Showing 228001 words to 231000 words out of 365757 words

Chapter 77 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1439

kamata, tasan yunwa da k'ishi ma kawai sun Isa su k'arar da numfashinsu, hawaye masu d'umi suka kuma gangaro mata a kumatu suna sauka jikin inno dake shafa kanta.



Shayi Aunty Mimi ta had'o mata, amma fir tace ta k'oshi, da k'yar inno ta samu ta lalla6ata tasha Quarter d'in kofin.

Mom tace,  wannan nono kid'an matsesu kozasu rage miki nauyi, dan shine yakawo wannan zazza6in .

Bata musaba aka kawo k'aramin bowl ta matse aciki, Aunty Mimi ta zubar a bayi ..

Tanason tambayar ina Galadima tanajin kunya, sukuma babu Wanda ya sanar mata komai, kodan gudun k'ara tada hankalinta.

Magani suka bata tasha takoma ta kwanta, yayinda sukuma suka mik'e duk suka d'aura Alwala suna mik'ama Ubangiji kukansu, danshi masanin sirrin 6oyene, yana kallon komai, kuma shine zai kawo iyakar komai d'in.





&&&&&&&





Duk wannan abun dake faruwa su Momma babu Wanda ya sanar musu, saidai sukaji a jikinsu tamkar akwai matsala, sunta kiran numbers amma daga wadda zasu samu a kashe sai wadda network zai hanata shiga.

Sai suka d'aura ko shagalin sunan ne yakawo hakan.





*******************



Tunda Munubiya suka koma gidan kuka takeyi, ko kad'an tak'i sauraren yaran da keta tsula kuka suma, balle tabasu nono.

Ba itaba hatta su Ayusher dasu feena kukan sukeyi, hakama Samha harda shid'ewa, dan itama su tabi bata koma masarauta ba, Yaa marwan da mama Rabi'a ne kawai ke k'ok'arin danne nasu suna lallashinsu.

Yayinda dare yay nisa duk sai suka d'aura alwala suka zo suna mik'ama Ubangijin talikai kukansu da k'ok'on barar bama wad'annan k'anan alhaki kariya da fatan ku6ta.









A 6angaren gidan su Munaya kam duk hassadarsu yau dai sun tausayama gudan jininsu da yaranta, sundawo gidane kowa yana sharar kwalla da addu'ar ku6tar yaran.

Ita innarsu Munaya ma ai ba'a magana, ALLAH kad'aine yasan halin datake ciki, ta shige d'aki ta rufe kanta tana jera nafilfili, dan wannance kawai gudunmawar dazata iya bayarwa a garesu akan wannan lamari mai sark'ak'iya da yawa.



Abban su munaya ma yau harda hawayensa, dukda bashi da tabbas akan hasashensa yasan komai zasu iya, saboda SD yanada kusanci da wannan masarautar sosai, duk abinda ke hannunsa da bayanan daya ajiye ya shiga tattarasu waje d'aya...............
'<���







=�?�Duk nisan jifa dai k'asa zai fad'o, kwana 99 na 6arawo, 1 kuma tak namai kaya.=�N�<���





Fans insha ALLAH dai abuwa sun fara warwarar zare, sai mubi su Galadima muga yanda zasu dawo mana da triplets d'inmu gida=�-�, yau Munaya tabani tausayi daga ita har Galadima, dan shima dai dannewa kawai yake saboda jarumta, ALLAH ya rabamu da sharrin mak'iyi komai k'an k'antarsa, Harun da sauran munafukai MAZA BISA KANKU<���<���<���<���<���<���<���<���<���<���.





Barkanmu da dawowa my sweet fans>��=�!�.



Yau bana cikin yanayin dariya=�!�















*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=�-�=�O�<���

*_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���2� 7�



................Tunda suka d'akko yaran suketa kuka, musamman Abdurraheem dahar shid'ewa yakeyi, ALLAH dai yabasu sa'a ne saida suka fito suka fara kukan, neman haukatasu ma sukaso yi tun amotar, jisukai tamkar su rufesu da duka, saidai babu damar hakan, dan basuga abin duka jikin wad'annan kwad'unan yaranba.

Da farko sunga kamar ana binsu, sai daga bisani ne sukaga ba haka baneba, har dai suka iso gidan y'an uku basu barsu sun shak'i iska ba.

Suna shiga suka danna musu wasu allurai, cikin mintuna k'alilan jikinsu dukya saki sukayi luf.



ganin lokaci yaja har kusan 10pm babu alamar wani motsi hankalinsu ya kwanta, dan sunsan dai tabbas sun tsira, wayar wadda ta sakasu aikin suka kira, amma tak'i yin picking.

Cikin matan d'aya tace,  kusan dai bazata d'aga ba, saboda nasan masarauta a haukace take yanzu, saidai mubari zuwa safiya .

Tsaki d'aya yaja,  kai nifa gaskiya a tsorace nake, gara ta d'auka asan mafita, bana buk'atar gawar yarannan takwana a hannunmu, kunsanfa babansu mayene wlhy, tsaf zai bibiyemu .

 kai dalla ai yanzu bashida wannan damar, caza'ayi a fad'ama police, sukuma aikinsu zai farane zuwa safiya, kafin sannan munma gama binne gawar yaran mun kama gabanmu .....

 eh kumafa hakane .



Suna tsaka da wannan hirarne su Galadima suke shigowa, gidan k'aton gaskene dan haka suka kasa fahimtar INA zasu dosa, Galadima Yakuma danne abin kunnensa da d'anyatsa d'aya cikin murya k'asa-k'asa yake fad'in  Sauban kufara muje .

 yauwa Yaya zaku shiga hannunku Na haggu, duk sunajin maganar dan haka sukabi hannun haggu, yayinda su Ameer ke binsu a baya suma. Galadima dake gaba ya bud'e k'ofar a hankali duk suka shiga, daga can Saleem yace,  duk Ku rarrabu sir, dan abin ya nuna yaran suna ainahin tsakkiyar gidanne .

Batare da sunyi magana ba duk suka rarrabu.



'Daya acikin 6arayin yace,  kai nifa kamar motsi nakeji gaskiya .

 to sannu mai kunnen maciji . cewar d'aya aciki.

Cikin matan d'aya tayi dariya tana fad'in  nakula kaidai bibo matsoracine halan? .

Hannu ya d'aga zai kwad'eta, a harzuk'e yana fad'in  k wlhy kacaccalaki zanyi, bar ganin kinfito daga masarauta, kubadan ma an had'amu aiki dakuba kun Isa saninmu ne? jimin y'ar iskar mara kunya .

Hak'uri y'an uwansa suka bashi, ya mik'e yana jan tsaki ya fito danya duba.

Galadima dake la6e cikin labule yay saurin fitowa, abinka da dogon mutum dan danan yasamu damar shak'osa ya shaka masa abin hannunsa, tun yana k'ok'arin kare kansa har jikinsa ya saki ya kwantar dashi a k'asa.

Jinjina Muftahu dake kusa dashi yamasa, sannan suka cigaba da shiga.

'Dayar baiwar tana kitchen tare da wani suna iskancinsu Nuren yasamu damar sad'ad'awa, (kunsan dai shahararren kidnapper ne>�-�=��) yauma tsiyar ya aikata wajen jefa ma namijin handkerchief a fuska, macen tai yunk'urin zuba ihu yasa k'afa ya tad'ota ta fad'in, sannan ya danne bakinta da ya shak'a mata itama.

K'arar fad'uwarta taso fargar da sauran, dan haka duk suka mik'e suna fara lek'e-lek'e, aikam Muftahu yasamu ya tad'e d'aya ya fad'i, Ameer dake bayansa shima ya shak'a masa, harda mangareshi yana fad'in  kwallon shege taka ta k'are, inakai ina satar sarakunanmu insha ALLAH .

dariya taso kufcema Muftahu amma ya danne bakinsa da hannu yana girgiza kai saboda tsiyar Ameer.

Fad'uwar wani da suka juyo ya sakasu kuma saurin waigawa wajen, Galadima ne ya sakeshi ya fad'i,  shegen k'arfin jinine dashi dak'yar abin yay masa tasiri . Galadima ya fad'a yana halbinsa da k'afa.

Gaban d'ayar baiwar dake la6e jikin labule ya fad'in, dan tabbas wannan muryar Galadima ce, kowa yasan bai iya R ba, zuface tashiga keto mata jikinta na 6ari, ta to she bakinta saboda kuka daya kufce mata, saigata tana tsilala fitsari saboda ganin Galadima yanufo ta wajen, shikenan itakuma tata tak'e, wannan zakin gagara badau d'in binneta kawai zaiyi da ranta.

Waige-waige Galadima ya fara saboda jin numfashin mutum dayakeyi kad'an-kad'an ta wajen, har yayi gaba ya dawo baya yana yaye labulen wajen. shi da farkoma ya zata aljanace saboda yanda ta zazzaro masa ido. fincikota yayi ya Watso tsakar d'akin, mamaki ya kamashi ganinta da kayan manyan kuyangin gidansu.

 tashi tsaye . ya fad'a cikin matuk'ar d'aure fuska, kad'an yarage kashi ya kufcemata.

 ina suke!!! .

Yafad'a cikin matuk'ar tsawa daya firgita hatta su Sauban dake saurarensu a waya.

Wannan tsawar tasa ce ta saka d'ayan fitowa a tsorace da gun a hannu, Aunty Salamah dake bayansa bai saniba ta hankad'ashi yay gaba zai fad'in, Nuren ya ida tad'eshi da k'afa.

Gun d'in data fad'i ta silalo gaban Galadima ya taketa da k'afa yana huci da taunar lips. Handkerchief d'in hannunsa yasaka ya d'auki bindigar, ya saita namijin da ita.

Mazari jikinsa ya fara yana d'aga hannu sama,  dan ALLAH ranka ya dad'e karka kasheni, wlhy bansan komaiba, oganmu ne yasan komai da wannan baiwar .

Kunamar bindigar Galadima ya d'ana, nanfa su Muftahu duk suka rud'e, Nuren yace,  Brother please karkayi harbi, nasan zasu fad'a mana, dan ALLAH kayi hak'uri .

Gaba d'aya jijiyoyin kan Galadima sun mimmik'e, sai fidda huci yakeyi a wahalce.

Muftahu ma yashiga rok'onsa, Su Saleem dake sauraren komai dagacan duk suka rud'e, Sauban yace  yaa Sam ALLAH ya huci zuciyarka, amma idan ka aikata haka a wajenwa Zamu samu hasken sauran abubuwan?, dan ALLAH kayi hak'uri badan mun isa mu saka ka ba, saidan halin da mahaifinmu ya tsinci Kansa tsawon shekaru, gakuma dama tazo mana ta Sanin sirrin 6oye, muyi amfani da ita ta sauk'ak'ak'iyar hanya....

Sakin gun d'in Galadima yayi ak'asa yana dafe k'irji, wani mugun bugawa zuciyarsa keyi, da baya-baya yanemi zubewa a k'asa, cikin hanzari Nuren da Muftahu suka taresa, da taimakonsu ya zauna akan kujera. Yana nuna baiwar da d'ayan hannusa.

Aunty Salamah data fahimci mi yake nufi tace,  ina yaranne? .

Jikin baiwar Na 6ari ta nuna k'ofar wani d'aki, shiga Aunty salamah tayi itada Ameer suka d'akkosu.

Saidai duk a firgice suke, dan yaran babu alamun rai tare dasu, zufa ta shiga ketoma Aunty Salamah, haka ta fito rungume da Abdurraheem da Amaturrahman, shikuma Ameer ya d'akko Abdurrahman yana fad'in  Aunty kamarfa yarannan sun mutu .

Wannan kalma caraf a kunnen Galadima.

Wata muguwar zabura yayi yamik'e tsaye, sai ya kuma dafe k'irjinsa da sauri hajijiya tafara katantanwa dashi, basu fargaba sai jinsa sukayi kawai a k'asa.

Gaba d'aya suka kuma rikicewa, sukayi kansa.



Muftahu yace,  bamuda isashen lokaci, asuba ma ta gabato, dolene mubar gidannan dan ko yaushe zamu iya gamo da abinda bamu shirya masaba .

Duk sunyi na'am da wannan maganar tashi, nan fa suka fara kwasar wad'anda suka sumar suna kaiwa mota, sannan suka tasa k'eyar d'ayar baiwar da wancan, suma.

Yayinda Nuren yad'an bincika gidan, ganin babu wani abunda zasu k'aru dashi yazo suka kama Galadima daya Suma suka fita dashi.

Hankalin Sauban ya tashi matuk'ar tuk'ewa, ya fito yana nufarsu da ta6a jikin d'an uwansa,  Yaa Nuren miya farune? miya faru da Yaa Sam? .

 Sauban bamu hanya, ba lokacin wannan baneba yanzu .

Sole Sauban ya matsa baya hawaye Na kwarara a idonsa, suka shinfid'ar da Galadima a bayan mota, sai lokacin Sauban yaga yaran a hannun Aunty salamah da Ameer, da hanzari suma ya nufesu, Aunty salamah ta bashi Abdurraheem, jujjuya yaron yayi yaji kamar baya numfashi,  innalillahi.... yashiga maimaitawa zufa Na keto masa, dolene Yaa Sam ya suma, hawaye yafarayi yana rungume yaron a jikinsa, Tausayin dukkan ahalinsa da suka kwallafa rai ga yaran ya kamashi, musamman ma iyayensu, ya ALLAH nasan bazaka jarabcemu da abinda bazamu iyaba, ALLAH kabamu juriya .

Muftahu yace,  su shiga mota, duk shiga sukayi, Nuren dasu Ameer suka wuce da wad'ancan sauran wani waje daban, Muftahu kuma ya kira police d'in da suka shirya komai dasu, a hanya suka had'u, sai sukai joining d'insu tamkar tare sukayi aikin, suka kira manyansu suna sanar musu gashifa sun kama wani matashi da baiwar masarauta da yaran....

Wannan labari yama su d.p.o dad'i ya kira IG shima ya sanar masa, yaji dad'i shima, koba komai mai martaba zai yaba k'ok'arin dasukayi, akace yanzu suna inane?.

Amsawa sukai da gasu a masarauta, dan harda Galadima sukayi aikin, yana kuma cikin wani yanayi shida yaran yanzu haka.

Basuda za6in daya wuce suce musu to suma gasunan zuwa masarautar.



Tun'a mota su Muftahu sun gargad'i baiwar nan da d'ayan mutumin akan suce su biyune suka sacesu, inhar sukace basu kad'ai bane wlhy saiya kashesu, sannan su tanaji fad'ar wani abun ba ainahin gaskiya ba, (dan Galadima baya buk'atar police su shiga cikin aikinsa yanzu, yafison saiya kama kowa sannan, dan inhar police suka shiga aikin mutane da yawa zasuyi escape ne) shiyyasa Muftahu yayma wad'ancan gargad'in tunma kan su k'arasa cikin masarauta.



Da yawa wasu basu rintsaba a masarauta gagara badau yau.

Munaya dai dole aka sake d'irka mata allurar barci mai k'arfi, dan kusan kuma haukace musu tayi gabannin asuba, dalilin wani barci daya figeta tayi mafarki mai matuk'ar tada hankali.

Su inno Na zaune har yanzu suna kai kukansu ga ALLAH Muftahu da Sauban suka shigo d'auke da Galadima da suka kamo tamkar gawa, sai Saleem da police biyu dake falo d'auke da yaran sukuma.

Zaram duk suka mik'e suna tambayar lafiya? Miya sami Galadiman?.

Basu sami wata amsaba, saida suka kwantar dashi a gadon sannan Sauban ya share hawayen fuskarsa yana fad'in  suma yayi inno .

Aunty Mimi da mom sukayi kan Galadima suna kuka, inno tace,  kun samo yaranne? .

 eh gasu can a falo tareda police, saidaifa duk sun mutu, shiyyasa ma Yaa Sam ya suma . yak'are maganar yana kuka.

Hawaye suka zuboma inno, waya ta d'auka ta kira papi, Wanda shima dai a zaune suka kwana dagashi har Sarki jalaludden.

A time d'in dama har ankai musu bayanin shigowar su Muftahu d'in.

Yau dai kam tilas Manyan Sarakuna biyu suka nufo sashen Galadima da Kansu, abinda waninsu bai ta6a yiba kenan.

Maganar ganin yara yafara baje Masarautar tun'a daren, dan kowa kunenensa a bud'e yake, da masu fatan a gansun da masu fatan kar'a gansun.



Lokacinda papi da mai Martaban suka iso Inno Na rungume da yaran duka tana hawaye, sukuma su Aunty Mimi suna bedroom wajen Galadima.

Kusan a tare Akash da Dr jalal suka iso dasu papi.

Mai Martaban da papi suka kar6i yaran daga hannun inno, Suna zama bisa kujerun.

Akash wajen Galadima ya nufa, dukda ba shine likitansa Na zuciya ba zai iya bashi taimakon gaggawa, shikuma Dr jalal ya fara kar6ar Abdurraheem dake hannun inno, yan d'ube-dube, yayi Na tsawon lokaci kafin ya ajiyeshi ya kar6i Na hannun mai Martaban, shima yagama duk abinda ya dace ya kar6i Amaturrahman a hannun papi, ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in  Alhmdllh duk basu mutuba, allurar barci mai k'arfi sosai suka musu, shiyyasa numfashinsu yay nisa sosai, danta musu k'arfi da yawa, amma idan kuka saka kunne nawasu mintuna saitin jikin zuciyoyinsu zakuji suna motsawa kad'an-kad'an, sai dai ta wannan tafi yin k'asa sosai gaskiya . Ya nuna Abdurraheem dake hannun inno.

Su mai Martaban suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala ga ubangiji.

A cikima Akash nata iya bakin k'ok'arinsa ganin Galadima ya farfad'o, Ahaka su mai Martaban suka k'araso cikin d'akin d'auke da yaran a hannun, Munaya Na gefen Galadima an lullu6a mata bargo batasan wainar da ake toyawa ba, dan barcin nata shine mafita fiye da zama ido biyu.

A gadon suma yaran duk aka shimfid'esu, Dr jalal yad'an musu dabarun likitoci sauran kuma aka barma ubangiji ikonsa Na jiran farkawarsu.

Hankali kuma duk saiya koma ga Galadima da aketa fama.

Har aka kirayi sallar Asubahi babu amo babu labari akan farfad'owar tasa. daga k'arshe dai Akash saida ya kira likitan Galadima na zuciya. Shiya dunga fad'ama Akash d'in yanda yadace yayi, lokacin shiga salla ya saka su mai Martaban fita masallaci dole, sukabar Akash da Dr jalal dake taimaka masa suna aikinsu, saisu Aunty Mimi da suka kasa matsawa ko nan da can, Sauban ma da k'yar su papi suka lalla6asa yabisu salla.



Har gari ya waye sashen Galadima ya cika da manyan masarautar irinsu mama Fulani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login