Showing 138001 words to 141000 words out of 365757 words

Chapter 47 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1482

 ALLAH ya huci zuciyarka ba haka nake nufiba, bayan barina wajenka jiya nima aka sanarmin, lokacin dana shigo kuma dare yayi .

Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke, yace  ALLAH yabashi lafiya, zuwa anjima sai su waziri suje dubashi ai, tana ina ne ita d'iyar tawa? .

 tana nan cikin masarauta .

Jin jina kai kawai Sarki yay bai kuma cewa komaiba, sai zuwa can yacigaba dayima Sauban tanbaya akan jikin Abie, shikuma yana bashi amsa. Galadima dai Na jinsu bai saka bakiba.





*************



Saida gari yafara haske ALLAH yabani ikon tashi, dan zazza6in kuma ya sauka, yanzu kuma haka yakemin, da dare yayi zan fara zazza6i, lokacin da gari zai waye saikiji ya sauka. Sai dai ciwon jiki.

Saida nayi wanka da ruwa mai zafi sannan nayo alwala, sallar asubahi data kwacemin nayi, Na jawo handbag d'ina danazo da ita Na d'akko wayata, sim card d'ina Na 9ja Na d'akko shima Na saka akan wayar, massage suka turomin Na adadin awannin da suka bani sim card d'in zai d'auka kafin ya cigaba da aiki. ganin haka saina ajiye wayar natashi domin gyara d'akin, ina cikin kakka6e gado idona yakai bisa wayar Galadima. dad'ine ya kamani, koba komai nakira wani d'an gidanmu Na sanar dasu nazo 9ja.

Wayar Na d'auka Na saka number Abbana, dan yanzu nafi kwad'aituwa dajin muryarsa fiye da kowa, kodan mafarkai marasa dad'i danakeyi a kansa, Mtn d'insa nafara kira amma a kashe, saina kira glo d'in, shima switch up, ban kawo komai a rainaba na maida kiran kan innarmu, bugu biyu aka d'aga, wani dad'ine ya kamani, cikeda d'oki nace  innarmu I miss you .

Aiyaan daya d'aga wayar yay dariya, aunty ba inna baceba. Nine, Nima Na iya waya yanzun .

Dukda naji dad'in jin muryar d'an uwana, hakan bai hana zuciyata shiga fargaba ba, nace  Aiyaan Kaine? ina innarmu d'in? .

 Tana wanka ne zamuje asibiti wajen Abba .

Da sauri Na dafe k'irji, nace  Asibiti kuma? miya sami Abban? .

 Lah Aunty baki saniba? Ai accident yayi fa, kuma innarmu nata kuka, hakama innaro dasu daddy .

 Aiyaan!!... nafad'a da k'arfi, kafin nace wani Abu naji an rik'emin hannu ta bayana an zare wayar daga kunnena.

Kuma rikicewa nayi, Na juyo da hanzari, cikin kuka naketa fad'in  abbana! Abba da gaske Aiyaan yake yi? Yalla6ai da gaske Abbana yayi accident? .

Wani tausayina yaji ya tsargashi, ya dafa kafad'una, cikin sigar lallashi yace  cool down mana my friend .

 to ka fad'amin da gaskene Abbana yayi accident d'in? .

Rasa mizaice min yayi, sai bin fusakata da idanu yakeyi, ya cije lips nashi yana fad'in  inhar kinason na kaiki ki gansa toki nutsu .

Share hawayena nayi da sauri nace,  to na nutsu muje .

Yaja hancina, a hankali ya furta,  good girl . Sai ya juya kuma ya fita.

Binsa nayi da kallo hawaye na zuba a kumatuna, kenan da gaske Aiyaan yakeyi Abba yayi Accident d'in,  hasbinallahu wa'ni'imal wakil . Na dafe kaina tareda zama a bakin gadon nacigaba da raira kukana.



Shikam yana fita ya dunk'ule hannunsa yana cije lips, yama akayi yabar wayarsa harta d'auka tayi kira dashi, ko kad'an baiso hakaba. Baiso tajiba kai tsaye.



Saida naci kukana na gode ALLAH sannan natashi na hau shiryawa, atamfa na saka zani da riga, bawata kwalliya nayi ba, na shafa fauda kawai da lips gloss, turarema kad'an na shafa. ina cikin Neman mayafi ya shigo, kamshin turarensa yasani juyowa na kallesa, sanye yake cikin oxblood d'in shadda, hularsa takalmi agogo duk black, link d'in hannun rigarsa yake sakawa, sai alk'yabba pink da ratsin milk a hannunsa.

d'auke kaina nayi naci gaba da neman gyalena a cikin kayan lefena.

Baimin magana ba ya tako har inda nake, hannu yasaka a kafad'una ya d'agoni, fuskarsa babu walwala ko kad'an, idonsa akan fuskata, kusancin damukai da juna sosai yasaka numfashinsa ke sauka akan fuskar tawa, janye idona nayi na maida kan design d'in gaban rigarsa, yayinda shikuma ya warware alk'yabbar hannunsa mai k'yau ya sakamin, d'agowa nai muka k'ara had'a idanu, ya jinjina min kansa kawai.

Jinai tamkar in fasa ihu, banason saka alk'yabba d'in nan nidai, dan nauyi sukemin, garama wannan batada nauyi gaskiya, dan tamkar riga After dress take, saidai suffar alk'yabba aka mata, kuma tanada kaurin dabaza'a ga jikin mutumba.

Hannunsa yakuma d'orawa akan kafad'una ya d'ago hular alk'yabbar dake kwance a baya ya sakamin, ni kaina koba'a fad'aba nasan nayi k'yau, yanzunma baice uffanba ya juya ya fita yana nunamin agogon hannunsa alamar time yana tafiya.

Handbag d'ita na d'auka da wayata nabi bayansa, dauriya kawai nakeyi na hana kuka tasirin zubowa.

A falo na iskeshi shida Sauban dake zaune a kujera shima cikin manyan kaya, dayake ba sakawa yakeba sainaga ya canjamin, ya kalleni cikin halinsa na tsokana yana fad'in  kaga sarauniya gagara badau ta gobe, takawarki lafiya 6auna mai tafiyar k'asaita....... .

Harar da Galadima ya zuba masa ce ta sakashi gimtse bakinsa yana had'iye dariya.

Nidai banma tankaba, dan yau zuciyata babu dad'i.

Galadima ne yay gaba mukabi bayansa, tunda muka fito hadimansa suke zubewa gaishemu, Sauban kawai ke amsa musu, shikam Galadima saidai d'aga hannu, Niko ko kallonsuma banayi. Hakan yasa suka fahimci har yanzu akwai matsala kenan, dansu bama Susan munzo nida Sauban ba.



Muna k'ok'arin shiga mota Harun ya iso wajen, gaidashi Sauban yayi, nima na gaidashi, ganin ni da Galadima kowa fuska a tamke sai abin yabashi mamaki, hannun Galadima ya kama suka koma gefe.

Nikuma da Sauban muka shiga mota.



 Sameer babu fad'a miya kawo gaba? .

Murmushi Galadima yayi, ya cije lips nashi kad'an yana kallon Harun,  bazaka ganeba Harun, na iske abinda ya dagula lissafinane kawai, naga kiranka jiya, amma ina cikin rud'ani a time d'in shiyyasa ban d'agaba .

 rud'ani? mike faruwa ne? .

 mahaifin munaya ne yay Accident, a time d'in ina hospital wajensa .

 ya salam, ya jikin nasa to? .

 Alhmdllh, zamuje canne bayan mun gaida jama'ar gidan .

 ok bara na k'arasa abinda zanyi kafin Ku fito saimuje .

Kai kawai Galadima ya jinjina masa.



Bud'e masa gefena akayi ya shigo, yad'an kalleni, kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.

Sashen mama Fulani muka fara Isa, amma sai aka sanar mana tasha maganin mura ta kwanta, daga nan muka nufi sashen matan Sarki, inda yafi ko ina k'awa da ado a gidan kenan.

Mun sami tarba ta musamman ga Uwar gidansa, nidai matarnan tana k'aunata na lura, kuma tafi sakarma Galadima fiye da kowa a Matan sarki, tanada kirki sosai, haka taita jan Sauban a jikinta, nakula suma sunfi sakewa da ita.

Sosai ta nuna damuwarta akan Accident d'in mahaifina da Galadima ya sanar mata, taita jinjina maganar tana lallashina da jerama Abba addu'ar tashi cikin k'oshin lafiya.

Tasa aka kawo mana break fast wai saimun karya anan, Sauban ne kawai yaci, amma Galadima cewa yay ya k'oshi, nima nace bazan iya ciba. dan burina kawai naga mahaifina, gaisuwarma duk akan k'aya nake.

Shima Sauban d'in bai wani ci abun kirkiba yace ya k'oshi, mun fito muka shiga sauran sassan, amma ba ko inaba.





Sauban da harun sun tafi a mota d'aya, nikuma ni da Galadima. Sai motar dogaran Galadima guda biyu, sai kuma kuyangi hud'u da Uwargidan sarki gimbiya Zulfah tahad'oni dasu, wai kafin mu dawo nima a turamin bayina da zasu ke kula dani, ni dai da to kawai na amsa, Galadima kam baima ce uffanba.

Babu mai magana a cikinmu daga ni harshi, sai saukar ajiyar zuciyata da share kwalla time to time danakeyi.







............................................





Innarmu na fitowa daga bayi Aiyaan ya sanar mata na kira, da mamaki tace masa kodai Munubiya ce? .

 wlhy Innarmu aunty Munaya ce, kuma batasan Abba bashida lafiya ba .

 ka sanar mata ne? . tafad'a a rikice.

 eh innarmu na sanar mata, kumafa naji tana kuka .

 innalillahi Aiyaan wayace ka sanar mata? da wace Number ta kira? . Tayi maganar tamkar zata make Aiyaan.

Runtse idanu yayi yana k'ank'ame jiki saboda tsoro. innarmu dukta rikice, tasan su Munaya da shiga Rud'ani akan Abu, yanzu haka tana cikin damuwar Munubiya itama, dan jikinta yakuma janga6ewa, ga laulayi ga wannan damuwar Abban.

K'ok'arin kiran Number tashigayi danta kwantarmin da hankaki amma sai tak'i shiga.

Har suka gama shirin asibiti wayar bata shigaba.

Koda suna mota taita gwadawa.



A asibitin suka had'u da mama Rabi'a suma sunje, ganin innarmu a cikin damuwa yasata k'ok'arin fara kwantarma 'Yar uwarta da hankali.

Innarmu ta sanar mata kato6arar da Aiyaan yayi.

 to Yaya ko su Munaya sunzo k'asarne? .

Anya kuwa Rabi'a, naga jiya mijinta na nan amma baiyi maganar zata zoba .

 ito da wannan dan wanann, amma ai bama fidda raiba .

 hakane . cewar innarmu.



Babu dad'ewa da zuwansu saiga gwaggon Haleematu da matan k'annen ta sunzo duba Abba, (dayake har yau bata dawoba ita). k'in gaisawa tayi da innarmu da mamansu yaa hameed, innarmu bata damuba, amma mamansu yaa hameed saida taja tsuka, babu dai Wanda ya tanka. Sukuma suka shiga suka ga Abban, dayake yau ana barin na jikinsa zuwa su duba shi.

Koda suka fito harda kuka takeyi, matan k'aninta suka tafi amma ita saita zauna, kaf 'yan gidanmu babu Wanda yace mata danmi, kowama tasa ta isheshi aransa.





&&&&&



Tunda motocinmj suka shigo harabar asibitin sai kallo ya koma sama, 'yan gidanmu dakeda yak'in Galadima ne kowa tsumayen fitowarsa yakeyi, sauran jama'a kuma da 'yan dubiya son ganin wad'anda zasu fito sukeyi.

Sai da aka bud'e mana sannan muka fito, suma su Harun duk sun fito.

Su yaa Hameed suka taho garemu sunama Galadima sannu da zuwa, cikeda kulawa yake amsa musu.

Kowannensu fuskarsa ta nuna farin cikin ganina, yayinda nikuma naketa faman zirar da hawaye.

Cikin d'okin ganina Fauziyya tazo ta kama hannuna itada Safara'u, saina rungumesu na fashe da kuka, kukana ya karyar musu da zuciya suma suka fara, sauran 'yan uwanama duk suka taso gareni, dama duk sun zo, ni kad'aice wadda nake nesa.

Saida baba k'arami yamana magana sannan suka sakeni, na matsa ina sharar kwalla na gaida iyayena, Munubiya ce kawai ban ganiba, ina share hawaye na tambayi tana ina?.

Aunty khalisat tace  sunje ganin doctor itada yaa marwan, dan batajin dad'i itama .

Kaina kawai na jinjina, na k'arasa gabansu innarmu na durk'usa ina gaishesu, duk sun amsamin cikeda kulawa, da tambayata ya hanya?, nace  Alhmdllh .

Matan gidanmu kowacce kallona take da mamakin canjawata a cikin wata 1 kacal. Na katse musu tunani da tambayar d'akin da Abba yake.

Aunty Ramlah ce taja hannuna muka shiga corridor d'in dazai sadamu da d'akin da Galadima yasa aka canjama Abba.

A ciki na iske Galadima da Harun da Sauban, sai doctor da yaa Shafi'u yaa Hameed.

Takun takalmanmu yasakasu juyowa suka kallemu, na zare hannuna daga na aunty ramlah ina toshe baki saboda kukan dake Neman kufcenin, taka wa nayi gaban gadon da Abba yake, na durk'ushe ina sakin kuka mai tsuma rai da zuciyar mai saurarona, tare da kife kaina jikin gadon.

Kukana babu zuciyar Wanda bai karya ba, Galadima ya tako a hankali inda nake, hannayensa biyu ya saka ya kamoni na mik'e tsaye, fad'awa nayi saman k'irjinsa na kuma sakin wani sabon kukan.

Bashida za6in daya wuce kar6ata, dan haka shima saiya saka hannayensa ya zagaye bayana dasu, ya d'ora ha6arsa saman kaina yana lumshe idanu da cije lips. kad'an-kad'an yake buga bayana alamar lallashi.

d'ai-d'ai su yaa Hameed suka zare jikinsu suka fice daga d'akin, aka barmu mu kad'ai sai Aunty Ramlah da muka birgeta, itama ganin sun fita saita fice taja mana k'ofar.



Munkai tsawon lokaci ahaka, saida na tsagaita da kukan sannan Galadima ya d'ago kaina daga jikinsa, hannunsa yasa yana gogemin hawayen fuskata, amma ya gaza cewa komai. sai girgiza min kai kawai yakeyi.

Ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jere, da hannu ya nunamin hanyar fita.

Banyi musuba nabud'e k'ofar muka fito, ina gaba yana bina a baya. tafiya nake a hankali saboda juwar dake Neman fara hajijiya dani, burina kawai nakai inda 'yan gidanmu suke zaune akan kujeru nima na samu na zauna.

Muna gab da k'arasawa wajen na dafe kaina, sai nayi baya luuuuuu.

Da sauri Galadima dake bayanta ya tareta ta fad'o jikinsa, gaba d'aya 'yan gidanmu da mutanen wajen suka mik'e tsaye cikin ambaton sunan ALLAH.

sosai Galadima ya tallafota jikinsa, yayinda wasu Nurses biyu suka iso da gudu domin kar6ar Munayar.

Amma saiya hanasu yana daka musu tsawa da ambatar su kira Doctor.

Basu ba kowama a wajen saida tsawarsa ta rikitashi....................
'<���







*_Comments d'inku shike k'aramin k'arfin guywar rububutun nan wlhy, amma da tuni na ajiye saina samu lafiya>�&�<���
@&, amma yanda kuke k'ok'arin Comments sai bana iya barinku banyiba=��, ina godiya kwarai da gaske, I love you all>�p�>�p�>�p�>�p�>�p�>��<���=�M�<���d'_*













*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���_*

*_Typing=���_*







*_Haske writer's asso...._*=ء�









*_f&RAINA KAMA......f&_*

_{Kaga gayya}_







*_Bilyn Abdull Ce_*>��<���







~Book 2~ =�I�<���7�





................Gaba d'aya ya rikice ya rikita Nurses d'in da jama'ar wajen, cak ya d'auki Munaya, gadonma da aka kawo masa domin d'orata ko kallonsa bai yiba. Wani d'aki suka nuna masa ya shiga da ita.

Da sassarfa doctor dazai duba munayar ya iso, dan dogaran Galadima tasoshi gaba sukaje sukayo.

Kai tsaye Galadima yace baya buk'atar namiji mace yakeso ta duba masa matarsa.

Hak'uri doctor d'in ya bashi, sannan yakira wata likita mace mai suna doctor Farida.

Isowarta yasaka Galadima da yay bake-bake a k'ofar bata hanya ta shiga.

Duk yanda taso yabata waje tayi aikinta yak'i, gashi duk yabi yagama rikitata da tsawarsa.

Doctor d'in da Galadima ya hana ya duba Munaya ne ya matsa kusada su harun yana fad'in  dan ALLAH sir Ku lalla6a yalla6ai ya fito danta samu damar aikinta, wlhy dukya rikitata .

Murmushi Nuren da isowarsa kenan asibitin aka masa bayani shima yayi, suma su harun duk murmushi sukayi.

Nuren ya kalli baba k'arami yana murmushi,  Abbanmu inharfa bakai kamasa magana ba bawai zai fito baneba .

Shikansa baba k'arami murmushin yakeyi, koba komai hankalinsu Yakuma kwanciya da zaman 'yarsu inda suke tunanin anfi k'arfinta.

Bayan doctor yabi zuwa d'akin, Galadima dake zaune, kan Munaya na bisa cinyarsa sai murza tafin hannunta yakeyi wai kozata farfad'o, yayinda doctor Farida ke k'ok'arin lik'a mata oxygen ita kuma .

Shima baba k'arami da k'yar ya lalla6ashi ya fito.



Tsawon lokaci doctor Farida tana ciki bata fitoba. Galadima dukya damu, danma ankawo masa kujera ya zauna, amma sai jan tsuka yakeyi time to time.

Hankalin 'yan gidansu Munaya ma duk a tashe yake, jiran fitowar doctor Farida kawai akeyi dan aji mike damun munayar.

Innarsu Munaya kam gefe ta koma tana sharar kwalla, itakam batasan yazata misalta wannan tsakaniba, miji da 'ya'ya duk babu lafiya, Munubiya ma fa sunacan ana k'ara mata ruwa.

Fitowar doctor


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login