Showing 3001 words to 6000 words out of 365757 words

Chapter 2 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1426

tamkar gasa wajen za6o 'ya'yan manya, dan kuwa Aisha ce kawai d'iyan talakawa acikinsu, tana zaunene kawai da k'arfin ALLAH dakuma Na Malam faruku, saikuma soyayyar mijinta Auwal, amma da dan ta innaro ne da tuni Auwal ya saketa.

Akwaima randa fada ya had'a mairo da Aisha akan Rabi'a ta doki hameed saboda yamata rashin kunya, dukan da mairo taima Rabi'a saiya sa Aisha kasa hak'uri a ranar ta tanka mata, nankuwa mairo tafara zuba mata gori da cin zarafi, da innaro tazo danjin ba'asin rigimar saitace dole Auwal yasaki Aisha, dukda kuma mairo ce mai laifi, Auwal yayta magiya amma innaro tace yaza6a ko ita ko Aishan, babu yanda zaiyi yasaki Aisha saki d'aya alokacin. Hankalin Aisha yatashi matuk'a, dan batasan inda zasu dosaba, tunda basuda kowa a Nigeria, ga innaro tsaye akanta tace atake saita bar mata gidan d'a.

ALLAH ya tak'aita abunne dai-dai sanda Aisha ke fitowa rik'eda hannun Rabi'a kuma saiga Malam faruku yadawo daga kasuwa, nanfa ya tambayi ba'asi, Aisha tasanar masa komai, maidata yayi gidan, yakuma saka Auwal ya maida aurensu atake awajen, sannan ya tabbatar masa ko bayan babu ransa yasake sakin Aysha bai yafeba, kuma inhar innaro tasake sakashi ya saketa itama abakin aurenta.

Wannan shine dalilin dayasa auren Aisha da Auwal bai sake rawaba. rayuwa kuma tacigaba da shurawa. Matan gidanmu 7.

Auwal matansa uku, Aisha (innarmu) Mairo (mama) Sadiya (gwaggon haleema)

Hameesu nada biyu, Ruk'ayya (umma) Hadiza (momy)

Jafaru Nada biyu shima, Suwaiba (maman safara'u) Hafsatu (maman Fauziyya).

Kowacce ta haihu acikinsu, amma banda Aisha, wadda saida sukayi shekara 20 da aure itada Auwal sannan ALLAH yabata ciki, zokiga murna wajen Auwal da ahalinsa, saidai banda matan gidanmu da innaro, dan aganinsu duk sunfi Aisha matsayi, (maman fauziyya) Ce kawai babu ruwanta, dan suna d'asawa da Aisha sosai, ita kad'aice bata raina innarmu ba, dan Yaya ma take cemata.

Babu irin wahalar da Aisha batasha agidanba acikin shekarunan, kullum cikin mata gorin haihuwa dana talauci ake, harma dana batada asali, tundaga kishiyoyinta har matan k'annen mijinta basu raga mataba, kowacce jitake ina wuta tasaka innarmu a gidan, dama ga d'aurin gidi daga innaro suna samu. innarmu bata cemusu komai, saidai tashiga d'aki tasha kukanta, 'ya'yan maman fauziyya ne kad'ai ke shigowa d'akinta, amma sauran duk an hanasu, gashi ta aurar da Rabi'a tuni, itama harta haihu uku ma.

to saikuma ga Aisha da ciki rana tsaka, bayan tagama fidda ran haihuwarma gaba d'ayanta. cikin ikon ALLAH cikinta yakai haihuwa, ranar data haihu saiga 'yan biyu k'yawawa kamarta duk mata, A zahiri matan gidanmu suna k'untatama innarmu ne saboda yanda innaro tagama 6ata Aisha awajensu, a bad'ini kuma suna k'in Aishane saboda tafisu k'yau da komaima Na halittar jiki, (dan cikakkiyar buzuwa Ce) mai k'yawu Na asali, dirarriyar macece doguwa, fara tas, gashin kai, idanu da komai ALLAH yabatasu. Sa6anin su daba haka sukeba. cikin ikon ALLAH kuma saigashi ta haifo 'ya'yanta masu tsananin kama da ita.

Hassana (Munubiya) da Hussaina (Munaya) wad'anda suke matuk'ar kama da juna, kamar Munaya da Munubiya ta 6aci matuk'a, ko Aisha saitayi da gaske take banbancesu, saida suka fara girmanema ake d'an banbantasu tawajen halayya shima ba kowaba, amma Aisha ita tana ganesu kai tsaye a sanan.

Munubiya tanada hak'uri tamkar Aisha, duk wahalar dasukesha wajen yaran gidan bata iya ramawa, saidai tasha kukanta tashare hawaye. sa6anin Munaya da take fitinanniya, bata bari a cuceta, koda anfi k'arfinta saitabi tawata hanyar tarama kuwa, wannan yasaka matan gidan da yara sukafi tsanarta, sai dai kuma basa iya banbancesu itada Munubiya, sometimes Munaya takanyi laifi akama Munubiya a daka, itakuma Munubiya bazata ta6a fad'in ba itaceba.

Ganin hakan yasaka Aisha yima Munubiya shaida saboda aringa banbantasu, amma Munaya Na k'yalla ido tagani sai itama tayima kanta irin ta Munubiya komai da komai, idan sau dubu akama Munubiya shaida ajiki Munaya ma zataje taima kanta, hakama Munubiya takanyi idan anyima munaya, hakan yasa Aisha ta hak'ura kawai harma suka Shiga makaranta, nanma rikicin Munaya bai k'areba, dan saima abinda yay gaba, tajawo fad'a akama Munubiya adaka, hakan kuma bazaisa gobe ta fasaba.

Shekarar su goma Aisha takuma haihuwar 'yan biyu duk maza, Aryaan da Aiyyaan, tundaga lokacin kuma bata sakeba.

Sai dai Munaya da Munubiya suna matuk'ar k'aunar junansu over abinma har saiya Baka mamaki, sannan suna k'aunar mahaifiyarsu da k'annensu, Munaya ce kan shiga idan ana cin zarafin mamansu, amma ita Munubiya saidai taita kuka.



Yanzu haka zancen danake muku shekarunmu 19 nida Munubiya, muna matakin farko a jami'a, munzama 'yan mata, k'yawunmu da tsananin kamarmu da innarmu yasake fitowa, mun fita daban a gidanmu, dan mukad'aine kamarmu daban, Ayyan da Aryan ma duk Abbanmu suka kwaso, wannan yasaka suke kama da 'yan gidanmu.

Tabbas bamajin dad'in zaman gidanmu, saboda k'unci da hantara damuke fuskanta muda mahaifiyarmu awajen Innaro da matan gidan, harma dawasu yaran gidan 'yan uwanmu, amma wasu muna shiri dasu sosai, musamman ma mazan yayyenmu manya, dansu babu ruwansu da gutsiri tsomar cikin gidan.

Gidanmu gidane tamkar gidan hayar daya had'a k'abilu daban-daban saboda yawan rikici, kullum cikin fad'a muke, ba iyayenba ba yaranba, kai kace muna ganin hanjin junane.

Gwargwadon iko akwai hali a gidanmu, dan iyayenmu sun rik'e gidanmu sosai da buk'atinmu, dukda yawa da ALLAH yabamu, bamu rasa ci da sha ba da situra, hakama matsalolin karatunmu, dan kai tsaye zance gidanmu gidan 'yan bokone, kullum cikin gasa da juna ake, burin kowa ace shine gaba, batun ilimin addinima kam Alhmdllh, dan tsaye iyayenmu suke akanmu, har gobe yaa hameed bai daina zama gaban malamai ba balle mu 'yan baya-baya. ak'alla yaran gidanmu munkai mu 43 kuma.

ALLAH yayma Malam jafaru kakanmu rasuwa shekara biyu kenan, innaro Ce dai tana nan daram, al'amuranta sai abinda yay gaba, dan har gobe bata k'aunar innarmu, kuma bata daina cin zarafinta ba agaban kowa da mata gorin rashin dangi.

Hakan yasa kullum cikin buri da k'udirin binciko dangin Innarmu nake, ko itama zata samu 'yancin kanta kamar kowa=�"�.



Wannan shine labarin gidanmu, sai ahankali zaku cigaba da fuskantar ainahin halayen jama'ar gidanmu da aiyukansu, harma da sunayensu=�
�.............
'<���









To masu karatu, sai nace yanzufa za'a fara, saiku kasance dani danjin labarin *_RAINA KAMA.... kaga gayya_* dan akwai babban al'amari a gaba, bawai gidan su Munaya kawai labarin ya shafaba, akwai wani lauje cikin Nad'i daga d'ayan 6angaren labarin Na Raina kama.....=� � suga gayya ba=�N�<���=��.













One luv>�p�















*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu=�-�=�O�<���_*

[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*











*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���3�



.........Fad'a sosai innarmu tamin akan Marin Safara'u danayi, sannan ta d'ora da nasiha kamar yanda tasaba, wani kam yashiga kunnena, wani kuwa tabaya yabi, dan harga ALLAH Na daina zama kowa yana taka mana mahaifiya a gidan.

Innarmu tace,  ku shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Ku tafi gidan mamanku Rabi'a Ku k'arasa hutunku, banason zamanku a gidan nan tunda fitina yake kawowa .

A sanyaye Munubiya ta amsa da  to innarmu .

Amma ni saina tunzuro baki gaba ina k'unk'uni, dan banason tafiya ko ina, canma saboda d'an mama Rabi'a d'inne Marwan, ko kad'an bama shiri dashi, saboda masifarsa.  kai innarmu, yanzu dan ALLAH saboda wasu can bazamu mik'e kafa yanda mukeso ba agidanmu, duka fa hutun sati biyu ne kacal, amma saimunje wani waje?, ni wlhy inkika barni babu mai k'ara mana koda kallon banza a gidannan, harma innaro bazan bartaba.........

Maficin danaga innarmu tajawo yasani tashi da sauri nabar gurin, Na tabbata shirin bugamin takeyi. Munubiya ta saka dariya tana kallona,  ke ga rashin arzik'i ga tsoron tsiya, dukan maficin kikema wannan gudun? .

Harara Na balla mata,  yo k'ya fad'i haka mana tunda ba jikinki baneba, tsoro kam kinsan waye matsoraci acikinmu ai .

Munubiya ta ta6e baki  naji dai, koma mizaki ce kije kiyita cewa, inama kayana dakika saka jiya? na wanke, dan dasu zanje .

Wayar innarmu Na d'auka ina dannawa, batareda na bata amsaba Na nuna mata laundry basket d'inmu.

Innarmu tace,  to Aljanar waya ajiyemin kafin ki k'ararmin kud'in ciki, ina taki? .

 kai innarmu, please mana, zan kira Ayusher nefa nasanar mata muna zuwa gobe, ALLAH wayata babu ko nera aciki Munu ta cinye min jiya .

 kiji tsoron ALLAH munaya, Nina cinye mini kud'in waya? bake kika kira Balkisu ba da kanki? .

 to dana kirata sai nace kuyita surutu har kud'ina ya k'are

innarmu Na shirin yin magana muka jiyo kururuwar kukan Safara'u da Rahama. dariya Na k'yalk'yale da ita, ina fad'in  o, ALLAH ga yaa hameed can yana gwajin kwanji a jikin gayu .

Harara innarmu ta ballamin, saikuma tamik'e tana shirin fita, nasan kar6arsu zataje, nai saurin fad'in  kai innarmu, kid'an barsu su lallasu mana .

Dakk'uwa ta watsomin tareda fad'in  K'aniyarki Munaya .

Dagani har Munubiya dariya muka sanya harda tafawa kuwa.



Ba'a rufa mintuna 3 da fitar innarmu ba muka fara jiyo hargowar Maman safara'u (dama ita bata magana a hankali) Yaa hameed takema masifa akan dukansu safara'u dayakeyi, maman su yaa hameed babu hak'uri, itama tafito suka fara cacar baki, yaa hameed kam ficewarsa yayi bayan innarmu ta kwaci su Rahama a hannunsa da k'yar. kafin kace mi gidan yakuma kaurewa.

Munubiya tace,  kai jama'a ko breakfast ba'ayi agidanba har antafi wrestling zagaye na biyu .

Na fad'a saman gado ina Dariya, danni mamaki 'yan gidanmu nakeyi da bala'insu. wayar Innarmu tayi ringing, da Sauri Na duba sainaga Abbanmu ne, cikeda d'oki Na amsa tareda masa sallama sannan Na gaidashi.

Yace,  Munubiya ina maman takune? .

 Abba ba munu bace, nicefa .

 to to munaya ce? hayaniyar mi nakeji haka agidanne Munaya? .

K'yafta min ido da zungurina Munubiya tashiga yi wai karna fad'a masa (dayake a Hans free nasaka wayar, tana jin komai) amma saina harareta da murgud'a baki nace,  Abba Mama Ce da maman safara'u suke fad'a .

Tsaki yaja da fad'in  ALLAH ya shiryesu to, ina maman taku ne? .

 Amin Abba, Innarmu tana can wajen rabon fad'an ai .

 shike Nan, idan tashigo kice takirani muyi magana .

 to Abba bye .

Yace,  ok dear bye . Sannan ya yanke wayar.

Ina yanke wayar Munubiya ta kaimin bugu, Na kauce ina dariya  yo da bakina a hanani fad'ar gaskiya .

 ba hanaki akayiba, amma kinsan idan Allura ta tono garma mune tushen fad'an ai, kinkuma san halin Abba da d'aukar zafi kamar baba k'arami .

 tab, ta k'are musu dai suda suka takalo wlhy, jarababbu dangin masifa .

 kina ciki kenan tunda kema dangin kine ai .

Dariya muka Sanya nida munubiya.





*washe gari*



Tafiyar mu gidan mama Rabi bai yuwuba, saboda dawowar Abbanmu, da innarmu ta sanar masa a waya zamuje can muk'arasa Hutu sai yace a'a muyi hak'uri mu zauna, Dan akwai bak'in da zaiyi a k'arshen sati (weekend), kuma yanason dukkan yaran mukasance muna nan.

Innarmu tace shikenan.

Wannan dalilinne ya hanamu tafiya Hutu, dama ni ba so nakeba, Munubiya ce keta zakwad'in tafiyar.



Yau ta kasance alhamis, tunda safe muka tashi da himmar wanki nida Munubiya, ina sharar sashenmu Munubiya na fidda kayan wankin, yayinda Aryan da Aiyan keta tara mana ruwa daga fanfo zuwa banbu.

Ina gama sharar na wanke hannuna na k'arasa bakin fanfo inda Munubiya ke k'ok'arin jik'a kayan. zama nayi bisa d'an dakali da akayi wajen saboda irin hakan, wanki ko wanke-wanke da sauransu, waya nake latsawa ina nemo mana wak'a, dan muji dad'in wankin, maganar aunty khaleesa kawai mukji a kanmu tana fad'in,

 k! Munaya tashi kije ki gyaramin d'akinmu, akwai wani zanina nan ki d'akkosa ku wankemin .

Banza namata ban d'agoba, sai Munubiya ce tace,  to aunty khaleesa .

Shirun danayi ina kuma tamke fuska yasata gane nice munaya, Dan haka ta kalli Munubiya dahar tatafi,  k Munubiya!... dawo, bakece zakiyiba, k! Dan uwarku Munaya tashi kije kimin .

Da sauri Munubiya tace, "Aunty khaleesa ai nice munaya, waccan Munubiya ce .

Hararta tayi,  mai dani 'yar iska to, ko kina tunanin ban ganeku nima d'in? .

Banyi niyyar d'agowa ba, amma jin abinda tafad'a yasani sakin guntun murmushi, nasan k'arya takeyi tace tana ganemu kai tsaye, yanzu ma dan kawai na nunu halin nawane shiyyasa tagane nice, kawai tafad'ane dai, mai da kaina nayi nacigaba da abinda nakeyi.......

Wata ashar ta lailayo ta makamin, tareda zaburowa tamkar zata dakeni, dai dai nan sallamar innaro ta karad'e tsakar gidan. mu duka kallonta mukayi, nikam kallo d'aya namata na d'auke kaina, (dan nikam natsani kakarnan tamu) Munubiya da aunty khaleesa suka gaidata, nikam a d'age nace  ina kwana .

 kin yima uwarki Ai'sha dan Ubanki , cewar innaro ta na nunani da d'anyatsanta manuniya=�I�<���, tacigaba da fad'in  ni zakima gaisuwa a haka? kamar wata sa'ar uwarki?, aiko Aisha da ubanki basu isa sumin gaisuwa hakaba balle ke haihuwar yanzun .

Baki na la6e, ba tareda na kalleta ba natashi nahau wankin, Munubiya kuma tawuce danta gyarama su aunty khaleesa d'akinsu. abinda nayi na nuna halin ko in kula saiya kuma tunzura innaro, ta fara hayagaga da matse kwalla wai naci zarafinta.

Wannan yasaka matan gidanmu da yara fara fitowa d'ai-d'ai suna kallonmu (dan al'adar gidanmu ce hakan, da anji kaya-kaya kowa zaiyo waje yaganema idonsa abinda ke faruwa).

Dady ya k'araso da sauri yana fad'in  Inna miya farune haka da kuka? Keda waye? .

 wannan shed'aniyar yarinyar mana tayi maganar tana nunani  waini yarinyar nan zataima d'ibar albarka saboda uwarsu kullum tana aibantani a gurinsu, shiyyasa duk sun rainani....

Baki bud'e nake kallon innaro da sherinta. wlhy wannan tsohuwar bazataga Annabi ba........

Maganar Dady ta dawo dani daga mamakin innaro. Yace,  Munaya ce ko Munubiya? miya farune keda inna? .

Dady yanada sauk'i, ba kamar Abbanmu da baba k'arami ba sun fishi zafi.

Nace,  dady Munaya ce. wlhy babu abinda namata, kawaifa daga shigowarta duk muka gaidata, shine kawai ta hau zagina wai ban gaidata da k'yauba.......

 amma ai gaisuwar rashin tarbiya kikai mata .  cewar Aunty khaleesa .

Dady zaiyi magana Aunty Ramlah tace,  wlhy Dady ba haka bane, duk abinda yafaru akan idona yafaru, dan nafito zan d'iba ruwa a fanfo .

Dakuwa Innaro ta mata,  kinci uwarki hadiza, kema ashe munafukace ban saniba, to ko hadizar ta haifama Ai'sha ne ke? .

Fakar idon Dady aunty Ramlah tayi ta dallama innaro harara, sannan tace,  yo daga fad'ar gaskiya, nidai wlhy Dady abinda nagani nakuma ji kenan .

Girgiza kai Dady yayi, sannan yace,  kiyi hak'uri Inna, Munaya tayi kuskure amma bazata sakeba. Munaya zoki bata hak'uri .

Ban musaba nazo har gabanta nace tayi hak'uri, bata amsamin ba, saima hararata datayi kawai. nima saina bar wajen nakoma kan wankina.

Dady Yakama hannun innaro suka shiga falonsa, matan gidanmu duk suka bar wajen, basuso wasan yak'are a nanba, sunso ace cin mutuncin innaro yasauka har kan innarmu.

Innarmu dake tsaye daga k'ofar falonta tanajiyo abinda ke faruwa dukda katanga ta shiga tsakiya, ta girgiza kai kawai tana komawa ciki da fad'in ALLAH ya k'yauta.



Ina wanki ina zubda hawaye, sosai raina ya sosu yau akan abinda Innaro tamin, dukda bawai yaune karon farko da hakan ya faruba, sai dai na yau yamin zafi ainun, har inaji natsani zaman gidanmu, a fili na furta ALLAH kabamu miji muyi aurenmu mubar gidannan .

Munubiya dabansan tazo wajenba naji ta amsa da Amin sweetheart, wlhy koni yanzu addu'ar danake mana kenan, sai dai banason mutafi mubar innarmu a wannan halin dasu Aryaan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login