Showing 294001 words to 297000 words out of 365757 words

Chapter 99 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1464

A hanzarce Baffi ya d'aga hannu sama yana mik'e da fad'in  yamai shari'a tambaya akaima lauyan mai k'ara, amsa kuma yakamata ya bamu baya sakko tashi tambayarba .

Hannu Alk'ali ya d'agama Brr Adam Sadiq Adam, yace,  Brr Adam ka gyara, amsa muke buk'ata, kanada dama kaima kayi taka tambayar daga baya .

Brr Adam Sadiq Adam ya risinar dakai alamun ban hak'uri sannan ya gyara tsayuwarsa yana fad'in  Yamai girma mai shari'a akwai abinda ke hannun Alhaji Auwal Fharuk Wanda mallakin su wad'annan mutane 11 ne, shine sukeda buk'atar kar6a .

Baffi yamik'e yana fad'in  yamai girma mai shari'a ko zamu iya sanin minene wannan Abu da suke tuhumar Alhaji Auwal Fharuk akansa, dahar suka kasa mik'ashi ga sharia domin kar6a har sai sunbi ta hanyar nuna k'arfin ikonsu? .

Brr Adam Sadiq Adam yay shiru yakasa cewa uffan, dan ganin tun a tashin farko yana shirin zurmawa.

Ganin yak'i cewa komai Baffi ya kuma cewa  ya mai girma mai shari'a idan baza'a samu amsaba ina buk'atar d'aya daga cikin y'an wad'annan tawaga domin ya amsamin tambayata idan shi Barrister bai saniba .

Alk'ali ya jinjina kai yana bada Umarnin tasowar d'aya daga cikin su Alhaji Mansur.



Dukfa abinnan dake faruwa Galadima yana kallon komai kai tsaye ta Computer, danshi baizo Court d'inba, babu damar hakan, yana fitowa a gidan police kamashi zasuyi, wannan yasa tukan zaman Shari'a Alk'ali yabada wannan damar ta had'a video call d'in da Galadima zai iya ganin komai da za'ayi kamar yanda IG ya buk'ata bisa umarnin shi Galadima d'in, kamar yanda ya shard'anta ko amasa hakan koya jeho gawar yaro d'aya ko yarinya. Hakan yasa sukai masa babu gardama.



Alhaji Abdul-Naseer dake farkone ya taso, ya shiga inda aka tanada domin buk'atar hakan, ya fad'i sunansa da matsayinsa, sannan Alk'ali yabama Baffi damar masa tambayar.

Baffi ya k'arasa jikin katakon d'aya shiga tsakaninsa da Alhaji Abdul-Naseer, idonsa a kansa yace,  Alhaji Abdul-Naseer, nasan kana d'aya daga cikin y'an wad'annan tawaga, shin kozaka iya amsa mana tambayar da lauyanku ya kasa? .

Murmushin Alhaji Abdul-Naseer yayi, cikin kwarin gwiwa yace,  Brr Usman, a ganina wannan sirrinmu ne, koma mi muke buk'ata a hannun Alhaji Auwal Fharuk mukeda alak'a dashi ai ba kowaba ko? .

Baffi yashiga jinjina kai yana murmushi, yayi taku d'aya biyu saikuma ya juyo ga Alhaji Abdul-Naseer, yace,  lallai wannan gaskiyane Alhaji Abdul saidai kuma dalilin sanin Court yanada alak'a da samo Alhaji Auwal Fharuk a hannunku, wanda ta silar kama y'ay'anku da surukinsa yayine kowa yasan hakan, saikuma gashi shi wannan bawan ALLAH Alhaji Auwal Fharuk a jiya daya farfad'o dukda baya cikin hayyacinsa, amma yana ambatar sunan Alhaji Halluru da jaddada lallai koda zaku kasheshi bazai bada wannan camera ba, domin shekarunma da kuka d'auka kuna ma rayuwarsa barazana bai bakuba balle kuma yanzu da lokacin Isar da ita ga Wanda akace ya Isar yayi, kenan Alhaji Auwal Fharuk k'arya yayi? .

Da sauri Brr Adam Sadiq Adam ya mik'e yana fad'in  ya mai shari'a wannan ai tamkar titsiyene Brr kema Wanda ake zargi, dan babu yanda za'ai la'akari da mutumin da baya cikin hankalinsa kamar yanda ya fad'a..... .

Shima Baffi azamar dakatar dashi yayi, yace,  yamai girma mai shari'a Barrister Adam bashida hurumin yanke hukunci akan yanayin Alhaji Auwal, sai ya bari bayanin likitoci ya tabatar mana hakan .

Alk'ali yay gyaran Murya da buk'atar ganin likitan dake kula da Alhaji Auwal Fharuk (Abba).



Cikin mintuna 3 saiga doctor ya shigo.

An sakashi d'ayan wajen, ya fad'i sunansa da aikinsa, sannan Alk'ali yace,  kaine likitan da ke duba lafiyar Alhaji Auwal Fharuk?  .

 eh nine yamai shari'a .

Alk'ali yace,  kozamu iya sanin wani Abu dangane da jikin Alhaji Auwal Fharuk?  .

 kwarai kuwa ya mai shari'a, an kawo mana Alhaji Auwal Fharuk cikin hali irinna suma, amma babu wani alamar duka ko harbi a jikinsa, saidai bincikenmu ya nuna an shak'a masa wani Abu. Daya saka numfashinsa Nisan zango, sai ajiyane bisa hukuncin ubangiji ya farfad'o, wad'annan kalamai sune abinda ya farka dasu a bakinsa, kuma kwakwalwarsa ras take, abinda aka shak'a masanne kawai bai sakesaba har yanzun, danma yanada jini mai k'arfine .

Cikin wad'anda suke zaune ma'aikatan Court d'in d'aya yaje ya kar6i wayar doctor da yay recording ya kaima alk'ali.

Alk'ali ya kunna recording ya saurara, ya ajiye wayar gefe da sallamar doctor cikeda gamsuwar abinda yaji. Sannan shima yabada Umarnin sanin ita camera ta micece?.

Baffi yakuma mik'ewa tsaye yana gyara k'atuwar rigarsa, yace,  ya mai shari'a, ita wannan Camera da wad'annan gamayyar mutane suke farautar rayuwar Alhaji Auwal Fharuk a kanta tanada alak'a da Muhammad Sameer Saifuddin Galadima ne, itace kuma musabbabin d'aukar yaran wad'annan mutane 11 dayayi yake tsare dasu a gida mai labba 67 dake anguwar tudun na ALLAH a tsakiyar binni, damin camera dai k'unshe take da abinda ya faru da tsohon Sarki dake jiyya a India, wato Mai martaba Saifuddin Abubakar tsawon shekaru 26 kenan ba'asan wad'anda suka aikata masa abinda ya kaisa da jiyyarba .



Turk'ashi, kallon kallo kenan, to lallai shine aka shigayi a wannan Court, nanfa k'ananun magana suka fara tashi tsakanin manya, Court ta harmutse da hayaniya babu maijin zancen wani, saida alk'ali ya tsawatar sannan akayi tsit.



Inda kuma a gefe tsantsar rud'ani da rikita ta mamaye su Alhaji Balala, ko kad'an basuyi zaton shigowar wannan maganar da wuri ba cikin shari'ar, shima kansa lauyansu haka, tunda wawantar dasu Galadima yayi akan Shari'ar ta shafi d'aukar Alhaji Auwal Fharuk ne da farko.

Alk'ali da shima kansa ya shiga wani yanayi ya buk'aci ganin Muhammad Sameer a Court.

Baffi ya kuma mik'ewa yana fad'in  ya mai shari'a, ai Muhammad Sameer Saifuddin Galadima bashida ikon zuwa court a yanzu, domin kuwa yana can tsare da yaran wad'annan mutane 11 ne, kuma yana fitowa y'an sanda zasuyi ram da shine a matsayin mai laifi babbama kuwa, dan yanzu akwai laifin garkuwa da yara d'in a kansa, saidai munada hanya sassauk'a ta had'a wannan adalar kotu da Galadima kai tsaye .

Alk'ali ya bada damar hakan.

Dandanan kuwa aka had'a Galadima da kotu, Wanda dama shi tuni yana ganin duk abinda sukeyi, sunedai basa ganinsa.

Galadima dake zaune a falon gidan da yake tsare dasu harun ya mik'e tsaye domin girmamawa ga alk'ali, sannan ya gabatar da sunansa kamar haka,  ya mai shari'a sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, ma'aikaci a hukumar bincike ta DSS .

Wani sabon kallon kallon aka koma, Wanda yaja hankalin mutane fiyema dana d'azun, hattada y'an masarautar gagara badau basusan da wannan aiki Na Galadima ba.



Alk'ali ya kuma tsawatarwa, sannan ya maida hankalinsa ga Galadima yana fad'in  To Muhammad Sameer minene alak'arka da iyayen yaran dakake rik'e dasu, danmu ka rikita mana tunani, da farko kallon Criminal muke maka, saikuma gashi sunanka yafito a d'aya daga cikin manyan hukumominmu Na tsaro masu muhimmanci? .

Murmushi Galadima yayi yana gyara tsayuwa, ya hard'e hannayensa a k'irji yana sauke numfashi da cije lips, yace,  ya mai shari'a wannan labarine mai tsawo, amma tabbas abinda lauyana ya fad'a shine gaskiyar zance, Camera dake hannun Alhaji Auwal Fharuk itace babbar alak'ar dake tsakanina dasu, wadda nad'au tsawon shekaru akan nemanta, sai a shekararnan ne cikin watanni shida nasamu labarin inda take dukda banida tabbacin ita d'ince, bansan mike cikin camera d'inba, amma su Alhaji Balala duk sun Sani, tunda har suka iya salwantar da rayuka da yawa akanta, shi kansa Wanda suka hara a yanzu ALLAH ne kawai yasaka yanada tsawon rai, amma da tuni sun kasheshin, ni kaina rayuwata tasha hare-hare iri-iri harda jariran yarana da aka sace kwanaki 7 kacal da zuwansu duniya .

Alk'ali da yay shiru yana sauraren Galadima yaja dogon numfashi yana ta faman jinjina kai tamkar k'adangare yaga abinci mai manja=�1�>�-�.

Yace,  lallai wannan Court tana buk'atar jin cikakken bayani daga Muhammad Sameer Saifuddin, dan haka ta d'aga wannan k'ara zuwa nan da kwanaki uku masu zuwa, kotu tana bama y'an sanda Umarnin subar Muhammad Sameer Saifuddin ya fito daga wannan gida a ranar da Court zatayi zama Na gaba batare da koda masa hararaba, sannan kuma kotu ta bada Umarnin a cigaba da tsare su wad'annan mutane guda 11, likitoci kuma su cigaba da bama Alhaji Auwal Fharuk kulawa ta musamman dan shima kotu Na buk'atar ganinsa a zama Na gaba saboda son sanin mike cikin camera d'in . Alk'ali ya buga gudumarsa yana mik'ewa.

Gaba d'aya kowa ya mik'e har alk'ali ya shige.



Galadima yay wani k'asaitaccen murmushi yana zaunawa cikin kujera bayan shigewar alk'ali.

Muftahu, Nuren, dasu Harun dake zaune gefe suma suna kallon komai tun farkon Shari'ar duk sunyi mutuwar zaune tun lokacin da Galadima yafad'i kasancewarsa cikin hukumar C.I.D.

Ameer ne kawai yay murmushi yana k'amewa da salute d'in Galadima.

Shima baki sake su Nuren suka bishi da kallo suna nunashi alamar dama yasani shi?.

Murmushi yay musu har hak'oransa Na bayyana ya had'e hannayensa waje d'aya alamar tuba a garesu.





&.....................................&





Yau kam Galadima wani farin ciki Na musamman ya tsinci kansa a ciki, ya shige d'akin da yake matsayin nasa a yanzu ya fad'a gadon yana rungume filo idonsa Na zirar da hawaye, ko a haka aka tsaya lallai yaci nasara, dan ya nunama su Alhaji Abdul-Naseer d'an zaki ya girma.

Wayarsa dake saman gadon a can gefe yasa hannu ya janyo, ya kunnata, massages ne sukaita shigowa a jere-jere kamar jira, bai bud'e ko wanneba ya shiga binciko number Munaya, ya dad'e yana kallon Number amma ya kasa dialing, yaja wasu seconds kafin yatsansa ya sauka akan number ya danna kawai.



Munaya Na zaune a falo tare da su Ayusher da kullum sai sunzo, d'an kunne ne ya shige cikin jikin Amaturrahman yanata cin jikinta basu saniba, sai yau da an ta6a fuskarta koyaya saita fashe da kuka, Munaya tarasa mike damun yarinya, dukta rikice ita kanta, saida laraba tace ta bata nono, tana kwantar da ita ta wajen kunnen sai takuma d'ad'ewa da kukan da Munaya ke jinsa har cikin jini, d'agota tayi tana duba wajen, Laraba tace,  Anya ba kunenta ke ciwoba? .

Munubiya dake kusada Munaya ta amshi Amaturrahman ta kifata a cinyarta tana dubawa, sai taga d'an kunne ne ya shige Ashe duk bayan kunnen yayi ruwa, tsoro ya kama Munubiya, cikin zaro ido waje tace,  innalillahi, d'an kunne natacin kunen yarinya bamu saniba . Da an fara k'ok'arin ciremata saita kuma fashewa da kuka tana mimmik'ewa, gwaggo safiya data shigo yanzu saboda jiya ta iso akan abinda ya faru da Abba, ta k'araso cikin falon tana fad'in  mike faruwane? .

Bayani feena tai mata, gwaggo safiyya ta kar6i Amaturrahman tana cewar asamo mata ruwan d'umi da k'aramin handkerchief.

Ana cikin hakane Galadima yayi kiran Munaya, tashitai tabar wajen tana had'iye kukan dake shirin taho mata saboda tausayin yarinyar.

'Dakinsu ta shiga, ta fad'a saman gadonsu ta kwanta tana amsa wayar.

A hankali Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana gyara kwanciya. Murya can k'asan mak'oshi yace,  babu fad'a miya kawo gaba yalla6iya? .

Murmushi Munaya tayi tana share hawayenta. Tace,  Kodai Kaine za'aima wannan tambayar? .

Jimm yayi saboda jin muryarta ba ayanda yasaniba. yace,  mike faruwa kike kuka? .

Mamaki ya kama Munaya, ta Yayama ya gane kukan take, cikin k'ok'arin kare kai tace,  ba kuka nakeba yalla6ai, ina yini .

bai amsa gaisuwarta ba yace,  kina wasa da sanin danai miki ko? . Yay maganar cikin d'an kausasa murya.

Munaya sai bataji dad'iba, tace  kayi hak'uri, dama Amaturrahman ce d'an kunne ya shigema a jiki taketa kuka, amma gashi can suna cire mata d'an kunnen .

Babu shiri Galadima ya tashi zaune yana fad'in  k ya akayi har d'an kunne ya ringa cin jikinta baki saniba? Anya kuwa kinason yarannan Munaya? .

Wani haushine ya kamata, tama rasa mizata Ce masa.

Shima bai jira amsartaba yace,  maza ki tashi kuje asibiti a dubamin yarinya, karkuce zakuyi gangancin cire mata a gida wata matsalar ta biyo baya .

 Uhumm . Kawai Munaya tace ta yanke wayar.

Ta jefar da wayar gefe tana hawaye, shi kawai yaransane damuwarsa, harma zaice yafita sonsune dazai dinga jifanta da bata sonsu kulum-kullum, itafa wannan Abu yafara kaita bango wlhy.



A can kuwa shima Galadima duk sai yaji ya damu, jiyake tamkar yay tsuntsuwa yafita yakai yarinyarsa asibiti da kansa, amma babu damar hakan.

Ya dad'e jikin window tsaye yana kallon mutane daketa zirga-zirga a anguwa da police d'in dake zagaye da gidan har yanzu.



Fita munaya tayi dan ganin ko ancire?, ta iske an cire ana gasa kunnen, Amaturrahman taci kuka harta koma ajiyar zuciya, Gwaggo Safiyya tace,  zoki zauna kibata tasha sai'a k'arasa gasawar .

Zuwa Munaya tayi ta zauna tana kar6ar Amaturrahman.

K'in k'ar6ar nono tayi, sai ajiyar zuciya taketayi, Laraba tace,  yaranan zuciya irinta Magajin gari suke da ita, yanzu inba sa'a ba bazatashaba .

Dariya su Ayusher sukayi.

Dak'yar dai Munaya ta turama Amaturrahman nono abaki ta kar6a. Akad'an kuma gasa kunnen dayay uwar huda naman wajen yafita sosai, k'ofar tazama babba.

Munaya dake kallonta tasaka hannu tana goge mata zufar data taru mata a goshi, saikace wata babba.



Galadima yanata kiran Munaya yaji kosun tafi asibitin amma bata d'agaba, dayake ta bar wayar a d'akinsu.

Saida Ayusher taje d'akin ta gano, ta d'akko da sauri ta kawo mata tana saka mata a kunne.

Maganarsa kawai munaya taji yana fad'an ina ta ajiye wayar.

Ajiyar zuciya ta sauke tabashi hak'uri kawai, dan bata buk'atar jan maganar.

Yace,  kunje asibitin? .

Munaya tace,  An cire mata ai, babu wata matsala tunda bai ta6a cikiba .

Ca yay ta d'auka hoton wajen ta turo masa yagani, kamar tace bazatayiba sai kawai ta cire wayar ta katse kiran, hoton wajen ta d'auka ta tura masa .



Tausayin yarinya ya kamashi ganin yanda wajen yay cinye sosai, Yakuma kiran Munaya yana jaddada mata karta sake akuma sakamata wani d'an kunne.

To kawai ta amsa masa dashi dan a zauna lafiya.







..............................&





Tun daga ranar Munaya bata sake jin Galadima ba, saboda yayi busy da yawa akan shirye-shiryen shari'ar dake gabansu, dan fatanshi wannan zaman yazama zama Na k'arshe insha ALLAH.





Alhmdllh jikin Abba anata samun haske sosai, dan sauk'i yana samuwa iya gwargwadon iko.



RANAR DA ZA'A KOMA KOTU................
'<���









Hummm=�,�



ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���



BOOK 3 =�I�<���1� 8�





.................Yauma dai kotun ba'a cewa komai, wad'anda ma basuzo zaman farkoba yau sunzo, Dan su sir Isa duk suna wajen da muk'arabansa, hakama tawagarsu Tanderu, Dan suma lauyansu a cewarsa yau yazo da sabon shiri, ranarma an mamesa ne kawai.

��



Galadima yagama shirinsa tsaf cikin wani lallausan yadi sky blue dayasha d'inkin boda, Dan rigar iyakarta Rabin cinyarsa, kayan sunmasa k'yau matuk'a, danya fito ainahinsa Na jinin Hausa Fulani, ya Mirza hularsa sky blue itama, fuskarnan tayi fayau Dan hardasu gyaran fuska yayi abinsa, danma ya tabbatarma mak'iya yana cikin farinciki fiye da zatonsu, yana cikin saka sock's Nuren ya lek'o yana fad'in  Brother ka hanzartafa mun makara .

 umhum kawai yace masa yacigaba da saka kayansa a tsanake kamar yanda yafara, danshi komai saurin dazaiyi akan Abu to anutse zaiyi abinnan, ganin haka sai kawai Nuren ya ida shigowa, ya durk'usa gabansa yana kama k'afar daya sakama sock's d'in ya saka masa takalmi.

Baki Galadima ya tsa6e yana cewa,  kaifa shegen gaggawane dakai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login