Showing 348001 words to 351000 words out of 365757 words

Chapter 117 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1491

kuma mabiya wannan addini masu tsananin ak'ida, Galadima ya ta6a sanarmin iyayensu sun dad'e basu saki jiki dasuba saboda kasancewarsu musulmai kawai, Gopal kusan sa'anni suke dashi amma babu wata shak'uwa tsakaninsu. To tayaya suke tunanin k'ulluwar aure a tsakaninsu inba Gopal musulunta zaiyiba, hakan kuma abune mai wuyar gaske, dukda ba'a yanke hujunci da ikon ALLAH.

Ana gobe zamu wuce saudia Galadima ya sallami Khumar da kuku, wad'anda suke kuka da idanunsu na bak'in cikin rabuwa damu, muma kuma hakanne, sai da Galadima yamusu bayani akan badan shima bayason rayuwa dasu ya sallamesuba, sai dan karya tauye hak'insune, yabasu Dama suje su nemi wasu ayyukan, duk sanda ya shigo k'asar zai nemesu su dawo kan aikinsu insha ALLAH.

Sunyi murna sosai da bayaninsa, haka muma munji dad'in hakan, domin kuwa dai ba'a rabuba kenan.





KOMAI YAY FARKO...=�-�=�N�<���





Zai iya zama k'arshe watan watarana, yau ga Abie daya shigo India cikin tsananin ciwo da fidda rai daga rayuwa zai barta cikin farin ciki da k'warin gwiwar rahma da falalar ubangijin al'arshi. Fuskokinmu kawai sun isa shaida maka muna cikin farin ciki muma.

Mun tafi cikin kewar India da jama'ar cikinta, musamman ma Momma da Abie da tunda suka shigota sai yaune zasu barta.

Tunkan mu Isa Galadima ya sanya Sultan nema mana masauki.

Muna sauka kuwa cikin mutunci akazo aka d'aukemu zuwa matsakaicin gida dazai d'aukemu babu wata takura.

Har kuka saida nayi a 6oye ganina a inda ban ta6a zato ko tsammaniba, kasa mai tsarki.

Hutun wannan ranar kawai muka samu, washe gari muka duk'ufa ibada da godiyar Ubangiji bisa ga ni'imomi dayay mana badan munfi sauran bayinsa da komaiba.



Tsawon kwana goma muna bautar Ubangiji, a randa ake saran ganin wata jirginmu ya d'aga zuwa k'asarmu ta haihuwa, Abie da Momma sunfi kowa zumud'i da k'aguwa.

Babu wanda yasan da zuwanmu sai Sarkin Mota, shima kuma bashi da tabbacin dawa za'azo d'in, Galadima dai yace ya saka a gyara masa 6angarensa da inda su Aunty Mimi ke sauka.





*****



Jirginmu ya sauka 9ja k'arfe 11:30pm. Mu muka fara fitowa, Abie da Galadima suka zama k'arshe.

Abie na sauka a jirgin yana Murmushi da hawaye, tareda shak'ar iskar k'asarsa daya bari tsawon shekaru, yama fidda ransa da kuma dawowa cikinta har Abadan.



Sarkin Mota da dogaran Galadima suna zaune a airport d'in suna jiran isowarmu.

Ganinmu da yawa yabasu mamaki, amma saisuka zube suna gaishemu, a cikinsu babu Wanda ya gane momma da Abie, Bama zai yuwu su ganesu d'inba, tunda sanda yabar k'arsar duk basa a wannan matsayin, sai dai iyayensu, wanda a halin yanzu mafi yawa acikinsu duksun rasu ma.

Dole saida muka k'ara da motocin haya, Momma da Abie suka shiga wadda sarkin Mota ke ja, Ni da Galadima da Samha muka shiga ta haya d'aya, Aunty Mimi da Yaa Sauban da yara suka shiga d'aya.



Mun Isa Masarautar tsit babu yawan hayaniya alamar mafi yawan al'ummar cikinta sun nutsu waje d'aya, sai wasu tsirarun hadimai dake kai kawo mussamman masu tsaro.

Duk muka fito amma banda su Momma, Galadima ya nufi mortar dan son taimakawa Abie fiwo, Sarkin Mota kuma na k'ok'arin biyan masu motarnan kud'insu.

Fir Abie yak'i fita, yace d'an uwansa mai martaba ne kad'ai zai fiddashi a motar, duk rok'on da sukai masa fir yak'i, gashi yanata sharar hawaye da handkerchief.



Galadima yasan yanzu Mai martaba ya shiga ciki, maybe ma matar dake dashi taje.

Rasa yama zaiyi yayi.

Momma Ce tabashi shawarar kiran wayar mai martaba, cikin damuwa Galadima ya kar6a wayan Sauban dabe dad'e da barin k'asarba, sim card d'insa zaifi saurin aiki fiye da nashi.

Hadiman gidan sund'an fara fuskantar akwai matsala gameda tsayuwar su Galadima, dan wannan ba halinsa bane.



ALLAH ma ya taimaka Mai martaba baiyi barciba, yana zaune ne yana duba wasu takardu, matarsa ta biyu na tare dashi dan yau kwanantane. Ya dad'e yana kallon wayar da nazarin mai kiransa, dan ba kowane keda Number mai martaba, sai jiga-jigai irinsu Galadima d'in.

Tamkar bazai d'aukaba yad'ai d'auka tana gab da katsewa a kira karo na biyu.

Cikeda girmamawa Galadima ya gaishesa sanann yay masa bayanin shine.

Da farko mai martaba tsorata yayi, dan babu Wanda yasanar masa Galadima ya dawo, cikin hikima da girmamawa Galadima yayma mai martaba bayanin yafito yaga abin mamaki a k'ofar sashensa.

Sosai mai martaba yayta juya kalmar abin mamakin, hakama matarsa, alk'yabba ta d'akko masa ya saka sannan suka fito a tare.

Jakadiya na niyyar tafiya makwancinta taci karo da mota a k'ofar turakar mai martaba, mamaki ya kamata, zatayi magana saitaga Galadima dake tsaye a jikin motor, ta rusuna tana gaisheshi, kamar yanda yasaba ya d'aga mata hannu cikeda izzar mulki.

Bata fita a mamakinba taga mai martaba da matarsa sun fito.

Galadima baice komaiba sai bud'e murfin motar da yay yana nunama mai martaba ciki da hannu.



Jikin baiwar mama Fulani mai kai mata rahoton motsin kowa na rawa ta nufi sashenta, hartayi shirin barci ma ta sallami Kuyanginta, amma dayake baiwar tanada fada sosai a wajen ta saita mata knocking k'ofa.

Cikeda masifa da izza mama Fulani ta bud'e k'ofar, jikin baiwarnan na rawa ta zube k'asa tana fad'in  Ki gafarceni ranki ya dad'e, abinda nagano yafi k'arfin barinsa zuwa safiya, yalla6ai Galadima ya shigo fada shida sauran iyalan tsohon sarki, maimakon yawuce sashensa tamkar yanda ya saba saiya nufi turakar mai martaba kai tsaye, gashi can naga yana nuna masa Abu amota, ban tsaya ganiba na nufo gareki ya uwar gijiyata .

Ai mama Fulani bata tsaya bata amsaba ta figi alk'yabba ta saka tana fitowa, baiwarnan ta take mata baya.



A can kuwa Mai martaba da mamaki ya kalli Galadima, amma sai Galadima ya girgiza masa kai yana sake nuna masa cikin motar.

Matsawa mai martaba yayi sosai domin ganema idonsa abinda d'an d'an uwansa keson ya gani, Momma ta kunna fitilar dake motar dukda haske mai k'ayatarwa daya haske ko ina na masarautar.

Koda mai martaba ya lek'a saiyay baya a zabure, cikin rawar baki da nuna motar yace,  Sameer yaushe kuma ka fara shirya min wasa da hankali har irin haka? .

 Ka gafarceni ranka ya dad'e, abinda kagani zahirin gaskiyane, wannan d'an uwankane ya dawo gareka cikin k'oshin lafiya da hukuntawar Ubangiji . Galadima ya k'are maganar da rank'wafawa ya taimakama Abie ya fito, itama Momma ta fito.

Hakan sai yayi dai-dai da isowar mama Fulani wajan. Da fuskar Momma mai d'auke da k'asaitaccen murmushi tafara tozali, ta k'araso gabanta da sassarfa tana rik'o hanunta da fad'in  Zeenah! .

A take Momma ta juya gareta, dan ko a mafarki bazata manta mai wannan muryarba, batareda tunanin komaiba ta rungumeta.

Yayinda shima takawa ya rungume Abie daga can.



Tun a wannan daren labari yafara karad'e masarautar, wasu kan basu aminceba kwata-kwata, burin kowa gari ya waye yayi kallon zahiri ba jita-jita ba.

Dole matar mai martaba ta koma sashenta, dan mai martaba yace Abie a sashensa zai kwana, jiyake idan ya barsa zuwa wani sashe tamkar da safe zai wayi gari yaga ba hakaba.

Itama Momma a sashen mama Fulani ta kwana tilas, yayi da mukuma muka nufi namu da yasha gyara ko ina yake need tamkar muna k'asar.



Yau dai kam na murzu wajen Galadima, acewarsa murnar sallah ce, dukda gajiyar tafiya darashin samun isashen barcin da muka tara a Saudia bai d'agan k'afaba, a cewarsa yamayi k'ok'ari, kwana nawa.



WASHE GARI



A Washe gari antashi da farin ciki guda biyu a masarautar gagara badau, Murnar Salla da dawowar Abie.

Dan zuwa safiya kam tabbataccen labari daga bakin sank'ira ya isa kunnen kowa, harma da k'yak'yk'yawan albishir na halattar sallar idi tareda Abie.

Kafin kace mi labari yafara fita wajen masarautar, su papi ma tun a Daren Galadima ya kirasu da wayar Sauban dake hannunsa.

Batareda sanin ya akayiba saiga magana tafara shiga kunnuwan jama'ar gari da y'an jarida, wasu gidajen TV Dana redio suka fara sanar da wannan zance dawasu ke k'arya tawa kansu tsaye................
'<���











ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���

[7:09 PM, 8/21/2019] +234 813 508 4146: Typing=���







=ء�HASKE WRITERS ASSO....





f&RAINA KAMA...!!f&

(Kaga gayya)





Bilyn Abdull ce>��<���

_______

Tawan miss xoxo tawa ni kad'ai, wannan gaisuwar takice ke kad'ai da babbar murya my dear, ALLAH ya bar mana zuminci mai d'orewa har Abadan, ke ta dabance a zuciyar bilyn Abdull, ina yinki irin Trillion's d'innan wlhy, na gaisheki da gaba d'ayan ahalinki da tawagar y'an Group d'inki na HOME OF NOVELS baki d'ayansu, alkairin ALLAH yakai gareku har gadon barci My Hafsy>�8�<���
@&=��=�M�<���.



_________







BOOK 3 =�I�<���3� 0�





...............Da asubahi na tashi jikina cike da gajiyar tafiya da wadda boss ya k'aramin, daga sallar asubahi bai samu dawoba, Dan ana fitowa salla dukan ahalin gidan mai ruwa da tsaki sun hallara ne ga yima Abie barka da zuwa dakuma tabbatar da gaskiyar zancen, domin tabbatar musu da kokwantonsu mai martaba yabasu damar ganin Abie d'in tareda shelar Sank'ira. Wannane dalilin yad'uwar zancen dawowar ta Abie har a wajen masarauta.



Dukda gajiyar dake tare dani bansamu komawa barciba, nashiga k'imtsa gidan iya bedrooms d'inmu zuwa nashi sashen da babu wata baiwa dakeda lasisin shiga. Sauran guraren zuwa kitchen kuma bayina dasukayo asubancin zuwa sashen saboda jin nadawo ne keta k'ok'arin gyarawa.

Na fito da nufin komawa d'akina na tashi yara na musu wanka cikin bayina d'aya ta zube Guywoyinta a k'asa tana fad'in  Ranki ya dad'e ga sak'on kayan abincin salla nan daga sashen mama fulani .

Cikin d'an mamaki Na kalleta tareda kayan abincin dake jibge, sai naman kaji cikeda k'atuwar roba irin wadda ake tarama mai jego ruwan wanka. Katsemin tunani tayi da kuma fad'in,

 Ki gafarceni ranki ya dad'e, wannan al'adar mama Fulani Ce, a duk daren salla takan aikama kowanne sashe Na y'ay'anta da manyan gidannan irin wannan kayan, yanzu zama a k'araso da sauran, kowane sashe dasu yake abincin salla .

Kaina Na jinjina tareda zama bisa kujera ina d'ora k'afa d'aya kan d'aya da kallon baiwar dani nama mance sunanta a yanzu. Nace,  Oh, yama sunanki? .

 Ranki ya dad'e Umimi .

 To Umimi wace shugabar hadiman sashen nan? .

 Nice rankai ya dad'e .

 Ok, ya zamuyi kenan? gashi mun kasance lokacj a k'ure, Dan yanzun kinga kusan 6:23am, bamuda isashen lokacin abincin salla kenan .

 Ranki yadad'e ki gafarceni, zamu iyayi insha ALLAH, tunda kinga ai munada yawa .

Shiru nayi inad'an nazari, saikuma Na sauke numfashi ina mik'ewa damata nuni muje kitchen d'in.

Alhmdllh inada kaso mafi yawa Na buk'ata, saidai abinda ba'a rasaba, Umimi nasaka ta tattaro sauran suka shigo da kayan, Dan danan suka fara rage aikin, ni kuma Na fito nad'an rubuta sauran abinda nake buk'ata nabama baiwa d'aya da kud'i takaima Sarkin Mota yabama wani ya sayomin.

Badansu Abdurrahman sun tashiba Na tadasu duknai musu wanka, shirin sune yad'an jani lokaci abinka daba d'ayaba, gashi sunfara wayo, sauk'i nama d'aya Umimi babbar macece kuma Na yaba da tsaftarta. Duk da dai namusu gargad'in jira nazo Na had'a komai da kaina. A gurguje nayi wanka nasaka simple gown dabazata takurani wajen aikiba, nasaka k'aramin hijjab Na fito nabarsu Abdurraheem a d'akin, insha ALLAH bazasuyi kukaba, Dan saida cikinsu yay taf sannan Na fito.

Naji dad'in iskesu sunci rabin aikin, to kusan su 15 kowa da abinda yakeyi. Dannan nasaka hannu nima wajenyin abinda yakamata ace ni nayi d'in, Dan Sarkin Mota yakawomin sak'ona tuni. Sannan ankawo sauran kayan daga sashen mama Fulani.



8:00am dai-dai Galadima ya shigo sashen, saboda yazo yay shirin massalaci, mamaki ya kamashi jin k'amshi ya baje ko'ina, shidai yasan bai tanadi komai d'aya danganci abincin salla ba.

Yana cikin tunanin Sauban ya shigo d'auke da k'atuwar ledar kayanda zai saka, Wanda tun muna India yabada umarnin a dink'a masa su.

Tare suka shiga sashensa da tunanin ko inacan, dukda yasan bazanbar y'an aiki akan girkiba, Dan yakula inada son komai naima kaina musamman girki.

Babu abinda ke tashi sai k'amshi mai dad'i anan d'inma, ga ko ina yayi k'al gwanin sha'awa da birgewa, saidai kuma tsit alamun babu kowa.

Sauban ya Shiga bedroom d'insa da kayan shima yana biye dashi.

Cikin sigar tambaya Galadima yace,  to ina take itada yaran? .

K'aramar dariya Sauban yayi, yace,  Yaa Sam kasan halin auntyn tamu dai, Na tabbatar k'amshin girkinnan daga sirrin iyawartane, kaga kenan tana kitchen  .

Hararsa Galadima yayi, Sauban ya rufe baki Dan tuna ta6argazar da yayi.



Ina cikin aikin Sauban ya shigo, bayin duk suka zube suna gaisheshi, da farko nama zata ko Galadima ne, saida Na waigo naga Sauban.

Bayan ya d'aga musu hannu dabasu izinin tashi ya kalleni yana fad'in  Aunty gimbiya kinsani jin yunwa mai yawa da wannan k'amshin girkin naki .

Murmushi nayi kawai ina wanke hannayena, nace  ALLAH Yaa Sauban akwaika da tsokana, ya gajiya .

 Ai tabi gado wlhy, tare muka shigo da Yaa Sam fa .

Nace,  Ok". Coffee Na had'a masa a k'aramin filas Na d'ora a tire mai k'yau da mug daduk abinda zai iya buk'ata.

Kar6a Yaa Sauban zaiyi nace,  A'a kabarsa Na hutar dake nikam .

Yay murmushi,  shikenan Aunty, inagafa nima zuwa zanyi Na shirya yau idin Na musamman ne ga jama'ar masarautar gagara badau .

 Gaskiyane Yaa Sauban, ALLAH yasa yau asamo mana amaryarmu .

Dariya yayi yana yunk'urin fita,  lallaima Aunty d'an k'araminnan dani wazai ban y'arsa? .

Ban samu bashi amsaba ya fice, Nima sashen Galadima Na Shiga INA murmushi.

Babu kowa a falon, Dan haka Na wuce bedroom d'insa.

Sallama nayi kawai Na shige. A bakin gado Na iskeshi zaune d'aure da towel, da alama wanka zai Shiga. Murmushi mukaima juna. nace,  Afuwan my King, aiki ya d'auke hankalina bansan ka shigoba .

Murmushi ya kumayi yana wani lumshe ido, Na ajiye tiren saman k'arim copy table d'in gabansa sannan Na zauna kusa dashi Na kwantar da kaina gefen kafad'arsa bayan Na sumbaci damtsen hannunsa .

Shima saiya karkato fuskarsa gareni ya shafa tawa fuskar da tattausan hannunsa, cikin magana rad'a-rad'a yace,  miya kaiki aiki keda ke tare da gajiya? .

Idanuna na d'ago na kallesa ina murmushi, nace,  my king ai yakamata ace anyi abincin salla a sashen Galadima, wannanfa shine karon farko da zakayi bikin salla da matarka a masarautar nan, bai kamata ace anyishi babu wasu alamuba ai OK? .

Yanda nai maganar da kashe ido d'aya saida tsigar jikinsa ta tashi, yad'an lumshe ido da sumbatar goshina, sannan ya rad'amin  ALLAH yay miki albarka acikin kunne.

A saman la66a na amsa da  Amin .

Ya tambayeni yara nace,  suna d'akina, maybe ma sunyi barci. Bamu tsaya 6ata lokaciba muka Shiga na taimaka masa da wanka, sannan muka fito nahau shiryashi, dukda lokaci yaja a nutse nake masa komai, danshi ma'abocin son komai a nutsene, bayason gaggawa ko yawan sauri koda a magana ne kuwa.

Inamasa shiri yana shan coffee, kaga d'an gatan Munaya.=��

Tsaf na shiryashi cikin farar shadda daduk salla yakanyi amfani da ita wajen idi, nakawo babbar riga na saka masa sannan na fesheshi da turare, ajiye mug d'in hannunsa yayi yana d'aukar hularsa zanna bukar daketa maik'o yay mata kari ya kafa bisa kansa yana dai-dai tawa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login