Showing 342001 words to 345000 words out of 365757 words

Chapter 115 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1535

yasani fad'in,  Toyi hak'uri bazan sakeba .

 Harkin karaya kenan? .

 Ba doleba, kamun nakane ai bamai sauk'iba .

Dariya sosai tabashi, amma ya had'iye abunsa kawai yayi murmushi yana cizar lips.

Munaya tace,  Wato a rayuwa duk d'an Adam zaka sameshi dawata d'abi'a data zame masa jiki .

Kallona yayi da alamar tambaya, amma baice komaiba.

Mik'ewa nayi tsaye ina cire hijjab da fad'in,  Cizon lips yazama maka jiki, harya zama d'abi'ar dake yawan birgeni agareka .

Lips d'in nasa ya ciza sannan ya saki wani k'asaitaccen murmushi da girgiza kai, Munaya kenan sarkin k'uruciya. Yafad'a a zuciyarsa yana mik'ewa shima.



Saman sofa ya zauna yana d'aukar system ya d'ora a cinyarsa, ganin haka saina sauke tiren Dana ajiye a saman table na tura masa gabansa, nasansa akwai son d'ora k'afa, abinka da jinin mulki.

Aiko saiya maida k'afafunsa duk biyu akai yana fad'in  thanks .

Bance komaiba sai murmushi dana d'anyi, na zuba abincin ina zama kusa dashi, tunda ya d'auki lap-top d'inan hanyar zamewa cin abincin yake Neman k'irk'ira, kuma saiya cishi.

Nace,  to yanzu ya za'ayi? Ga abinci .

Batareda ya kalleniba yace,  Kici da nawa kawai ya wadatar .

Ni dariyama ya bani, amma na daure banyiba,  Nikam ina mamakin yanda kake k'in abinci saikace wani Khaleel .

Murmusawa yayi hankalinsa nakan aikinsa. Yace, bazaki ganebane, nifa wlhy abinci takuramin yakeyi, shiyyasa ko sau d'aya nacisa a rana ya watar dani .

Nace,  Nikam dai ban wadatuba, bud'e baki wannan bashida nauyi, nasandai gudun k'aton ciki kake kawai .

Dariya ya sanya kawai.

Nima nad'an dara ina kai abincin bakinsa.

ALLAH yanzu saikaga mutun nata hora kansa da yunwa wai karyayi k'iba, shikuma ALLAH ba ruwansa, idan haka yayoka ko ruwane kawai abincinka sai kayita .

Abincin ya shiga taunawa da murmushi saman fuskarsa hankalinsa nakan system d'in.



Haka nacigaba da bashi abincin da janye hankalinsa da hira, yayinda yake aikinsa da saurarena, idan na murmushine ya murmusa, Wanda zaiyi magana ya amsamin a tak'aice, Wanda tuni na fahimci al'adarsace tak'aita magana yabaka a dunk'ule kawai ka fassara sauran.

'Dagowa yay fuska a marairaice,  My mata ki tausayamin hakanan cikina karya fashe .

Dariya nayi da nuna masa plate d'in daya koma empty.

Ya waro idonsa waje yana shafa ciki,  Dan ALLAH da gaske kike dukni na cinye? .

Nakuma tuntsurewa da dariyar danake dannewa,  Yo dawa kukaci? Wlhy duk kai kacinye harma d'an k'arawa nayi .

 Chiii yarinyarnan kin gama dani, amma gama dariyar muguntar ai kanki zata k'are wlhy, ke zakiji nak'ara miki nauyi .

Dukda na fahimci inda ya dosa saina shareshi ina cigaba da dariyata, nama mik'e daga kusa dashi.

 Humyim zaki gane kuranki ne .

Yay maganar yana cije lips.



Da lokacin isha'i ma yayi shine ya jamana jam'i, ya kuma komawa kan aikinsa, ganin aikin ya d'auke dukkan hankalinsa saina d'auka wayarsa Na kira su Zuhuriyya y'an Niger, muka gaisa dad'an ta6a hirar zuminci cikeda nishad'i. Sannan Na kira aunty Salamah itama nasha labari.

Ganin harna gama wayoyina yana aikin still saina d'auka Novel d'insa d'aya nai zaman karatu.

Sai wajen 10 ya dafe kai yana sauke ajiyar zuciya.

Kallonsa nayi da tausayawa. Nace,  Ka huta haka nan mana my king .

Huci yakuma furzarwa yana k'aramin tsaki, ya taso daga gaban tebir d'in ya dawo bakin gadon ya zauna.

Hannunsa Na kamo, Na kwanto kansa bisa cinyata inad'an shata goshinsa, idonsa a lumshe yace,  wlhy sonake naga na had'a kud'in jirgi da abubuwan buk'atar mu idan zamu wuce Nigeria, Dan Dr Erfan Fahad yamin albishir da k'arshen watannan insha ALLAH zai sallami Abie, gashi ina cikin matsalar kud'i Munaya, narasa yanda zanyi, bazai yuwu Na kwashe kud'in kasuwa Na narkarba kuma .

Ajiyar zuciya Nima nayi cikin damuwa, ganin ya bud'e idonsa saina murmusa ina d'an matsa masa kafad'unsa. Nace  ga shawara to .

 Ina saurarenki . Yafad'a cikin maida hankali gareni tareda hard'e hannayensa a k'irji.

Yatsana d'aya Na d'ora saman girarsa ina kwantar da gashin a hankali,  My King mizai hana gifts d'in dana samu Na aure da haihuwar yarannan kayi amfani da kud'ad'en ciki, abinda ya kasance Na kud'i a siyar dashi Dan banga amfanin ajiyesuba ai .

'Dan Murmushin gefen baki yayi yana lumshe ido, sannan ya bud'e a kaina,  Munaya duk abinda aka baki ko yarana halalinkine, idan Na kar6a nazama mai handama kenan, ta wani faninma zaluncine, nine yakamata Na baki domin sauke wasu nauye-nauyenki Na y'an uwa da makamantansu, saikuma Na amsa Dan nine baba rodo sarkin babakere .

Na 6ata fuska ina janye hannuna daga saman girarsa dukda dariyar da furucinsa Na k'arshe ya bani,  Shikenan tunda baka d'aukeni yanda Na d'aukeka ba, yanzu tsakani da ALLAH idan kabarni dasu mizanyi dasud'in? Ashe abuna ba naka baneba? . Nai maganar cikin matso hawaye.

Da Sauri ya tashai zaune yana rik'oni amma saina kwace ina niyyar sauka ma gaba d'aya daga gadon. Gaba d'aya yasani a jikinsa yana fad'in,  Sorry tsaya muyi magana to kinji my sweetness, ya kikeso ayi yanzun? .

Hawayen nakuma sharewa nace,  Ka kar6a kawai .

Shiru yay yana kallona da nazarin maganar, saikuma yad'an numfasa yana gyara zama. Yace,  to ai naga suna Nigeria?  .

 A'a suna nan, Dan dukna had'osu Na taho dasu wannan karon .

 Ok babu damuwa, da safe zamuyi magana, shirya yara nakaisu wajen Momma dare nayi nafara jin barci .

Naji dad'i daya amince zai kar6a, Dan haka Na rungumeshi ina dariya.

Bayana yad'an bubbuga kawai yana cewa  jeki shiryasu .

'Dagowa nayi ina kallonsa,  Amma my King zamuke takura mata itama ai, ka barsu kawai .

 Babu wani takurawa, bazaki gane bane y'ammatana .

Babu yanda Na iya, dan babu jayayya a tsakaninmu, shiryasu nayi Na shayar dasu kowanne yay d'if, ya d'auka biyu yakai yadawo ya d'auki d'ayan shima. Nikamdai wannan Abu ya girmeni, amma babu damar magana.



Ya dawo yana dariya da bani labarin gargad'in da momma tamasa akan wlhy mu tashi da wuri, kokuma da anyi sallar asuba yazo ya d'aukesu, Dan bazai yuwu ake barinsu da yunwaba.

Sai Na k'arajin duk kunya ta lullu6eni, amma shi ko'a kwalar rigarsa, saima wata tashar daya kamo.





A gurguje please=�
�.







********



Washe gari ya koma Kashmir, yaso mu tafi tare amma Na nuna masa Momma yakamata ta fara zuwa, Dan tunda aka kai Abie babu Wanda yaje saishi kad'ai.

Daga baya dai sai muka tsaida shawara akan zaije yafara ganin halin da ake ciki a yanzu, da wannan shawarar yatafi.

Ba k'aramin abin mamaki Dr Erfan ya shiryama Galadima ba, shiyyasa gaba d'aya ya hanashi ganin Abie.

Da yamma lik'is Galadima ya isa Kashmir, saboda bai tafi da wuriba, kai tsaye asibiti ya nufa dukda yana tunanin mawuyacine ya samu Dr Erfan Fahad a can, saboda lokacin tashinsa aiki yayi, saidai idan wani muhimmin aiki ya tsaidashi ko Emergency ya riskeshi.

Ilai kuwa a harabar asibitin Galadima yaci karo da Dr Erfan Fahad ya fito zai wuce gida, sosai Dr Erfan Fahad yay mamakin ganin Galadima, Dan basuyi waya yana hanyaba. Ya bashi hannu sukayi musabaha da rungume juna,  wai my friend dama kana hanya? .

Galadima ya murmusa da shafa kansa,  Kabari kawai, ya aikin? .

 Alhmdllh .

 To inaga kawai muwuce gida. Dan wlhy nagaji sosai, yau nayi aikin daya wuce kima .

Galadima yay d'an jim alamar tunani.

Murmushi Dr Erfan Fahad yayi yana dafa kafad'ar Galadima,  Sameer nasan kana tsananin buk'atar son ganin Abie ko? Karka damu, kaidai muje gida kawai abokina .

Galadima baice komaiba ya bisa suka wuce, Dr Erfan Fahad nata jansa da hira, amma shi iyakarsa murmushi ko eh da a'a.

Ko kad'an Dr Erfan Fahad bai damuba, danya fahimci halin Galadima Na rashin son hayaniya tsaf, dama tun a baya bashida yawan magana, Ashe halin Na nan bai canjaba, saima k'aruwa dayay.

Shikam Dr Erfan Fahad mutum ne faran-faran, ko jama'ar dake jiyya namasa wannan shaidar ta yawan tsokana.

Ahaka dai suka isa gida, shidai Dr Erfan Fahad yanata murmushinsa.

A k'ofar falo ya tsaida Galadima, tareda fidda handkerchief a aljihunsa yace Galadima ya rufe idonsa.

Da mamaki Galadima ke kallonsa, amma yagaza furta komai.

Dr Erfan Fahad ya jinjina masa kai da had'e hannayensa alamar rok'o.

Ruf Galadima ya rife idonsa, Dr Erfan Fahad ya saka handkerchief d'insa ya d'aure masa ido, sannan ya kama hannunsa suka shiga ciki.

A tsakkiyar falon ya tsaidashi, ahankali yace,  my friend are you ready? .

Cikin sauke numfashi Galadima ya d'aga masa kai.

Dr Erfan Fahad ya murmusa yana kwance masa handkerchief d'in sannan yace,  Bud'e idonka .

A hankali Galadima ya shiga bud'e idanu, harya bud'esu gaba d'aya akan k'yak'yk'yawan dattijo zaune bisa kujera, fuskarsa ta k'awatu da murmushi, yasha gyaran fuska mai k'ayatarwa, sai gashi kad'an mai adon furfura da aka bari ya zagaye fuskarsa.

Wata zabura Galadima yay mai kama da firgita, Dr Erfan Fahad yay saurin tarosa, Dan kad'an yarage ya zube a k'asa.

Cikin rawar baki data jiki yake kallon dattijon, dak'yar ya iya fusgo numfashi da magana mai cike da in'ina daga bakinsa  A..b..ie k..ai.ne? .

Abie ya share hawayen da shima suke ziraro masa, cikin tsantsar so da k'aunar d'an nasa yabashi amsa da fad'in  Tabbas nine Muhammad Sameer sanyin idaniya, Abie d'inka ne zaune yau agabanka, Wanda ya tashi cike da hukuncin Ubangiji gagara misali .

Galadima ya maida kallonsa ga Dr Erfan Fahad.

Murmushi Dr Erfan Fahad yayi,  Karkayi kokwanto da ikon ALLAH Sameer, shike kwantar da Wanda yaso, Yakuma tasheshi a lokacin da yaso, dama ba'a yankema rayuwa hukunci, mai jiyya saiyayi rayuwa mai tsayi amma mai lafiya a wayi gari yazama gawa, ciwo bashi bane mutuwa, kwanaki 10 kacal Na d'auka ina treatment d'in Abie ga66ansa suka fara aiki, a sauran sati uku danayi tare dashi muna koya masa yanda zaiyi tafiyane, da zama, d'aukar Abu, da sauransu, Dan duk ga66ansa sun manta, kamar yanda ka sanarmin addu'ar da kukaita masa lallai itace babban magani daya zama mai tasiri a garesa, domin nikam abinda ba'a rasaba Na k'arasa, duk Wanda yabar addu'a lallai dole matsala tazama ma'abociyar rayuwarsa, a yanzu haka ina mai tabbatar maka Abie zai iya tafiya dayima kansa wasu abubuwa, amma bamasu yawaba, tafiyarma bamai tsaho ba, Dan yawanyin ne zai bama ga66ansa kwari da sabo, shekara 26 mutun Na kwance sai na'urori ke sarrafashi ba k'aramin Abu bane Sameer, Dan dolene akira Abie d'an baiwa, masu irin nasarorinsa kad'anne a cikin al'umma wlhy, kaje ga Abie, domin kuna buk'atar juna .

Tamkar Dr Erfan Fahad yama Galadima allura ne, cikeda sasaarfa ya k'arasa ga Abie, a gabansa ya zube yana sakin wani kuka maiban tausayi tamkar mace .

Abie ya sakko daga kujerar ya rungume jarumin d'ansa shima yana hawaye, sun dad'e a haka, jisuke tamkar karsu saki juna, a tunaninsu Kodai mafarki sukeyi, suna tsoron rabuwa su farka suga ba haka baneba.

Shi kansa Dr Erfan Fahad hawayen tausayinsu yake sharewa.





Ni kaina masu karatu wannan lamari yasani hawaye Na gaske=�-�, da zaka k'iyasta hakan a kanka wane farinciki kake hangowa yayinda waraka ta riskeka?.=�-�



Wad'annan bayin ALLAH yau lallai suna cikin tsantsar farin ciki, ko kad'an Galadima ya kasa gusawa daga jikin Abie, Yakuma k'i kiran kowa, burinsa shima yabasu mamaki tamkar yanda Dr Erfan Fahad yabashi. A yau yay niyyar su juya amma Dr Erfan Fahad ya hana hakan saidai gobe, Dan dare yayi kam a yau.

A gado d'aya Galadima da Abie suka kwana, dukda sunma cinye rabin daren da fira=��.



****



Hankalin Munaya duk a tashe yake, saboda tanata kiran Galadima yak'iyin picking, tun tana daurewa harta gaza tafara kuka da shiga tsantsar tashin hankali.

Momma Ce ta lura da canjawarta, ta tambayeta lafiya?.

Kasa magana tayi saboda kunya, saida Momma ta kuma maimaitawa sannan tace,  Momma inata kiran Number Abbansu ne yak'i yin picking tun d'azun .

Ita kanta Momma ta kirashi baiyi picking ba, amma ta d'auka ko wani uzirine yasha kansa, sai yanzumefa hankalinta ya fara tashi itama, waya ta d'auka tashiga kiransa amma babu amsa, kusan kira 10. Cikin firgici ta kalli Munaya da aunty Mimi da itama take kan gwada kiran nasa, amma itama ba'ayi picking.

 Kinga Munaya tura masa massage mu gani .

Jiki a sanyaye Munaya ta tura massege, amma kusan 30minutes babu reply.

Hankalinsu fa yakai k'ololuwar tashi, amma sun rasa mafita.



***



Shikam Galadima baima San sunaiba, wayarma kanta baisan inane ya jefar da itaba, gabaki d'aya hankalinsa ya tattarane ga Abie, harkuma suka kwanta barci bai nemi wayarba.





*****



Yau kam inhar wani yay barci a cikinsu to bana kwanciyar hankali baneba, dan kowa damuwa tamasa katutu, dai-dai da Hadiman gidan suma duk a damuwa suke, sai dai tamkar yanda suka saba yauma sun mik'a lamarinsu ga Ubangijin talikai.





Washe gari



Tunda safe Momma ta nemi Number Dr Akash da Dr Ajey akan rashin jin Galadima, duk sun amsa mata da zasu bincika.



Can kuma su Galadima sun wayi garine da shirin dawowa New Dhalhi, cikin tsantsar farin ciki irin Wanda misaltashi ma 6ata lokacine.................
'<���

















ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���

[7:09 PM, 8/21/2019] +234 813 508 4146: Typing=���



https://2gnblog.blogspot.com/



=ء�HASKE WRITERS ASSO....





f&RAINA KAMA...!!f&

(Kaga gayya)





Bilyn Abdull ce>��<���





BOOK 3 =�I�<���2� 9�



https://2gnblog.blogspot.com/

.................Gaba d'aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud'e gate da shigowar mota. Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d'auke da wani irin k'ayataccen murmushi daya fidda sirrin k'yawunsa.

Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad'a akan son rungumarsa ko Sauban amma yau saigashi ya bud'e mata hannu dakansa tazo ta shige jikinsa.

Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da hanzari suma

Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen farin ciki.

Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki murmushi yana share hawaye, yana k'asa d'aya da iyalansa amma bai ta6a sanin muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k'yau.

Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya rungume Momma da aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk'ar tada hankalinsu.

Da sauri suka d'agosa hankali tashe suna tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?.

Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe idonsa .

Babu musu sukabi Umarninsa, har Munaya dake gefe.

Yace,  kun tabbatar kowa ya rufe? .

A tare suka amsa masa da eh.

Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan ya juya ga motar ya bud'e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik'eda sandarsa mai k'yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu tafiyar batai kwariba.

Saida Abie ya jingina jikin Mota ya tsaya da k'yau sannan Galadima yace,  Kowa ya bud'e idonsa .

Har rige-rigen bud'ewa suke.

Akusan tare Aunty Mimi da Munaya da Samba suka kwalla k'ara, Momma kam sai tayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login