Showing 123001 words to 126000 words out of 365757 words

Chapter 42 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1524

sofa na zube Ina sauk'i numfashin wahala, wani zazza6ima nakejin yana neman rufeni, harna rufe idanu naji wayata na wringing, lalubowa nayi na duba mai kirana, nasan dai duk Wanda zai kirani to daga Nigeria ne, dan su Samha duk suna gida, Galadima kam bai ta6a kirana a wayaba, banmayi tunanin yanada number ba duk da shine ya sayi layin.

Sunan munubiya dana gani yasani fad'ad'a murmushina, saida nabari ya katse sannan na kirata.

Bugu biyu ta d'aga, jin muryarta can k'asa sai hankalina ya tashi, nashiga tambayarta ko lafiya.

 sweetheart wlhy banajin dad'i, ko school nakai sati banjeba, ya kuke? .

 ayya sorry sweetheart, mike damunki? .

 wlhy zazza6i, kema naji muryarki wata iri ai? .

 nima lafiyar sai a slow wlhy, ina yaa marwan? .

 tofa, ciwo a time d'aya mu duka? ALLAH yabamu lafiya to, yaa marwan yafita gaida su mama, ya jikin Abie da Galadima? .

 everything Alhmdllh dear, jikin Abie ma yanata sauk'i, sun fara masa amfani da addu'oin, amma naji kamar doctors d'inshi suna complain wai abar shafa masa abinda ake shafa masa .

 karku wani sauraresu, Ku cigaba kawai, ALLAH yasa muji alkairi .

 insha ALLAH dear, dama haka Galadima yace shima .

 ALLAH ubangiji yabashi lafiya, bara na barki ki huta, a gaida minsu .

 ok sweetheart bye .



Ina ajiye wayar na mik'e, bayi nashiga nahad'a ruwa mai zafi nagasa jikina kozanji dad'i, haka nake kusan yini wanka da ruwan zafi, wai ko zan dainajin ciwon jiki, amma a banza, danayi wanka bana wuce mintuna talatin ciwon yake dawowa sabo.

Wani ash d'in wando da Riga na jawo na saka, kayan basuda nauyi sosai, wandon kad'an yawuce guywata, rigar kam hannunta iya kafad'a ya tsaya, kamardai vest d'in maza take, saidai daga gaba tanada banbanci data maza. nasan Galadima bazai dawo gidan yanzuba saboda koya tashi aiki saiya biya ta asibiti kafin yazo gida, yanzu kuma akayi isha'i nasan sai zuwa irin 11, shiyyasa nayi tunanin sakasu ko zan ragema kaina nauyin jikin. komawa nayi saman sofa data zama gadona na kwanta, amma sai naji dukna takura, najujjuya naji babu dad'i kwanciyar, tsaki nayi namik'e nakoma saman gadon na kwanta, insha ALLAH kafin maishi yadawo dai natashi=��.

Banfi 5minutes ba da kwanciya barci ya d'aukeni.





*****

Kansa daya fara matsa masa da ciwone yasashi tattara kayansa yabaro office, Dan yau sunyi overwork ne, suna shirin fidda laptop sabon k'ira, saida yashiga office d'in vijeey da Alexander yamusu sallama sannan yanufo gida, ko asibiti bai biyaba, Dan har wani jiri-jiri yake gani a idonsa, yasan barcin dabasa samun yine ya haddasa masa ciwon kan, bama kamarshi, Dan gara ni idan yafita nakan kwanta nayi barcin.

��

Da k'yar ALLAH yabashi Damar isowa gidan. Ko rufe motar baiyiba sai a cikin bayin ne wani yataso yarufe, a falo ya wuce Samha na barci itama, tunda muka shigo ta zube a wajen, tun yana taka steps d'in yafara cire bottom d'in Indian suit d'in dake jikinsa white color, burinsa yana shiga d'akin yagansa a gado kawai.

Ganina baje a gadon yasashi yin turus yana kallona, yay saurin kauda idonsa gefe saboda kayan jikina sun kamani sosai, sun mugun fito da surar jikina d'as, gashi sun bala'in min k'yau, yau da ace matar dayake soce babu abinda zai hanashi yabawa harma yabata tukuycin wannan kwalliyar, tsigar jikinsa sai tashi takeyi, gashin jikinsa duk ya mimmik'e, rigarma yakasa k'arasa cireta, ya dafe kansa yanajan guntun tsaki, miya kawo yarinyarnan gadonsa?. Yayi maganar cikin zuciyarsa.

Jin jiri na neman zubdashi a k'asa yay saurin zama bakin gadon, samu yay ya lalla6a ya ida cire kayan, duk da yafi buk'atar kwanciyar haka ya daure yad'an watso ruwa, sannan yafito yasha magani, koma shafa'i da wutiri baiyiba, a nufinsa sai zuwa anjima zai farka yayi.



Abin dariya, saiya jawo dogayen filullukan gadon yajerasu a tsakkiyar gadon sannan ya kwanta can k'arshe, shima babu dad'ewa barcin yay gaba dashi. (Wlhy kafad'o babu ruwana fad'ama fans zanyi Galadima ya tik'o k'asa ehe=��>�(�>�#�>�#�)

Can cikin barci Galadima yafara juye-juye, yasaba shi kad'ai yake kwana abinsa, jin fillos a gabansa yasa hannu ya d'aukesu yayta wurgawa k'asa cikin barci, sannan yay juyi zuwa tsakkiyar gadon.

Munaya kam tasaba da kwanciyar mutum biyu. dan haka ko juyin zatayi bata barin inda take kwance, duk da ma batasan da Galadima a gadon ba, tunda batasan ya shigoba.

Barci yay barci saiga su yalla6ai Galadima masu jera fillos a jikin munaya=��, d'umin jikinta yasashi kuma nanik'e mata, saboda zazza6in daya rufeta, kasancewar yanajin sanyi-sanyi sai jikinta yamasa dad'i.

Itama saita kuma lafe masa a jiki saboda jin sanyi-sanyi da k'amshin turarensa kuma, sunbi sun k'adandane juna kaikace ana shirin rabasune, kowa yana amfanuwa da yanayin jikin d'an uwansa.





Humm, bara na lek'o su innaro 'yan Nigeria suma>��, mai tuk'ulluma a goshi ba>�-�>�+�, ni nama godema mamansu yaa Hameed>�#� dama k'afar suka karya=��.







_____________________________



Anbama innaro magani a wani camix suka dawo gida, gidanta aka kaita, innarmu tad'an dafa ruwa tazauna kusada ita tasaka k'aramin towel danta gasa mata goshin koza'a samu yarage tukullumar dayayi.

Innaro ta 6ata fusaka zatama innarmu tijara.

Baba k'arami yay saurin tareta da fad'in  haba inna, Dan ALLAH kibari tamiki, naga wad'anda suka miki abunma ko kallo baki ishesuba balle su nuna damuwarsu akai, wai shin minene laifin Ai'sha agarekine? .

Abbanmu da daddy suna zaune basuce uffanba sudai. Harara innaro tazuba ma baba k'arami kawai amma batace komaiba, itakuma innarmu ta saka towel aruwan tafara gasa mata.

Tanama innarmu masifa dai har akad'an gasa mata, aikam saigashi wajen yad'an saki, baba k'arami yamik'a mata kofin tea d'in da maman fauziyya ta had'a.

Kar6a tayi tana yatsine Baki, amma saigashi ta shanye tas, aka bata magani shima tasha ta kwanta.

Basu bar gidanba saida tasamu barci, da innarmu tace zata kwana annan, sanin halin innaro Abba yace a'a tatashi suje gida tunda ga habiba d'iyar gwaggo safiyya dabata komaba.

Badan innarmu tasoba tahak'ura, Dan aganinta innaro itama uwace agareta, kodan hallacin da mijinta yama iyayensu da darajar abbanmu, amma takula ran Abba a 6ace yake, kad'an yake jira a ta6ashi ya fashe, shiyyasa bataja zancen yay tsawoba ma.



Koda suka shiga gida kowa sashensa yayi, innarmu harta kwanta saiga Abba yashigo d'akinta, abinda bayayi kenan, yakan shiga sashen matansa amma baya kwana, saidai mace tabishi nasa d'akin.

Tana yunk'urin tashi zaune zata tambayesa lafiya? ya d'aga mata hannu kawai ya hawo gadon tareda janta a jikinsa suka kwanta.

Bai bata damar maganaba Dan haka tayi shiru kawai kamar mai barci.

Kamar yanda Abba bai isashen barciba hakama innarmu batayiba, Zarah ma kwana tayi kuka akan rashin shigowarsu Sa'eed.

Hakama mamansu yaa Hameed da Gwaggon Haleematu basu rintsaba dasukaje gida.



Kwana biyu da faruwar lamarin Abba yak'i cewa komai, yakuma k'i sauraren wayar da ake masa daga gidan matan nasa.

Innaro harta fara samun sauk'i itama.

Sa'eed kam dadynsa ya taso k'eyarsa washe gari gidanmu, an tattauna akan maganar, yafad'i dukkan abinda zarah ke masa, wani ta amsa laifinta wani kuma ta musa ba ita tayiba, sai wani cikin iyayenmu ya harareta take shiru.

Nandai aka musu fad'a bayan itaba dad d'insa yace tafad'i abinda yake mata, saboda kar ahanata komawa saitace ita baya mata komai, wannan yasa aka musu fad'a da nasiha kawai akace yad'auki matarsa su tafi.

Dad'i tamkar zai kar zarah kuwa, saitaji zuciyarta wasai, bata tareda damuwar komai, (kota manta uwarta bata gidansu itama a dalilinta kuma>��?).



Washe garin rana ta uku tunda safe saiga mamansu yaa Hameed tareda yayanta ya maidota, (dayake babanta ya tsufa sosai, komai nasu yanzu sai yayan nata, ko kud'inma dashi suke tak'ama yanzun, duk da mahaifinsu ya tara musu).

Abba dai k'in saurarensa yayi, saida yaje ya kama k'afa da baba mai kanwa aminin marigayi mal. faruku, daddyne yamasu jagora zuwa gidan innaro dake kwance tana jiyyar goshi, damma kullum sai innarmu ta gasa mata safe da yamma, duk da masifar innaro da take sha batayin zuciyar ko nuna gazawa.



Ansha fama akan Abba kafin ya sauraresu, danma akwai baba mai kanwa ne a zancen, amma ya tabbatar musu da Cewar shifa yagaji da iskancin dasuke masa a gida, tun zamanin k'uruciya har girma yafara kamasu sun k'asa canjawa, yabama kowaccensu damar k'arshe inhar suka kuma Tayar masa da rikici agida kowacce zata nemi hanyar gidansune, kuma tatafi kenan har abada, Dan bazai duba 'ya'yan dake tsakaninsuba ma.

Tunda ga ranar mamansu yaa Hameed tadawo gidan, Gwaggon Haleematu kam bata dawoba, itada iyayenta sunce sai Abba yazo da Kansa koya turo anbasu hak'uri.

Shikuma ya rantse saidai tayita zama inhar saiyaje bikonta.



Gidanmu dai kam kwana biyu tsit kakeji, Dan baba k'arami da daddy ma summa matansu kashedi da sharad'in barin gidan gaduk wacce tasake fad'a da wata, wannan dalilin yasaka gidan yin lafiya, 'yan anguwa da makwafta sukaji kasiririt.



Innaro ma ta warke abinta, saidai kam sun k'ulla da mamansu yaa Hameed, Dan yanzu ko 'ya'yanta basuda farinjini wajen innaro, ko Naziru autansu yamata Abu saita makeshi (ho innaronmu ta mutunci>�#�=��).







***************







Zazza6i dai yahana Munubiya sakat, yaa marwan yagaji da lalla6ata ga ciwo na cinta, yau dai yakwasheta zuwa asibiti tana kukan batason zuwa, amma yak'i saurarenta.

Haka dai sukaje, bayan yankar kati dabin layi suka sami ganin doctor, gwajin farko doctor yabasu albishir d'in samun rabo na wata d'aya kacal (yaa marwan sharpshooter>�-�, Munubiya dai inaga tuntu6e akayi>�+�>�#�).

Wayyo zokuga murna wajen ogan miskilanci, babu kunya yakira Abbansa ya sanar masa, shima murna yaytayi ata cikin waya, kafin kace mi zance yabaje dangi, har innarmu labari yakai kunnenta.

Harda kukan dad'i tayi, ikon ALLAH kenan, ita saida ta jera shekara 20 tana kuka da shan gori kafin ta samesu, amma ga Munubiya wata 1 da sati d'aya da aure har ALLAH ya kawo rabo. Saura munaya, k'ila itama d'indai an samu, tunda shekaran jiya dasukai waya take mata complain batajin dad'i. haka innarmu taita murnarta a d'aki ita kad'ai, babu Wanda ta sanarmawa tabarma cikinta, a cewarta idan yafita ko Munubiya tazo gidan sagani.



Abin nema yasamu fa, yaa marwan tamkar zai maida Munubiya ciki, kokuma ya maido cikin nata jikinsa yarage mata wahalar laulayi haka yakeji, Dan tana d'an shan wahala gaskiya. ko girki yanzu bata iyayi balle gyaran gida.

Hakanne yasaka mama rabi'a cewa yadawo da Munubiya wajenta harta samu sauk'i.

Saiya fara fushi da rok'on tabarta Dan ALLAH shima zai kula da ita ai, abasu Ayusher ko feena takoma wajensu saita taimakawa Munubiya da aikin gidan.

Mama Rabi'a tace a'a, Ayusher itake taimaka mata itama, feena kuwa ba cikakkiyar lafiyace da itaba, ba kowanne aiki take iya yiba ko agida (kunsan masu sikila dai>�&�<���
@&, ubangiji ALLAH yabama dukkan masu irin wannan ciwo lafiya, ALLAH yasa yazamema rayuwarku kaffara kuda iyayenku da kullum suma hankulansu ba a kwance sukeba=�"�, duk mai wannan ciwon ina tsananin tausayinsa wlhy=�-�).

Babu Wanda yaa marwan ya iya, dole ya tattaro kayansa shida Munubiya suka dawo gidan kawai, ai ko su Ayusher sunci dariya, danma fadeel bayanan, saidai a waya suka bashi labari.

Munubiya tacigaba dasamu kulawa wajen mama Rabi'a, bata aikin komai saidai amata, sai idan boss nason rage nauyi ya janyeta d'akinsa da wayo ya kashe arna=� �=��.

Mama Rabi'a duk tana kula da su, amma saitayi kamar batasan bikin dasukeyiba, Dan taga idon yaa marwan a tsakar goshi yake=��=��.







>�%�kai jama'a mu koma India.=����&<���
@&�&<���
@&







....................................................

______________________________

....................................................







Zafin jikinane yafara masa yawa, dan yafara shiga sosai jikinsa, cikin barci ya laluba danson jin minene mai zafi ya rungume haka? jin kamar mutum yasashi k'ok'arin bud'e idonsa dasukai masa nauyi saboda barci, dishi-dishi yafara ganin fuskar munaya, hardai yasamu nasarar bud'e idon gaba d'aya a kanta>�+�.................
'<���

















_ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�>��<��� '<���_

*_Typing=���_*







*_Haske writer's asso...._*=ء�









*_f&RAINA KAMA......f&_*

_{Kaga gayya}_







*_Bilyn Abdull Ce_*>��<���







~Book 2~ =�I�<���3�





............Shiru kawai yayi yana kallon fuskarta ta cikin d'an hasken mai kalar jaa, sai fuskar tabada wata kala data k'ara mata k'yau. yaune ranar farko dazaice yamata kallon k'urilla irin haka, yadad'e yana kallonta kafin ya janye idanunsa dake cike da barci. hannu ya mik'a ya kunna ainahin fitilar, haske ya gauraye d'akin, cikin dabara yafara yunk'urin janye jikinsa, amma tak'i yarda, saima farkawa datayi, tabud'e idanunta dasukai nauyin barci a hankali, kad'an take kallon face nashi, ta lumshe idon tasake bud'ewa.

 wannan d'aurin goronfa? .  galadima yay maganar a hankali cikin muryar barci, yanabin hannun munaya da ta zagaye cikinsa da kallo .

Sosai Munaya ta waro idonta yanzun, ganinta a jikinsa kwance, gashi tawani dabaibayesa saita sakeshi da sauri tana matsawa baya da waige-waigen inda take kwance. gabanta ne ya fad'i, dan ita harga ALLAH tama mance ta hau masa gado, tayi saurin rik'e kanta dake sara mata tana tashi zaune.

Shima saiya tashi yana binta da kallo, a mugun sanyin murya yace  bakida lafiya ne? .

Hawaye suka wanke mata fuska, muryarta na rawa tace  kaina kamar zai tsage .

Saida yaja 1minute kafin yad'an matso kad'an, yatsunsa biyu ya d'ora gefen wuyanta, saiyaji jikin zau da zafi, ya janye ya d'aura zuwa gefen kanta, jijiyar wajen sai motsi takeyi d'ass d'ass d'ass d'ass, alamaun kan namata ciwo sosai. hannun ya janye tareda sakkowa daga gadon gaba d'aya.

Ya zagayo 6ari da take, hannu yasa ya zame nata hannun data tallafe kanta dashi, ta tad'ago idanunta dake cike da barci, sunyi d'anja sun k'ara girma, idonsa a kanta, Dan haka ta janye nata ta maida k'asa tana cigaba da hawayenta.

Kad'an yad'an furzo iskar bakinsa, kafin a hankali yace  mike miki ciwo bayan kan? .

Saida takuma matso wasu hawayen sannan tace,  duk jikina .

 kin fad'ine? .

Kanta kawai ta iya girgiza masa, ya cigaba da tsura mata idanu batare da yace komaiba, ganin tana hawaye duk sai yaji babu dad'i, koba komai itad'in Friend nashice ai, kamar yanda yafad'a tun farko. yad'an sauke ajiyar zuciya mai sauti kafin ya mik'e, bayi yashiga, mintuna kad'an yafito, tana a inda ya barta dafe da kanta, yace  taso kid'an watsa ruwa, ko jikin zai huce .

d'agowa tayi ta kallesa, sai taga ya tsatstsareta da mayun idanun nan nasa, tayi saurin janye nata, amma takasa tashi. matsowa yayi kusada ita, ya mik'a mata hannunsa, alamar takama ta tashi, ta d'ago ta kallesa ya d'aga mata kansa yana mai lumshe idanunsa alamun tabbatarwa.

Hannunta ta saka a cikin nasa, ya had'e waje guda sannan ya taimaka mata ta tashi tsaye, kallo d'aya yamata ya kauda kai, dukda kayan nata masu kaurine saida yaji wani Abu daban, dansu fidda surarta sosai. Har wajen wankan yakaita, sannan yafito batare da ya ce uffanba. da kallo tabi bayansa, a ranta tana mamakin sauk'in kai irin nasa, ada kallon mutum mai girman kai take masa, amma tunda suka fara rayuwa a tare saita fara fahimtar ba haka baneba, kawai dai shi mutumne dabai cika hayaniya da surutu ba, shiyyasa inbaka gama saninsaba saika dunga masa kallon mai girman kai.

Koda ya fito saiya had'a mata tea, shi dama baya rabo dasu a d'akinsa, magani ya d'akko shima ya ajiye, yakoma bakin gadon ya zauna yana tsumayen fitowarta.

Kusan mituna 10 tagama watsama jikinta ruwan, lallai naji dad'i sosai, saidai kuma bazan iya maida kayan dana cireba, inajin kunyarsa, kuma jinsu nake sun d'auki zafi, towel naja Na d'aura, saidai bashida girma, bazan iya fita a haka dashiba Galadima yana d'akin, kad'an nabud'e k'ofar Na lek'oda kaina, yad'an juyama k'ofar bathroom d'in baya kad'an, a hankali cikin muryata mai nuna alamun banida lafiya nace  please


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login