Showing 150001 words to 153000 words out of 365757 words

Chapter 51 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1471

gayya, tafiyar hawainiya bashike nufin gazawar kuzarinta bane, lokuta da dama hanzari kan katse igiyar cikar buri, a sannu kowa zai fahimci wanene *_RAINA KAMA....._*=�N�<���

https://2gnblog.blogspot.com/

Ba Nuren ba hatta da sarkin mota maganganun Galadima ya shigeshi, tabbas mutane dayawa sunama Galadima kallon mutum mai yawan sakaci da rashin ho66asa, koshi yana d'aya daga ciki, amma wannan zantukan nasa sai suka sakasu a rud'ani, kenan akwai abinda sud'in basu saniba...........

Dole tunaninsu ya katse saboda isowarsu gidansu Munaya.



Fita sarkin mota yayi yanema musu iso, babu dad'ewa saiga baba k'arami ya fito, sarkin mota ya bud'ema Galadima, yayinda Nuren ya bud'e da kansa, zuciyarsa sai jujjuya hannunka mai sandar Galadima yakeyi.

Dukda baba k'arami yayi mamakin zuwan Galadima haka ya danne, yaymusu k'ar6a ta girma, sannan suka shiga cikin gidan.

Gidan tsitt tamkar babu mutane, saikace ba gidannan bane mai kama Dana 'yan dambe=��, (yo kowa Na tsoron a korashi gidansu>�#�=��).

A falon daddy aka musu masauki, dan danan aka cika musu gaba da kayayyaki, baba k'arami ya fita domin basu damar cin wani Abu.

Babu abinda suka ta6a, dukda kuma Galadima ma yunwa yakeji, a haka daddy da baba k'arami suka dawo.

Daddy yace  anya kuwa wannan d'an namu yana d'aukar gidannan matsayin nasu? .

Murmushi Galadima da Nuren sukayi, Galadima yace  sosaima daddy .

Baba k'arami yace  ta INA zamu amince da haka kuwa, bayan inada tabbacin ko ruwan gidannan Baka ta6a sha ba .

Kunya Ce ta kama Galadima, sai kuma yaga bai k'yautaba, ya rissinar da kai yana fad'in  amin afuwa zan gyara .

Mik'ewa baba k'arami da daddy suka kumayi,  to mun bada dama ta biyu . cewar Dady yana dariya.

Bayan fitarsu Nuren ya bud'e kulolin shima yana dariyar, danbun shinkafane daya samu nutsuwa ta musamman, sai k'amshi mai dad'i yakeyi, daga Galadima har nuren saida kwad'ayin cin abincin yazo musu.

Kallon Galadima Nuren yayi yana d'aga gira, Galadima yay murmusa tareda fad'in  kadaiji kunya .

 kaima jinta zakayi yanzu, dan nasan ci zakayi .



Yau dai kam Galadima yaci abincin gidansu Munaya, kuma gashi girkin innarsu, babu kunya sukaita zuba Santi shida Nuren sunama juna dariya, Galadima harda su6utar baki yana fad'in  amma my mata muguwace, bata ta6amin irin wannan ba .=�@�

Mi Nuren zaiyi inba dariya ba>�#�, su Galadima anji dad'i har kwalwar kai Baki ya bud'e=��=��.



Saida suka mammala tsaf sannan su baba k'arami suka dawo, sunji dad'i dasuka iske sunci.

Daga nan sukayi gaisuwa, su baba k'arami suka d'ora da godiyar d'awainiyar Abba da Galadima ya d'auke musu.

Murmushi kawai Galadima yayi.

Nuren ya gyara zama, a ladabce yamusu bayanin son fidda Abba da Galadima kesonyi, dan likitoci sunce ana buk'atar kulawa saboda karayar hak'ark'arinsa data k'ugu,  to yanzu haka dai angama setting d'in komai gameda tafiyarsa, har asibitin daza'a kaisa, visa d'insa da komai, sai dai anason tafiya da mutum biyu a cikinsu, mi kuka gani akan Wanda za'aje da shid'in? .

Daddy da baba k'arami suka kalli juna, summa rasa wane irin farin ciki zasu nuna dan Galadima yasan sunji dad'i? sunta jero masa k'yawawan addu'oi, kafin daddy yace  ai kawai sai atafi da jafaru da Ai'sha, dan bai kamata mutafi mu duka ba gida babu kowa, dukda akwai su Anas, gakuma su Hameed zasuke zagayowa, amma hakan yafi dai.

Duk sun gamsu da hakan, dan haka suka buk'aci passport d'in baba k'arami da inna, ita inna babu, sai sunje an mata, amma baba k'arami an samu.

Sun bari akan zuwa anjima za'azo akai inna tayo.

Daga nan Galadima ya buk'aci number da aka kira aka sanar musu da accident d'in Abba.

Daddy yace Ai'sha aka kira, saidai akawo wayar tata. Kiranta yay yace tabama cikin su Aryaan ya kawo wayarta.

Babu dad'ewa saiga Aryaan d'in da ita, yanda yaron ya gaishesu saida abin ya birge Galadima, ya yarda yaran gidan akwai tarbiyya babu laifi kam.

Galadima yace,  amma Dady ko numbers nawa Abba ke amfani dasu? .

baba k'arami ya bashi amsa da cewar  uku ne .

Nuren yace  kozamu samesu dukansu? .

Dukda baba k'arami da daddy sunshiga mamaki, dansu zukatansu basu kawo musu akwai wani Abu a k'asa ba, sun d'auka kawai Abba yayi Accident ne dai.

Baba k'arami yabasu Numbers d'in duka.

Bawani bincike Galadima yayi a wayar innarsu Munaya ba, wani Abu kawai ya saka (Wanda Nima ban saniba=�1�) yabama Dady wayar yana fad'in  zata bar wayar anan dan a can bazatayi aikiba, kuma gashi muna buk'atar wayar, dan haka daddy saika rik'e a hannunka tunda kai kana gida .

Dady ya amsa da to, duk su Galadima sun kuma sakasu a duhu.

Sallama sukai musu suna fito domin tafiya.

Harsun Shiga mota saiga Aiyaan da gud'u d'auke da wata Leda.

Sarkin mota ya tareshi yana fad'in yaro miya farune? .

 Auntynmu za'a kaimawa inji innarmu .

Galadima yayma sarkin mota nuni da yabar Aiyaan d'in ya k'araso.

Bud'e murfin Galadima yayi, Aiyaan ya k'arso, Galadima ya kamo hannun Aiyaan yana murmushi,  my friend ya akayi? .

'Uncle innarmu ce tace akaima Auntynmu dan ALLAH .

murmushi Galadima yakumayi, sannan ya kar6i ledan yana fad'in  ita kad'ai banda ni? .

Aiyaan yad'an zaro ido waje, sai kuma yace  to bara naje Na fad'am innarmu kaima ta baka naka .

Da sauri Galadima ya kamo hannunsa dan yana neman tsillawa da gudune,  kaga dakata, idan naje saimu raba wannan da ita, yanzu dai ka fad'ama innarmu ta shiryaka gobe zan aiko a d'aukeka kazo ka zauna damu tunda kuna hutu  .

Cikin murna Aiyaan yace,  wajen auntymu? .

Galadima ya jinjina masa kai.

 to amma kuma Aryaan fa? .

Cikin mamaki Galadima yace,  wanene Aryaan d'in? .

 lah baka San mu 2wins bane ba? .

 da gaske? .

 ALLAH kuwa .

 to shikenan, kacema innarmu ta shiryaku Ku duka biyun zakujema Aunty hutu .

Cikeda murna Aiyaan ya shek'a da gudu gida danya kai labari.

Galadima yay murmushi yana rufe k'ofar motar, Nuren ma murmushi yakeyi, a fili yace,  yara sunyi wlhy .

Galadima ya kalleshi, cikin d'age gira sama yace,  kayi aure .

Sosai Nuren yay dariya.





******

A inda suka d'auki Nuren anan suka ajiyeshi, su kuma suka koma masarauta, sun iske tuni dogaran sun dawo abinsu.

d'akinsa ya Shiga, ya iske Sauban nata barcinsa.

Bai tadashiba, yadawo falo ya zauna.





_____________________________





Da daddare Galadima Na falonsa zaune yana aiki a system akayi knocking d'in k'ofa, izinin shigowa ya bada, sarkin mota ya shigo hannunsa d'auke da leda.

Galadima dake aikinsa bai d'agoba, a haka ya amsa gaisuwar sarkin mota.

Sarkin mota yace  ranka ya dad'e kayi mantuwane a mota  .

d'agowa Galadima yayi ya kallesa, ganin ledar da Aiyaan ya kawo yatuna masa sak'on munaya, nuni yama sarkin mota daya ajiye.

Sarkin mota ya ajiye yana masa saida safe.

Nanma bai tankaba, kansa kawai ya jinjina masa.

Bayan fitar sarkin mota ya mik'e d'auke da laptop d'insa da ledar, dama tunda ya shigo baima lek'a ta ba, dan Sauban yace yakai mata abinci, kuma tun d'azu suna tare suna hira. Hakan yasa yagane shine ta raina kenan. wannan haushin ya hanashi Neman inda take.



A bakin gado ya isketa zaune tagama waya da Munubiya, k'in d'agowa tayi ta kallesa, tadai amsa masa sallama.

Shima bai kula taba ya zauna bakin gadon d'an nesa da ita.

Shiru kowa yayi suka share juna, haushi ya turnuk'e Galadima, lokaci yayi dazai daina d'agama yarinyar nan k'afa, yakamata su goga raini shi da ita. ta gefen ido ya saci kallonta, sai wani cika da batsewa takeyi, ya cije lips nashi.

 k baki iya gaisuwa bane? .

Saida takuma tura bakin sannan tace  ina yini tana mik'ewa da nufin bar masa d'akin, tana k'unk'uni

Bai amsata, sai mik'ewa da yayi shima, matsawa tashiga yi baya yana binta, fuskarsa a matuk'ar d'aure, da jikin bango ta manne, shikuma ya mata runfa, hannunsa d'aya a dogare da bangon yayinda yasaka d'aya ya rik'o hannunta ya matsa da k'arfi, zatai magana ya jawota tafad'o jikinsa, ya manne bakinsa kan nata, duk yanda taso kwatar kanta hakan ya gagara, dan ya kama hannuwanta biyu ya murd'esu ta baya yanda ta kasa koda motsi. A haka ya wulk'itata takoma saman gadon, shima yabi bayanta.

Ya d'ora hannunsa kan bakinta dan karta ishesa da tsiwa, idonsa ya saka cikin nata ya hanata kata6us, cikin tsare gida yace  dolene yau Na kora miki warning na musamman danki ringa banbance inda zakiyi tsiwa .

Bai bata damar dazata fad'i nata ba yashiga aikata yanda yakeso da ita>�%�=�F�<���.................
'<���







Kutttt Galadima auren Contract nefa=�1�=��, ba ruwana kaida masoyan Munaya aradu>�#��&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&>�'�.





i miss you wujiga-wujiga my sweet fans=��=��=��=��>�s�.



















*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=�O�<���=�-�

*_Typing=���_*







*_Haske writer's asso...._*=ء�









*_f&RAINA KAMA......f&_*

_{Kaga gayya}_







*_Bilyn Abdull Ce_*>��<���







~Book 2~ =�I�<���9�





.................Salon nasa yasani bashi ragama, dan Galadima yazo min da sabon salo mai tafiya da gudun jini dana zuciya.

Duk da kasancewata farin shiga, hakan bai hanani gane Galadima Na daban bane, kamar yanda kuka sanshi mutum mai izza da k'asaita, hakan bai canja ba ta wannan fanin, komansa a nurse da izzar k'asaita yake gudanar dashi. ban tashi farga nayi kuskure ba saida labari yafara nisan zango, anzo wajenda tsorosa yafara tasiri a gareni, Sai dai kuma nayi sakacin da Galadima yazama kurman dutsen dabaya ji baya gani. Sai lokacin hawaye suka fara ambaliya ga fuskata, hannayena na k'ok'arin d'agawa domin rok'o, sai dai ya hanani wannan damar gaba d'aya..........





>�%�=�F�<���kai babu ruwana, iya nan nagani nima>�+� aradu aunty Magajiya da aunty Ni'ima zasuci k'aniyata ne idan na k'arasa fad'a=�1�>�-��&<���
@&�&<���
@&�&<���
@&.





Tabbas na gurzu, dan yau na banbance tsakanin aya da tsakkuwa, banbancin baya cikin hayyacinsa da yau d'inma kad'anne, dukda babu yanda za'ayi daren farko yayi dai-dai da kowacce rana ta bayansa.

Duk ajiyar zuciyar danake saukewa yana jina, amma yay luf a gefena, hakan ne Yakuma tunzurani, a zalinceka akasa lallashinka saboda jin kai, wlhy kasaitar bawannan tayi masa yawa, duk randa yazama sarki kam fadawa sunga takansu, dan magana dai idan sarki na uku a fada toshi bazaiyi ko guda d'aya ba=��.

Galadima daduk yake sauraren kukan nata da ajiyar zuciya ya juyo kad'an yana fuskantarta, hannu yasaka ya tallafo fuskarta ta matso dai-dai da tasa, jinai kawai ana huramin iska saman ido, tsaf na fahimmci iskar bakinsa yake huramin, amma saina dake nak'i bud'e idona.

Muryarsa can k'asan mak'oshi ya furta  my friend are you okay? .

Banza na masa, nakuma k'i bud'e odon, lallai mutuminnan yacika d'an latsin rainin wayo number 1, yanzunan Galadima har yanada bakin yimin wannan banzar tambayar?, idona a rufe har yanzu na bud'e baki cikin salon tsiwa zan maka masa bak'ar magana, amma saiya d'ora yatsansa saman bakina yana fad'in  shiiii!>�+� da bakinsa, shirun kuwa nayi kamar an rufemin bakin Dan Nina Na tuna illar yin tsiwar.(=��=��)

Ya matso dani jikinsa ya rungume, hannunsa na buga gadon bayana k'ad'an-k'ad'an, ya d'ora bakinsa saitin kunnena,  yanzu kin gane banbancin Sameer da Munaya right?, idan kuma har yanzu baki fahimta ba to bakinki ya cigaba d'amin tsiwa OK?, nikuma bazan gaji da punishment nashi ba sala-sala yalla6iya=؋� .  ya k'are maganar da sumbatar cikin kunnena .

Babu shiri na k'ank'amesa dan har cikin kwalwar kaina naji sumbar nan.

Kad'an ya buga bayana sannan ya janyeni daga jikinsa ya sauka daga saman gadon.

 hasbinallahu wani'imal wakil na iya maimaitawa kawai, na k'ank'ame pillows d'in gabana ina rintse idanu da cije lips (copy copy=��).



Kusan mintuna 15 duk nazata yama fitane, sai kawai jinai an d'aukeni. a razane na bud'e idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, da matuk'ar Sauri na maida nawa na lumshe.

Wani muskilin murmushi Galadima yayi yana cije lips.

Ba shiri na bud'e ido, saboda jina cikin ruwan zafi, yunk'urawa nayi zan mik'e cikin 6ata fuska ya maidani ya zaunar yana fad'in  za6i ya rage naki, zama kiyi da kanki, kokuma ni nayi miki..

Banma bari yakai k'arsheba na koma na zauna ina kare k'urjina.

Kafad'a ya d'age sama yana ta6e baki da fad'in  hummm .

Fita yay daga bathroom d'in ya rufe mata K'ofar.



Na kai tsawon lokaci a bayin ina Gasa jikina, dan nasan idanma banyiba kaina nama mugunta, saida naji ko ina ya saki sannan nayi wankan tsarki ina hawaye, bansan yanda zan fassara wannan muguntar ta Galadima ba kuma, wannan karon kuma tsautsayin zaice kokuwa ba yin Kansa bane?.

Haka dai na kammala na d'aura towel d'ina, a zuciyata ina addu'ar ALLAH dai yasa ya fita, dan towel d'in guntune, bai gama rufe cinyoyina bama baki d'aya.

Da sand'a na fito, yauma inajin zafi kad'an-kad'an, amma ba kamar na ranar ba. ganin baya d'akin saina ida rufe k'ofar na tako cikin d'akin sosai.

Ina neman kaya a wardrobe ina share hawaye, indai rashin tsiwar dayake fad'ace na daina masa, dan bazan zauna ya illatani a banza ba, wannan k'addararren cikinma daya hanamin gangar jiki hutawa da ciwuka ya isheni, basai na cigaba da 6alloma kaina wata muguntar tasa ba.

wata 'yar riga mai d'an nauyi-nauyi na samo, na cirota dan sanyi nakeji, juyowar da zanyi saina gansa zaune bakin gado yana danna laptop, hannunsa d'aya rik'e da glass cup yana shan fresh milk hankali kwance.

Saida nad'anja baya, nakuma bud'e rigar ina kare jikina.

Duk abinda takeyi yana kallonta ta gefen ido, amma yawani share kamar baima San da itaba.

Da bin bango da sand'a na koma bayin, ta gaba kuma ina karewa da rigar.

Saida ta shige ya d'ago kai yana kallon k'ofar bayin, saikuma ya girgiza kai yana murmushin gefen baki. cigaba yayi da aikinsa a nutse.

Barci nakeji, ga zazza6i yafara rufeni, hakan yasa ina gama saka rigar na fito, naci serious kawai sannan na fito.

d'ago idanu yayi muka had'a ido, da sauri nad'an rankwafa inajan rigar barcin k'asa wai danta rufemin cinya zuwa kwauri.

Baki ya ta6e yana wani janye ido cikeda basarwa. Irin shi baiga abin kallo d'in nanba.

Ni kuma na dalla masa Harara ina k'ok'arin hayewa gadon.

 ji mana .  yafad'a cikin izza .

Banza na masa zan haye gadon.

Yace  iyim, bakije daddarawa ba kenan yarinya, saina sake kaiki yanzunnan.... .

Kafin ya rufe baki nama iso gabansa na tsaya.

d'agowa yayi yana kallona yana kur6ar fresh milk nashi, ya d'agamin gira d'aya.

Baki na turo masa ina share hawaye.

Ya kamo hannuna ya zaunar kusa da shi,  nikam yalla6iya karki haifomin abin cikin kwan da halin kuka, bana son ragwan taka, 'yata ko macece jaruma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login