Showing 177001 words to 180000 words out of 365757 words

Chapter 60 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1517

yunk'ura zan mik'e yace,  oh haushi kikaji? to sorry zauna kiga wani abu .

Komawa nayi Na zauna INA k'unk'uni.

Hotunane da yawa ya nunomin daga cikin Computer, ya danna hoton farko ya fito sosai. Batareda ya kalleni ba yace,

 wannan sunansa *Kabiru Ibrahim*, nasanshi shekaru kusan 9 da suka shige a dalilin neman bayanan sirrina tacikin Computer, nabashi dama yashiga sosai saboda a time d'in yaci k'arfina, inada yak'inin wanine yabashi wani yanki sirri daga abinda nake da shi, ganin ya zuk'i bayanai 90 a cikin 100, saina tura masa goman gaba d'aya, saida ya zamana 99 duk sun shige ga Computers d'insa sannan Na nuna masa banbancina da shi, Na lalata abinda yake da shi da Wanda ya samu agareni, tundaga wannan ranar kuma nafara bibiyar rayuwarsa. Abin mamaki saina gano yanada Ubangida, shine wannan, *Timothy yoha*, dukkan abinda ya aikata agareni Umarnin uban gidansane Timothy, Na maida akalar tunanina ga Timo, saina iske shima aiki yakema wani, ba kowa bane face tsohon shugaban k'asarmu *Labaran Ahmad kachia*. shine wannan, nasan kuma k'ila kisansa dukda dai lokacin dayayi shugabanci bana tunanin an haifeki ma gaskiya, ta silar *Former p... Labaran Ahmad Kachia* nasamu wani kundin bayanai akan tsantsar abotar dake tsakaninsu su a k'alla 15, babu maijin sirrinsu saboda Kansu a matuk'ar had'e yake, ALLAH yayima 4 daga cikinsu rasuwa shekarun baya kad'an, saisu 11 suka rage .

Ya kumayin wasu 'yan danne-danne nidai duk ina kallonsa da mamaki, hotunan mutane 15 suka bayyana, sai dai an lik'e fuskar mutum 4 alamun wad'anda suka mutu kenan.

Gaban frigate d'in d'akin yaje ya had'a Coffee a mug, sannan ya tako zuwa gareni ya mik'amin, kaina Na girgiza masa alamar a'a, ya d'aga kafad'a sannan ya juya zuwaga Computers d'insa.

 wannan mutane hud'un sune jiga-jigan wannan abota, d'aya ya rasu a cikinsu saura uku, *Josaya Bamma* shine mataimakin *Alhaji Lawan tanderu*, bayan mutuwar tanderu shugabancin wannan abota ya dawo hannunsa, dukkan wani shigi da fici na man fetur dake faruwa a Nigeria josaya Bamma yasanta, dan sune masu yinsa, yanda ake fita da mai a k'asar da yanda suka mallaki rijiyoyin mai ba bisa k'a ida ba, gwamnati kuma batada damar magana domin sune masu fad'a aji, sune tsoffin shugabanni da suka San dukkan sirrin k'asar, sai *Bana baba gana*, dukkan wasu magunguna dake shiga Nigeria saida saka hannunsu, akwai wad'anda batareda k'a idaba suke kaita shi da *Alhaji balala* da *William Solomon*, domin manyan likitocine masana sosai, *Hajia A'i Barnawa*, babbar d'iya ga tsohon soja *Garba mai dala sokoto*, tashiga wannan group d'in sanadin k'awarta *Victoria*, dukkan wani cin zarafi mata ko cin dunduniya suke saka ido, kullum suna ik'irarin sune masu Kare hak'in mata a zahiri, amma a bad'ini ba aikin da sukeba kenan, suna aikin gyara aljihunansu ne. wannan shine *Mansur Habibu Abu*, wannan kuma *Abdul-Naseer Nafi'u*, da *Miracle Asun*, wad'annan dukkansu manyan 'yan kasuwa ne, amma a bayyane, amma a 6oye su sukasan tsiyatakun dasuke shiryawa a k'ark'ashin k'asa *Sagir sulaiman Sulaiman* minister mai mulki a yanzu, sai wannan da wannan duk sun mutu banida matsala a yanzu tsakanina dasu, Munaya inason sanin alak'arsu da Mahaifina, wad'annan mutanen, domin sune mahaifina yay zama dasu ana gobe wannan ciwon zai sameshi, a daren ranar kuma Abie yashiga wajen mama Fulani domin gaisheta, jakadiya data masa rakkiya ta tabbatarmin da lallai yafito ransa a 6ace daga wajenta. Sannan a wannan ranar matarsa ta uku ce ta kawana a turakarsa, alhalin kuma kwannan matarsa ta biyuce, amma saboda kud'in data bama jakadiya da dad'in bakinta saita kaita turakar Abie a wannan daren, takuma sanarma matarsa ta biyu cewa takawa bashida lafiya yana fama da mura. kwana biyu kuma kafin faruwar dukkan wad'annan abubuwan Abie yayi zama Na musamman da Hakimansa saboda kama Wazirinsa da yayi Dacin amanar Masarauta wajen d'aukar sirrin cikinta ya bama wasu bak'in turawa da ba'asan dalilinsu na yin hakanba, a bincikena d'aya a cikin turawan ya Mutu, amma d'ayan yana nan da ransa. Abie ya kwanta jiyya da sati biyu aka kashe babban malaminsa, limamin masallacin sarki maikuma bama Abie shawara akan addini. dukkan wad'annan dana ambata miki sunayensu a kwai hotunansu anan d'akin, akwai abokin mahaifinki da kika fad'amin, shine Alhaji Mamman k'afur Wannan babban yaron Alhaji Lawan tanderu ne, dan wannan group sunema suka tsaya masa ya fito takarar shugaban k'asa, babbar matarsa k'anwar matar tanderu ce, wadda a gidan tanderun ta taso tun tana k'arama. Senetor halluru garba abokin Alhaji Mamman k'afur Ne sosai, akwai wani 6oyayyen sirrin dake tsakaninsu kuma, sai dai ban saniba ko Abbanki yasan wani Abu a ciki. Idan nace zan cigaba damiki bayanin sirrikan dake cikin d'akinnan kanki bazai iya d'auka ba Munaya, amma nabaki damar kimin kowace tambaya ni kuma zan baki amsarta batareda shamakiba .

Ajiyar zuciya Na sauke, Dan tabbasa kaina bazai iya d'aukar wannan bayanan nashiba inhar suka wuce zurfin haka, Na yink'ura zan mik'e, saiya matso ya taimaka min da kansa, zaman silifas d'ina Na gyara a k'afata, sannan Na taka ga wasu hotuna, hotona na nuna masa dana muftahu, yad'an murmusa yana ta6e baki, kafin ya ajiye cofin hannunsa ya hard'e hannayensa a k'irji,  Ba manufar wannan hoton ke d'inba, dan haka manta da wannan kawai, sai nan gaba watak'il zaki iya sanin wani abu .

Zanyi magana ya girgizamin kansa, alamar karnace komai.

Idona na janye daga garesa kawai, na maida kan hoton Muftahu tareda nunashi da yatsa.

Takowa yay har inda nake, ya kama hoton yana kallo tamkar yau ya fara saninsa,  Muftahu d'an uwa nane, kuma abokina, sai dai bakomai ne nake sakin jiki da Shiba, domin lokacin muna yara mutumne shi mai yawan k'arya, hakanne yasaka ko yaushe muke fad'a, babu abinda na tsana ga hallayar d'an Adam irin k'arya dacin amana, wannan halayyar tasa saita gaza barin zuciyata har girmanmu, kullum kallonsa nake bai canjaba, wannan yasakani fin yarda da harun fiye dashi, saikuma yake gwadamin wasu halaye na rashin gaskiya a lokuta da dama, ban k'ara tsinkewa da lamarinsa ba sai a time d'in da abinnan yafaru tsakanina da ke a birnin gayu, Muftahu shine Wanda yakawomin shawarar mizai hana na aureki ko ta wannan hanyar zansan wani Abu, da farko na d'ana masa tarkone, na yarda da auranki na shekara d'aya, yanda yacigaba da rawar jiki sai lamarinsa yacigaba da tsoratani, randa ya saka mana pill's a fresh milk daga ranar na yarda 100% shi maicin dunduniya tane, kuma akwai wani 6oyayyan al'amarin da yake son cimma buri, wannan yasakani kauda idanu a kansa, nabashi dukkan dama, dukda kullum Harun kan nusar dani illar hakan, amma na share komai tamkar bana gani, sai dai wannan zuwan danayi maganar da kika ta6amin a wani dare ya sakani cikin dogon nazari, daga time d'in kuma na saka idanuna akan Muftahu da Harun, zuwannan da nayi na k'arshe Nigeria, naga wani abin mamaki da ban al'ajabi. akwai wani d'aurin Aure da mai martaba yace mu wakilcesa ni da Hakeem (Wambai) amma sai Harun da Muftahu sukace zasumin rakiya, ba rakkiyarce ta sani Ankara a kansuba, yanayinsu ya nusar dani kowanne akwai manufarsa, ban kulaba mukaje muka halacci d'aurin auren, anatashi Hakeem yace shi zai wuce, Dan yanada wajen zuwa, banbi ta kansaba Dan bana d'aukar raini, karramawar da aka shirya yima mai martaba sai ta juye kaina, aka karramamu sosai, ni bammaci abincinba, sai Harun da Muftahu ne sukaci, suna tsaka da cin abincin sai aka kira Harun, bai d'aga wayar a gabanmu ba ya tashi ya fice, ko alama ban kawo komai a rainaba, muka cigaba da hira ni da Muftahu, abinda na lura da shi rabin hankalin Muftahu akan Harun yake, dan yanayinshi ya nuna, zuwa can sai shima ya mik'e ya fice, yacemin yana zuwa, fitarsa babu dad'ewa d'ayar wayar Harun tayi ring, ni mutumne dabai damu da shiga abinda babu ruwansa ba, amma a ranar saina tsinci kaina da duba wayar, bansan Number d'inba, amma nasan fuskar wadda take jikin hoton da Number ta bayyana, ba kowa bace face d'aya daga cikin matan Abie na .

 Matan Abie kuma? .

 kwarai kuwa, wannan shine abinda na gani, Wanda ya zaunamin a rai, koda Harun ya dawo yaga wayarsa kusa dani sainaga kamar baiji dad'iba, na bashi ina fad'in hajia ta kiraka, kinga kuwa yanda yanemi zubewa? humm saida Muftahu ya taimaka masa, dana tambayesa se cewa yayi wai tunkan mu taho dama kansa na ciwo, nasan ba haka baneba amma na sharesa. tunda muka taho na lura ana kallon kallo tsakanina Muftahu da Harun, kuma duk sanda hakan tafaru, Muftahu kanyi wani murmushi mai tattare da ma'anoni masu yawa, Wanda har yanzu nakasa fasarasu .



Huci na fidda daga bakina, na koma Inda na taso na kuma zama, shima saiya tako zuwa inda nake, ya durk'usa a gabana tare da d'ora hannayensa bisa Gwiwoyina, idanu na d'ago a hankali na sakasu cikin nashi, k'ok'arin janyewa na farayi, saboda wasu abubuwa danake hangowa cikin idanunsa. Amma saiya hanani wannan damar, yay wani sassanyan murmushi yana fad'in.............>�+�
'<���









Barkanmu da dawowa sister's=��>��<���>�p�>�p�>�p�.

















*_ALLAH k'a gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���_*

*_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���1� 6�





................. Kin shirya taimakon Mijinkine Munaya? .

A salon da yay maganar saida tsigar jikina ta tashi, nad'an lumshe idanu sannan na bud'e a kansa, muryata na rawa nace,  ni bansan komaiba. kuma ina ganin a wajen Abie yakamata ka k'ara samun haske ai, tunda yanzu yana magana .

Murmushin takaici yayi, sannan ya kamo hannuna cikin nashi,  Kinsan miyasa nabaki dukkan wannan labarin daba kowanne mahaluki ya sansu baki d'aya ba? .

Kaina na girgiza masa a sanyaye.

Ya murmusa, tareda d'ora hannunsa saman cikina, hannun nasa na kalla, shima idonsa na a wajen, yace,  saboda kece wadda zata zama uwar d'ana ko 'yata, ina fatan koda nabar duniya ban cimma burina ba kibama duk abinda kika haifa labarinnan domin ya ida cimma manufata, wannan wasiyyace ga abinda zaki haifamin, dan inaji a jikina komi zaki haifamin insha ALLAH ba zai zama ragoba, sannan kuma tabbas kin cancanta, domin kece mutum ta farko dana ta6a yarda bazataci amanata ba bayan Mahaifiyata da kakannina da yayata da k'anina. daga k'arshe ina rok'onki girman ALLAH ki sanarmin da abinda kika Sani game dani, dan tabbas nasan kinsan wani Abu, nasha auna fik'irarki a ma'auni kuma ina samunta dai-dai, dan haka batun 6oyemin ma kibarsa zuwa yanzu, kinga Abba jibine zasu koma, to lallai rayukansu tana cikin had'ari kuma komai zai iya faruwa, saboda a yanzu mak'iyansa sunyi shirin dayafi na farko ma, a zatonsu Abbanki yasanar dani komai ne. ni kuma ban ta6a wannan maganar dashiba, sannan Abie da kike magana likitoci sunyi gargad'in kar'a tuna masa da abinda ya wuce yanzun, saboda gudun dawo da hannun agogo baya, kuma kodama na tambayesa zai iya dakatar dani yace ya yafe, ni kuma nariga nataso da BURIN 'DAUKAR FANSA, a cikin zuciyata da kwanjina, Ni nasan Yaya nayi jiyana, yau d'ina ma a wahale take kasantuwa, dan haka nakeson gyara gobena da goben 'ya'yana da dukkan ahalina, inason sanin dalilinsu nama mahaifina hakan, inba hakaba bazan ta6a samun kwanciyar hankaliba .

Nad'an muskuta domin gyara zamana, ina fad'in  shikenan, amma kabani lokacin please .

 Nabaki . yafad'a yana mik'ewa tsaye.

Binsa kawai nayi da kallo, saiya kuma bani tausayi, dukda kasantuwar rayuwarsa cikin Rud'ani, hakan bai habashi zama kamilin mutum mai tarin Nutsuwa ba, gashi da sauk'in kai, saidai idan baka fahimceshi baneba, kamar yanda na kasa fahimtarsa a farko, saika masa kallon mai girman kai.



A gaba d'aya yinin wannan ranar cikin nazarin maganganun galadima na yisu, tabbas abotar Alhaji Mamman kurfe da Senator Halluru da Abbana abin dubawace, na shiga tunano wasu abubuwa danaita karo dasu a d'akin Abbana ni da Munubiya, a wani time d'in da Innarmu ta sakamu masa wani gyaran d'aki, Wanda shine sanadin shigowarmu wannan cakwakiyar kuma, na dafe kaina saboda saramin d'in da yakeyi, motsin da d'an cikina yayine ya sakani dafe cikin ina lumshe idanu, gaba d'aya kaina yana Neman kullewa, har a washe garin ranar haka naita fama da tunani, danma yana hanani, amma danaga ya matsa zan d'ora daga inda na tsaya, yanzu ma dazai fita aiki saida yamin gargad'i, yace na sauka k'asa wajensu innarmu nayi hira, to kawai nace masa, amma yana fita ban fasaba, ganin lokaci na k'ara k'urewa saina d'auki waya na shiga rubuta massage mai tsawo dazan turama Munubiya.



Duk abinda takeyi a idon Galadima ne, tun d'azun yana lura da dukkan motsita ta camera d'in daya ajiye a d'akin wadda koda wasa Munaya batasan da zamanta ba, ya murmusa tareda godema ALLAH, dan yasamu damar kamata a hannu, ta wannan hanyarce kawai zaiyi amfani da ita wajen samun abinda yake buk'ata ga Abbanta, dan Abba yak'i bashi kowacce k'ofa dazai san wani abinda ya sakashi shiga wannan halin, alhalin yaga tarin damuwoyi a idanunsa, masu kuma matuk'ar muhimmanci a aikinsa.

Wayarsa tai 'Yar k'ara alamar Munaya na sarrafa wayarta, saurin saita abinda ya saka mata a wayarta bata saniba yayi, harta gama typing ta tura sak'on akan idonsa, shiga yayi ya duba, saiyaga Munubiya ta turama sak'on, yay hanzarin bud'ewa. (Galadima ya had'a wani tarko a wayar Munaya batareda ta saniba, dukkan wani Abu dazai shiga wayarta ko fita saiya gansa a wayarsa, ta wannan hanyarne yaga na yanzu, saimu bishi muga abinda Munayar ta rubuta to).



_  Yar uwata, tabbas Allurafa na shirin to no galma, anzo ga6ar da lallai yakamata mu sanarma Galadima komai akan abinda muka Sani, danna fahimci lallai zatonmu yazama gaskiya, wannan sunedai ahalinnan da mukaga bayanai a Kansu, dukda nakula Abbanmu nasan basarwa, saidai bansan manufarsa tayin hakanba, bayan wannan itace damarsa ta k'arshe dazai yadda kwallon mangwaro ya huta da k'uda, sweetheart minene shawararki? dan burina dana haife cikinnan auren contract ya k'are a tsakaninmu, domin babu alak'a kuma kenan, kinga nima na samu 'yancin kaina, nayin auren din din din kamar kowacce mace ._



Babu shiri Galadima ya mik'e tsaye, jikinsa har wani tsuma yakeyi, lallai anzo ga6ar Ashe, hasashensa yazama gaskiya kenan kokuma zai zama, tomi wad'annan yaran suka sani? kenan Munaya Nada dalilinta na yarda da auren su na Contract? Mi Muftahu ya Sani gameda Munaya dahar ya d'anata a gareshi a matsayin tarko?, bayan shi yana nan yana ik'irarin yima Muftahu tarko da auren Munayar. Lallai kan yakula itama Munaya da 'Yar uwarta da Muftahu suna Neman zame masa RAINA KAMA.



Baifi mintuna 15 ba da tura sak'on da Munaya tayi, saiga Munubiya ta kirata, duk Galadima yana kallo daga camera d'insa da kuma saitin wayarsa, dukda kuwa yana office ne, Munaya bata d'aga kiranba, saida ya katse sannan ita ta kirata, munubiya na d'agawa Munaya race,  Sweetheart kinga sak'ona kuwa? .

 Na gansa sweetheart, amma fa ni duk kin rikitani, kinga wata alamace data tabbatar miki ahalin Galadima ne? .

 Munu, tabbas alamomi da yawa sun nunamin hakan, sannanfa shima yasan Alhaji Mamman k'afur fa, kuma kinga ai a takardarnan munga sunan Alhaji Mamman k'fur d'in, gashi abokin Abbanmu sosai, nifa yau wlhy abubuwa masu yawa ya fad'amin game da sirrinsa, dukda kasancewarsa mutum mara yarda, duk dai da inaji a raina kamar ya fad'amin wani yankin sirrinsane danya bigi cikina be, amma ni wlhy tausayi guy d'innan yake bani da gaske .

Munubiya tayi murmushi daga can, cikin tsokana tace,  to ALLAH yabar k'auna dai, sweetheart .

 ban ganeba, k'aunar mi zai bari? .

 keda Galadima mana, ai soyayya kan fara da tausayine .

 Mtsoow dan ALLAH muyi magana mai amfani Munu, yanzu ya kika gani, danya rok'eni ALLAH akan nafad'a masa mina Sani, nikuma ina tsoron koba akansa d'in baneba Abbanmu yake cikin damuwar, karmuzo kuma muyi aikin Baban giwa .

Ajiyar zuciya Munubiya ta sauke, ta gyara kwanciyarta tana fad'in Munaya kodai mu sanar da innarmu ne kozata bamu shawara? .

 kai amma bakida hankali yasin, sokike innarmu taci k'aniyarmu Ashe, zatace miyasa tun a farkon lamarin bamu sanar mataba, k'ilama tayi fushi, Dan nima wlhy ayanzu ina ganin munyi wauta fa .

 to komadai miye munrigada mun aikata. Yanzu mafita zamu nema, mizai hana ki rok'eshi inhar bashi bane kokin fad'a Dan girman ALLAH karya tada zancen kawai, yakuma rik'e mana sirrinmu, idan kuma zai taimakemune akan Wanda kema Abbanmu barazana da mutuwa ai kingani munsamu madafa muma, kinga dai yanda sukaso cin galaba wajen kashesa, wlhy Munaya jinake kamar kar Abbanmu su dawo k'asarnan .

 Ni kaina tsoron dawowar tasa nakeji, musamman da jiya Yakuma maimaitamin, shiyyasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login