Showing 291001 words to 294000 words out of 365757 words

Chapter 98 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1477

ya kashe yaron Alhaji Bana, shin wannan halin mutanen kwaraine? Wannan hanyar dayabi fa bazata ta6a 6ullewa da shiba sai 6ata masa suna damu kanmu, daga fitowar maganarnan zuwa yanzu nasamu kira babu adadi .

Mai martaba yace,  kayi hak'uri Abba. Insha ALLAH zan shirya naje wajen zuwa anjima kad'an .

 Shikenan. Idan naga nima abin yayi tsamari zan taho .

Sallama sukayi kowa yana jimami akan lamarin.



Tunda labari yakaima mama Fulani tashiga tafa hannu tana sallallami da fad'in  A lallai zai iya zai aika, yo wannan yaron mai ido a tsakar goshi, fitinanne zai 6atama masarautarmu suna akan wani banzan talakan surukinsa, akuwa yanda ya kashe d'an mutane shima kasheshi za'ayi, idan munan ya rainamu yanzu kam ya d'ebo ruwan dafa kansa, fand'ararre kawai gagararre .

Haka taita k'ananan magana da jifan Galadima da munana.



Oho shi baimasan tanayiba9&=��.





********



A asibiti likitoci sun Shiga bama Abba taimakon gaggawa, Dan ba'asan minene ya sumar da shiba, tunda babu wani alamar duka ko harbi ko makamancin wannan a jikinsa..





******



Suma police sun buk'aci Galadima ya basu gawar Ahmad.

Murmushi yay yana kallon Ahmad d'in dake zaune yana shan ruwa saboda tsoratar dayayi sosai ta harbin da Galadima yayi, har yanzu yakasa sakin jikinsa, salla ma da sukayi a d'arare yayita, yazata da gaske shid'in aka harba, saida Galadima yayma Saleem nunin abashi ruwa, Saleem yakawo ma Ahmad ruwa, a lokacinne ya farga da Ashe yanada rai bai mutuba>�#�=��.

Ya kar6i ruwa kuwa jiki Na rawa ya shiga kwankwad'a idonsa akan Galadima dake masa murmushi, yana bama su IG amsa da fad'in  karku damu yalla6ai. Inada freight d'in dazan dunga saka gawarsu anan, bayan aiki ya kammala saisu d'auki y'ay'ansu sumusu sutura, idan kuma sunyi abinda nakeso kaga magana ta k'are, gawar Ahmad kawai ce a k'asa dai yanzun, sai idan ank'imin yanda nakesone za'a samu fiye da hakan dai .

C.P ya jinjina kai yana gyara tsayuwa, idonsa nakan ginin, yace,  to miye buk'atarka ta gaba yanzu?, tunda gashi an maka ta farko ai .

 Eh tabbas anmin, dukda dai ankawoshi ba'yanda Na soba .

 amma ranka ya dad'e suma ai ankashe musu yaro d'aya .

Gira Galadima ya shafa da d'an yatsa yana ta6e baki,  ito dakuma wannan Dan wannan fa, yanzu dai inaga buk'atata tagaba shine ku kama mutanen nan guda 11 dazan lissafo .

 Muna saurarenka, dawa-dawa? .

Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, cikin Nisawa ya gyara zamansa yana d'aukar takardar dake gabansa ya shiga lissafosu.  Alhaji Balala, Alhaji Bana baba gana, Alhaji Abdul-Naseer Nafi'u, William Solomon, Hajiya A'i Barnawa, Alhaji Sageer Sulaima Sulaiman, madam Victoria, Mansur Habibu Abu, Josaya bamma, Alhaji Mamman k'afur, Alhaji Halliru garba .



Kallon kallo aka tsayayi tsakanin IG da sauran police, sai C.P ne yasamu k'arfin halin cewa  amma to Ranka ya dad'e akan wane dalili? Kasan dai bazai yuwu muje kama mutane babu dalilin komai damuka saniba .

Wani muskilin murmushi Galadima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujera yana lumshe ido da cije lips,  Dalilin ai a fili yake yalla6ai namu, bisa dalilin Samun Alhaji Auwal Fharuk a hannunsu mana, dan yakamata asan dalilin samunshi a hannunsu, miya musu? Mi suke nema a wajensa? Baniba nasan dukan jama'ar garima abinda sukeson ji kenan, kunsan dai bazan ajiye ayukan gabana da jiyyar mahaifina nazo Nigeria Na zauna Ina kama yaran mutane saboda rashin aikinyiba ai, aimin kokuma nakuma aika yaronsu biyu barzahu yanzunnan!! . Galadima ya k'are maganar cikin tsawa da matsanancin fushi.

Tsawarsa saida ta kad'a hanjin yaran, hatta da Harun dasu Muftahu saida suka rumtse ido, suma haka police d'in dake sauraren Galadima.

IG ya mik'e daga zaunen dayake yashiga safa da marwa Na mamakin wannan lamari, sukan ai ansakasu a tsaka mai wuya, cikin tsakkiyar fad'an manya. C.P ya kira suka koma gefe suna tattaunawa.





............................&



A can kuwa hankalin su Alhaji Sageer ya kuma k'ololuwar tashi, Alhaji Mamman yace,  lallai yaronnan anyi tsinanne, dama wannan ranar Na ringa gudu tun boss nada rai (tanderu yake nufi), amma wasunmu sukace yaron bai Isa mana komaiba, gashinan rana tsaka yana Neman zame mana RAINA KAMA....

 Yama zama ai, Dan gayya kawai muka fara gani yanzun .  Hajia A'i ta fad'a a tsorace .

Duk sun kasa zama waje d'aya, Miracle yace,  yanzu nan da mutuncinmu za'ace wai y'an sanda su kamamu a k'asarnan?, lallai yaronnan yataro March wlhy .

 Kokuma mune muka taro March d'inba . Alhaji Bana dayake cikin kukan mutuwar d'ansa yafad'a yana share hawayen.





...............................&





IG sun yanke shwarar bin umarnin Galadima kawai, kodan tseratar da yaran, yad'anyi magana da manyan dake kusa dashi dukda shine Oga kwata-kwata, kowadai yabada goyon bayan a kamasun kawai.

Dan haka IG da kansa yay kiransu, Yakuma basu dama a girmamame akan sukai Kansu kawai station d'in dake kusa dasu, kodan rayukan yaransu, daga baya za'asan abunyi insha ALLAH .

Galadima dake saurarensu a zuciyarsa yace, abinyi kuma ai saidai a prison.



Duk sunk'i amincewa, wasunsuma sai bak'ak'en magana suke fad'a.



waya Galadima ya jawo yana daddannawa, sannan yayma Marcel nuni yazo, Dan yaji babansa yafi kowa zak'ewa, jikin Marcel sai 6ari yakeyi, ahaka ya rarrafo gaban Galadima.

Galadima yace,  'Dauka wayarka anan .

Jikin Marcel na rawa ya d'auka.

 Kira daddynka .

Dandanan yay kiransa, bugu d'aya kuwa ya d'auka shima jiki yana 6ari, duk suma sukayi tsitt suna jiran mizaice.

Galadima ya d'orama Marcel binduga a tsakkiyar kai, ya juya idanunsa alamar yay magana.

Marcel ya sanya kuka saboda tsoro. Rikicewa daddynsa yayi yana tambayar mi aka masa? Badai yay musu komaiba ba ko?.....

Katseshi Galadima yayi da fad'in  Zandai yimasa, Dan kaima yanzu d'anka zai wuce Inda Na Alhaji Bana yatafi .

 kai kai dakata please ka dakata, nidai Na yarda zan mik'a wuya, karka ta6amin yaro kaji Na rok'eka .

Cire bindigar Galadima yay yana maida kunamar da fad'in  shawara mai k'yau, lallai kanason d'ankan nan, ka tambayi abokanka, Wanda bazai mik'a wuyanba saiya fad'a yanzun nan .

 karka ta6a mana yara please, duk zamu mik'a wuya .

Galadima ya tuntsire da dariyar da wanima zai iya rantsewa bai ta6a ganin yayiba, yace, OK, good dattijan k'asa, saina jiku acan .





>�#�>�#�ana shagali a Nigeria yau kam>�8�<���
@&>�8�<���
@&>�8�<���
@&>�8�<���
@& amma Nigeria novel ba tamuba=��.





Su Alhaji balala dai kam sun mik'a wuya, da Kansu suka kai Kansu police station mafi kusa, daga can suma d'aukesu zuwa inda IG yace.

Galadima yay hamdala ga ubangiji dukda bawai komai yagama kammaluwa bane, amma lallai an d'akko hanya.

Ya bada Umarnin tashi suyi sallar La'asar, kafin a dawo a cigaba da gashi=��.





....................................&



Bayan sun idar da salla C.P ya kira Galadima, suka shaida masa su Alhaji Bana suna hannunsu yanzu haka.

Galadima dake tsaye yace,  Alhmdllh, zuwa safiyar gobe kuma sai a kai case d'inmu Court, Dan inason komai yafarune cikin gaggawa ya k'are, bana son jan jiki a aiki .

C.P ya kalli IG Dan jiran amsa.

Kai IG ya jinjina masa alamar za'ayi hakan.

C.P ya shaidama Galadima amsar IG.

Galadima yace, shikenan, shi yatashi daga aiki, saikuma safiyar gobe.

C.P zaiyi magana I.G ya dakatar dashi alamar ya barsa kawai.



Ta6e baki Galadima yayi yana yanke wayar, ya maida kallonsa gasu Muftahu da duk suna maidashi television, gira d'aya ya d'age musu, sukuma sukai masa jinjina=�M�<���.

Kauda idonsa yayi ya maida ga yaran, yace,  yaya akwai mai buk'atar wanka ko barci? .

Gaba d'aya suka amsa da duk suna buk'ata.



Kallon Ameer da Saleem yayi yabada Umarni da ido.





..............................&



'D'aya bayan d'aya suka dinga kaisu suna wanka, duk Wanda yagama sai abashi lemo, batare daya San miye acikiba saiya shanye, daga sha ko mintuna 3 basa k'arawa suke 6ingirewa barci>�#�.



>�#�>�#�ho Galadiman mu kasan takan tsiya, Zuma kenan, ga zak'i ga harbi>�8�<���
@&, kaga Na Munaya baban triplets, bada kanka a sare kaje gida kacema su mama Fulani an k'illesa=�L�<���=��=��.





Da akazo kan Harun k'in tankawa yayi, Dan haka Galadima yace su barshi kawai, amma harsu Malam Saminu da Alhaji Darma su Farhat duk sunma Kansu gyad'ar dogo sunje sun mik'e zasu huta.



Nuren ya kalli Galadima cike da tausayi yace,  Brother kaima kad'anje ka huta mana .

Murmushin gefen baki Galadima yayi, yajawo lap-top gabansa yana girgizama Nuren kai alamar a'a.................
'<���



















ALLAH ka gafartama Iyayenmu=�-�=�O�<���







BOOK 3 =�I�<���1� 7�





...................Abin surutu lallai ya samu, mak'iyan Galadima kuwa duk sun kasance a tsorace, Dan ba kowane ya fahimci inda shirinsa ya dosaba, hakama a cikin masoyan nasa, wasu suna ganin daidainsa wasu kuskurensa, kowa da irin fahimtar dai da yayma lamarin.



Yauma dai haka suka kwana zagaye da police.

Amma su IG duk sun tafi, d.p.o ne kawai tare da tawagarsa, kamar kuma yanda ya buk'ata sunakan tattara case d'in zuwa Court.



6angaren su Baffi kuwa lauyan Abie dukkan shirye-shiryen shiga Court suma suna akanyi. Dan dukkan shirin Galadima yasan dashi tsaf, hakan yasa koda yagani baiyi mamakiba, kisan Ahmad daine da akace yayi yabashi mamaki, dukda zuciyarsa bata aminta Galadima zai iya kashe yaro ko d'ayaba. Amma lallai hakan ya sakashi a rud'ani, harma ya kira sir Isa sukayi maganar. Sir Isa yace shima yagani a labarai amma gaskiya bai yardaba, akwai dai abinda duk basu saniba, Dan Galadima bazai aikata hakanba.

Da wannan maganar ne Baffi yad'an samu Nutsuwa yacigaba da tattara bayannsa daduk abinda zasu kafa hujja dashi a court.



Duk abinda ke faruwa Momma tasan komai. Dan Galadima ya sanar mata, baya kuma 6oye mata dukkan shirinsa akan wannan case d'in dama, amma sai tayi lup tamkar batasan anaiba, koda labari yazo musu saita taya su Aunty Mimi rud'ewar itama, harda pretending d'in kukanta tana Neman number Galadima, amma sai tak'i wucewa.

Daga Baffi har mai martaba babu Wanda ya kirata akan batun, duk a nufinsu Na 6oyemata kar hankalinta ya tashi balle Na mahaifinsa dake kwance yana fama da kansa.

Amma saiga kira daga mama Fulani, tafad'ama Momma maganar daduk yazo bakinta ta 6atanci akan Galadima, itadai momma cikanki batace da itaba, har tayi ta gama ta yanke wayar.

Saiga gimbiya Zulfah ma ta kira Momma, itakam ai harda kukan makirci irinna y'an duniya. Itama dai tayi kid'anta tayi rawarta Momma Na saurarenta.

Koda ta Yanke wayar saita kira munaya. Taita kwantar mata da hankali da lallashinta akan ta kwantar da hankalinta. Insha ALLAH komai zaizo k'arshe, kowace rayuwa takan tafine da jarabawa. Babu wani rai dazai rayu cikin farinciki da samun yanda yakeso 100%, dolene kowacce rayuwa akwai NATA k'alubale, nakowa kuma akwai ta hanyar dayake fuskantar nashi.

Sosai Munaya ta gamsu da nasihar momma hakannema yad'an samu mata nutsuwa tad'an rintsa a wannan dare.





.................................&



WASHE GARI



Nasara ta farko da aka wayi GARI da ita shine farfad'owar Abba cikin hankalinsa, saidai har lokacin baya sanin Wanda yake a tare dashi, hakanne yasaka likitocin fad'in a k'ara masa lokaci yasamu isashen hutu.

Ahalinsa sunsamu Kansu a farinciki ainun, hakama masoyansa, shikansa Galadima Yakuma samun kwarin gwiwa da karsashi akan aikinsa.



An kuma shigar da case d'in Court kamar yanda Galadima ya buk'ata, abinka da lamarin manya har antsaida washe gari a matsayin ranar da za'a zauna Court d'in.



Yinin ranar zubur Galadima baiyi magana da police ko d'ayaba, koda sun buk'aci magana dashi saiya had'asu da Muftahu ko Nuren. Daga k'arshe dai dolensu suna k'yaleshi.





&&&&&&&&



�&RANAR SHIGA COURT�&



Yau ta kasance ranar zaman court, shari'ar su Galadima Ce kuma farko da za'a fara saurara a court d'in, lallai wannan shari'a ta manyace, Dan court d'in ta cika da manyan k'asa wad'anda sunfi kud'i wahalar gani, amma yau gasu available, y'an jaridar ma manya-manya aka bari, k'ananun suna awaje sunyi tururuwa domin rajin nemawa d'an uwansu hak'insa wato Alhaji Auwal fharuk dayake a asibiti har yanzu cikin halin ni y'asu.

Mukuwa talakawan gari y'an jiran jin yazata kaya mu sai dai gani a tv9&.



Yo Wayaba asibi laya ubanta ba malam ba=�,�, ai ko babama da babansa aradu>��.



Court d'in tayi tsit babu abinda kakeji sai gudun fankoki da tarin manya jefi-jefi, dan babu alamun fara'a a fuskar kowa.

Daga masarauta dai k'anin mai martaba ne yazo wato Garkuwa Hayatudden Abubakar, sai wasu daga tawagar y'an majalissar Sarki, harda waziri dayazo bisa tirsasawar mai martaba.

Daga masarautar su Papi kuwa yarima mai jiran gado mahaifin su Nuren wato Wambai Abubakar Abdul-fatah Wanda yagaji sunan kakansu Galadima marigayi Abubakar kenan. Saikuma wasu daga jiga-jigan masarautar suma.



Fitowar alk'alin alk'alai Othman Ibraheem gwannu tasaka dukkan jama'ar Court d'in mik'ewa domin girmamawa a garesa, (dan shima Alk'ali baba uban su babane shima>�-�=��).

Saida ya zauna sannan yabada izinin kowa ya zauna, Court d'in tayi tsit kowa ya Zubama alk'ali dake karanta takardar k'arar hankali kwance ido, kusan mintuna 3 ya d'ago yanabin Court d'in da jama'ar cikinta da kallo ta cikin eyeglasses nashi daya jawo k'asan ido, d'auke idonsa ya ya maida ga Lauyoyi dake zaune suna jiran kule, suce cas.

Gyaran murya yayi yana maida idonsa ga takardar da fad'in  Ina wad'anda suke k'arar da kuma wad'anda akai k'ara? Idan kuma Lauyoyine to na masu k'ara da wad'anda ake k'ara suna inane? .

A tare Baffi suka mik'e shida abokan aikinsa su uku, cikin girmamawa ga alk'ali ya risinar dakai yana mik'a gaisuwa da fad'in  yamai girma mai shari'a sunana Barrister Usman Audu Tsanyawa, nine lauya mai kare Wanda yake k'ara, tare dani akwai Yohan Emanuel, da Bilkisa Ibraheem Musa (kutu melesi su bilyn Abdul anzama lauyoyin novel>�8�<���
@&=��>�#�=��).

Bilkisu da yohan suka risina alamar girmamawa.

Alk'ali ya jinjina kai alamar gamsuwa, su Baffi suka zaune, lauyan wad'anda ake k'ara shima ya mik'e, ya rissina tamkar yanda Baffi yayi, sannan yace,  ya mai girma mai shari'a sunana Barrister Adam Sadiq Adam, nine lauya mai kare wad'anda ake k'ara, tare dani akwai Barrister Aliyu Sa'adu yaro .

Barrister Aliyu ma ya mik'a gaisuwa ga alk'ali sannan suka zauna.

Alk'ali yabama Baffi damar tashi domin yin magana.



ALLAH Sarki dattijon kwarai kenan, masu wahalar samu cikin k'asa a halin yanzu, ya gyara hularsu ta lauyeyi dake Kansa, tare da farin eyeglasses d'insa dan rayuwa taja, ijiya duk sun raunana, ya kalli jama'ar cikin Court d'in sannan ya dawo da kallonsa ga alk'ali, yace,  yamai girma mai shari'a! Kamar yanda kowa yasani Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar (Galadima) shine yake Neman son sanin miya saka wad'annan mutanen 11 yin gamayya wajen kama surukinsa harsu wahal dashi? Bayan kuma shikeda alak'a dasu bawai surukinsa ba? .

Kai Alk'ali ya jinjina, cikin sauke numfashi yace,  Lauyan wanda ake k'ara gareka .

Barrister Adam Sadiq Adam ya mik'e shima yana fitowa fili, yayinda Baffi Yakoma ma zauninsa ya zauna, Brr Adam Sadiq Adam yace,  yamai girma mai shari'a wace irin tambayace ke fitowa daga bakin lauyan mai k'ara? Ai sune yakamata ayima tambayar minene dalilin shi Galadima Na kama yaran wad'annan mutane 11 yayi Garkuwa dasu yau tsawon kwana biyu? harma da kisan wani a cikin su.........


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login