Showing 309001 words to 312000 words out of 365757 words

Chapter 104 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1489

yace yaje ya zauna.

Yad'anyi rubuce-rubucensa sannan yace  kotu tana buk'atar son ganin Waziri a gabanta .

Waziri Munafuki, saikace an tsamo 6era a ruwa haka yafito yana wani kakkange fusaka, shima inda kowa ke tsayuwa yaje ya tsaya, bayan ya fad'i sunansa Alk'ali ya jeho masa tambaya.

 humm Waziri, kotu zataso sanin minene ya had'aka da Sarki Saifudden da zafi haka? Harka za6i cutar dashi wajen had'akar wasu bare can? .

Waziri yakuma k'asa da kansa, murya a raunane yace,  maganar gaskiya son zuciyane kawai ba wani abuba, danshi mai martaba ya kasance mutum mai zama akan ra'ayinsa, sannan mai gaskiya da sauk'in hali, nikuma nacika tsugunne-tsugunnen rashin gaskiya, sannan inada sonkai, komai nafison a masarautar gagara badau a fifitani saman kowa, akuma girmamani, wannan halin nawa nason handame komai Na mutane yasaka kullum Sarki kemin nasiha dason gyara halayyata, nikuma nak'i saurarensa, saina kallon hakan danake matsayin cin zarafina yakeyi a kullum, lokacin dana fara ganin take-taken Sarki nason tu6eni sai hankalina ya tashi, nafara Neman mafita, (kusan dai ita sarautar waziri ba gadonta akeba a k'asar Hausa) ina cikin fad'i tashine Neman mafitane wad'annan turawa biyu su Mike sukazo min da tayin mak'udan kud'i da wasu alk'awura, bisa sharad'in sonjin sirrin masarautar gagara badau, babu wani 6oye-6oye Na sanar musu komai, karaf sai'a kunnen wani dogari amintacce ga Sarki, shine yaje ya sanar masa komai, Sarki yakirani har turakarsa ya titsiyeni, yaci mutuncina iyakar iyawarsa, wannan Abu shine ya fusatani, naje Na samu su tanderu muka had'e, dan aganina Sarki ya tozartani a masarauta, tunda gashi yana niyar tu6eni kamar yanda ya fad'amin, nikuma aganina kafin ya tu6eni ya tozartani gara ni nahad'a kai da wad'anda zamu tu6eshi, wannan dalilinne yasakani basu had'inkai, akuma washe garin dana amso allurarna da asuba muna salla, anyi sujudar farko ta sallar asubahi Na kafa masa allurar a cinya Na tsiyaye ruwan kafin a d'ago, amma Sarki dukda nasan yaji zafi, yakumasan cutar dashi akeyi baiko motsaba, saida aka idar da sallar dashi, anayin sallama ya juyo muka had'a ido, baisamu damar min maganaba ya yanke jiki ya fad'i, tun daga wannan lokacin yakoma shida gawa banbancinsu kad'annane, to dama shima wazirin Sarki Abdul-Fatah kuma d'an uwansa shima da nashi shiri akan Sarki Saifudden, dan yanajin haushin ba jikokinsa y'ay'an y'arsa gimbiya Marawuyane (mama Fulani) zasuyi mulkiba, dan lokacin su zaharadeen sunyi had'arin jirgi sun mutu, to burinsa kullum ya durk'usar da Sarki Saifudden jikansa Jalaludden ya gaji mulki, wai tunda gimbiya Kahdija matar Sarki Abdul-fatah ta gaje musu masarauta, shima dolene d'iyarsa mama Fulani ta gaje ta gagara badau, wannan ya sakashi shigowa cikin tawagarmu dasu tanderu, Sarki Saifudden Na kwanciya jinya kuwa aka d'ora Jalaludden bisa karaga a matsayin mai ruk'on kwarya, bisa alk'awarin zan cigaba da wazircinsa, sannan kuma sarautar waziri tazama din din din, y'ay'ana ma zasu iya gadona, shiyyasa lokacin da aka sanarmin ga camera a hannun mai dawakai nayi azamar son kar6a, amma yamin gardama, nikuma Na kashesu shida matarsa dan karsu tonamin asiri, nakuma saka yara subimin d'ansa daya gudu da camera, a masarauta kuma nace Badi da kansa ya kashe iyayensa. Maganar gaskiya mama Fulani batasan mahaifinta yayi wannan shirinba, danya ta6a tuntu6arta da batun kashe Sarki Saifudden amma tace Sam bata aminceba, bazata ta6a kisan kaiba, shiyyasa bai ta6a sanar mata yanda akayiba, shikansa Sarki Jalaludden baisan komaiba, dan yana masifar son d'an uwansa, bayason abinda zai ta6ashi, shiyyasa nikuma Na dinga kwantar masa dakai dan karma ya fahimci wani Abu, nasaka d'ana Harun yake bibiyar mana dukkan motsin Sameer. Wannan shine dalilina yamai shari'a .

Alk'ali yace,  toshi mahaifin gimbiya zulfa uwargidan Sarki na yanzu minene ya kawo shi a ciki? tunda dai yanzu bashida k'arfin da zaizo kotu ya bamu amsa saboda girma ya kamashi sosai, nakuma San Kasan komai shima a kansa? .

Waziri ya gyara tsayuwa yana jinjina kai, yace,  shima dai shirinsa bai wuce akan mijin y'arsa yayi sarautar ba, wato Sarki Jalaludden Na yanzu kagadai dolene jikokinsa su gaji sarautar anan gaba, sannan kuma yanajin haushin sarki Saifudden d'in, dan shi yaso ya auri d'iyarsa zulfa amma sai Marigayi Sarki Abubakar ya had'ashi da d'iyar Amininsa gimbiya Zaitun, bayan rasuwarta ma Yakuma masa tayin wata y'ar tashi amma sai aka maye gurbin gimbiya Zaitun da gimbiya Zeenah, shi burinsa dai ya nuna inhar ank'i aurama Sarki mai sarauta y'arsa to jikokinsa koda tsiya saisunyi sarautar gagara badau d'in, lallai wannan dai shine dalilinsa shima .





Babbar magana, wai dukdai akan mulki kayan duniya aketa wannan k'ulla-k'ulla, Wanda gashi yanzu a cikinsu wasuma sunbar duniyar baki d'aya, wannan wace iriyar masiface haka?.

Alk'ali ma kasa magana yayi, saida yad'au ruwa yasha tukunna, Galadima kam ai babu mai iya tantance halin dayake ciki, ya kwantar da kansa jikin kujera yasaka handkerchief ya lullu6e fuskarsa gaba d'aya.



Alk'ali yace,  Lallai a gaisheku, Ku yanzu dan girman ALLAH bakuji kunyar kankuba? Kamarku manyan mutane da k'asa ke alfahari daku da girmamaku Ashe ru6a66une a bad'ini, maciya amanar k'asa, lallai barin irinku ma ai had'arine wa duniya baki d'aya, dan duk abinda aka nema Na wulak'anta k'asarku zaku iya mik'awa domin cikar burinku, kune masu 6ata shugabanni Na kwarai masu k'yak'yk'yawar zuciya, ALLAH ya cigaba da tona mana asirin irinku a k'asarmu .

Gaba daya Kotu ta amsa da Amin!!!,



Alk'ali yay k'asa da kansa yana bincike a k'aton books d'in gabansa kusan hud'u, kotu tayi tsitt kowa ya zuba masa ido, ya d'auki tsawon lokaci yana rubuce-rubuce kusan 30minute's sannan ya d'ago yana cire eyeglasses d'in idonsa, yasaka handkerchief ya goge fuskarsa sanan ya goge eyeglasses d'inma ya maida a idonsa yana kuma gyara zama dayin gyaran murya. Yace,  Bisa ga hujjoji da bayanan da suka fita a bakin wad'anda ake zargi kai tsaye, wannan kotu mai adalci ta yankema wad'annan mutane 20 da sukayi gamayya wajen ciwon Sarki Saifudden hukunci d'aurin rai da rai a gidan kaso, saboda kisa da suka dinga sakawa a nayi bayan laifinda suka aikata .

Kotu ta d'auki sowa gaba d'aya, saida alk'ali ya tsawatar ta hanyar buga gudumarsa, kowa yay tsitt.

Alk'ali yacigaba da fad'in  Wazirin Sarki kuwa hukuncinsa shine kisa ta hanyar rataya, sakamakon kisan mai dokuna da matarsa, Hakama Alhaji Shehu darma, d'aurin rai da rai da horo mai tsanani saboda bada had'in kai wajen kisan d'an Uwansa Alhaji Abdul-Hakeem uba, dakuma tsiyatakun da suka dinga sakashi yanayi. Akwai yaransu dake hannu bisa laifi daban-daban da suka sanyasu, suma dai d'aurin rai da rai ne akansu, Irinsu Alhaji Halluru, Timothy da sauran su shekaru 30-30 ne hukuncinsu, da horo mai tsanani, dukansu babu maganar beli, dolene saisun rayu a gidan kaso. Sannan wannan kotu ta wanke Muhammad Sameer Saifudden bisa zargin ta'addancin Garkuwa da yara da yayi, dan bai ta6a kowaba a cikinsu, dagashi har tawagarsa da suka bashi gudunmawa kotu ta wankesu tas. Akwai d'angidan Waziri mai Suna Harun, kotu ta yanke masa zaman kaso Na shekaru goma bisa ga cin dunduniya Muhammad Sameer daya dingayi wajen sato bayanansa, ina fatan kowa yasamu hukunci dai-dai da abinda ya aikata, kuma duniya ta gamsu da hukuncin da muka yanke? .



Kotu ta d'auki sowar gamsuwa da ALLAH wadai da halin irinsu waziri dasu Darma. Kowa tur yakeyi da halin masu.

Alk'ali ya buga gudumarsa alamar kotu ta tashi, daganan kowa ya mik'e saida ya shige sannan aka kacame da hayaniya, harda masu kaima su Alhaji Halluru duka, ana musu ihu, saima da aka fidosu mutane sukaita jifansu da duwatsu, sai y'an sanda suka dinga karesu har aka zubasu a mota, wasunsuna kuka sukeyi rurus dan ganin iyalansu ko damuwama basuyiba, wasu a cikin yaransu ai ko'a kwalar rigarsu, k'alilanne a cikinsu suka damu.



Galadima har kowa yafita a kotun shi yakasa motsi, saida Abba Hayatudden da baffi da Abban munaya sukazo kansa, baffi ya cire Handkerchief d'in daya lullu6e fuskarsa saisukaga ashema a sume yake?, rikicewa sukayi, aka samo ruwa Abba Hayatudden ya shafa masa a fuska ya kawo numfashi.

Zabura yayi, saida Abba Hayatudden ya rungumesa, jinsa a jikin k'anin mahaifinsa saiya saki wani irin kuka maiban tausayi, daga Abba har Baffi suma idonsu yacika da kwalla, Abba Hayatudden yashiga shafa bayan Galadima alamar allashi. Kusan mintuna uku ya d'ago da hanzarinsa yana fad'in  Abba Munaya da Nuren, lallai ban yarda darashin zuwansu kawo camera ba, alamun sarkin mota sun nuna akwai wani abu .

Da sauri baffi ya fita Neman sarkin mota, a waje ya iskeshi tsaye yana jiran fitowar Galadima.

Baffi ya tambayesa miya faru, bai 6oye masaba ya sanar dashi komai, hankalin Baffi a tashe yakoma ciki yace su fito suje, hakkanne ya tada hankalin Galadima da tabbatar da lallai akwai matsala.

A rikice suka shige mota, ko kallon y'an jarida dakeson jin bayani a bakinsu basuyiba, balle bi takan jama'a dake jiran su fito sumusu jaje....................
'<���







Lallai K'arshen munafuki dama duk inda yake jin kunya, duk yanda kakai ga k'ulla kuttun sharri watan watarana saikaga k'arshenka, a duniya ne kokuwa a lahira, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, Idan khairan ka shuka lallai saika girba khairan, idan kuma sharranne shima saika girbe abinka, duk danne Gaskiya da k'arya zatai wlhy watan watarana sai gaskiya tadawo sama k'arya ta koma k'asanta, kwanaki 99 ne suke zama Na masheranci, 1 tak kuma suzama namai gaskiya da k'yak'yk'yawar zuciya, d'ayarnan kuma saikaga yazo maka da nasarorin daka rasa shekaru aru-aru, duk nisan jifa k'asa zai fad'o, gashi dai yau su Harun sunzama a k'asa, k'asanma cikin matuk'ar k'ask'anci, musamman ma iyayensu.



Ya rabbi ka tsaremu ka tsare mana zukatanmu, ka hanamu cutar da wani koda da fatar bakice, ko'a social media bana fatan kwana da hak'in wani ko hassadar wani, idan nabar duniya wace amsa zanbama ubangiji akan d'aukar zunibin wandama banta6a ganiba a zahiri=�-�, ya ALLAH ka gafartamana muda iyayenmu da dukkan musulmai baki d'aya, ALLAH ka rabamu dacin hak'k'in kowa koda kwayar zarrane=�-�=�-�=�O�<���.



Kumuje zuwa asibiti, danjin wane hali Munaya take ciki itada Nuren kuma?.=��





*_Nagode sosai da addu'oinku gareni, da mahaifina, ALLAH ya bada ladan zuminci Yakuma kar6a mana baki d'aya, bansan yazan nuna godiyata ga masoyanaba, saidai nace kuma ALLAH ya biya muku buk'atunku, kaini har mak'iyinama ALLAH ya biya masa buk'atarsa ta alkairi, dan saida mak'iyi duniya ke dad'in zama>�8�<���
@&>�8�<���
@&, idan babusu tamkar miyace lami babu gishiri da magi>�(�=��=��.>�8�<���
@&>�8�<���
@&

















ALLAH ka gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���









BOOK 3 =�I�<���2� 0�





.................Galadima ganima yake kamar Sarkin mota baya Sauri, amma baiyi maganaba, zuciyarsa tamafi motar gudu, dan bugawa take da sauri-sauri tamkar zata fito.

Suna isowa bai saurari an bud'e masaba ya bud'e da kansa yay cikin asibitin, dayake k'aramin asibitin ne, na kud'i su Ahmad suka kaisu, da sauri Nurses d'in dake reception suka masa sannu, tare da gaisheshi, dan 6atancin da aka musu Shida sh Munaya a wancan lokacin yakuma sakawa wad'anda basu sanshiba ma suka sanshi, ga kuma abinda ya faru a kwanakinnan.

Uffan baice da suba yay gaba abinshi, cikin takunnan nasa Na k'asaita da izza, Wanda a yanzu yak'ara armashi da 6acin rai.

Su Ahmad da suka hango tahowarsa duk suka mik'e a tare suma suka nufosa, kallon mamaki yake binsu dashi, suma duksun lura da hakan.

Gebiral yace,  Uncle! .

Kallonsa Galadima yayi idonsa sakaye cikin eyeglasses daya 6oye jajayen idonsa, kafin wani ya sake rmagana a cikinsu doctor ya iso wajen, duk hankalin su suka maida ga doctor d'in suna tambayar ya jikin Aunty?.

Doctor yace,  ku kwantar da hankalinku, insha ALLAH komai zai zama normal, Ranka ya dad'e barka da zuwa .

Hannu kawai Galadima ya iya d'aga masa, a lokacinne suma su Abba Hayatudden suka k'araso wajen.

A hankali Galadima ya bud'e baki yace,  Ina matata da d'an uwana? .

Cikin girmamawa Doctor yace,  Ranka ya dad'e inason magana dakai idan babu damuwa .

Kamar Galadima bazaiyi maganaba saikuma ya gyara tsayuwa yana fad'in  Inason ganinsu tukunna .

Doctor yay jimm baice komaiba.

Hakanne ya d'arsa tashin hankali a zukatan kowa Na wajen, Galadima ya yunk'uro zaiyi magana doctor yay saurin taresa ta hanyar fad'in  Amma ranka ya dad'e namijin kawai, dan gaskiya ita ba'ason ayi wani kwakwkwaran motsi a kusa da itane .

Kowa Na wajen ajiyar zuciya ya sauke, danjin sunada rai, Galadima daya kasa koda motsi doctor ya kuma kalla, zaiyi magana ya d'aga masa hannu alamar baison jin komai.

Abba Hayatudden da Baffi da sukasan halinsa idan yana cikin damuwa suka kalli doctor, baffi yace,  doctor yakamata ko shi kad'aine ya ganta, mu saimu duba Nuridden d'in .

A sanyaye doctor ya gyad'a kai, dan inda sonsamune babu mai shigar.

Nurse ya had'a su da ita takaisu inda Nuren yake, amma kar ayi hayaniyar dazai farka, dan ana buk'atar yasamu barci sosai.

Doctor kuma yayma Galadima jagora da kansa, amma a k'ofar d'akin suka cire takalmansu, dagasu sai sock's d'in k'afarsu suka shiga.

'Dakine madaidaicine da gad'o d'aya, asibitin sunada Kayan aiki babu laifi, tamkar an zarema Galadima lakar jiki haka yake takawa cikin sand'a, doctor ya nuna masa kujera guda d'aya dake kusa da gadon, idonsa a kanta tunda suka shigo, harya zauba yakasa janyewa, tana kwance sam6al a gadon tamkar wata gawa, kanta nad'e da bandeji alamar taji ciwo akan, dan har fuskarta tanuna saboda kumburi da tayi, alik'a mata oxygen a hanci Wanda da alamar shike taimakawa numfaahinta fita, ya maida kallonsa ga damtsen hannunta da shima yake anad'e, sannan kuma tafin hannunta ma haka, wasu hawaye masu zafi suka gangaro tacikin eyeglasses d'in idonsa daya hana ganin tahowarsu tun daga cikin idon.

Ya kalli doctor da shima yake tsaye kansa duk'e a k'asa alamun damuwa, baice komaiba ya mik'e ya fito abinsa, doctor ya biyoshi a baya shima da hanzari.

Da hannu yamasa alamar ya kaisa inda Nuren yake.

Nanma shine yamasa jagora, duk inda suka gitta idanun mutane akansa, oho baimasan sunayiba, abinda ya dameshi shine gabansa.

Su Abba Hayatudden suna d'akin har yanzu, shigowarsu Galadima ya sakasu juyowa suna kallonsa gaba d'aya, ya k'araso gaban gadon idonsa akan Nuren dake barci shima, saidai shi babu bandeji ko d'aya a jikinsa, dan baiji rauniba, dukansa da sukayi a kai ne ya sakashi suma, anama zuwa asibitin babu dad'ewa ya farfad'o, shine sukai masa allurar barci da saka masa k'arin ruwa danya huta, sanda zai farka ya farka da k'arfi a jikinsa..

Galadima ya durk'usa a gaban gadon ya kamo hannun Nuren cikin nasa, yana k'aunar Nuren sosai har cikin ransa, danshi mutumne simple, idan yamaka wani abun bazaka ta6a cewa shi jinin sarauta baneba, ko kad'an bashida damuwa a rayuwarsa, tunba yanzuba Nuren yake bama rayuwarsa gudunmawa, baita6a k'osawa ko gundura da halinsaba, balle yace masa bazaiyiba, saidai inhar abin baida tsarine zai bashi shawaran a canja kokuma ayi haka ko haka..........

Wayarsa datai ring ce ta katse tunaninsa, yad'an karkata yana cirota a aljihun wandon yadinsa, ring d'in daya sakama papi shi kad'aine ya sakashi fahimtar waye, ya mik'e daga gaban gadon yana picking call d'in, saida ya fice a d'akin gaba d'aya sannan ya amsa sallamar da papi yamasa cikeda girmamawa da tsantsar damuwa.

Daga can ajiyar zuciya papi yayi, dan baiyi zaton samun Galadima cikin k'oshin lafiya hakaba, cikin tausasa Murya papi yace,  Muhammad kana inane? .

Shiru galadima yayi, kamar bazai iya maganaba, saikuma ya bud'e baki da k'yar yace,  papi asibiti .

 Asibiti kuma? Wanene babu lafiya? .

Kasa danne kukan daya taho masa yayi, ya fice daga cikin asibitin da sauri, mota ya bud'e ya shiga, ya kife kansa a sitiyari ya fashema papi da kuka mai tsima rai da 6argon jiki, gaba d'aya jikin papi yay sanyi lakwas, saima ya kasa magana shima, yay shiru kawai yana sauraren jarumin jikansa mai yawan hak'uri da juriya akan abu, saida yay kusan mintuna biyu yanayi, papi ya tabbatar nauyin da zuciyar galadima tayi ta ragu sai yay gyaran murya, cikin tausasa harshe yace,  Muhammad Sameer mike faruwane? Kokuwa kukan farin cikin cikar burine? .

Da k'yar Galadima ya iya bud'e baki yace,  papi yanzunan duk abinda suka aikata a gareni tsawon shekaru bai ishesuba? Saisunyi yunk'urin kashemin d'an uwana da matata? Papi minayi musu da zaifi haka? Miye laifin mahaifina danyak'i goyama k'arya da cin amana baya? Miye laifinsa danya zama shugaba? Bayan hakan ba shirinsa bane tsarin ALLAH ne? Miyasa suka manta babu abinda ke dawwama sai ALLAH, papi inhar matata ko d'an uwana suka rasa ransu wlhy bazan hak'uraba, saina kashesu da hannuna nima s........


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login