Showing 102001 words to 105000 words out of 365757 words

Chapter 35 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1468

mamakin su na zuwa gaisheni, dan bansa akaba nikam, araina nace ko jama'ar gidanmu dun fara canja haline dai?.

Muna haka saiga innaro tamkar an jehota, kowa ido ya zuba mata, dan shigowa tayi tana masifar wai bamu fara shiga gidan taba nida Galadima.

Na kalleta a d'age ina ta6e baki,  yo banda abinki innaro ai sai nafara ganin Uwata, dan banida kamarta kaf duniya .

Ha6a tarik'e tana kallona  eh lallai kam, yo ai Dama ke halin uwarki gareki, ba mutuncine dakeba, ballan tana yanzun kuma ido yak'ara fetsarewa ansan komai na aure .

Zan maida mata murtani innarmu ta harareni, shiru nayi na k'yaleta badan nasoba.



Shima Galadima yana falon Dady yasamu tarbar mutunci daga maman Fauziyya, dan matan gidanmu babu wadda ta aika masa dako ruwa, yaji dad'in tarbar daya samu kuwa, musamman yanda su Abba suka nuna masa tamkar d'ansu, baiyi dubi da sarautar dake kansaba ya duk'a har k'asa yakwashi gaisuwa wajen iyayena uku.

Hakan yamusu dad'i, domin ya mutuntasu, kuma sun kuma tabbatarwa shid'in mai tarbiyyane.

Anan yamusu bayanin munzo musu sallama ne zamu tafi India.

Fatan alkairi su abbanmu sukai mana da k'yak'k'yawar addu'a, daga nan sukad'an ta6a hira dashi, dukda yana nonnok'ewa saboda kunya irin ta jinin hausa Fulani.

Nikam can innarmu ta iza k'eyata nashiga kowanne d'aki na gaidasu, sai kallon k'urulla suke bina dashi, anason ganin wata makusa a jikina, amma sai basuganiba kuwa, komai sai sambarka. Aikam bak'in ciki tamkar ya karsu, kowa hassada nacin zuciyarsu (kai jama'a ALLAH yarabamu da cutar hassada komai k'ank'artatta=�"�=�O�<���)

Na dad'e d'akin maman Fauziyya sosai, dan acanma naci abinda tad'an girka mana mara nauyi, yaa Hameed yazo ya d'auki na Galadima da kansa.

Sashenmu na dawo inatama innarmu shagwa6a, duk nabi na nanik'e mata, dukda tureni datakeyi. Nashiga tsohon d'akinmu harda kukana, komai nanan yanda yake, harma dawasu 'yan tarkacenmu daba a gama badawa ba, haka kawai bamu mutuba d'akinmu Yakoma kango, anan na d'akko cajata da wayar Galadima daya barmin a filin idi, sai wad'ansu 'yan abubuwa danake buk'ata.



Na fito ina tambayar innarmu waye ya d'auki wani hotonmu dake saman mirror nida Munaya?, tacemin maybe Ameeran inna lami Ce ko Bilkisu, dan taji suna rigima akan d'aukar Horton.

Shigowar Galadima da yaa Hameed tasaka innarmu yin shiru, nikam ban daina daddaga k'afa k'asaba ina k'unk'unin miyasa tabari suka d'auka?.

Galadima dake k'ok'arin zama yad'ago ido yad'an kalleni sannan ya janye.

Yaa Hameed ne yace kekuma lafiya?.

Fad'a masa nayi tamkar zanyi kuka, yace  to kuka zakiyi? .

 ALLAH yaa Hameed inason hotonfa .

 ai saiki hak'ura yanzun tunda sun d'auka ko? .

Innarmu da Galadima dai gaisuwa sukeyi, babu Wanda ya tanka mani. shi saima mamakin ta6arar danakeyi yake a zuciyarsa.

Nikam bansan yana yiba.

Sosai yaji innarmu ta burgesa, yakula ko kad'an ba halinta nabiyoba, dan ita tanada sanyi, dagani batada hayaniya, amma nikam ai sai addu'a.



Yad'an jima anan dukda ba hira sukeba, kowa kunya na cinsa, a raina nace dama yanda kunya guy d'inan ashe?.



Alkairi mai yawa ya ajiyema innarmu, dawata leda da yaa Hameed yabiyosa da ita, sannan yafita innarmu na saka masa albarka yana amsawa cikeda jin dad'i, jinta yake tamkar Momma d'insa.

Daga nan saida yashiga kowanne d'aki, sannan yaa Hameed ya rakashi gidan innaro.

Abba ne yashigo yana fad'in a tattaro lefena muwuce da kayanmu.

Na marairaice fuska nace Abba abarsu anan, kagaba tafiya zamuyi can d'in babu kowa.

 a'a Munaya bazai yuwuba, idan mun ajiyesu anan mizamuyi dasu?, kitafi da kayanki, duk randa dai kuka dawo suna d'akinki ai.

Badan nasoba na amince, amma naje wajen kayan ina fitar da wasu, ni saima yau naga lefen, gaskiya su Galadima sun zuba kud'i a wajennan.

Duk matan gidanmu atanfofi na fidda musu, maman fauziyya kam guda biyu, sannan yaran gidanmu 'yan matan yanzu kowa nafidda masa wani abun, su Aryaan ma dukda mazane kowa na fidda masa abinda zai iya amfani dashi.

Sai su Ayusher da inna lami da Ameera, Bilkeesu ma da nata, hakama mama rabia, na ware akwati guda na lodama Munubiya kaya sosai aciki, aunty salamah ma da nata, sai gwaggo Safiyya da yaranta mata, itama innaro jarabatu na fidda mata, su Abbanmu ne dai narasa mizan basu aciki.

Innarmu na kira tagani, ta kalleni tana fad'in  munaya bazasuga an kwashe kayanba? .

 a'a wlhy innarmu bazasu ganiba, kowafa da sashensa a gidan, kuma babu mai shiga harkar wani, idan na barsu mizanyi dasu? Kayan sunmin yawa ai .

 to shikenan, ALLAH ya saka da alkairi .

Na amsa da ameen ina fad'in  ganaku nan keda su Aiyaan innarmu .

 a'a ni bazan d'auki komaiba, bakiga yama kawomin abuba, ga kud'i dama bansan ko nawa bane .

Kuka na Sanya mata akan saita kar6a, babu yanda ta iya ta amsa, amma saida tarage. Sai dai tana fita na maida mata harda k'arima.

Zainab Ce ta kaima kowa nasa, kowacce rai babu dad'i ta amsa, sotayi ace daga 'ya'yantane wannan abun arzik'in yafito bawai innarmu ba, (basusan shi Ubangiji babu ruwansaba, yakan azurta Wanda yaso Yakuma k'ask'antar da Wanda yaso a lokacin dayaso).

Babu wadda tazo godiya sai maman fauziyya, nace  oho dai, aikin banza wai talaka ya girmi sarki>�7�<���
@& .

Banyi maganar su d'auki motarba, dan sonake nasami cikon d'ayar nabasu su duka ukun.

Nima naje na gaida innaro, dasu Abbanmu, naje gidan innaro lokacin su Galadima harsun fito,, na iske Ashe gwaggo Safiyya tama koma jiya, sai d'iyarta Habiba datake zawarci aka bari anan.

Munsha hira da ita, tanata yaba k'yan da nayi.

Innaro kam dukda jana datake ajiki sai basar da ita nakeyi, amma hakan bai hanata yaba Galadima ba, catake wai na more miji, nafi kowa morewa a gidanmu.

Nidai banda ta6e mata baki da bak'ar magana babu abinda nakeyi, bata damuba saboda neman gindin zama take ajikina.



Bamu baro gidanmu ba sai gab daza'a shiga sallar juma'a, an taho da motata da lefena, duk kayan daza'a bana mutane kuma na barsu a can, harna Munubiya.

Su Abba sunsha alkairi awajen Galadima Ashe, hakama matan gidanmu d'akin kowacce daya shiga saida ya ajiye alkairi, sunata kukan zuci da fad'in inama-inama 'ya'yansu ne a wannan daular>�#�>�t�.

Zamu shiga motane ina sharar kwalla baba k'arami yace namusu godiya wajen Galadima, kaina kawai na iya d'aga masa.

Innarmu bayan tafiyarmu har 'yan kwalla tayi, matan gidanmu kam duk haushinta sukeji, idan kacire maman fauziyya.



Daga nan gidan Munubiya muka nufa, amma anan bai shigaba, yace naje zuwa anjima zai dawo mutafi, dan yanzu zaije sallar juma'a.

Kai na kawai na d'aga masa, nafita bayan dogari d'aya yabud'emin k'ofa, basu bar gate d'inba saida sukaga na shige ciki, ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tareda lumshe ido, abinda yafaru a gidanmu kawai yake tariyowa, yakula family nawama sai a hankali dai. Sunada shigen irin halallayyar family d'insa.



Nikam da gudu nashiga ina kwala kiran sunan Munubiya, itama yafito aguje muka rungume juna, sai muka fashe da kuka kawai, ALLAH ma ya somu yaa Marwan yarigada yafita masallaci.................
'<���







*_Masoya bansan yanda zan nuna muku tsantsar farin cikinaba, amma tabbas inajin dad'in Comments naku, kuyi hak'uri da rashin amsawata d'ai-d'ai, kunmin yawane wlhy, ga massages na PC, idan kuma nagama typing d'inan kaina d'aukar zafi yake, ko son ta6a waya banayi wlhy, naga wasu suna d'auka kamar wulak'ancine rashin amsawar, wlhy ba haka bane, kumin afuwa da uzuri please & please, duk da nasan bazan iya k'yautatama kowa acikinku yanda yakamata ba, dole wani yaga gazawata koyayane tawani fannin=��._*













*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���_*

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 8�





...........Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida 'yar uwata Munubiya, abin kawai ba'a magana.

Duk da bata yarda zan zo d'inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, tarasa inda zata sakani dan dad'i, gaskiya gidan munu yayi k'yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had'a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara'a a fuskarsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad'i. Haka muka yini muna tad'i har lokacin sallar la'asar yafita salla.

A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce takirata ta fad'a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k'yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.

Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d'auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d'auki nawa da muhimmanci baneba.

Wajen 5 tatafi, tafiyarta babu dad'ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad'e a k'ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.

Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza'ayi mijin 'Yar uwarta yak'i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.

Murmushi yayi ya zauna yaci kad'an, yayinda mukuma muka shiga d'aki dan mu basu waje suci abincin, d'an kuskus d'inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu 'yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d'in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kuma nabashi hak'uri akan hakan, nace  to amma tayaya zan basa hakurin? .

'Yar takarda ta d'auka tayi rubutun tabani wai nabashi.

Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d'inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar nayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad'a, Dan nashiga rud'ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.

tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.

Itama k'yauta mai tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.

Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi'a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka rukunkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.

Bamu dad'e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud'i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k'asa.

Nanma saida nayi kuka dazamu taho.

Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k'asaita yana ta6e baki,  ke wai bak'ya tsoron hawayenki su k'are ne? .

Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.





&&&***&&&





Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad'i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d'aure kaina gaskiya.

Mai martaba kam munsha addu'a a wajensa, sannan muka fito.

Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace  kiyi azamar shirya kayanki trolley d'aya, karki wani kwashi kaya dayawa .

Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.





*_7:30pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d'aya, muna baya tana gaba.

d'ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.

Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k'alilan daga masarautar.

Tom nidai ba k'auyace a airport, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,>�(� saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.

Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita k'asar, harun yad'an sha cukuniya a kaina tunda rana.

9pm dai-dai jirginmu ya shilla a gajimare=��=��=���.



Lokacin da akace asaka belt ban sakaba, sai shine ya jawo yasakamin batareda yace uffanba, yana jikin window nikuma ina gefensa, sai bayan mu khaleel da Samha, can baya kuma aunty Mimi da Sauban.

Ina lafe jikin kujera, yayinda shima yake kwance ya jingina bayansa, wani English novel ne a hannunsa yana karantawa, dama tun amota yake rik'e da kayansa.

Da akazo tambayarmu mi muke buk'ata Coffee kawai yace yacigaba da karatunsa, nima ta tambayeni saina girgiza mata kai alamar bana buk'atar komai.

Janye book d'in yayi yana kallona, saikuma ya janye ya maida kanta, harta bar wajen ya kirata, yace takawo min abinda su Samha sukace sunaso.

Bance komaiba nidai, shima saiya cigaba da karatunsa.







(*************)







Alhmdllh mun sauka kasar India, k'asar da nake gani a films, abin mamaki sainaga dogarawa ne sukazo tarbarmu, saikuma Akash dawani danaji Galadima yakira da beejay.

Bamu 6ata lokaciba mukabar airport d'in, a nawa tunanin sainaga rayuwar tasu kamar dai tamuce gaskiya, saidai banbancin sutura zuwa wasu mu'amullat haka, mutane sunata hidimarsu da kai kawo hankali kwance.

Masha ALLAH na fad'a yayinda muka isa gidan danake k'yautata zaton nasu Galadima ne. gidan kam yamin k'yau gaskiya, su beejay basu shigaba suna saukemu suka juya, mune muka Shiga hannuna aunty Mimi tarik'e, yayinda su Samha suke agaba.

Galadima kam mun barsa a harabar gidan yana waya.

Ai kaina bai gama kwancewa ba saida muka shiga falon gidan, hummm manyan k'asarmu sunajin dad'insu gaskiya, yo kanada irin wannan gidan a k'asar daba takaba to k'asarka kumafa?.

A falo muka zube bayi suka Shiga hidima damu, muna zaune a wajen Galadima yashigo, shima zaman yayi ya aza k'afa d'aya bisa d'aya, Sauban yazuba ruwa a cup yabashi, kar6a yay yana fad'in  thanks .

Ya kalli baiwar datake shirya abinci daga can gefenmu,  k zonan .

Da sairi ta ajiye spoons d'in hannunta tanufo inda muke, agabansa ta zube tace  gani ranka ya dad'e .

 kisamu wata ta tayaki Ku gyara d'akin can nakusada Samha yanzun nan .

 angama ranka ya dad'e . tayi maganar cikeda tdantsar ladabi.

Aunty Mimi Na najinsa batace uffanba. Shigowar momma tasaka khaleel tashi da gudu yaje ya tarbota, itama Samha zuwata ta kwakwameta, tunkan ma afad'amin nagane mahaifiyarsu Galadima ce, koda yanda fuskar kowannensu ta washe da farincikin ganin juna.

Hankalinta Na kaina tana murmushi da fad'in  oyoyo d'iyata .

Zamowa nayi daga kujerar na durk'usa har k'asa ina gaisheta, ta k'araso inda nake ta kama hannuna ta tadani nakoma saman kujerar,  zauna kinji, sannunku da zuwa, kinsha hanya ko? .

Murmushi nayi ina duk'ar da kaina.

Galadima yace  wai Momma dan ALLAH duk baki ganmu baneba? .

Kallonsa tayi cikin Hararar wasa, tace,  yo naganku bata taku nakeba .


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login