Showing 33001 words to 36000 words out of 365757 words

Chapter 12 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1446

Duk mun rame mun zuge nida munubiya, dama gamunan bawani aukin kirkiba, ahaka muka cinye satin da abin yafaru.



Yau ta kasance lahadi, wasu a yaran gidanmu sunata shirin ziyartar gidajen amare, kaf sa'aninmu 'yan matan gidan sunyi shirinsu, Fauziyya, Fiddausi, Safara'u, Haleematu, amma ban da mu, Dan kogaya mana mu shirya ba'ayiba, saima Fauziyya Ce data tashigo da safe gaida innarmu take sanar damu wai mushirya zamuje gidajen amare.

Dagani har Munubiya bamuce da ita komaiba, sai 'yar dariya damukayi.

Koda suka gama shirinsu basu nememu ba, sai Fauziyya Ce tashigo danta mana magana akan mufito.

Turus tayi Dan ganinmu babu wani shiri, hasalima muna falo zaunene, Munubiya ta kwantar da kanta bisa cinyata ina kwance mata kai, innarmu kuma Na zaune gefe suna waya da mama Rabi'a, sai Aiyaan da Aryaan daketa faman buga game.

Hira mukeyi da Munubiya akan wasu write-ups datake dubawa a Instagram da akayi akan maganarmu da galadima, cikin damuwa take karanta writeup d'in, shiyyasa bamuga shigiwar Fauziyya ba saida tayi magana...

 wai sisters kuna nufin ma ko shiryawa bakuyiba? .

Gaba d'aya muka kalleta, nayi murmushi ina fad'i  kiyi hak'uri Fauziyya, kutafi kawai, har yanzu fita bata kamacemu ba, dan abubuwa basu gama daidaitaba tukunna .

Cikeda damuwa ta gyad'a kai, jiki a sanyaye tace  shikenan saimun dawo .

 ok to Ku gaida mana amare .

Kanta ta jinjina nanama tana ficewa.



Munubiya tace,  ALLAH Sarki Fauziyya, itadai tana sonmu .

Nad'an murmusa ina taje mata Wanda Na tsefe,  Munu.... nima ina k'aunar Fauziyya wlhy itada mamansu, sune kad'ai suke sonmu agidannan, Na tabbata wannan fitar dama ba'a sota damuba, itace kawai taketa k'ok'arin taga munje d'in .

 wlhy hakane sweetheart  .  cewar Munubiya .



Innarmu dai tanata waya, Dan haka batace mana komaiba.....







&&&&&&&&&



Lokaci na gabatowa yay shiri yabar hotel d'in, zuwansa airport babu dad'ewa jirginsu yad'aga, sun tsaya a Dubai Abu-dhabi sukayi hutun 1hour sannan suka nufi India.

Tunkan jirginsu ya sauka Sauban da Samha sukazo d'aukarsa.

Dan haka yana fara taka matakalar jirgin suka hangosa, cikeda jin dad'i suka nufo gareshi.

Duk da fuskarsa babu walwala hakan bai hanasu nuna farincikin ganinsa ba, shima dai yayi farin cikin ganinsu, duk da kwanaki 4 kacal kenan da barinsa k'asar.

Sauban ya kar6i bag d'in hannunsa yana fad'in yaya welcome .

Kansa ya shafa yana lumshe ido alamun amsawa.

Samha ma tace  Wellcom back Uncle Sam .

Ahankali ya furta Thanks you dear, ya school? .

 Alhmdllh Uncle, ya kabaro Nigeria?  .

Murmushi kawai yayi batareda ya amsa mata ba, yasan surutun Samha bamai k'arewa bane, yana amsa wannan wata zata jeho masa.



Sauban ya bud'e masa back seat ya zauna, sannan yarufe shi yakoma mazaunin driver, Samha Na gefensa.

Idonsa ya lumshe ya maida Kansa ya jingina da kujera.

Wani madaidaici Gida suka isa, Wanda baza'a kirashi k'aramiba, sannan ba k'ato baneba, sai dai muce tsaka tsaki.

Samha ce tafita da kanta tabud'e gate d'in, Wanda ana ganin komai dake farfajiyar gidan ta jikinsa daga waje. Sauban ya ida shiga da motar, kusada wasu motoci uku yay parking, Samha data k'araso tabud'ema Galadima yafita.

Kusan atare suka shiga falon gidan, yana gaba suna baya.

Masha ALLAH nafad'a saboda ganin tsaruwar falon, sai dai shiru gidan alamun babu kowa a ciki.

Ya zube bisa rukunin kujerun farko dasuka kasance golden color and white. Isaka yad'an turo daga bakinsa sannan ya kalli Sauban dake shirin zama shima.

 yanaji gidan shiru? inasu Momma ne? .

 duk suna hospital, har jakadiya ma, zamu tafi d'akko kanema Aunty Mimi tatafi itama, dama ita kad'aice agidan saboda mu muna school  .

 Ok, ya jikin Abie? .

 hummm da sauk'i yaya .

 mik'ewa yayi yana guntun murmushi, tunda yafara girma yafahimci mahaifinsa Na kwance yakejin idan antanbaya Momma jikin Abie tana cewa da sauk'i, amma shi shekaru kusan 25 Abie Na kwance amma shifa baiga wannan sauk'inba, kawai suna dai fad'ane, sauk'i d'ayane zai iya cewa yagani shine magana da idanu da Abie keyi kawai.

Da wannan tunanin ya haye steps d'in benen, yana tafiya yana sasaauta tied d'in wuyansa. ahaka harya k'arasa d'akinsa.

Komai needs kamar yanda ya barsa, (kullum ne babu fashi sai Samha ta gyara d'akin) Komai a d'akin fari ne, sai golden dasuka kasance d'ai-d'ai. d'akin yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshin turarensa daya manne yakeyi, gakuma na air fresheners, saiya had'u yana bada wani ni'im taccen k'amshi. kayansa yashiga cirewa d'ai-d'ai yana sagewa jikin hanger. wanka yashiga sannan ya gabatar da sallan data riskeshi a hanya .........





&&*&&*&&*&&*&&





Da daddare muna zaune munacin tuwo saiga kiran Abba yashigo wayar innarmu, tana d'agawa yace ta turo masa mu.

To kawai tace ya yanke wayar.

Kallonmu tayi ad'an sanyaye, tace  idan kun gama cin abincin kuje abbanku Na kira .

Daga ni har Munubiya sai da gabanmu yafad'i, jiki a sanyaye muka amsa da  to innamu .

Kasa cigaba Dacin abincin mukayi, dole muka ajiye kawai mukaje muka wanko hannu..................
'<���







>��ko wane kira kuma Abba yakema su Munaya=��?.







Barkanmu da dawowa '<���, ina fata duk kuna cikin k'oshin lafiya?=��>��<���.



To gashinan Na k'ara yawan page Masu k'orafi=���&<���
@&�&<���
@&











*_ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=�O�<���=�-�

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���1� 3�





.......Mun d'anji sanyi a ranmu, ganin kiran bamu kad'ai baneba, hardasu Safara'u Ashe, waje muka samu muka zauna, sannan muka gaidasu.

Fiddausi kad'ai ake jira, itama babu jimawa sai gata ta shigo da sallama, duk muka amsa, ta gaida su Abba.

Falon yay tsit Na mintuna biyu, sannan Abbanmu yay gyaran murya, kallonmu yake mu duka cikin nazari, ganin muduka mun hallara yace  mun kiraku nan ne saboda dalilin abinda yafaru kwanan nan, hankalina yakasa kwanciya da zamanku a gabanmu, mun yanke shawara nida 'yan uwana zamu aurar daku duka kawai, kowace saita cigaba da karatunta a d'akinta, muma hakan zai sama mana kwanciyar hankali. dan haka kowacce saita sami mai zuwa wajenta ta sanar masa munason ganin magabatansa inhar da gaske yakeyi .

gaba d'aya muka amsa da to abba kanmu ak'asa.

Wasunmu murna suke da hakan, amma banda ni da Munubiya, dan bamuda wasu tsayayyu a hannu, bawai samarinne bamu dasuba, a'a wad'anda zamu kawo amatsayin Na aurene matsalarmu.

Maganar Dady ce ta katsemin tunani, danaji yana fad'in su sutashi suje, amma ni Na tsaya.

Haka suka fice suka barni, duk tsoro yakuma cika zuciyata. bayan fitarsu baba k'arami yanuna min gabansu alamar Na matso.

Tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki haka natashi Na isa gabansu, na zauna kaina ak'asa.

Baba k'arami yace  Munaya! .

Muryata Na rawa Na amsa da  na'am baba .

Ya gyara zamansa sosai,  Munaya na sanki bak'ya k'arya, kifad'a min tsakaninki da ALLAH miye had'inki da Galadima? .

Gabanane yafad'i daaam!, nai k'ok'arin had'iye kukan daya taho mini  wlhy Baba banida had'in komai dashi, hasalima ban ta6a saninsaba sai awajen hawan sallah, shima ba ganin fuskarsa na ta6a yiba, sai kuma randa mukai karo dashi a filin idi ina neman su kamal, kuma wlhy aranar hak'uri kawai nabashi, koma amsamin baiyiba yatafi, ni banma san shibane alokacin .

 amma miyasa aka buga hotonku kuna cikin plaza d'insa? .

 Dady kuyi hak'uri, tabbas nasan munyi laifi anan, amma Ku yafemin, dan nasan da bamuje plaza d'inba a daren da k'ila hakan bai faruba, amma wlhy abinda yafaru shine...................., cikin nutsuwa ta zayyane musu komai, saidai batace Munubiya ce zata fad'inba, tace itace.

Koda basuga ainahin abin da idonsu ba sai zukatansu sukayi sanyi, baba k'arami yace  to ALLAH ya k'yauta, wannan akwai wani Abu daban dabamu saniba acikin lamarin, ALLAH ya warware komai cikin sauk'i .

Duk mukace amin.

Dady yace,  Munaya! bisa hak'uri damukaita bama yaya kin sami sassauci akan sati 2 daya ce ki fidda miji, yanzu saiki nutsu ki kawo kamar sauran 'yan uwanki, insha ALLAH bayan babbar salla zamu aurar daku gaba d'aya kawai, ALLAH yayi muku albarka kinji, kucigaba da kare mutuncinku, sannan Ku koma zuwa makaranta tunda abin ya lafa .

Kai na gyad'a sannan nayi godiya.



Na iske innarmu da Munubiya jigum-jigum a falo suna jiran dawowata, nasami waje na zauna jikina a sanyaye.

Innarmu tace,  miya faru kuma? .

Guntun murmushi nayi INA share kwallar data zubomin,  babu komai innarmu, sun tanbayeni gaskiyar abinda yafaru ne, sannan since sun janye maganar sati biyu nafiddo miji da sukace nayi. nima za'a had'a danawa zuwa bayan salla kamar su Munubiya, kuma since mukoma makaranta ..

Daga Munubiya har innarmu ajiyar zuciya suka sauke,  to Alhmdllhi, ALLAH yabaku mazaje na gari .  cewar innarmu .

A zukatanmu muka amsa mata da amin.



Washe gari.

https://2gnblog.blogspot.com/

Mukayi shirin zuwa makaranta, gudun abinda zaije yadawo sai muka saka nik'af dagani har Munubiya kamar yanda innarmu tabamu shawara muyi.

Alhmdllh tunda muka fita bamuci karo da abinda ya Sosa zuciyarmu ba, saboda fuskokinmu arufe suke.

A ajima babu Wanda ya shaidamu sai Bilkeesu, nanma dai munyi mun fito lafiya babu wata damuwa. amma saboda a d'ar-d'ar Muke bamu wani sakeba, ana fitowa lectures muka nufi gida.

Haka muka cigaba da zuwa makaranta kulum fuska arufe, ko cikin anguwa za'a aikemu saimun saka nik'af, dan yanzu fuskokinmu sunrigada sun zama sannanun fuskoki....





https://2gnblog.blogspot.com/

&&&&&&&&&&



Yana gama kimtsawa yafice, ko abincin da Samha ta shirya nasa bai sauraraba, kai tsaye yanufi Hospital d'i. da Abie ke jinya.

da jakadiya yafara cin karo tana rik'e da Khaleel a hannu, khaleel yakwace yataho da gudu yana fad'in  Uncle oyoyo .

Hannayensa ya bud'e masa yafad'a jikinsa, ya shafa kan yaron yana fad'in  my boy ykk? .

 lafiya Uncle Sam... yaushe kadawo? .

Murmushi Galadima yayi, yad'an ja kumatun khaleel  to maganatu yau na dawo .

Dariya yaron yayi, zai sake joho wata maganar Galadima ya d'ora yatsansa akan bakin yaron alamun yayi shiru. Shirun kuwa khaleel yayi dan yasan halin Uncle Sam.. saraii.

Jakadiya ta rissina tana gaidashi, amsawa yayi fuskarsa da 'Yar fara'a, ya tambayeta ya jikin Abie.

 jiki Alhmdllh ranka ya dad'e .

Kansa kawai ya jinjina mata yay gaba rik'e da hannun Khalel.

Da sallama ya shigo d'akin da Abie ke jinya, d'akine babba kamar Bana asibitiba, daka gani Kasan anyisane saboda manyan mutane irinsu, Momma na zauna akujerar gaban gadon da Abie ke kwance, gadon Kansa bawai ainahin gado bane na asibiti, duk wasu na'urori ne ajikinsa, da alama sune suke taimakama jikin Abie d'in, k'umba Momma ke yanke masa.

Aunty Mimi na zaune bisa kujerun da aka shirya a gefe tamkar falo, System Ce agabanta tana danne-danne.

Sallamar Galadima yasata d'agowa tana murmushi,  My k'ani oyoyo tafad'a tana ture system d'in daga cinyarta.

Murmushi yamata shima, cikin maganarnan tasa ta k'asaita maikama da anmasa tilas yace  my dear aunty barkanki .

Hannu tasa tad'an bigi damtsen hannunsa, cikin wasa tace barka zakace ba bagyka ba .

Shafa Inda tad'an bigesan yakeyi yanda 6ata fuska kamar wani k'aramin yaro,  ALLAH akwai zafi aunty Mimi, wai har yanzu ban girma da buguba awajenki? .

 tab ai da sauranka, sai randa kayi aure zan daina .

Bakinsa ya ta6e yak'arasa inda Momma take yana fad'in,  aiko k'yadad'e baki barinba kenan .

Momma dake murmushi saboda drama d'in tasu ta kalli Abie da shima fuskarsa take a washe alamun yayi farinciki da ganin d'an nasa.

Gabansa yaje ya durk'usa, saitin Face d'insa, ya saka hannunsa cikin NASA fuskarsa d'auke da murmushi yace,  my Abie barka da rana .

Da idanu Abie ya amsa masa, dan sune bakin maganar yanzu.

Yakuma masa magana da ido alamar yaka barosu?.

Murmushi Galadima yayi na takaici, sannan yace,  mai martaba na gaidaka, shima zaizo nextweek .

Farin cikine Yakuma fad'ad'a a fuskar Abie, dasu sukasan yanayinsa, sukad'ai zasu iya fahimtar farin cikinsa ko damuwarsa, musamman ma Momma.

Momma dake kallonsu tayi murmushi, Galadima ya maida kallonsa gareta,  Momma na yana sameku? .

 Alhmdllh Muh'd, yaka barosu? .

Baki yad'an ta6e sannan yace  lfy lau, ya jikin Abie? .

 jiki Alhmdllhi, dan randa ka tafi yatsun hannun damarsa sund'an motsa .

Da Sauri Galadima yace  da gaske Momma? yay maganarne yana kallon hannun Abie d'in, sannan cikeda farin cikin ya sumbaci hannun yana fad'in Alhmdllh ala kulli halin, ALLAH yabaka lafiya my sweet Abie .

Lumshe idanu Abie yayi farinciki na k'ara fad'ad'a a face nashi, aunty Mimi da momma da jakadiya suna kallonsu cikeda tausayi suka amsa da amin. khalel yata6a kafad'arsa, juyowa yayi yana kallonsa. yaron yakai hannu yana sharema Galadima hawayen dasuke kwance a kumatunsa. galadima yajawosa ya rungume yana sumbatar kan yaron, fuskarsa d'auke da murmushi.





&&&





Yau mune k'arshen tafiya school, saboda lectures d'in yamma ne damu, Fauziyya kuma batada lafiya bazatajeba.

Kasancewar abubuwa sun kuma lafawa yau sai bamu saka nik'af ba, amma yana rik'e a hannunmu idan mun shiga cshool zamu saka.

Mun fito bakin titi muna jiran taxi ko napep saiga wata bak'ar mota wulik ta faka agabanmu, dagani har Munubiya d'auke kanmu mukayi gefe.

Mai motar ya sauke glass d'in yana kallonmu, sallama yayi mana, Munubiya ta amsa, nikam koma kallo bai isheniba.

Ganin haka saiya bud'e motar yafito, matashin saurayine bak'i k'yak'yk'yawa mai yawan fara'a. Yace,  haba 'yan mata, babu fad'a miya kawo gaba .

Cikeda tsiwa nace  sai aka cemaka mu 'yan matane? to matan aurene .

Murmushi yayi, sannan ya gyara tsayuwarsa,  dear hakan ma dakikayi yakuma tabbatar min da Bahaka baneba .

d'an hararsa nayi na d'auke kaina, danni yanzu maza duk haushi suke bani wlhy.

Dariya yayi,  oh sweety karkisa na sume mikifa a titinnan .

Ganin yana neman shiga hancinmu yasani jan hannun Munubiya muka bar wajen, k'yalemu yayi Yakoma mota ya zauna. har muka sami abin hawa yana kallonmu. haka yayta bin mai napep d'in har k'ofar makaranta, daga nan kuma bamusan ya akayiba mudai muka shige.



Kwana biyu da faruwar haka muna wanki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login