so.

Kamar yadda shima baya sonta IFTI ce aransa...tuni yasake zuciya bbu annuri a fuskarsa ya ida isa gunsu..

Abbas kuwa daurewa kawai yake amma hankalinsa inyyi dubu tashe yake sbd yalura bbu sassauci afuskar yah Suleiman din ."



Cikin tsawa had'e da karaji yace kai dan k'auye !dak'iki me yashigo dakai gidan mutane?"bbu izininsu.....da sauri baby ta katsesa da pls yaya kayi hkuri wlh na laifinsa bane laifinane amma yah Abbas be.....wani gigitaccen mari yawanko mata "saida taga stars namata shawagi tuni tadafe gurin tasaki k'ara.. Abbas yyi karfin halin cewa gsky wannan ba adalci bne dazaka kamata kadaketa sbd..wata wawar fincika yah Suleiman yyi masa had'e da makasa jikin bango atake bakinsa yafashe.

Cikin isa yah Suleiman yace yes na mareta sbd na isa ne kuma kaima yanxun zan Nuna maka isata ta hanyar yimaka hukunci da laifinka duk da nasan.bakasan wanene niba!

Tuni yasaita bindigarsa zai harbi Abbas ....da sauri baby dke tsaye dafe da kunci tana kuka tamatsa gaban Abbas cikin dakiya tace ah ah ni zaka kashe bashiba ,ta fad'a had'e da tare Abbas d'in kafin yah Suleiman yyi wani abu yaji Abba abdullahi na masa tsawa had'e da cewa kada kasake kayi Harbin nan....tuni yah Suleiman yyi wurgi da bindigar ya finciko baby da hannu daya ,hannudaya yakaiwa abbas wani wawan punch a fuska tuni hancinsa yafashe yyinda Abba ya iso afusace ya wanke yah Suleiman da mari had'e da cewa me yamaka ?"



Beyi mgn ba idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa duk sun mik'e rad'o rad'o, yanajin zafin hanasa da Abba yyi yama Abbas hukunci......sai botsare botsare take tanaso yacikata ta taimakawa Abbas ganin halin dayake kuma sbd ita"amma yarik'e ta gam.



"Abba ne daya lura yah Suleiman bazaiyi bayaniba sbd dokin zuciyar dayahau " yasa Yakama Abbas suka nufi get .

https://2gnblog.blogspot.com/

Shikuwa gogan ganin abinda baby keyi yasake bata masa rai azafafe yadauketa da bindigarsa yyi part d'in sa da ita tanata ihu da kiran sunan Abbas din.



Abba kuwa suna fita saiga motar yah Yusuf tuni yatsayar dashi suka shige hade da nufar asibiti.



Bayan duk anbasa treatment d'in da yadace aka samasa drip had'e da yimasa allurar bacci sannan Abba yakira abbu yace su had'u a asibitin.



Shikuwa yah Yusuf yanufo gd yana tambayar kansa wanene wancan saurayin ?"kuma waye yajimasa ciwo haka acikin gidan?"



"Xuciyarsa tace yah Suleiman ne"



Shiru yyi had'e da yin parking yafito yanufi part d'in su...zubaida dke kallonsa ta window tana Dakon zuwansa tun dazun ,jitake kamar ta bisa saidai zuciyarta nace mata hmmm kije kici dukaba....



**********



Abbu kuwa byn yaje asibitin nan Abba yyimasa bayanin iya abinda yasani game da abbas,ajiyar zuciya yyi yace hmmmm wannan Yaro ALLAH yarabasa da Wannan zafin zuciya tasa! Yanxun dabakazoba fazai iya kissan kai "oh ALLAH yakyauta ,amma yanxun mujira asallamesa muwuce gd naga Suleiman din yyimun bayani meye hujjarsa na zubarwa da wannan Yaro jini.



Abbu yyi ajiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login