Showing 273001 words to 276000 words out of 365757 words

Chapter 92 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1509

zuwanta ba, to mizaisa kuma zuwansu duniya yazama salon tauye hak'k'ina? Na amintane da aurenka domin warware k'ullun da akaimin da wanda yake kan mahaifina, bawai dan bansan y'ancin kainaba ko darajata, idan har nice a matsayin Amaturrahman zakaso wani ya aureni a matsayin auren shekara d'aya ko biyu domin cikar wani burinsa ya rabu dani?, addininmu da al'adarmu duk basu koyar damu hakaba, anayin aurene domin ibada, saboda bautar ALLAH ne, sannan ana ginashine bisa tausayi da rahama, inhar zuciyarka bazatayi dad'iba a matsayinka na mahaifin Amaturrahman idan hakan ace akanta ta kasance, to ya kake tunanin randa nawa mahaifin yasan gaskiyar matsayin nawa auren zaiji?, tunda nataso nake d'and'anar zafi da d'aci na zamantakewar rayuwar gidan yawa, taya zanso saka rayuwata a walagigin kila wa kala, na shigo wannan yak'inne domin neman y'ancin kai badan ribantuwa da ganima ba, amma lokacin dana wayi gari da abinda ban shiryamawa ba a cikin jikina haka na hak'ura na kar6a da hannu biyu saboda k'ok'arin cinye jarabawa, miyasa kakeson yin wasa da rayuwatane wai? Duk motsi dai yaranka! Yaranka! Karka manta nimafa y'ar wasuce, kamar yanda kakeji haka suma sukeji akaina, inason nima nayi aure na zauna tamkar kowacce mace a gidan mijinta, na fidda hak'insa da ALLAH ya wajabta min, shima ya fidda min nawa da ALLAH ya wajabta masa...... .

Hannu ya d'agamin alamar ya isheshi haka, yakuma matsowa gabana cikeda izza yace,  mikikeso yanzun? .

Nace,  sanin matsayin aurena, inhar yaranka ne zan muku sadakar shayarwa na wata shida na yayesu nayi aurena da mijin dazai soni ya k'aunaceni domin ALLAH .

Bakinsa ya ta6e yana cije lips, jijiyoyin kansa duksun mimmk'e saboda 6acin rai, cikin takaici yace,  Yarinya har abada babu shegen namijin daya Isa na k'etara gona shima ya k'etarata, koda kuwa wannan gonar ta jinginace, ko ayanzu nabar duniya wani yayi hakan ban yafeba, duk gonar dana ra6a tawace ni kad'ai koda banyi noma a cikinta ba, wannan yazama first and last da zaki kuma kawomin irin wannan maganar, kodan kinga ina k'yaleki ne shiyyasa kike d'aukata wani sauna kiringa min zancen wani banza can daban, Munaya karki yarda na nuna miki a salin true color d'ina wlhy, ina kuma gargad'arki a karo na k'arshe .  ya k'are maganar da bugamin yatsunsa biyu saitin fuska ya fice abinsa .



Baki na ta6e ina bin inda yabi da harara, sannan na saka gyalena na goge hawayen dake zarya a kumatuna nai kwafa na fice abina nima nabar yaran.







**********



Tunda ya fito Muftahu ke binsa da kallo, harya bud'e mota ya shiga baiko kalli Muftahun ba shi.

Dama shine ya kawoshi, amma yana ajiyeshi ya koma saboda wani aiki daya bashi, dawowarsa kenan yana k'ok'arin kiransa yace zai shigo su gaisa da Munaya shine yafito a fusace.

Baice dashi uffanba ya bud'e motar shima ya shiga ya tada suka tafi, saida sukayi nisa da tafiya sannan Muftahu yace,  Ranka ya dad'e wai mike faruwane? .

Shiru yamasa yak'i tankawa, shima Muftahu sai yaja bakinsa ya kulle ya cigaba tuk'insa.

Sai jera tagwayen tsaki yakeyi, Muftahu ya kuma kallonsa sannan ya maida hankali ga tuk'insa, ya kuma rik'e sitiyarin yana fad'in  ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, idan kana ganin bazaka juri zuwanba kace ta dawo mana kawai .

Cikin jan wani tsakin yace,  inhar taci gaba damin zancen wani wawa lallai zan datse harshenta wataran .

6oyayyan murmushi Muftahu yayi, a zuciyarsa yana jero hamdala wa ubangiji, dan babu abinda yake hange tattare da galadima sai tsantsar kishin matarsa, dukda baisan miya had'asuba yaji dad'in hakan, koba komai yanzu ya fita daga damuwa da fargabar rabuwar wannan auren. cikin son kuma fahimtar wani Abu yace,  to amma ranka ya dad'e yazamuyi idan lokacin rabuwarku yayi kenan? Kasanfa alk'awarin da mukai mata .

 Oho! Maka . Galadima ya fad'a cikin tsananin fusata.

Da k'yar Muftahu ya iya had'iye dariyarsa, bai sake cewa komaiba har suka isa gidan baffi, dan karya mazgeshi a banza. Muftahu ya fita domin nema masa ison shiga ciki, a lokacinne yasamu yay dariyarsa mai isarsa, lallai Galadima akwai kishi, tashin hankali, irin wannan ajiyar zuciya haka.







*********



Tunda na shiga Munubiya take bina da kallo, ta ce,  ina yaran? .

 Suna can .  nafad'a ina shigewata ciki .

K'ala bata sake cewaba tafita abinta.



Har dare ina fushi, nak'i kula kowa, innarmu yitai kamarma batasan inayiba, dukda batasan mike damunaba, Munubiya ma shareni tayi, sai laraba Ce ke tambayata kodai banajin dad'ine?, nace a'a.





__________



Saida Muftahu ya raka Galadima har falon Baffi sannan yace zaije ya dawo kafin su gama.

kansa kawai ya d'aga masa amma bai tankaba.

Fitar Muftahu babu dad'ewa baffi ya fito shima, zama yay idonsa akan Galadima, dan ganinsa cikin damuwa,  d'an baffi miya farune haka? .

Galadima yafara k'ok'arin saita kansa cikin k'ak'aro murmushi yace,  Babu komai Baffi .

Duk da bai gamsu ba saiya k'yaleshi, dan maybe ba huruminsa baneba, yace  Alhaji Rabilu yakai maka bak'o ko? .

 Eh d'azunnan muka rabu dasu, abindama ya kawoni kenan, dan ina ganin insha ALLAH mun sami dukkan bakin zaren, zan fara aikina kawai .

��

Murmushi baffi yayi yana gyara zamansa, yace,  eh to ansami bakin zare kuma ba'a samuba, dan yanzu binciko Wanda Camera d'in take hannunsa shine babban aikin dake gabanmu, dan itace babbar hujjarmu bayan d'unbin hujjoji da muke dasu a k'asa .

Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kai,  hakane Baffi, amma akwai dai wasu y'an bayanai danake dasu a hannu yanzu haka, sai dai banida tabbacin dai-dai ne? Kokuwa akasin haka, amma kama SD da mukayi shine zai fito da gaskiyar hasashen nawa .

 To shikenan, ALLAH yasa muji alkairi .

 Amin, saidai ni a bayanin Baba Rabilu akwai abinda har yanzu yakemin rawa a zuciya .

 tofa, minene kenan? .

 Maganar siyasa dayacemin ya shiga a wancan shekarun, bayan kuma lokacin mulkin sojane, kenan wace siyasa sukayi? .

Baffi yay murmushi,  wato abinda na fuskanta anan shine, yasako kalmar siyasa ne domin mu mufasa sauran bak'in da kanmu, amma tabbas a wancan lokacin babu wata jam'iyyar siyasa, wayema ya Isa d'aga murya akan mulkine? Saidai bincikena ya nuna Dalilin kafa Group nasu tanderu yanada nasaba da son kafa mulkin farar hula, wato sunason mulki yabar hannun sojoji kenan, saidai a 6oye sukeyin dukkan abinsu, har suka ringa jawo ra'ayin mutane mabanbanta a cikin tafiyar tasu, abinda na kasa fahimta nima shine, shin sunjawo Alhaji Rabilu ne dansu tabbatar Camera na hannunsa? Kokuwa shine yakai kansa garesu domin lek'en asiri? Dole cikin biyunnan a samu d'aya, kodan yunk'urin kasheshi da suka saka Darma yayi .

Galadima dayay shiru yana fassara zancen Baffi dak'i-daki ya shiga jinjina kansa alamar gamsuwa da bayaninsa, zuwa can yace,  Baffi ka bani kwanaki biyu zanyi bincike insha ALLAH, dan zan tattauna da SD da kuma Harun, sannan akwai yaron da aka saka yay aikin da aka buga a jaridarnan, shima inason yazo hannuna insha ALLAH  .

 ALLAH ya cigaba da dafa maka, Yakuma tsareka da dukkan sharri, lallai ka ringa kulawa, dan yanzu dukkan wata hanya da zasubi domin cuta maka sun tanadeta, karka d'auka suma basa bibiyar lamarinka kamar yanda kake bibiyar nasu, dan ranar naga Alhaji Abdul- Naseer da wani masanin Computer, saidai shi bai ganniba, nasha jinin jikina kwarai da gaske, amma nikam inamason tambayarka, minene alak'ar Surukinka da senator halluru ne? .

 kamar dai abokinsa ne baffi .

 Ok! Ok! To lallai ka sanar masa ya lura, dan Senator Halluru yaronsu tanderune, za'a iya bi ta hanyar surukinka a 6ata mana aiki, tunda sun san akwai alak'a tsakanin kai da shi .

 wannan gaskiyane Baffi .

Sun cigaba da tattaunawa akan matsalolin da ayanzu zasu fuskanta, baffi na kuma bama Galadima dabaru a shara'ance Wanda bazai aikata abinda shima zai rufta ba.



Sai dare ya koma masarauta, yinin yau gaba d'aya a tsaye yayisa, shiyyasa duk jikinsa ciwo yake masa, yanayin zirga-zirga amma ba irin wannanba mai cikeda cajin kwakwalwa da rikitar tunani. Ga maganganun Munaya dake cin ransa, ya tabbata duk gaskiya ta fad'a, hakan datake yana kuma tabbatar masa da tasan darajar kanta, inda watace shiru zatayi sai yanda yaso yi da ita, duk kuma abinda zai mata koda Mara k'yaune zata shanye saboda kasancewarsa d'an wani, amma duk da kasantuwarta mace kuma wadda take k'ark'ashin mulkinsu ALLAH bai sakama zuciyarta tsoro ko kwad'ayi ba, itadai kullum burinta shine asan darajarta da kimar ahalinta, sa6anin y'an matan yanzu da duniyar Ce kawai burinsu da son ganinta a tafin hannunsu, auren mai kud'i ko mulki, mai k'yau ajin farko, na nunama k'awaye da yin alfahari a duniya, yasan darajarta kona iyayenta wannan ba matsalarta bace, yanada addini ko kula da addinin shiyya Sani, son gaskiya yake mata ko albarkatun jikinta yakeso batada matsala, ya zube a kujera yana sauke tagwayen numfashi.

Sauban dake zaune yana kallo yakuma kallonsa, yayansu na bashi tausayi, saidai shi taurinkai da rashin yarda da kowansa ke had'ashi dashi, amma ta wani fannin yakan kalli hakan a matsayin gaskiyarsa, dan massarautar tasuce abar tsoro, ba kowane abin yardaba, yanda zaka tantance na kirkin shine mai wahalar kuma.





*******





Na kasa hak'uri da danne maganganun Galadima, hakanne ya sakani yanke shawarar tambayar Munubiya kota Sani, saida mukai shirin barci dukda sharenin da takeyi nadai danne nawa Fushin na zauna kusa da ita tana shayar da Meenat data tashi. Kan yarinyar na shafa sannan nace  Munubiya in tambayeki mana please? .

Kamar bazata kulaniba sai kuma ta kalleni. Tace,  Ina saurarenki .

Ajiyar zuciya nayi ina gyara zamana, nace,  dan ALLAH idan namiji yace gonarsa mi yake nufi? .

Jimm tayi alamar tunani, ta kwantar da meenat tana fad'in  Matarsa .

Da mamaki na kalleta, yayinda wani sanyi ya ratsa raina, amma na danne.......

Ta katseni da fad'in  Munaya ki fito fili ki sanarmin abinda ke faruwa, kinsan banason kwana-kwana, sirrinki keda mijinkine kawai a rayuwa bazanso saniba, domin ALLAH ya haramta bud'e wannan, saikuma yankin sirrinsa na rayuwa Wanda yarda da matarsane kawai zaisa ya fad'a mata, shima wannan kirik'e masashi, amma Munaya na fuskanci har yanzu babu dai-daito tsakaninki da mijinki, duk da kin sanarmin da manufar aurenku nazata darajar zuri'ar data shigo tsakkiyarku zai kawo muku sasanci Ku manta da wani auren Contract, duk da na fahimci mijinki jinin mulki na yawo a jikinsa, danne Abu a rai da basar dashi tamkar jinin jikinsa yake, kekam nasan halinki mutumce maison a damu da ita, sannan a nuna mata komai a aikace da furucin baki, kema danaki jinkan Wanda bansan gidan uwarwa kika samoshiba, amma mike wakana a duniyar aurenki? Mikuma kuke shiryawa keda surukarki? .

Shiru nayi nakasa magana, dan banso fitar da wannan sirrinba har zuwa lokacin da Momma ta bani, duk da nima rashin sanarma y'ar uwata yana damuna, dan bamu ta6a 6oyema juna wani abuba, ko akan aurena daga baya kasa daurewa nayi na sanarmata, duk da na 6oye matanne saboda gargad'in da baba mai kanwa yamin......

Kwanciyarta tayi tana cewa,  idan kinga bazaki iya fad'aba kibar abinki arai yayta cinki, daga k'arshe idan kika rufta auren ya tsinke kekika Sani, kinsandai minene wannan gidan da irin mutanenen cikinsa, dama kullum burunsu kenan .

Idona cike da kwalla na kamo hannunta,  kiyi hak'uri sweetheart tashi muyi magana .

Munubiya taiyi kamar ta shareta saikuma ta tashi tana share mata hawayen dake bin fuskarta.

Ta gyara zamanta tana fad'in  wato Munubiya.................>�+�
'<���









Kumuje zuwa page nagaba my guys=� �>�)�.

















ALLAH ya gafartama iyayenmu=�O�<���=�-�













ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���





BOOK 3�=�I�<��ߠ1� 3�





.............. Wato Munubiya abinda yasa kikaga inata 6oye miki shine, bansan manufar mahaifiyarsa ba kai tsaye, nidai bayan tabani tarihin



masarautarsu takuma rok'eni nabama Galadima gudunmawa wajen saka idanu akan motsin kowa dazai mu'amulanceni, abinda ta lura shi yafi maida hankalinsane ga mak'iyan waje, gani yake kamar a masarautarsu babu mai iya cutar dashi. tace min Galadima bashi da yarda ko kad'an, sannan mutumne mai zama akan ra'ayin kansa, tankwarashi sai ita da baya iya bijirema umarninta .

���� Na damu kwarai da gaske Munu.. Dan rayuwa da irin mai wannan halin yanada wahala, musamman mutum mara yarda, wlhy nadad'e a gidannan bai bar zargin an turoni Na cutar dashi bane, saida Momma tafara koyamin dabarun zama dashi, tace nadaina jin tsoronsa, inhar yafad'amin magana Na daurema zuciyata Na dinga maida masa murtani, a tak'aice dai nake masa tsiwa. A lokacin da taimin wannan maganar abin yaban mamaki, Yaya uwa za tace aringama d'anta rashin kunya ko rashin raga masa?, kema kinsan bawai bazan iya baneba, amma yanamun matuk'ar kwarjini, bansan kuma miyasaba nakejin shakkarsa a zuciyata, har gobe idan yamin Abu zan maida masa murtani wlhy saina dage saboda tsoro. Saida zamanmu yad'an fara nisane Na fahimci abinda take nufi, inda bana nuna masa banida tsoroba zansha wahalar zama dashi, sannan bazai ta6a aminta dani ba ya saki jikinsa, zaita d'aukatane a y'ar lek'en asiri, Dan babu abinda ya tsana irin karinga masa Abu kana nuna tsantsar biyya da kwantar masa dakai, shi a wajensa kazo cutar dashine kawai. Maganar zuwana wanka itace tadage akan sainazo, sannan tace duk zuwan da zaiyi wajena Na nuna masa cewar.��nifa bazan koma gidansa ba, dan bazan iya da hallayarsa ba, tadai nunamin dukkan dabarun dazanbi Na dinga zungurinsa da zancen, to ni wlhy ban fahimci manufartaba, tunda nasan babuma Wanda yasan mafarin ginin auren namu, daga ni sai shi, saikuma ke dana sanarmawa. yau kuma namasa zancen rabuwarne da nuna masa zan shayar dasu Abdurraheem ne Na wata shida nayi aurena nima, shinefa yahau kaina da bala'insa, wai babu wawan daya Isa shi ya k'etara gona wani yako ra6eta, koda kuwa ace gonar ta jinginace, inkuma hakan ta faru kobaya numfashi bai yafeba .

������Munubiya ta zaro ido waje Dan mamaki, saikuma ta tuntsure da dariya harda rik'e ciki, galala nayi ina kallonta, danni banga abin dariya ananba.

����Saida tayi mai isarta sannan ta zauna dak'yau tana fad'in  yi hak'uri sweetheart, wlhy mijinkine yabani dariya, amma anya kuwa mahaifiyarsa batasan manufar aurenkuba? .

������� Ta ina zata Sani Munu.., shidai wlhy nasan bazai fad'aba, Dan nakula yanada masifar zurfin ciki, balle yasan abinda yay bamai k'yau bane, tunda a al'adarmu da addininmu hakan ba tsarinmu bane, nadad'e ban iya fahimtar matsalarsaba, saikuma naita tambayarsa yamin banza, sai daga bayane naringa Neman dabarun samo kansa harya sanarmin da damuwarsa .

��������� Eh bank'i ta takiba, amma a ganina koshi bai fad'a mataba kina ganin Muftahu bazai fad'aba? Nifa tun pills daya zuba muku nafara zargin anya bada k'yak'yk'awar niyya yayi hakaba? .

������ Kai Munu.. ALLAH bana tunanin haka, gani nake kawai itama da tata manufar, Dan batason halayyarsa ta shiru-shiru d'innan da k'untata kansa dayake akan yawan damuwa kodan ciwonsa, Dan tace min ciwonsa Na yawan motsawa a baya saboda yawan shiga damuwa da yakeyi, gashi bazai yarda kowa yasan matsalarsa ba saboda tsatstsauran ra'ayinsa, itakuma bataso Dan abaya yanda kikaga Sauban k'animsa da faran-faran haka shima yake, amma tunda ya fahimci miya kwantar da mahaifinsa saiya canja musu gaba d'aya, maganar ma saiya gadama idan kayi yake amsaka, abinda Na lura yanzu kuma wannan abun yarigada yazame masa jiki gaskiya .

��������� dukna fahimceki Munaya, amma abinda Na lura kamar wata alak'a mai k'arfi da kusanci takeson ginawa tsakaninki dashi, Dan babu wata uwa dazatasa matar d'anta ta ringa ma yaronta rashinkunya, itakuwa tasan halin d'anta ciki dabai, tanada dabarun dazata d'oraki domin shi su k'ayatar dashi harya ringa kallonki a matsayin mata ba auren wucin gadiba,��dukkan maganganun daya fad'a miki d'azun wlhy Na mutumne mai nuna tsantsar kishi, ALLAH ma yasoki dabakizo da kumburarriyar fuskaba wlhy . ta k'are maganar da sanya dariya.

����Harara Na zuba mata ina fad'in  nikuma kamar wata sokuwa saina zauna ya dakeni, danma gaskiya shiba mutum bane mai yawan saurin hannu, saidai k'asaita da shariyar tsiya, kaita magana yayi tamkar bai jikaba .

������� Yo Sweetheart ai mulkin kenan ko, wannan shine ake kira sarautar, idan bashida wannan izzar da k'asaita lallai baicika jinin basarakeba, shi nashi ai da sauk'i tunda yasan darajar d'an Adam. Amma lallai ki godema ALLAH da samun suruka irin wannan, to amma ke kina sonsa yanzu? .

�����Harararta nayi, nazame Na kwanta batareda Na bata amsaba, ta d'akamin duka a cinya tana fad'in  Munafuka kema sonshi kike, wannan jan ajin naku dukshi ke cutarku, shi mulki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login