Showing 141001 words to 144000 words out of 365757 words

Chapter 48 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1506

Farida yasaka kowa mik'ewa anason jin bayani, Galadima dai yana daga zaune ya zuba mata idanu shima. Doctor Farida tace su kwantar da hankalinsu ta farfad'o, amma tamata allurar barci, yanzu tanason ayo gwajin jinin Munayar data d'iba.

Galadima ya lumshe ido yana ambatar  Alhmdllh akan la66ansa.

Sauban ne ya kar6a suka tafi shida Sarkin mota lab d'in.

Dr Farida ta kalli Galadima tana murmushi,  ranka ya dad'e zaka iya Shiga ka ganta yanzun .

Nuren ya kalli Galadima ya jinjina masa kai alamar yaje.

Saida yaja wasu seconds sannan yamik'e cikin takun nan nasa na k'asaita da izza, duk idon jama'ar wajen akansa yake, yana birge kowa.

d'akin ya tura ya shiga, ya taka har gaban gadon da Munaya ke kwance, idanu ya tsura mata, tayi wani fayau da ita, ya jawo kujerar dake wajan ya zauna, har yanzu idonsa na kanta, cikin cije lips da lumshe idanu ya d'ora hannunsa bisa sumar kanta da d'ankwalinta ya zame ta fito, saikuma yasaka d'ayan hannunsa ya shafi kumatunta, a kan la66ansa ya furta  sorry my friend, ALLAH yana tare da masu hak'uri kinji .

Daga haka bai sake cewa komaiba, ya janye hannunsa daga kanta ya mik'e ya fito.

A k'ofar d'akin ya iske Doctor Farida tsaye, kallonta yayi cikin maganarnar tasa mai kama da an masa tilas yace  zata iya kaiwa wane lokaci bata farkaba? .

 Ranka ya dad'e inaga daganan zuwa kamar awa d'aya .

Kansa ya jinjina mata, bai sake magana ba yanufi d'akin da Abba ke kwance. ya Tatar da doctor d'in dake kula da Abban a d'akin.

Da sauri doctor yabashi kujera ya zauna, k'afa d'aya kan d'aya ya d'ora ya Ciro waya a aljihu yana danne-danne. batare da ya kalli doctor ba yace,  kunyi gyaran karayar? .

Doctor yace,  eh ranka ya dad'e duk an gyara, saidai na hak'ark'arinsa yaso kawo matsala, amma Alhmdllh komai ya dai-daita .

 humyim, maganar bayanan danace a tattara minfa? .

 shima komai ready ranka ya dad'e  .

 o right, insha ALLAH zuwa jibi nakeson mu tafi, amma wai har yanzu bai ta6a farfad'owa bane? .

 ai ba'a sume yakeba, allurar damuke masace kawai takesakasa yawan barci .

d'ago ido Galadima yayi yana kallon doctor d'in, yace  amma danme ake masa? .

 itace ke taimaka masa wajen rage masa rad'ad'in ciwukan, dan maganar gaskiya yana cikin matsanancin ciwo .

Cije lips Galadima yayi kawai, yace  ALLAH ya bashi lafiya .

 amin ya rabbi .  cewar doctor.



Daga haka suka fito shida doctor d'in.

Inda Harun yake Galadima ya nufa,  brother yau ba zakaje aikiba kenan? .

Kallon agogon hannunsa Harun yayi, sannan ya kalli Galadima,  ka rikitamu ne ranka ya dad'e shiyyasa ban kula time ya tafi hakaba .

Murmushi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.

Harun yay musu sallama ya fita da nufin zuwa anjima idan yatashi aiki zai dawo.

Su yaa Hameed sukai masa godiya da fatan alkairi sannan yatafi.

Daddy ya kalli su yaa Hameed d'in yace ai kuma da tafiyar kukayi, karku makara wajen aiki .

A ladabce suka amsa masa da to, suna shirin barin wajenne saiga motocin su waziri sun shigo, dole su yaa hameed suka dakata.

Waziri ne da matawalle, sai Garkuwa da baraya, sai kuma wasu manya-manyan 'yan majisar Sarki. dogarai duksun kasa sun tsare, wasuma zato suke sarkinne yazo da kansa.

Su daddy ne suka musu iso har d'akin da Abba yake kwance, sosoi suka nuna tausayawarsu gareshi, sunja doguwar addu'ar samun lafiya da fatan alkairi ga Abba. Sannan suka Isar da sak'on Sarki.

Sun d'an jima a d'akin suka fito da nufin tafiya, a dai-dai time d'inne kuma doctor Farida ta iso gaban Galadima cikeda sassarfa. Bakinta a washe tamkar gonar auduga. Wani dogari Na k'ok'arin dakatar da ita Galadima ya d'aga masa hannu alamar ya barta tazo.

Cikin girmamawa doctor Farida tace  wannan asibiti da dukkan jama'ar cikinsa suna taya masarautar gagara badau murnar samun k'aruwa daga jikin gimbiya Munaya, insha ALLAH nanda watanni 7 dawasu satittika zata zama uwa, ma'ana tana d'auke da cikin wata 1 da sati uku .

Atare dogarai suka d'auki kabbara, Galadima dake tsaye baki bud'e cikin tsantsar mamaki ya kafe doctor Farida da idanu, sai kawai yashiga zame agogon hannunsa mai masifar tsada da k'yau ya mik'ama doctor Farida.

Sauban yazo ya rungumesa, hakama matawalle.

'Yan gidansu Munaya sai suka koma 'yan kallo kawai, amma bakin kowa yakasa rufuwa.

Doctor Farida ta kalli Galadima cikin mamaki da al'ajabi,  ranka ya dad'e ni Na cancanci wannan agogon mai d'unbin tsada kuwa? .

Wani murmushin Daba a cika gani Galadima yayiba ya saki, ya gyara tsayuwarsa yana fad'in  idan duk abinda na mallaka a duniya kike buk'ata zan baki shi, saboda wannan shine albishir Na farko da aka ta6amin Na farinciki a rayuwata, kifad'i dukkan abinda kike buk'ata inhar baifi k'arfina ba kafin nabar asibitinnan za'a kawo miki shi .

Kanta ta shiga girgizawa, kafin ta d'aga agogon ga mutane su gani.

Mamaki ya cika kashe matan gidansu Munaya hassada da al'ajabi ya cika zukatansu, tunma ba'a haifi cikinba Galadima yake wannan rawar kan inaga an haifoshi?, Kansu bai kuma kwanceba saida sukaji waziri da baraya Na sanarda tasu k'yautar ga doctor Farida, hakama matawalle da Nuren.

Doctor Farida fa ta rikice, itakam yau taga farar rana, (=�D�idan ta ALLAH ake niya kamata abama wad'annan k'yaututtuka ma=��).



Nuren da matawalle suka hau rabon kud'i a asibitin, tamkar basu San ciwonsu ba.

Waziri kam d'akin da Munaya take kwance aka musu rakkiya, sun mata addu'a kafin su fito, kowa bakinsa a washe, wasukam ta cikin Na ciki kawai=�3�>�-�.



Kafin kace mi labari yagama zagaye asibitin, gidan Sarki kam kafin su waziri su Isa labarin cikin Munaya yaje.



hakama Sauban ya kira su Momma ya guntsa musu, Momma saida tayi sujudar shukur.

Abie bakinsa yakasa rufuwa, kamar daga sama sukaji yace  ALLAH ya inganta .

Dukda a hankali yayi maganar hakan bai hanasu ganin motsawar la66ansa ba, Khaleel dake kusa dashi yace  Lah Abie yayi magana Momma!! .

ba momma ba hatta da jakadiya sakin kwanon hannunta tayi ta waigo tana kallon Abie. Aunty Mimi ta tura laptop d'in gabanta tafad'o, hakama Samha wuntsilowa tayi daga kujerar datake zaune tayo inda gadon Abie yake.

Gaba d'aya suka rufu akan abie, kowa yanason sanin gaskiyar batun Khaleel, murmushi Abie yamusu yana jinjina kai alamar gaskiyane, sannan a hankali yakuma furta  da gaske Khaleel yake .

Ai yau babu kunya Momma ta rungume Abie a gabansu aunty Mimi ta fashe da kuka mai ban tausayi.

Aunty Mimi ta had'a momma da Abie d'in ta rungume itama.

Jikin Samha har 6ari yakeyi takira Number Galadima ta Nigeria.

Ya rako su waziri da zasu tafi kiran Samha ya shigo, bai d'auka ba, itakuma bata gaji da kira ba.

Saida su waziri suka wuce sannan yaciro wayar a aljihunsa cikeda haushin wanene mai nacinnan. yana dubawa yaga Samha Ce.

Murmushi yayi kawai sannan ya kirata da kansa, bugu d'aya Samha ta d'aga, kuka kawai ta fashe masa da shi, zuciyar Galadima tashiga tsitstsinkewa. tsawa ya daka mata yana tambayar lafiya?.

Share hawayenta tayi, murya Na rawa tace,  Uncle Sam wlhy Abie yayi magana, yanzun nan da Uncle Sauban ya kira yace aunty gimbiya nada ciki sai Abie yace ALLAH ya inganta ..

Galadima ya ciro wayar a kunnensa ya kuma kallon number, tunaninsa wasune kawai keson masa yawo da hankali, ganin dai da gaske number Samha d'in ce saiya maida a kunnen, cikin sanyi murya ya kira ainahin sunan Samha,  Zeenah! banason wasan banza kema kin sani .

 wlhy Uncle ba wasa nakeba, ga Momma ma kaji awajenta .

Kafin yace wani Abu yaji muryar Momma namasa sallama, yanayin muryarta yasakashi lumshe idanunsa. Momma tace,  Muh'd! Yau ranace dabazamu manta da itaba a tarihinmu, k'yautar abinda kud'i baya saya, ALLAH kuma yabama takawa damar magana, narasa yanda zan musalta farin cikina Muh'd .

Wasu hawayene suka gangaro a kumatun Galadima, ga murmushi yak'i barin fuskarsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yace  Momma ko yanzu Ubangiji ya d'auki raina yagama min komai, Momma mizanyi duniya tasan ina cikin tsantsar farincikin da tunda nazo duniya ban ta6a riska ba? .

Dariya momma tayi, tace  godiyar ALLAH ta wadatar da komai Muh'd, lallai yarona zai zama baba .

Galadima yayi dariya yana goge hawayen fuskarsa,  Momma bama Abie wayarnan .

Cikin tsokana tace,  nawa zaka biya? kasan mu yanzu komai Na kud'ine .

Sosai yasaka dariya, har jerarrun hak'oransa Na bayyana. Dogaransa duk sun saki baki suna kallonsa, duk da bajin maganar da yake sukeba, tunda suke da shi basu ta6a ganin yana dariya makamanciyar wannan ba, Sauban kan ai hotuna yaketa masa bai saniba.

 shikenan Momma, inhar baki had'ani da Abie ba kema kuwa d'iyarki bazata dawo India ba ashe? .

 a'a miyay zafi? indai takawa ne gashi .

Nanma dariyar Galadima yayi, Abie da tun d'azu yaketa murmushi shima saboda a Hans free momma tasaka wayar duk sunaji, a hankali yace Daddyn Unborn! .

Galadima baiji mi Abie ya fad'a ba, amma tabbas yana jiyo alamun motsi, da sauri yace,  Momma video call please  .



Mota ya bud'e ya shiga, Sauban ma ya k'araso dan kuma taya d'an uwansa murnar k'aruwar daya samu. tunda aka bayyana maganar cikin Galadima bai samu Kansa ba, balle su ke6e.

Motar yashigo shima, ganin video call Galadima ya had'a dasu Momma saiya matso kusada shi sosai yana d'aga musu hannu.

Momma tace,  ho autana ina ka shige wai? .

 momma ina zaki ganni nazama Abban Unborn .

Dariya sosai suka sanya, Galadima ya rankwashi kansa.

Wayar aka saka kusada Abie sosai, a hankali yace,  lallai wad'annan iyaye akwai zumud'i dai .

Basuji miya fad'aba. Amma sungane ta hanyar motsin la66ansa. cikin zaro ido Sauban yace  Abie!! . Sai kawai ya rungume Galadima ya fashe da kukan farin ciki.





Humm masu karatu, nabama kowa damar k'iyasta wannan farin cikin a zuciyarsa shima=��=� �.







&*&&*&*&&*&*&&*&



A lokacin da Galadima suke can suna waya dasu Momma Munaya ta farka, doctor Farida ta cire mata k'arin ruwan danya k'are.

Ta kalli doctor Farida tace  doctor Abbana fa? karki cemin dai Abbana ya mutu Dan ALLAH? .

Hannunta doctor Farida ta rik'o, fuskarta d'auke da murmushi tace,  gimbiyarmu Abbanki nanan da ransa, insha ALLAH kuma zai tashi, kedai kici gaba da masa addu'a kinji .

Kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace,  to zanyi fitsari .

Doctor Farida ta amsa da to, da kanta ta taimakama Munaya tashiga bayi, fitowa tayi tabata waje, saida ta gama sannan ta kuma taimaka mata ta fito.

 doctor 'yan gidanmu fa? .

Murmushi Dr Farida tayi, cikin tsokana tace,  Gimbiya Galadima yakamata ki fara tambaya ai .

Murmushi Kawai Munaya tayi, amma batace komaiba, Dr Farida tace  to bara Na musu magana .



Babu dad'ewa saiga 'yan gidanmu nata shigowa, yanda kowanne fuskarsa ke a washe sai suka bani mamaki, nakasa hak'uri nace,  Abba ne ya tashi? kuke farin ciki haka? .

 shima insha ALLAH zai tashi 'Yar albarka . Cewar innaro tana dariya.

Ni duk sun kuma d'auremin kai da addu'ar da sukeyi suna fad'in ALLAH ya inganta.

Mamansu Fauziyya tace minakeso akawo min naci.

Nace,  banajin yunwa mama, ni sonake ma Na kuma ganin Abba ..

 karki damu, Abba yana barci ne, kedai kisamu kici abinci babynmu yak'ara k'ato kafin ki haifo mana .

Ban fahimci maganar ta Fiddausi ba, Dan naga awajen akwai masu ciki da yawa, aunty Ramlah, aunty Khaleesat, aunty Hauwa'u, Siyama, Zarah, aunty Raihana duk cikinsu ya tsufa, haihuwa yau ko gobe.

Na kalli innarmu dake tsaye batace komaiba, murmushi namata, itama saita mayarmin, nace,  wai har yanzu Munuhiya ba a cire mata ruwanba? .

Mama Rabi'a tabani amsa da cewar  an cire, barci takeyi .

Cikin marairaicewar murya nace  ALLAH sarki Sweetheart d'ina, ALLAH yabaki lafiya .

Duk suka amsa da amin.

Doctor Farida tashigo tana sanar musu ga Galadima nan zai shigo.

'Yar rige-rigen fita iyayena suka farayi, kowa yana jin nauyin suruki ya shigo ya iskeshi, ni dariyama suka bani, nayi murmushi ina komawa Na kwanta.

Saida suka fita kaf sannan nafara jiyo takun takalminsa.

Idanu Na lumshe kamar mai barci.

Tunda ya shigo idonsa Na kaina, yacigaba da takowa gaban gadon, duk tunaninsa barcin gaske nakeyi, maimakon ya zauna saiya dafa gadon ya rankwafo kaina, da sauri da sauri zuciyata tafara bugu saboda kusantoni da ya keyi, fuskarsa daf da tawa tamkar zai had'e bakinmu, mikuma ya tuna saiya janye ya maida saitin goshina ya manna min kisses guda biyu a goshi da saman hanci.

Cikeda mamaki Na waro manyan idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, ya d'aga min gira d'aya.

Saurin kauda idanuna nayi gefe.

Shikuma yaja kujera ya zauna dab da fuskata yana murmushi.

Munja wasu seconds sannan yasaka hannunsa bisa kumatuna ya juyo da face d'ina inda yake, kin bud'e idona nayi Na kallesa, bai damuba yace  yalla6iya dama haka kike da saurin cafke Abu? .

Babu shiri Na waro idanuna kansa, nace  yalla6ai mina cafke? .

Idanunsa ya d'an jujjuya alamar tunani, saikuma ya kalleni, har yanzu hannunsa Na tallafe da fuskata, yace  uhuumm mima kika cafke? Na manta ma . Ya k'are maganar da d'age kafad'a yana ta6e baki.

d'an hararsa nayi ina tura baki, mutuminnan ya iya rainin wayo.

Yanzunma murmushin yamin, saikuma ya d'ora hannunsa saman shafaffen cikina mai kama da babu ko kayan ciki balle kayi tunanin akwai mutum.

Da sauri Na rik'e hannunsa ina fad'in  yalla6ai lafiya kuwa? .

Cikin basarwa yace  itace ta kawo haka, bakimin murna ba .

Nace,  Murna kuma? tami? .

Cikin d'age gira d'aya yace  Muhammad Sameer Saifudden yazam pah-pah .

d'auremin kai maganarsa tayi, Na yunk'ura a hankali zan tashi, mik'ewa yayi ya taimakamin Na zauna yana fad'in  yi da kula karkima jama'ar gari 6arna, dan akwai sarkinsu anan .

Waige-waige Na farayi, nidai banga kowa ba bayan mu biyun dake zaune, saina d'auka da kansa yake, na d'an ta6e bakina kawai.

Shima saiya ta6e bakin yana komawa ya zauna. kusan mintuna biyu duk mukai shiru.

Zuwa can nace,  nikam dai na dawo normal, kace musu su sallameni kawai .

Batare daya d'agoba yace  nafi buk'atar hakan, mi kikeso Sameer yamiki k'yauta da shi? .

 k'yauta kuma? akanmi?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login