Showing 30001 words to 33000 words out of 365757 words

Chapter 11 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1441

zuciyar sarauniyar sarakuna.

Duk abinda ke faruwa Momma naji kuma tana gani, amma dayake Galadima yana bayan laptop d'in bataga miyayiba, hasalima bataji ko sau d'aya yayi magana ba, hakanne ya tada hankalinta, mama Fulani Na barin wajen ta katse call d'in, waya ta d'auka takira number Galadima, amma harta tainke bai d'agaba.

Kira Na biyu ta sakeyi, hakan yay dai-dai da shigowar Galadima falon dafe da kansa.

Da k'yar ya iya d'aga wayar, muryarsa a shak'e yace,  Momma zan kigyaki anjima bai jira cewarta ba ya yanke wayar.

Hankalin Momma yakuma tashi, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, da sauri ta danna kiran Harun, yana d'agawa ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace,  Harun maza jeka duba min Moh'd yanzunan .

Yanda yaji Momma Na magana shima kansa saiya kid'ime.....







&.&.&.&.&.&.&.&.&.&





Ayusher tafita tasiyo min credit domin kiran Fu'aad.

Jikina a sanyaye nagama loda katin, tunani nakeyi shin Fu'aad zai kar6eni bayan yaji abinda yafaru a jiya zuwa yau? tunda komai akan idonsa yafaru. Na dad'e ina juya wayar a hannu kafin Nayi dialing d'in Number d'insa d'in, harta tsinke bai d'agaba, ban damuba Na sake kiransa da tunanin ko baya kusa da wayarne.

Bugun farko kuwa ya d'aga wayar...........
'<���







Humm masu karatu, mi kuke tunanin zai faru tsakanin Munaya da Fu'aad a waya, zai kar6eta kokuwa sa6anin haka?.

Yaya zata kasance ga Galadima kuma?.



Wannan amsar tana a page 12 da zaizo muku ranar Monday=��=�L�<���.







Barkanku da juma'a.



Musha weekend lafiya>��<���>�p�>�p�.









Team *_INNARO & MAMA FULANI_*>�t�>�t��&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&.









*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*=�-�=�O�<���

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�1� 2�





.......Murya a sanyaye Munaya tace,  Assalamu alaika .

 wa'alaikissalam .  wata murya ta amsa sa6anin Fu'aad .

 Uhhm 'yar uwa please, ko ina mai wayar dan ALLAH? .

 Mai wayar kuma? ai nice mai wayar .

Wani iri munaya taji a zuciyarta, suka kalli juna itada Munubiya dan a Hans free tasaka wayar. alama munubiya tamata akan tayi magana. kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace,  ayya 'yar uwa sorry dan ALLAH, wlhy wanine yabani number d'innan mai suna Fu'aad .

 Fu'aad! .  yarinyar ta maimaita daga can , saikuma tace  to gaskiya 'yar uwa yabaki wrong Number, ni sunana Afnan, ina Katsina state ne .

Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Munaya,  shikenan ngd sis..., kiyi hak'uri .

 no babu damuwa .

Bayan Munaya ta katse wayar ta dafe kai tana hawaye, daga Ayusher har Munubiya basa Neman k'arin bayani, tunda sunji komai, Munubiya ta share hawayenta tana murmushin takaici,  kibarshi karki sake kiranshi, nasan shine yabama yarinyar nan wayar akan tace wrong number ne, ya ALLAH ka kawo mana sauk'i a wannan lamari dai .

Tsaki Ayusher taja, ta kamo hannun Munaya  sweet sis..., please wannan karya zama abinda zai ta6a zuciyarki, ki d'auki hakan matsayin ba komaiba, kuma hakan da Fu'aad yayi yasani kuma tabbatar da zargin danake a kansa, ku duba yanda yazage saimunje birnin gayu plaza aranar .

Gaba d'ayansu zuba mata ido sukayi cikin wani yanayi.

Feena dake kwance tatashi zaune,  humm aini wlhy tunda zancen jaridar nan yafito zargina yana kan Fu'aad ne, Na barine akirashi dama danna sake tabbatarwa .

Munubiya tace,  sisters nifa duk Na kasan fahimtar zancennan naku fa, zargi babu k'yau ai, miye ribarsa idan ya aikata hakan? dukama yaushe muka San juna dazai yi hakan a garemu? yarasa kuma dawa zai mana hakan sai galadima? .

Zama Ayusher ta gyara, tafara musu bayani dalla-dalla.  tad'ora da fad'in kinsani ko saboda galadiman yayi? .

 to amma Dan zaima Galadima mu miye Na had'awa damu kuma? .

 wannan amasar tana wajen Fu'aad sister  .

Hankalin Munaya yatashi ainun, itafa ko kad'an bata ta6a kawo Fu'aad acikin wad'anda take zargiba, amma maganar Ayusher tasata dogon nazari yanzu, duk da dai bawai tama yarda baneba kwata-kwata..







&&&&&&&&&&



Lokacin da harun ya iso sashen Galadima bai wani jira isoba yashiga, kwance ya iskeshi bisa 3seaters sam6al, hannunsa d'aya dafe da k'irji, d'aya dafe da kansa.

Da sassarfa ya k'arasa gabansa  Sameer lafiya kuwa? .

Da hannu Galadima yamasa nuni da k'irjinsa da Kansa.

 ya salam, Sameer! Shiyyasa naketa cemaka kacire abunnan a ranka, kafasan matsalarka batason yawan takura da tunani . Wayarsa dake ringing ya Ciro a aljihu, Momma Ce ke kiransa.

Cikeda girmamawa ya amsa sallamar data masa, sannan naji yace,  wlhy Momma bashida lfy, kuma k'irjinsa yake complain akai .

 ok Momma  .

Yana yanke wayar sai yayi kiran Dr Jalal.

 Jaalal please kana gida kuwa? .

Bansan wace amsa ya bashi ba daga can, naji dai yace,  please kazo kaduba Galadima .



Babu dad'ewa saiga Dr Jaalal, damuwa sosai Nagano a fuskarshi saboda ganin halin da Galadima yake ciki.

Harun ya taimaka masa suka kaishi bedroom, sannan yamasa allurar barci.

Babu dad'ewa kuwa barcin ya kwasheshi.

Su duka ajiyar zuciya suka sauke, Dr jaalal yama harun sallama yatafi.

Yana fita Muftahu Na shigowa, gaisawa sukayi da Harun, sannan ya tambayi jikin Galadima d'in.

Harun ya amsa masa Cesar da sauk'i.



Anan sashen Galadima suka kwana, sai dai kowanne acikinsu da dalilin kwannan nasa.



*_Washe gari_*



Alhmdllh Galadima yatashi jikinsa da d'an sauk'i, yakuma ji dad'in ganin Harun da Muftahu a tare dashi. bai iya zuwa masallaciba sai a d'aki yayi salla.

Yana zaune akan sallayar yana azkar su Muftahu suka shigo, zama sukayi bisa Sofa suna jiran yak'arasa azkar d'in nasa.

Bayan ya k'arasa ya juyo garesu, hannu ya mik'a musu sukayi musabaha, suka tamyashi jikinsa.

Yace da sauk'i Alhmddlh, sannan yace,  Muftahu inason ticket, dan yau zan wuce India, ina buk'atar ganin doctor d'ina .

 ok babu damuwa, bara na bincika idan akwai jirgi mai zuwa India daret .

Harun yamik'e yana fad'in  bara ahad'a maka ruwan wanka to .

Kai ya d'agama harun, ya maida idonsa ya lumshe tareda jingina da Waldrop.

Muftahu dake latsa waya yad'ago ya kallesa,  babu jirgin dazai tashi a yau, sai gobe 1:30pm .

Batareda ya bud'e idonsa ba yace,  bincika min ta Abuja ko legos. dan bazan iya kuma kwana a k'asar nanba yau, ina buk'atar ganin lilita .

Kai Muftahu ya jinjina ya cigaba da latse-latsensa a wayar, kusan mintuna 4 sannan yad'ago,  an samu, amma zai biya Abu-Dhabi ya sauke Passenger's, daga nan zasuyi hutun kamar na 1hour .

Idomsa a lumshen yace  yaushe zai tashi daga Nan? .

 12pm, yanzu na saya maka ticket d'in zuwa Abuja, jirgin zai tashi 8am ne .

 Ok bara na shirya to .

Harun dake tsaye yana saurarensu yace  bara naje Na watsa ruwa nima .

Shima Muftahu mik'ewa yayi suka fita tare.

Galadima yashiga bathroom, kusan mintunansa 40 sannan ya fito, dauriya kawai yakeyi, amma shi kad'ai yasan irin suyar da zuciyarsa ke masa. tsaf ya shirya cikin Suit blue, rigarshi ta ciki Orange, yayi k'yau sosai, yana zaune bakin gado yana saka takalminsa Muftahu yashigo da sallama.

d'ago idanunsa yayi akan Muftahu, sannan yatashi tsaye yana gyara belt nashi,  ya maganar binciko yarinyar nan? .

 Nagama komai, inason kasami nutsuwane sai muyi maganar daman .

Galadima dake gyara 'yar sumarsa da bawani yatarata da uban yawa bane yace  ok, katura min komai zan duba, sannan inason kaje kuyi magana da commisshiner of police akan iyalan Manager d'innan .

 ok yalla6ai angama insha ALLAH .

Sallamar Harun suka amsa gaba d'aya, ya zauna kan sofa sannan yace  amma yakamata ma'aikatan plaza su koma aikinsu, naga jama'a kamar suna fassara abin dawani Abu daban kuma .

Murmushin gefen baki galadima yayi, ya ajiye Cumb d'in hannunsa yajiyo yana kallonsa  aini yanzun kuma babu kuma ta sigar dabaza'a fassara ni ba, inaga akan mace kawai yarage jaridu su buga duniya ta ganni, so sukoma aikin su kawai .

Daga Harun har Muftahu kallonsa suke cike da tausayawa. Muftahu yace wannan d'inma kansu sukai mawa, kuma ALLAH bazai barsuba .

 insha ALLAHU .  cewar Harun .

Galadima baice komaiba, sai d'an kimtse kimtsen da ba'a rasabane ya k'arasa, su Harun kam suka fice suka bashi waje.

Baifi mintuna 10 ba yafito suka fice, bayan yatsaya da bayinsa na mintuna biyar, bansan miya fad'a musuba, naga dai sunata faman godiya damasa addu'a.

Aka bud'e masa mota yashiga, duk wanda yake k'ark'ashimsa saikaga fuskarsa ta canja alamun baya son tafiyar tasa.



Kai tsaye fada suka nufa, bayan motocin sun tsaya aka bud'e masa yafito.

Shi kad'ai yashiga fadan, cike take da dukkan masu ruwa da tsaki anata fadanci.

Saida ya gaida sarki, sannan ya zauna mazauninsa kusada sarkin, sauran fadawan suka gaidashi cikin girmamawa, shima ya amsa cikeda mutuntawa.

 ya adalin sarkinmu yau zan koma inda na fito, saboda inason ganin likitana .

Murmushi sarki yayi, sannan ya gyad'a kai bare da yayi maganaba.

Da sauri Dogarawa suka d'auka da fad'in Sarki yajika Galadima, Yakuma amsa, yana maka addu'ar sauka lfy kuma.

 ina godiya da wannan alfarma .  galadima yafad'a cikin rissinar da kai alamun girmamawa .

Sarki yad'an gyara zamansa, ahankali ya furta  ka gaidamin da d'an uwana da gimbiya Zeenah, insha ALLAH nima nextweek ina nan zuwa .

 ina godiya ranka shi dad'e, insha ALLAH d'an uwanka zaiji .

 gyad'a kai kawai sarki yayi .

 An gaisheka galasima, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya kaika lafiya yabama adalin tsohon sarki lafiya, Alkairin ALLAH da ni'ima sukai a garesa, gaba dai gaba dai Galadima mai jiran gado, d'an sarki jikan sarakuna k..... .

Hannu ya d'aga musu alamar ya Isa.

Ya risinar da Kansa domin girmamawa ga fada sannan yamik'e suna jera masa addu'oi, yayinda shikuma yake amsawa asaman la66ansa.



Bai shiga sashen kowaba yay tafiyarsa, suna isa filin jirgi ko 20 minutes basuyiba jirgin su yatashi zuwa Abuja.

Muftahu da Harun da dogaransa suka dawo cikeda kewarsa.

Koda ya isa Abuja hotel yanufa kai tsaye, yakama d'aki danya huta, akwai kusan 3hours nan gaba kafin jirginsu ya tashi. Rigar suit d'insa yacire tareda tie d'in, sannan ya zame wandon da rigar cikin ya kwanta dagashi sai boxer da vest.

Juyi kawai yakeyi agadon, Dan barci yakasa d'aukarsa, abinda yafaru a kwanaki biyunnan yakasa barin zuciyarsa, yarasa wane irin hasashe zaiyi ga masu aikata masa hakan... Ringing d'in da phone nasa tayine yasakashi bud'e idanunsa, wayar yajawo yana kallon mai kiran. *_Sweet papi_* yagani ajikin wayar, yay saurin d'agawa kafin ta tsike.

Cikeda girmamawa tamkar yana a gabansa ya rissinar da kansa bayan yatashi zaune,  Barka da hantsi ranka ya dad'e .

Daga can aka amsa  da yauwa Muhammad, ina fata kana lfy? .

 Alhmdllh ranka ya dad'e .

 To masha ALLAH, dama mamanka Ce takirani takemin wasu bayani, duk da kafin kiran nata dama naga zantukan dake yawo a jaridu da yanar gizo, zuciyata bata yarda zaka aikata hakanba Muhammad, amma inason sanin gaskiyar zancen? .

 wlhy ranka ya dad'e sunyi hakanne kawai domin 6atamin suna, amma ainahin abunda yafaru shine.............

Nan Galadima ya zayyane masa komai.

Murmushi mai sauti tsohon yayi, har Galadima Na jiyosa, sannan yace,  hummm! to yanzu kai kana wace nahiya ne? .

 Ina Abuja zan koma India, saboda jikina yana Neman motsawa .

 to to, hakanma dakayi dai-daine, amma a kwantar da hankali, komai mai wucewane, komai kaga yafaru da d'an Adam rubutaccene a littafinsa, dama ita rayuwa tana tafiyane da k'addara, yanzu zan isa fada, bayan kasamu nutsuwa idan kaje zamuyi magana, duk da watak'ilma nashigo ganin mahaifin naka k'arshen watannan .

 to shikenan, ngd sosai, ALLAH yak'ara tsahon rai da lafiya mai amfani .

 amin ya rabbi Muhammad cikin tsokana tsohon yace  kaga d'annema, duk kabi ka susuce akan k'aramin Abu, kazo Na sanmaka jarumtata mana .

Dariya Galadima yayai (karon farko danaga yayi dariya=�J�=��) cikin tausasa harshe yace  haba dai, ai sai dai Na sammaka tawa, nifa sabon jinine, ta ina mai shekaru 80+ zai fi mai 29 jarumta? .

Daga canma Sarki dariya yayi, cikeda k'aunar jikan nasa,  uhmyim tunda kace haka idan kazo saimu gwada kwanji ai .

 hhh tom kafad'ama inno ta tsumaka sosai, inba hakaba zatayi takaba .

 ja'irin gora zan kamakane ai, ALLAH ya tsare hanya, ka gaida iyayen naka .

 zasuji ranka ya dad'e, a gaidamin inno, tayi hak'uri wannan karon ban shigo naci tuwon taba, nazo k'asarne da uzurori dayawa, gashima banyi ko d'ayaba .

 zataji insha ALLAHU, babu komai, adage dai da addu'a watarana sai labari, *zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi jikana kaji*.

Murmushi Galadima yayi dan jin maganar kakan nasa, sukayi sallama cikeda k'aunar juna .



Ajiye wayar yayi yakoma ya kwanta fuskarsa d'auke da murmushi, yana k'aunar kakansa (mahaifin Momma) saboda shima yana nuna masa k'auna da kulawa, akan la66ansa ya furata  ALLAH ya k'aramaka tsawon rai my sweet papi .





Amin Galadima.

�&<���
@&bara nalek'o su munaya.









&&&&*&&&*&&&&



Bansan yanda zan musalta muku irin bak'in cikin danakeba a yau, tundaga kiran Fu'aad zuwa yanzu zuciyata sai suya takemin, banida wata walwala, sai dai ina dannewa kodan kwanciyar hankalin innarmu da 'Yar uwata Munubiya, dama tun randa abunnan ya faru bamu sake fita koda tsakar gidaba dagani har 'yar uwata, abinci sai dai innarmu kosu Aryaan su kar6o mana.

Habaici dai da gugar zana muna shanshi acikin gidanmu, innarmu bata cemusu uffan, nikuma mai maida murtanin damuwa ta hanani iya cewa komai, 'yan biki dai zuwa yau kowa yakama gabansa, yanzu dagamu sai mune agidan.

Sauk'inmu d'aya tun ranar innaro bata sake shigowa gidanba, inaga baba mai kanwa yahanata.

Babu Wanda yay mana maganar komawa makaranta, muma kuma bamuyi yunk'urin zuwanba, kullum dai innarmu NATA k'ok'arin ganin munkwantar da hankalinmu, a koda yaushe cikin mana nasiha take dayimana kwatance da rayuwarta itada mama Rabi'a, takan Nuna mana muhimmancin hak'uri da amfanin yinsa, koda baka ci ribarsa anan gidan duniyaba zakaci ribarsa a lahira inda kowa ke rububin tara ayyukan alkairi.

Alhmdllh muma mun fara rage damuwar kodan ganin farin cikinta, Abu d'ayane kecin zukatanmu shine maganar fidda miji da Abbamu yace nayi acikin sati biyu kacal, gashi kuma babu wani tsayayye a hannu.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login