Showing 345001 words to 348000 words out of 365757 words

Chapter 116 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1523

luuu sai gata a k'asa kawai ta sume.

Abie da Galadima dasu Munaya duk kanta sukai suna kiran sunanta, shima Abie ya tuzgud'e zai fad'i, Dr Ajay daya kawosu yay hanzari rik'esa yana fad'in  A sannu dai Sir, k'afafunka basukai k'warin wannan hanzarinba .



Da gudu Munaya takoma ciki sai gata da ruwa, ta zuba a hannu tana shafama Momma, da k'arfi takawo Numfashi.

Bin yaran nata tayi da kallo tana fad'in  mafarki nakeyi ko yarana? Nasan irin mafarkin dana sabane dama, ba takawa Na bane ba .

Cikin dariya da kuka Aunty Mimi tace,  Wlhy shine Momma, shine agabanki ba mafarki kikeba, Momma Abie d'inmune wlhy tallahi kinji Na rantse .

Zumbur Momma ta tashi daga jikin Aunty Mimi, Abie dake tsaye har yanzu bisa taimakon su Galadima ya murmusa yana fad'in  Zeenah ki cire kokwanto, da gaske wannan Saifudden d'inkine ba Wanda yasaba zuwa miki a mafarkiba kinji .

Tasowa Momma tayi garesa, ta shafa fuskarsa domin tabbatarwa, takuma binsa da kallo tundaga sama har k'asa, lallai da gaske wannan Saifudden d'intane bana mafarkiba, Ai sai kawai ta rungumeshi babu kunya ko tunawa dasu Galadima a wajen.

Sai duk'ar da Kansu duk sukai suna Murmushi.



Gaba d'ayansu kowanne soyake ya nuna ajintarsa ga Abie domin nuna masa gamsuwa da farincikin samun lafiyarsa, aka kawo masa y'an Uku ya had'a duka ya rungume yana maijin k'aunarsu har cikin jininsa, Khaleel ma yana nanik'e dashi.

Munaya dai nadaga gefe bata zak'eba.

Idon Abie ya sauka akanta, Murmushi yamata yana fad'in  'Diyata zo mana .

Takowa tai cikeda jin kunya tazo gabansa ta durk'usa, cikin girmamawa ta gaisheshi da masa addu'ar k'arin samun lafiya mai d'orewa.

Ya amsa yana mai k'ara jin farin cikin kadancewarta suruka agaresa uwa ga jikokinsa.

Galadima ma yakasa d'auke ido daga gareta, sai yaga tamasa y'ar rama tsakanin jiya da yau.

Breakfast d'in dabai samu shigaba d'azun aka baje domin ci, amma shi Abie kasancewar an hanashi cin wasu Abubuwan Kuku yay azamar tanada masa Wanda yake buk'ata.

Daka gansu kasan suna tareda matsanancin farin ciki .

Koda suka kammala Galadima ya taimakawa Abie shiga d'akin Momma, shima ya haye sama shida matarsa.

Tun'a falo ya d'auketa cak yana juyi da ita cikin hajijiya, babu shiri Munaya tahau k'yalk'yata dariya da k'an k'ame wuyansa da hannayensa tana cusa kanta cikin k'irjinsa.

A haka suka k'arasa cikin bedroom, ya jefa abarsa saman gado yabita tareda jan bargo yay musu runfa.





An hanani ganin abinda akeyi>�(�, sauk'inma inada mijin Nima=��=�D�.



Farin cikin da wannan ahali suka tsinci Kansu wlhy 6ata lokacine, Momma kam sai ko ganinta bama ayi>�-�=�H�.





��

A gurguke please>�z�=��.





Walwala da farin cikin wannan gida tadawo kam, ga nutsuwa mai saka zukata samun damar yawan ibada, ko yaushe suna manne da Abie, sai idan time d'in hutunsa ne yayi, Galadima yayma kowa gargad'i akan sanarda tashin Abie, burinsa kowa yaga abin mamaki, 100% Momma ta yarda da shawararsa, hakama Abie.

Yanzu dai kam sun yanke shawarar Isa k'asarsu ta haihuwa ranar salla k'arama, zasu azumi na kwanaki 20 a india, su biya Saudiyya suyi Umrah ta kwana goma su isa Nigeria a ranar salla ayi idi dasu.

Gaba d'aya azumi saura kwanaki 6 a farashi.







******



AZUMI



Alhmdllh kowanne musulmi yau ya tashi da azumin watan Ramadan mai mai albarka, saidai irin masu ak'idar saimun gani da suka kasance k'alilan acikin wasu k'asashe irin namu Na yankin Africa.

Duk da shayarwa hakan bai hana ni zama cikin jerin masuyiba, dan raino dai bani nakeba, tsakanina da yarannan idan sunji yunwa, koyaushe suna tare dasu Momma, sunyi 6ul-6ul dasu tamkar y'an watanni 6, amma har yanzu suna cikin wata Na hud'une ma kacal.

Tunda safe Galadima ya fice, Na d'an tashi nai gyaran saman sannan Na sakko, yau babu maganar shiga kitchen, Dan tunda Abie ya dawo nakoma nike mishi girkin abinda zaici, wataranma nakan had'a da namu muma, babu abinda zan cema wad'annan mutane sai godiya, soyayya dai mai cike da k'auna ina samunta a garesu, ni da mijina kam ai sai hamdala, yana tattalina da tarairayata, saidai d'an sa6ani Na yau da gobe Wanda baka Isa raba ma'autara da Shiba, shima kuwa bai wuce wasu awanni muke shiryawa ba, inko Momma ta lura ma takan kiramu tamana Nasiha, hakama Aunty Mimi.

A falo Na iske Abie daga can gefen falon inda wasu kujeru biyu suke da kanta mai d'aukeda buks Na karatu, tundaga kan Na addini har zuwa Na makaranta dadai sauransu, zaune yake yana nazarin wani littafi da banga sunansa ba saboda tazarar dake a tsakaninmu.

Sai Samha dake falon kwance a kujera tana kallon film, zaman gyalena Na gyara, Na taka a nutse zuwa garesa, saida Na durk'usa a gabansa sanann nace  Barka da safiya Abie .

'Dago k'yawawan idanunsa da Galadima ya gado yay yana kallona, ya zare medical eyeglasses d'in idonsa yana Murmushi,  'Diyata barka dai, kin tashi lafiya? .

Kaina a k'asa ina murnushi nace,  Lafiya lau Abie, ya ibada da k'arin k'arfin jiki? .

 Alhmdllh d'iyata, ai jiki kam sai godiyar Ubangiji, Muhammad fa? .

 Ya fita tunda safe . Na fad'a cikin kuma duk'ar dakai.

Murmushi Abie yayi, ya maida eyeglasses d'insa yana fad'in  ALLAH ya dawo dashi lafiya to .

A saman la66a Na amsa, sannan Na mik'e da k'yar zuwa d'akin Momma.

Abie ya bita kallo zuciyarsa cikeda k'aunar wannan yarinya, irinta yaytama y'ay'ansa addu'ar samu amatsayin abokiyar rayuwa, Alhmdlh Ubangiji ya amsa masa, saura Sauban kuma.



Nidai nashiga Na gaida Momma, Na iske tanama su Amaturrahman shiri, da alama wanka tamusu, Na gaisheta cikeda girmamawa kamar yanda Na saba, itama ta amsamin da kulawa tareda d'an jana da hira tamkar yanda ta saba, nad'an jima a d'akin, harta fito tabarni Na gyarashi tsaf kamar yanda nakeyi tun bayan dawowarmu, Dan tuni Na dakatar da Samha ni nakeyi.

Na fito da nufin shiga Na gaida aunty Mimi saina isketa tama fito falo, anan muka gaisa Na zauna muka d'ora da hira tamkar yanda muka saba, mafi yawama firar ta Sauban Ce, Dan kowa yayi missing d'insa, yace azumi da kwana 3 zai zo sai salla zai koma, Galadima bai hanashiba, dukda yana tareda tattalar kud'i a tsakaninnan saboda sun masa k'aranci, to saima papi ya d'auki nauyin zuwan Na Sauban da komawarsa.

Mund'an ja lokaci Muna hira barci yafara rinjayata, mik'ewa nayi Na gudu sama, nad'an rage kayan jikina Na haye gado sai barci.



Kusan 10am saiga Galadima ya dawo, bai iske kowa a falonba, da alama barci suke kokuma suna harkokin gabansu a ciki, kai tsaye d'akin su Momma ya nufa, yay knocking aka bashi izinin shiga.

Abie Na zaune saman abin salla ya idar da sallar walha, yayinda Momma ke zaune bakin gado tana bama Abdurraheem Magani saboda zazza6in dake jikinsa.

Galadima ya zauna a saman sofa yana gaidata da tambayar miya sami Abdurraheem d'in?.

Cikeda kulawa ta amsa masa tana gogema yaron inda maganin ya 6ata masa a wuya da fuska.

 Tunda muka tashi yau Na kula bayajin dad'i yaronnan, inagafa yakamata ka kaishi a bincikasa, basai mun zauna wata 6 ta cikaba, tunda kasan ciwon yana zama iri daban-daban, karmuyi tunanin ko irin nakane azo ba hakaba, Dan Na kula yafika yawan laulayi shikam, Abdurraheem baya had'a sati biyu da isashsshiyar lafiya .

Jin jina kai Galadima yayi, tausayin d'an nasa Na ratsashi, ya had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi da k'yar yana amsar Abdurraheem d'in daga hannunta.

Abie daya shafa addu'a ya maido hankali garesu.

Mik'ewa Galadima yay yakoma inda yake yana gaisheshi, Abie ya shafa kansa hakama Abdurraheem, cikeda tsokana yace,  Like Father like son .

Dariya Momma tayi, yayinda Galadima yay Murmushi mai k'ayatarwa har hak'oransa Na bayyana.

Yace,  Abie ai dakai suke kama duka, Amaturahman cema tad'an d'ebo mamansu kad'an .



[8/19, 6:14 PM] =�G�<���
@&Da Rarrafe=�G�<���
@&: Abie yay Murmushin jin dad'i, yana shafa kan Abdurraheem da yay barci, gaskiya Galadima ya fad'a, dan shima tun randa yafara ganinsu ya lura da haka.

Sund'an ta6a hira, har Galadima ke kawo maganar Aunty Mimi akan yakamata tayi aure hakanan, domin zaman bashida amfani haka, ko wani yamaka k'yak'yk'yawar fahimta wani bazai makaba, tunda ba wuce auren tayiba.

100% iyayensa sun gamsu da zancensa, sunkuma amsa masa da isha ALLAH zasu zama Na musamman da ita.

Kwantar da Abdurraheem yay musu sallama akan zaije yad'an rage barci.





Tunda ya shigo yay tozali da Munaya barbaje a gado, murmushi yad'anyi yana cire Bottoms d'in rigarsa harya k'araso cikin d'akin, hanging d'in rigar yay sannan ya zauna saman sofa yana cire takalmansa, mitsawar da Munaya tayi tana juya kwanciya yad'ago ya kalleta, aransa yace hajiyata ko an farajin azuminne?.

Harya gama hidimarsa yazo gefenta ya kwanta bata saniba, dayake ba motsi mai k'arfi yay tayiba, Dan yasan batada nauyin barci, gudun karta tashi yay tayin komai a sannu.





*****



Duk musulmin ALLAH Na k'warai daya wadatu da ibada inhar lokacin salla tayi ko barci yake saiyaji a jikinsa, kokuma yayta mafarkin ana sallar, hakance ta kasance ga Munaya da Galadima, kusan atare suka farka, kowanne bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci.

mamaki ya kamani ganinsa gefena, Dan bansan yama dawoba, ya min murmushi nima Na mayar masa da murtani ina shafa fuskarsa.

Cikin lumshe ido nace,  Yaushe ka dawo? .

Hannunsa ya d'ora saman nawa dake kan fuskarsa, yad'an rufe ido ya bud'e akaina, murya k'asa-k'asa yace,  Tun d'azun mana, kinata barci abinki .

Yatsine fuska nad'anyi ina zame hannuna da k'ok'arin tashi. Nace,  Wlhy barci bai wani isheniba shiyyasa nad'an rage yanzu kafin time d'in shiga kitchen .

Shima tashi yay zaune yana jinjinamin kai.

Shiya fara shiga wanka, saida ya fito sannan nima Na shiga nayo.

Koda ya fita salla ya dawo bai koma cikiba, sai suka zauna a harabar gidan shi da Abie suna hira, dayake kullum Galadima cikin bashi labarin abubuwan da suka dingi faruwa yay lokacin yana jiyya, wani yay murmushi, wani dariya, wani kuka, yana kuma yabama Galadima bisa ga gwarzan takar dayayi ta kare mutuncin ahalinsa da rik'e martabarsa.

Har time la'asar suna zaune a wajen, da taimakon Galadima Abie yataka zuwa massalaci, dan inhar yana gida haka sukeyi, bayan sun dawo awajen suka sake zama, Galadima ya kirani nabama Samha System d'insa takai masa.

Da to Na amsa, Na hau sama Na d'akko nabata.



K'arfe biyar dai-dai muka shiga kitchen ni da Samha da kuku, sai Hadiman gidan guda biyu dake taimaka mana da wasu ayyukan.

Cikin nutsuwa muka gabatar da dad'ad'an abincin bud'a baki, wasu namu Na Hausa wasu kuma Nan.

Gab da magrib muka gama, munbarsu k'arasa komai Na k'imtsa kitchen d'in da shirya abincin.

Wanka nakesonyi ga Amaturrahman Na kuka, Momma kuma tace babu inda zani saina shayar da ita.

Dole Na zauna ina dungure kanta. Oho batasan ma inayiba, itadai taji abinda take buk'ata a baki kawai. Ganin tad'ansha na d'auketa muka haye sama dan karma Momma tace saita k'ara.

Na iske Galadima yana wanka, ni bammasan ya shigo cikiba, Na kwantar da Amaturrahman Na kuma sauka, nasan dole yana d'akin za'a kira salla, dabino da ruwa Na d'oro a k'aramin tire nazo Na ajiye, ina ajewa kuwa yana fitowa.

Sannu da aiki yamin, Na amsa ina manna masa Sumba a hannunsa dana kama, nai saurin shigewa bathroom.

da kallo ya bita yana murmushi, ya kalla hannunsa data sumbata shima ya sumbaci wajen.

Fitowata wanka yay dai-dai da cikar lokacin kiran sallar magrib, a bakin gado Na iskesa zaune Amaturrahman Na kwance kusa dashi tana wuntsil-wutsil da k'afafu, idonta nakan hasken globe, shikuma yana kallonta yana murmushi da video d'inta awaya.

Batare danayi tunanin komaiba Na k'araso garesa da nufin bashi dabinon, amma saiya jawoni nafad'o jikinsa, dukda laimar ruwan dake jikina.

Babu wani k'arin bayani ya d'aura bakinsa saman la66ana, idanu Na waro masa Na tsorata da mamaki, amma saiya kashemin ido d'aya da cigaba da abinda yake.

Kusan mintuna biyu nasamu ku6ta. Ina yunk'urin tashi ya kuma hanani.

 O ALLAH, azumi fa kakai my King, shine kafara da jan magana mai makon Neman ruwa ko dabino? .

Wani miskilin murmushi yayi da huramin iska saman ido. Farfar Na fara da idanu.

Yakuma Murmusawa,  Bazaki ganeba babie na nayi missing d'inkine, kinga ai lada biyu, gatakai azumi gata d'abbak'a sunna, ni ai ga dabino Na nan, yawunki kuma shine ruwana . Ya k'are maganar yatsansa a la66ana.

Tura kaina nayi a jikinsa ina Murmushi.

Ya rungumeni da shafa bayana shima yana murmushin.



K'arshe dai sai a d'akin mukai sallar magrib sannan muka sauka k'asa shan ruwa.

Jinai gaba d'aya kewar y'an gidanmu tazomin a yau, Na tuna yanda muke had'uwa k'wanmu da kwarkwata a runfa shan ruwa, murmushi naita saki dajin kewarsu mai yawa da d'okin son ganinsu.

Aunty Mimi data lura dani tace,  My K'anwa yadai? .

Nakuma fad'ad'a fara'ata ina cewa  Na tuno gidane kawai Aunty .

Murmushi duk sukayi, Galadima dake gefena ya mintsini cinyata kad'an, d'agowa nai Na kallesa ina d'an 6ata fuska, gwalo yay min kad'an yana d'auke kai cikeda basarwa tamkar bashi yayiba.

Saida na tabbatar bamai kallonmu sannan nima na rama, aiko zafin yasakashi kad'an garage ya 6arar da kunun da yake sha, yay saurin rik'ewa.

Sannu muka shiga masa, na Fiske abina tamkar banyi komaiba.

Muna had'a ido ya cije lips da min gargad'i da ido akan zai kamanine.

Nima gwalo namasa.



Abinda basu saniba tun farkon fara lamarin Abie da Momma suna kallonsu, dan haka yanzu sai suka kalli juna suna murmushi.





A gurguje please�&<���
@&=��





&&&&&&&&&



Kwan uku da fara azumi Sauban ya iso India, bak'aramar birkicewa yay da ihun ganin Abie ya samu lafiyaba, hardasu kuka rurus, Abie ya rungume Autansa d'aya zama sangamemen Saurayi yana mai jin farin ciki da k'aunarsa. A ranar sai sabuwar murna ta tashi kuma, haka muka wuni cikin farinciki biyu, na zuwan Sauban da gimama farincikin daya riska.

Haka azumi yacigaba da gangarawa, kullum saina kira su Abbanmu da sauran jama'ar gidanmu namusu barka da shan ruwa, hakama y'an uwana sunta turomin sak'on massages kenan kulum namin barka da shan ruwa.



Azumi na kwana 15 muka kai Abdurraheem Asibiti, Yakuma samun binciken kwararrun Likitocin zuciya, suka dubashi da k'aramin dabaru wajen kula da rainonsa, sai magunguna da zai iya sha a matsayinsa na yaro k'arami.



Dukkan sayayya da Galadima zaiyi ya kammalata, harma ya tura mana kayanmu ta jirgin ruwa.

A kwanakin bashida wani sukuni, yawan shigi da fici na damk'a amanar harkokinsa kawai yake ga mutane, dan zai jima a 9ja bai dawoba a yanda ya hasaso, inma ya shigo India bazai dinga wuce sati biyu zuwa uku ba zai barta, shima saboda Company nasune, danma yanata k'ok'arin ganin sunzo sun kafa reshe a Nigeria dan shima yabada gunmawa ga k'asarsa.



Muma dake cikin gidan bawani zaman mukeba, munata kimtse-kimtsen kayan gidan waje d'ayane. Da sallama da mak'wafta da abokan arzik'i da akai sabo.

A wannan yanayinne na gane Ashe yayan Dhibya Gopal soyayya suke da Samha, wannan ne kusancin dake k'ara k'arfi tsakanin Dhinya da Samha, ban sanarma kowaba, haka itama ban mata maganaba, tunda gashi ALLAH ya kawo sanadin da zasu nisanci juna cikin sauk'i, babu yanda za'ayi aure ya iya yuwuwa a tsakaninsu, yaudarar juna kawai sukeyi, Su Dhibya y'an k'abilar Hindu ne,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login