Showing 282001 words to 285000 words out of 365757 words

Chapter 95 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1534

dazai bashi camera d'innan, shi wancan banzan Alhaji Halluru babu tsiyar da y'ay'ansa zasuma mutane, kullum sai tsarin banza yake mana .

������� Karka damu Alhaji shehu, mu bashi damar k'arshe daya buk'ata, tunda ya tabbatar mana a wannan karon zai kar6o camera d'in ta hanyar matan y'ay'ansa,��yana son takara, yakuma San inhar burinmu bai cigaba shida takarar Governor saidai kallo .

������ shikenan boss, bara naje ance nayi bak'o .

����� Ok ngd .



���Galadima ya gimtse recording d'in dai-dai nan yana murmushi da kallon Alhaji Darma dake tsuma dukan jikinsa na 6ari.

�����Cikin d'age gira Galadima yace,  wannan ma ba matsalata bace? Kasanfa shikad'ai ya isheni hujjar gurfanar dakai gaban K'uliya, shikenan babu girma babu mulkin da ake mana Homa da tak'ama dashi right?  .

������Mi Nuren zaiyi kuwa inba Bushewa da dariya ba, dan yatuna Alhaji Shehu ne yafad'ama Galadima maganarnan randa suka kamoshi.

�������Cikin Fusata Darma yake kallon Muftahu da Nuren dake dariya, ya mik'e tsaye yana nunasu da yatsa,  y'an samari lokacin dariyarku baiyiba, dan camera d'in da kuke farfagandar nema tana gab da zuwa hannunmu, kunga kuwa ai kune abin dariya . Ya k'are maganar da kwashewa da dariya.

�����Dukda furucinsa ya daki zuciyar Galadima bai nunaba, saiya mik'e yana murmushi da kallon Darma. Yace,  lallai kaine ka cancanci ayima dariya, indai camera ce tadad'e da zuwa hannuna .

����Yana gama fad'a ya fice, su Nuren suka kuma sanya dariya, dukda yanayin Galadima ya tabbatar musu akwai matsala. Sunama Alhaji Darma dariya suka fice abinsu daga d'akin.



����A falo suka iske Galadima yanata safa da marwa cikin tsantsar damuwa, sai danna waya yake yana sakawa a kunne alamar Neman wani tak'i shiga.

�����Cikin sassarfa duk suka k'araso garesa suna tambayar lafiya?.

�������Bai tanka musuba, saboda Munaya ta d'aga wayarsa,  Abba ya dawo kuwa? . abinda kawai yace mata kenan.

������A tsorace tace,  Miya farune? .

�����Tsawar data rikitata ya daka mata,  ya ina tambayarki kina tambayata? .

�������Cikin in ina tace,  Kayi hak'uri, bai dawoba .

��� ya salam yafad'a cikin dafe kai. yace,  Kinyi waya dashi? Ko kinji wani yayi waya dashi? .

����� A'a gaskiya, Jiya da safe dai nayi waya dashi nida Munubiya, amma yau ko innarmu banji sunyi wayaba.......

����Cikin katseta yace  kinga maza bincikamin waye yay wayar k'arshe dashi a gidanku, sannan kuma awa nawa dayin wayar .

������ Okay munaya tafad'a tana yanke wayar.



�����Shima wata Number yashiga nema yana fad'in  Lallai akwai matsala, tunda kukaji Harun da Alhaji Shehu sun fad'a to sunsan misuka shiryama Abba, gashi nabaza su Ameer sumin wani aikin... ya k'are maganar da saka wayar a kunne saboda daddy ya kira.

����������Bayan sun gaisa ya tambayesa ko sunyi waya da Abba a yau?.

�������Daddy yace,  eh da asuba yakirashi akan zai dawo yau .

�������Galadima yace,  Alhmdllh Dady wace number ce? .

������Dady yace bara Na turo maka.

����Koda Galadima ya yanke wayar saiya kira baba k'arami shima, shima ya tabbatar masa sunyi waya da Abba bayan fitowa salla, Dan wannan al'adarsu Ce ko a ina wani cikinsu yake saisunyi gaisuwar safe da bankwanan kwanciya barci, sannan idan wani cikinsu yayi tafiya zai kira y'an uwansa yayin dazai kamo hanya.

����������Hankalin su Nuren ma duk a tashe yake, balle uban gayya Galadima.............
'<���







=�F�<���Turk'ashi, ana wata ga wata kuma>�&�<���
@&.

�������Lallai yaukam tura na shirin kaiwa bango>�&�<���
@&.















ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���











Typing=���







=ء�HASKE WRITERS ASSO....





f&RAINA KAMA...!!f&

(Kaga gayya)





Bilyn Abdull ce>��<���

__________



Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Ubangijin Al'arshi kama mahaifin takwara (Bily s Fari) rahama, ka yalwata kabarinsa da Ni'ima, ALLAH ka yafe masa, harda iyayenmu=�-�=�O�<���.

Takwara ALLAH ya k'ara mana hak'urin rashinsu, muma ALLAH yasa randa zaka d'auki ranmu muna cikin masu imani da tsoronka, da soyayyay Manzonmu ANNABI MUHAMMADU S.A.W.=�-�=�-�=�O�<���



__________



BOOK 3 =�I�<���1� 5�





.................Duk da Munaya a rikice take haka tayi jarumtar danne zuciyarta, cikin hikima ta dinga bin jama'ar gidan d'ai-d'ai tana tambayar wad'anda tasan Abba zai iya kira kai tsaye, amma kowa yakance tun daren jiya basuyi wayaba, hankalinta a tashe ta sulale gidan innaro ba'a saniba, itama dai tace tun bayan sallar asuba bai sake kiranta ba. Munaya tafito jikinta sai rawa yake, kiran Galadima tayi, lokacin yana waya, tamkar zata fasa kuka ta cire wayar daga kunnen ta, tana niyyar sake kiranshi saigashi ya kirata.

Da sauri ta d'aga.

Yace,  yauwa Yayi waya da wani? .

Muryarta na zuga alamar tahowar kuka tace,  A'a, innaro kawai ya kira bayan sallar asubahi, amma yau koda su innarmu baiyi wayaba . ta k'are maganar hawaye na gangarowa a kumatunta.

Galadima ya furzar da huci daga can, a hankali yace,  Munaya .

Muryarta na zuga ta amsa tana share hawayen da bakin hijjab.

Had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi yayi da k'yar, muryarsa takuma komawa can k'asan mak'oshi, cikin sigar lallashin da Munaya bata ta6a sanin galadima ya iyaba yace,  insha ALLAH babu abinda zai faru da Abba, kiyi mana addu'a, sanan karki sanarma kowa wani Abu har inna, wayarki tazama kusa dake, Dan zan dunga kiranki idan buk'atar hakan ta taso .

Munaya takuma goge hawayen dasuka gaza tsayawa, cikin had'iye kukan tace,  ALLAH yabaku nasara, ya tsareku da tsarewarsa .

 Amin ngd . Galadima ya fad'a yana yanke wayar.

A bakin fanfo Munaya ta tsaya ta wanke fuskarta, akuma lokacinne Zarah da Siyama suka shigo kusan lokaci d'aya.

d'agowa nayi Na kallesu ina k'ak'aro murmushin da musu sannu da zuwa. Saidai ayanda suka amsamin cikin sanyin jiki saina tsorata, nabaro bakin fanfon da hanzari zuwa garesu ina fad'in  Kai lafiyarku kuwa? .

Duk d'insu murmushi suka k'ak'alo, Siyama tace,  babu komai fa sis... .

Dukda ban yardaba haka nayi murmushi, sannan Na kar6i yaransu duk biyu Na rik'e ina yaba Girman da sukayi, saikace tagwaye.

Daga Siyama har Zarah basuce dani Uffanba duk suka shige, kowa tanufi d'akin Uwarta. Duk binsu nayi da kallo, saida suka shige Na sauke ajiyar ziciya nima Na nufi sashenmu Ina tunanin mike faruwa? Dan alamu sun nuna akwai dai wani Abu a k'asa.

Saidai bankai ga Shiga d'akinmu ba mamansu Yaa hameed ta tareni ta kar6i yarinyar Zarah. Ban musaba Na bata tundai ALLAH yasa Nima Na Haifa balle ace, na shige falonmu da d'an Siyama nima.



Bayan Galadima sun gama waya da Munaya, number da daddy ya turo masa ya duba, ganin wadda yake da itace saiya gwada kira, switch up, ya ciza lips yana kallonsu Nuren da suma duk suka zuba masa idanu.

Muftahu yace,  Ranka ya dad'e mu sanarda y'an sanda mana? .

Murmuahi takaici Galadima tayi, ya girgiza kansa yana fad'in  Hakan zai 6ata aikinmu, duk indama yake a safiyar yaune suka sameshi, akwai zoben dake hannunsa zamu iya bibiyarsa tanan, saidai matsalar d'aya dole sai wayarsa Na aiki, gashi number sa kuma switch up .

Nuren yace,  to mizai hana mu bincika kozamu samu daga inda Number tabar aiki .

Da sauri Galadima yace,  yes, yes Nuren, shawara mai k'yau.....

Shiru yay yakasa k'arasawa, saboda tuno da matsalar da Computers nasu suke ciki kuma, ya dafe kansa.

Daga Muftahu har Nuren duksun fahimceshi, zuwacan kuma miya tuna saiya mik'e da hanzari zuwa cikin d'akin, babu dad'ewa yafito dawani k'aramin abu a hannunsa, lap-top yajawo ya manna a jiki, ya had'a da waya ya Shiga sarrafata cike da kwarewa.

Zuwa can yad'ago yana kallon su Muftahu da tura musu lap-top d'in gabansu, yana sanar dasu titin da wayarsa ta daina aiki.

Cikin takaici yace,  Sunriga da sun tsara komai, mubarma tunanin plan A, muje zuwa plan B kawai .

Cikin mamaki duk suka kallesa alamar miye plan B d'i?.

Lips d'insa yad'an ciza yana d'age gira d'aya da buga yatsan saman bakinsa, Yace  maida hankalinmu a nemansa shine target d'insu Na farko wajen janye ra'ayinmu, plan d'inmu mukuma anan shine bazasu ta6a kasheshi ba inhar bai basu Camera d'inba, a yanda Na lura kuma yanada taurin kai shima, bazai ta6a basuba ko fad'a musu inda take. Sunada damar yin amfani da surukan senator halluru wajen turasu gida su nema musu camera d'in, kodai ta hanyar musu barazana da mutuwa, kokuma akan aurensu, ko kashe mahaifinsu, kodai wani Abu daban, shiyyasa dolene mumaida matsalarsa cikin plan B d'in .

Duksun gamsu, dukda sufa har yanzu yak'i sanar musu miyake shiryawa a plan B d'in.

Cikin damuwa Nuren yace,  Amma nasan zasu wahalar dashi .

Galadima baice komaiba dan shikad'ai yasan azabar da zuciyarsa kemasa, bayason ya nuna karayarsane saboda karsuma su Muftahu su karaya, sannan koda sanyin jiki yanemi tasiri gareshi sai kalaman Munaya su masa allura, inhar yarinya k'arama kamarta zata iya tasirantuwa da abinda ta fad'a, mizai hana shima ya samu jarumta cikin tagomashin fik'irarta.

Mik'ewa yay tsaye yana tattara kayansa da fad'in  Bara Na wuce, sai kunji yadda zata kaya kawai .



Basu barshi yatafi shikad'aiba, saida sukai masa rakkiya har masarauta, koda ya shige sashensa saiya kulle kansa, domin yin shiri.





Hummm,>�8�<���
@&shirya da k'yau Galadiman mu.







&&&&&&&&&&&



Abinda ya faru da Abba shine, bayan yagama kammala shirinsa domin baro inda sukaje shida S... halluru daya jashi domin masa rakkiyar tafiyar kwanaki biyu kacal.

Lafiya lau suka shiga mota zasu taho, amma sai shi S... Halluru ya dakata da cewar Abba yayo gaba, shi anmasa kiran gaggawa, bai kuma kamata ace ya tsaidashiba shi, tunda ya sanarma iyalansa yau zai dawo.

Da farko Abba kamar zaice suzauna kawai harya gama, saikuma tunanin yariga da ya sanarma su innaro zai dawo ya fad'o masa, shiyyasa kawai yataho, basuyi wani nisa da tafiya ba driver ya tsaya wai motar Na d'aukar zafi, ALLAH Sarki Abba, sai shima ya fita domin taimaka masa, suna tsaka da duba motarne garadan samari hud'u suka fito daga ma6oyarsu sukai ma Abba d'aukar amarya. Duk yanda yaso kare kansa ya gaza.

Driver da dama duk cikin shiri yayi haka saiya hau tsallen k'arya cikin pretending yana ihun azo a taimakesu, (>�&�<���
@&bayan yasan baza'a samu kowaba a wajen tunda jejine9&).



Abba mutumne mai dagiya akan ra'ayinsa, hakan yasa duk yanda sukaso yabasu had'inkai akan zancen Camera yak'i, yama dage shi baisan Cameran da ake magana a kaiba, kuma dayaso basun tun lokacin da ake bibiyarsa da dukiya mai tsoka daya bada, amma basuda kud'in dayakai darajar camera d'in, sannan inda zai bada kodan barazana da rayuwarsa da sukasa aikaitayi tunba yanzuba daya bada, amma yasan ruhinsa Na hannun Wanda ya halicceshi, shine kuma mai kar6a aduk lokacin da yaso, inma sun kasheshi dama kwanansa ya k'arene, Dan haka subar wahalar da Kansu kawaima.

Wannan maganar Ce ta fusatasu, wani ya daki Abba a baki harya fashe, dukda yaji zafi saiyayi murmuahi kawai yana kauda kai gefe.

Wanda sukasa yamusu aikin lalata documents d'in Galadima Na cikin Computers ne ya ankarar dasu zoben hannun Abba akwai wata kimiya a cikinsa, wannan ne ya sakasu cire zoben daga yatsansa, shi Abba saima yanzune yasan manufar zoben, yay murmushi, Dan hakan ya tabbatar masa cewar Galadima yasan wani Abu game dashi.

Duk yanda suka ringa k'ok'arin yima Galadima mugunta a sirrinsa Na Computer Abba Na kallonsu, hankalinsa kuma a tashe yake, amma jarumin namijineshi mai iya sarrafa kai aduk yanayin daya kasance, ko'a fuska bai nuna musu yana tare da damuwar abinda sukeyinba, saida Galadima ya kashe komai nasune Abba ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, dukda yasan hakan ba shine nasaraba.

Wanda suka saka aiki mai suna William yashiga rud'anin abinda Galadima yayi, Dan da farko yanata cika baki babu wani d'an African daya isa ja dashi a fannin ilimin Computer, bak'ak'en fatar ai a wajen su suke koyan komai, ta Yaya kuma zasu fisu Sani?.

wad'annan kalamai nasa sun Sosa zuciyar Abba da sakashi cikin takaici, shiyyasa yayta jerama Galadima addu'ar samun nasara a zuciya.

Yayinda sukuma wad'anda akema aiki suke kuma hurama William kai da kwanzartashi (ko kishin Kansu basayi=��, a zageku da kuma k'ask'antar daku kuna yabon mai ganinku marasa daraja>�&�<���
@&, wata dai bahaguwar rayuwa sai bak'in fata=��=�D�.



Dak'ilesu da Galadima yayi ta hanyar kashe komai ya fusatasu suda William d'in, suna kuma kunna Computers d'in komai naciki ya goge, wannan Abu ya rikita William matuk'a, gashidai yagama proud d'in shi kwarone kuma bak'in fata d'an Africa ya masa kwaf d'aya, dukkan fushinsu saiya dawo kan Abba.

Ana cikin haka saiga Alhaji halluru da sauran tawagar y'an group d'in, wad'anda sai yanzune suka samu k'arasowa, da farko Abba ya zata Alhaji Halluru taimakonsa yazoyi, saida yaji suna masa izgilanci sannan ya fahimci komai, cikin tsantsar mamaki yace,  Alhaji Halliru da kanka? .

Ta6e baki Alhaji Halluru yayi, yace,  zaka bani takarar Governor ne? .

Abba yay murmushin takaici yana fad'in  Tir da kai Halluru, wannan ai jahilcine, ALLAH shikad'aine ke bada mulki ga Wanda yaso, akuma lokacin dayaso,, yanzu kana nufin duk shekarun daka d'auka a jikina kai dama da manufa kake tare dani? .

Alhaji Halluru ya kuma ta6e baki yana murmushin mugunta, yace,  Alhaji Auwal kenan, ai bama zaka tabbatar da hakanba sai y'ay'anka da kansu sun d'akko min camera sun kawo, sannan mukuma kasheka a gabansu babu yanda zasuyi, yanzu haka suna gida, zuwa anjima kad'an kuma camera zatazo garemu .

Zufa ta fara karyoma Abba a dukkan sassan jikinsa, danjin za'ayi amfani da gudan jininsa wajen tarwatsa abinda yad'au shekaru yana rik'ewa amana, k'ala baice da Alhaji Halluru ba, su kuma sai kiraye-kirayen waya suke Na had'ama Galadima tarko.>�&�<���
@&

Abba ba tausayin kansa yakejiba, tausayin Galadima yakeji matuk'ar tik'ewa, Dan ganin rai kusan 15 kowa k'iyayyarsa akansa take da muguntarsa...







&&&&&&&&&&





Tunda Galadima ya shigo bai zaunaba, saida yagama had'a komai dazai buk'ata, yabama sarkin mota yakai cikin motar dazaiyi amfani da ita, alwala yay yafita salla massalacin masarautar, bai yarda sun had'u da Sarki ba, yay fitowarsa, koda ya dawo saiyasha magani ya kwanta, kaikace bashida wata matsalane, babu dad'ewa kuwa barci yay gaba dashi.

Bai tashiba saida aka kira sallar la'asar, nanma massalacin yaje, bayan ya dawo yay kiran Momma ta video call, duk suna asibitin hardasu Samha, d'aya bayan d'aya ya gaisa da kowa, Samha harda kukanta tanason zuwa Nigeria, ita missing nasu takeyi sosai. Galadima yace a'a ba yanzu ba, tashi tai tabar gaban lap-top d'in tana kuka, Galadima ya girgiza kai kawai.

Yasha hirarsa da Abie sosai, saboda Alhamdullah jikinsa saidai godiyar ALLAH, dama ciwo keshiga farat d'aya, sauk'i kam sai a hankaki. Addu'a kuma takobin muminice ako yaushe.

Bayan ya gama waya dasu Momma Sir Isa ya kirashi, ya tabbatar masa da komaifa is done, Dan ansami kowanne acikinsu, yanzu haka wasu sunma iso.

Galadima yay murmushi yana shafa fuskarsa. Yace,  Nama canja shawara, zamu canja gidan da zamu ajiyesu da, yanzu akwai wani gida annan kusada plaza d'ina, nagama magana da Saleem komai yayi ready, Ameer duk yakaisu can, insha ALLAH ana idar da sallar Isha'i zan fito .

Sir Isa yace, hakan yayi, dan acikin yaran nasuma za'a iya samun munafukai, tunda duk sunsan gidan daza'a ajiyesun, yanzu kuwa shi Ameer kad'ai zaisan da wannan.



Galadima ya kira Munaya, dama tun d'azun kiran nashi take jira, ta d'aga tana shigewa cikin bayin d'akinsu Dan kar wani yaji.

Galadima yace,  haryanzu kukan? .

 a'a ta fad'a cikin share hawaye.

Yad'an murmusa kawai yana fad'in,  Akwai bak'in da sukazo gidanku? .

 A'a babu Wanda yazo, sai Siyama da Zarah .

Galadima yay murmushin gefen baki yana cigaba da danna lap-top, hasashensa yazama gaskiya kenan, gyaran murya yad'anyi kad'an yana fad'in,  kina jina? .

Munaya tace,  eh .

 Ki saka ido akan d'akin Abba, motsin kowa yazama akan idonki koda cikin matansane, ko yayyenki maza, Dan za'a iya yin amfani da kowa, inda da dama ma key d'in d'akin yazama a hannunki .

Munaya tayi d'an jimm alamar tunani, zuwa can tace,  babu damuwa, zan gwada hakan insha ALLAH, amma kunji labarin Abban? .

 Karki damu, insha ALLAH Abba zai dawo gida, addu'a muke buk'ata .


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login