Showing 81001 words to 84000 words out of 365757 words

Chapter 28 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1514

suka take musu baya.

Daga mama Rabi'a har innarmu babu wanda ya dakatar dasu.

Aiko sai innaro ta saka kuka wai su Ayusher sun zageta agaban innarmu batace komaiba.

Duk abinda ke faruwa 'yan gidanmu na tsaye cirko-cirko suna dariya.

Yaa Hameed daya shigo gidanne yazo har inda innaro ke tsaye a k'ofar fallon innarmu yana tambayarta lafiya?.

Cikin kuka da shar6e majina ta kora masa bayani, Kansa kawai ya girgiza, danshi lamarin innaro baya burgesa. Da lallashinsa tahak'ura tafita yarakata har gidanta da ledar da mama Rabi'a ta zuba mata kayan bikin.

Acanma zage-zage taitayi tana aibanta innarmu, kunya dukta ishi gwaggo Safiyya ga sauran 'yan biki suna saurarenta, gwaggo Safiyya fitowa tayi ta baro gidan, gidanmu tashigo tazo tana bama innarmu hak'uri.

Murmushi innarmu tayi, tace,  wlhy babu komai gwaggonsu, ai inna nima mahaifiya tace, mizaisa dantamin Abu yazama ya 6atamin rai, ai ta Isa danine shiyyasa .

Innarmu ta bama gwaggo Safiyya tausayi, tana k'ara jinjina hak'urin innarmu a ranta, tabbas da acikin sauran matan gidanne da innaro ta magantu, dan ba raga mata zasuyiba, danma suna Shankar mazajen gidan su Abbanmu.





&&&&**" �" �" �" **&&&&





Su Munubiya amaryar yaa marwan, =�J�baiwar ALLAH taban tausayi, dan kallo d'aya namata nasan yaa Marwan ya ajiye muskilamci ya kashe arna=��.

Duk takuma zama wata silent, tana kwance a falonta dayayi k'yau da tsari, hannunta dafe da kanta, idonta arufe tamkar nai barci, tunanin innarsu da kewar 'Yar uwarta ya gallabeta, gashi tun shekaran jiya yaa Marwan ya kar6e phone nata ya kashe, tayi rok'on duniya yabata takira Munaya da innarsu amma k'ememe ya hana, yadai kira mata innar sun gaisa jiya da daddare, amma munaya yace ba yanzun ba. hawayene suka ziraro ta gefen idonta.

Tun d'azun yashigo yake kanta tsaye bata saniba, tsigunnawa yayi saitin fuskarta yafara share mata hawayen, da sauri ta bud'e idonta, ganinsa yasata tashi zaune tana k'ak'aro murmushi damasa sannu da zuwa.

Bai amsaba, sai zama dayayi kusada ita yajawota jikinsa ya rungume,  haba my baby yanzu kukannan bazai k'areba? ko har yanzu wajen yana ciwonne nasake had'a miki ruwan zafin ki shiga? .

Kanta ta girgiza masa tana kuma matso hawaye, murya na rawa tace  ina kewar Munaya .

Tausayi ta bashi, tareda mamakin tsantsar k'aunar da sukema juna itada 'Yar uwar tagwaicinta, shikuma wlhy bayason kiran Munayar ne saboda karsu shiga hak'in Galadima, amma yanzu kam bashida mafita, yakai dubansa ga agogon falon, 11:49am, maybe zuwa yanzu sun tashi, wayarsa ya d'auka ya lalubo number Munaya yafara kira. cikin sa'a kuwa sai gata tashiga.

Mik'ama Munubiya yayi, cike da d'oki ta kar6a tana murmushi tana hawaye, shi saima abin yaso bashi dariya.



Ina cikin barci naji ringin d'in wayata, da k'yar na lalubota batareda na dubaba nayi picking kawai, a kunne na kara cikin muryar barci nayi sallama.

Daga can Munubiya ta amsa mani.

Ai zumbur namik'e zaune danjin muryar gudan jinina,  Sweetheart kece? Wlhy I Miss u so much  .  nafad'a ina share hawayen dasuka ziraromin .

Itama Munubiya hawayen takeyi, muryarta na zuga tace  miss u 2 sweetheart, I love you I love you for ever . sai kawai ta rushe da kuka tareda fad'awa jikin yaa Marwan dake kallonta tana rera kukanta.

Hannu yasaka yana bubbuga bayanta yana murmushi, yayinda nima naketa maimaita mata kalmar I love you ina kuka.

Wayar yaa marwan ya kar6a, muryarsa kawai naji yana fad'in  to kukan ya Isa haka kema, kar Galadima yagani ya d'auka munyi miki wani abune, sai anjima idan kin nutsu masake kiranki .

d'if ya yanke, batareda yajira amsa taba.

Sai kawai nakuma ruahewa da kuka na fad'a saman filoluwan da suke zube a saman gadon.



Galadima dake tsaye bakin k'ofar yazo dubani saboda dangin mom da zasuzo mana sallama, saiya koma da baya bai bari na gansaba, zuciyarsa tana masa tunanin dawa nake waya? har nake jera masa kalaman I love u?.

Ya d'an ta6e bakinsa, tareda kauda tunanin a zuciyarsa, to shi inama ruwansa, kwana nawane zai bani takardata na kama gabana.

Falonsa yakoma ya zauna yana jan tsakin Aiken mama Fulani na d'azun data tuna.

Yakuma jan tsakin yana gyara zamansa, dolene ya takama tsohuwarnan birki da wuri, inba hakaba tana neman Shiga masa hanci.



Abinda yafaru d'azunne da safe kusan around 7:30, yadawo daga masallaci bayan yaje ya tadani yadawo d'akinsa, zaune yake a doguwar kujera a falonsa yana azkar kamar yanda yasaba a kowacce Safiya ta duniya. sarkin k'ofane yamasa knocking.

 waye? yayi tambayar batareda ya bud'e idanunsa dasuke a rufe ba.

Sarkin k'ofar ya amsa da  nine ranka ya dad'e, dama Amintacciyar kuyangar Fulani Ce ke Neman iso .

Saida yaja guntun tsuka sannan yace tashigo.

Babu dad'ewa saigata kuwa, saida tayi sallama a k'ofar yabata izinin Shiga sannan ta shigo, risinawa tayi (dan ya hanata durk'usa masa saboda ta manyanta sosai) tana fad'in  barka da Safiya ranka ya dad'e .

Idonsa yabud'e a kanta yace  kin tashi lafiya .

 lafiya lau ranka ya dad'e, dama Fulani ce tace azo a d'auki yankin jiya .

Bai fahimceta ba, dan haka yace  miyene hakan? .

 ka gafarceni ranka ya dad'e, yankin farin k'yallen mutuntaka da aka shinfid'a a gadonka jiya .

Bakinsa ya ta6e, ya maida kansa ya jingina tareda maida idonsa yanda suke, kusan minti 1 harma ta fidda ran zai amsa, saitaji yace  kije kawai, zan kawo mata da kaina .

Idanu tad'an zaro waje saboda mamakin zancensa, amma babu yanda ta iya, kowa a masarautar yasan murd'ad'd'en hali irinna Galadima, saidai akwaishi da kirki da yawan k'yauta. ta risinar da kai,  na barka lafiya ranka ya dad'e, afito lafiya .

Uffan baice mataba harta fice tarufo k'ofar.



Azkar d'insa yacigaba dayi batareda ya maida hankaliba.

Mom ce takirasa a waya, bayan ya gaidata cikin mutunci ta sanar masa gasunan zuwa sashensa suyi sallama, dan jirgin 1pm zasubi ya maidasu tasu masarauta.



Wannan dalilinne yasakashi zuwa Sanar min, amma saiya Tatar ina Waya da fad'in I love you ina kuka kuma, shine yajuya batareda yayi maganaba.



Kamar na sani natashi na gyara gadon fes, nad'anyi shara dukda babu wani datti, toilet nashige nayo wanka.

Ina tsaka da shiri najiwo sallamar da wata murya ketayi tun d'azun, a gurguje na shirya naje na bud'e k'ofar.

Yarane matasa a durk'ushe can gefe a falona, sai wad'anda suka d'an girme musu su biyu.

Ina fitowa suka zube suna gaidani, abinda baka saba ganiba to, duk sai kunya ta kamani, nace  please Ku tashi minene ya faru? .

 d'aya acikinsu tace  gimbiya ranki ya dad'e, ki gafarcemu mune masu miki hidima. ni sunana Alawiyya nice mai gyara miki makwancinki kawai da shiryaki, sukuma wad'annan zasu cigaba da sauran hidimominki, irinsu gyaran falo, girki, wanki, baki labari, da sauransu .

Babbar jaka uba, shirinma sai anmin kamar wata 'Yar baby, nidai naga idi gaskiya, wannan wace iriyar rayuwacw haka?.

 ranki ya dad'a zamu iya fara aikinmu? . Alawuyya takuma maimaitawa a aladabce.

Kafin nabata amsa muka jiyo gyaran murya a abayanmu. dandanan naga sun juya suna kwasar gaisuwa, jikinsu har 6ari yakeyi.

Hannu kawai ya d'aga musu, kafin yabud'e baki da k'yar yace,  miya faru ne? .

Alawuyya takuma rissinar dakai tace,  ranka ya dad'e mune masuma gimbiya hidima .

Shiru tamkar bazai amsaba, yad'an yamutsa fusaka yana gyara tsayuwa  wanene ya turoku? .

 ranka ya dad'e mama fulani ne .

Baice komaiba ya ra6a ta gefena zai wuce ciki, harya kusa shiga sannan yace,  zaku iya tafiya zan nemeku .

Atare suke fad'in godiya muke ranka yadad'e, ALLAH ya kiyayeka, yatsare bayanka da gabanka.

To tunima yariga yashige, nikam tausayi suke bani wannan abun dasukeyi, nace  please kutashi kuje kawai .

 to ranki ya dad'e, godiya mukeyi........

Nidai juyawa nayi nashiga d'akin nima, dan banason wannan kirarin wlhy.................
'<���















*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=�O�<���=�-�

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*



_____________________________



_Wannan page d'in na sadaukar dashi agareki Hafsat writer d'in *HAFEEZ* na gode sosai, ALLAH yabar zuminci, Bilyn Abdull na yinki irin sosai d'inan dear>�p�>�p�>��<���d'._



______________________________



=�I�<���2� 3�





..............A saman sofa na iskeshi zaune, ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana waya. Idanu ya d'ago yad'an kalleni ya janye.

kunyace takamani saboda babu ko gyale ajikina, gashi kayan sket da rigane, kamar munafuka haka nawuce inda akwatina yake da aka kawo da safe, nima farkawa nayi kawai na gansa a d'akin.

Gyale na d'auka na yafa, sannan naje bakin gadon na zauna ina sauraren wayar dayakeyi, abinda na fara lura da halayensa shine, shi mutumne marason hayaniya, komai nasa zaka sameshi a nutse yakeyi, yanzu haka a d'aki d'aya muke zaune, amma ba komai nakeji ba a maganar dayakeyi, ga jan aji tamkar wani mace, jinin mulki dake yawo a jikinsa ne ke k'ara masa k'asaita da izza.......

Gyaran muryar da yayce yasakani d'agowa na kalleshi, idonsa a kaina, Dan haka muka had'a idanu, kowa janye nasa yayi cikeda basarwa.

Saina samu kaina da cemasa  ina kwana .

Saida yaja wasu seconds sannan yace,  kin tashi lafiya? .

 Alhmdllh kawai nace masa nayi shiru.

Shiru mukayi babu Wanda yasake magana, yanata aikin latsa wayarsa, nikam ina satar kallonsa da mamakin wannan halayya tashi, shi koma takura bayayi? ina dad'i dan ALLAH kai kenan kullum baki 6am>��.

Kusan mintuna 5 muna a haka, bakajin komai a d'akin sai k'arar AC, ni dukma sanyin ya isheni. batareda ya d'agoba yace  mikike buk'ata akawo miki break fast? .

ALLAH shi k'yauta, nafad'a a raina kafin nace,  ko miyema .

Idanunsa ya d'ago yana kallona, baice komaiba ya janye ya mada ga wayar. sai kuma yasaka a kunne,  mom ki basu su kawo abincin ta tashi .

Bansan mitace masaba daga can, naga dai yayi murmushin gefen baki tareda yanke wayar.

Ya kalleni yana gyara zamansa, tareda kuma shan mur alamun maganar da zaiyi important ce,  ki kimtsa su mom zasu iya shigowa a kowanne time, dan zuwa anjima zasu tafi, duk yanda dai zaki nuna musu wani Abu yashiga tsakanina dake kiyi, dan banason su tafi dawani zargi a ransu OK? .

Duk da na fahimci inda zancensa ya dosa, hakan bai hanani yimasa kallo mamakiba, nace,  kamar ya ban ganeba fa ni .

Shima kallon mamakin yamin, kamar zaiyi magana saiya fasa kuma, yad'an furzo huci a bakinsa kafin ya cije lips nashi da d'an k'arfi. tsaye yamike yana zuba wayoyinsa cikin aljihun ash d'in wandonsa, sannan yafara tafiya, sai da yakusan fita sannan yace,  ki nuna musu tamkar wata mu'amullar aure tashiga tsakaninmu, wannan shine kawai mafita, idan kin gama kizo kiyi breakfast . ficewarsa ya ida yi.

Yayinda nikuma na sauke ajiyar zuciya, danni maganganun nasa duk sunzomin a cirkud'e, to mom d'in nasa ba'a gidan takeba kome? Sannan kuma ai mu yakamata muje mu gaisheta bawai ita tazoba aganina, mi hakan ke nufi?. banida mai bani amsata, dan haka namik'e a gadon ina sauke numfashi, inason kiran Munubiya amma ina tsoron yaa marwan. wayar innarmu nakira, amma a kashe, idona yacika da k'walla, murya na rawa nace  wayyo innarmu I miss u wlhy .

jinake tamkar nayi tsintsuwa naganni a gida, dama ashe akwai randa zatazo na kwana Na tashi ba'a gidanmu tareda munubiya taba? gaskiya masu cewa aure da dad'i basuda kai wlhy, dan ALLAH ina wani dad'i anan?.

Da Sauri Na goge hawayena saboda jin maganar Samha a kaina, jikinta a sanyaye ta zauna kusada ni, nima saina yunk'ura natashi zaune ina murmushi da share sauran hawayen fuskata.

 Samha yaushe kika shigo .

Kanta ta langa6e gefe cikin damuwa tace,  Aunty yanzu na shigo, miya sakaki kuka? ko Uncle Sam.... ne? .

Murmushi namata, danni dariya wannan shagwa6ar tata ke bani, ko kad'an bata d'aukar kanta ta girma,  A'a Samha, ba shi baneba, ina kika shigene haka? .

 ina nan, tun d'azun naso zuwa Amma mummy ta hanani, yanzu ma tare muke dasu mom, suna falo kisaka Al'k'yabba muje .

Kallon jikina nayi, nace  bara dai na saka hijjab, ALLAH Alk'yabba d'inan nauyi takemin .

Dariya Samha tayi,  lallai aunty ai Indai kina gidannan dole saikin sakata, sai dai indan kun taho india, yanzu mafa dole ki saka .

Badan nasoba na d'akko Samha ta tayani sakawa, sannan muka fita bayan nafesa turarrurruka na masu dad'in k'amshi.

A zatona suna falona, ashe suna nashi, Samha na rik'e da hannuna tamkar wata 'yar jagora har sashensa, Wanda sai yanzune nake d'an kallon wasu abubuwan, dukda face d'ina arufe take da hular alk'yabba. Sallama mukayi a k'ofar falon akabamu izinin shiga, gabana na dukan tara-tara muka shiga, duk zatona irin sunada yawa d'innanne, saina gansu su 5 kawai, kuma duk manyane, mom kawai na gane acikinsu, sauran ban sansuba, saikuma shi boss d'in yana zaune a kujerar mai zaman mutum d'aya kamar ma yana wayane. ban zauna akujera ba sai a k'asa, mom tayi saurin fad'in  a'a d'iyata tashi ki zauna saman kujera mana . kaina na girgiza muryata a raunane nace  a'a nanma ya isa sannan a ladabce na gaishesu. cikeda fara'a da sha'awa suka amsa, shi kansa uban gayyar saida ya kalleni, yaji dad'in girmamawar dana bama k'annen mahaifiyarsa.

Samha ta gwargwad'ama mom magana a kunne, wai ta iskeni ina kuka. murmushi kawai mom tayi, tasan kukan bai wuce na shiga kwaryar manyaba, ga d'an nasu dagani jarumine (aikam mom ragone tunda ba abinda kike tunanin bane=��>�'�).

Kallon Galadima tayi dake harar Samha,  gulmammiya mikike fad'a? tashi kibar falon nan .

Tashi tayi tana tunzura baki,  wlhy Uncle Sam ni Vance wani abuba, Mom dan ALLAH wani Abu nace? .

Murmushi mom tayi, tace  a'a bakice komaiba .

Batareda ya kalleta ba yace,  naji, tunda kin rakosu wuce ki tafi .

Fita tayi tana daddaga k'afafu, yaja guntun tsuka, yayinda su mom suke mata dariya da tsokana irinta kakanni, nidai kaina na k'asa nima ina murmushin rigimar 'ya da Uba, duk dama har yanzu bansan yasukeba, naji dai tana Uncle kawai.



Bayan fitar Samha d'aya acikin matan ta kalleni, d'iyarmu cire hular kisha iska kinji, mu nan duk iyayenki ne, daina jin kunyarmu.

Babu yanda na iya, dole na zame hular Alk'yabba d'in, amma kaina na duk'e sosai yanda bazasuga fuskataba, nasiha mai ratsa jiki da 6argo suka Shiga mana daga ni har harshi, duk jikinmu sai yayi sanyi k'alau, nikam kukama nakeyi, Dan dama kad'an nake jira a ta6ani na fashe. sun dad'e sosai sannan suka ajiye min k'yaututtuka suka tafi harda shi domin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login