Showing 78001 words to 81000 words out of 365757 words

Chapter 27 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1485

'yammatan masarautar.

Ahaka muka dinga zuwa sashe -sashe inda duk sun firfito, duk muna akan dokin bamu saukaba, sai dai mukan risina alamar gaisuwa. fuskata kuma tana abud'e yanzun kowa Na ganina, saida muka zagaye ko ina a masarautar sannan aka maidani wajensu mom. Lokacin la'asar tayi.



Dukna damu saboda kiran munubiya danaketa yi wayar akashe, tsakin danakeyine ya saka Ayusher tambayata, na fad'a mata.

Dariya tayi,  yo banda abunki ina zakiji munubiya kuwa, yaa marwan nacan nashan amarci kema kin sani ai, kema zuwa gobe wazai kiraki ya samu, Galadima nacan yana kwa..... .

Filo na d'auka Na jefa mata a fusaka, suka sanyamin dariya kuwa.





&&&&



Nasha kuka yayin tafiyarsu Ayusher, inaji ina gani suka tafi suka barni nikad'ai cikin wad'anda ban saniba.

Tun magriba aka shiryani tsaf cikin wata tattausar atanfa, sannan aka d'oramin alk'yabba, wlhy nagaji da saka alk'yabba r nan, saboda nauyi sukemin, har mamaki nakeyi yanda su basu damuba.

Zan iya cemuku nidai yau wanka akamin da turare dan kowane lungu da sak'o na jikina saida yasha ruwan turare, ruwan danayi wanka dashi kansa na musamman ne, nayi k'yau harna gaji.

An fiddoni aka sakani cikin mota, sannan aka nufi sashen Galadima dani. Dukda nasan auren Contract nayi, hakan bai hana zuciyata luguden dakaba, tunda bamuyi wata yarjejeniya dashiba ta zaman da zamuyi, addu'a natayi a zuciyata ina tunano innarmu da munubiyata da kewarta ta gallabeni, jinake tamkar mun shekara 5 bamuga junaba, bamu ta6a yini ba'a tareba, saigashi yau munyi kwana da yinima, ko'a waya bamuji muryar junaba.

Duk da fuskata a rufe take hakan bai hanani shaida 6angaren Galadima ya had'uba, dan k'amshinsa ma da banne.

Muryar wata na tsinkayo a cikinsu tana fad'in wai falon Galadima za'a kaini, gabana yakuma fad'uwa.

Nidai naji mun iso inda turaren Galadima yafi ko ina yawa, inaga nanne falon nasa, gawani lallausan Abu danake takawa a k'afata, sun zaunar dani akan wani laushin dayafi Wanda nake takawar, sannan sukayi addu'a suka fice.

Tunda suka fita ban iya d'ago kainaba, dukda falon tsitt yake alamar babu kowa cikinsa, sai k'arar AC kawai da ni'im taccen k'amshin dake tashi, a falon, sai TV dake magana can k'asa an rage k'arar sosai, hawayen danaketa rik'ewa tun d'azun suka shiga ziraro min a kumatu. a hankali nakejin takun takalmi na tunkaro falon.........
'<���





Muhad'u tomorrow idan munkai da rai da lafiya, yau kaina namin ciyo kuyi manage da wannan please>�&�<���
@&.





Ko Galadima zai angwance oho mar=��>�s�.

�&<���
@&�&<���
@&













*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=�O�<���=�-�_*

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 2�





..........Takun takalminsa yana bada sautine dai-dai da kowacce dak'ik'a na bugawar zuciyata, gaba d'aya saina nemi jarumtata na rasa, musamman da firarsu a Ayusher tashiga dawomin a zuciya.

Zuciyata tashiga tsitstsinkewa, saikace ba Munaya mai tsiwarnan ba da rashin barin kota kwana, kululu cikina yabada sauti lokacin da aka murd'a handle d'in k'ofar. kamshinsa ne ya buso min har cikin hancina.

Shikam cak yatsaya yana kallona da mamaki, yasan wannan aikin aunty Mimi ne ko mom, yakuma tamke face saboda tsaro ba tsoroba=��.

Oho ni bamma san yanayiba, nima tawa ta isheni a zuciya, dan wani tsoronsa ALLAH ya dasamin lokaci d'aya. kusan mintuna 2 yana a tsaye tamkar bak'on falon, yayinda k'amshin turarena ke dukan hancinsa, yau da ace auren soyayya yayi da wadda yakeso, babu abinda zai hanasa sauke nauyin daya damesa tsawon shekaru. a hankali yacigaba da takowa har cikin falon, ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu cikeda izza, k'afarsa d'aya a kan d'aya yana wani kallona a k'asan idanu, shiru kakeji tamkar bama a cikin falon.......

Muryata a sanyaye nace  ina yini .

tamkar bazai amsaba, saikuma yace  lafiya .

Daga nan kowa yay shiru.

Knocking d'in k'ofar da akayine yasakashi sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai kama da anmasa dole ya tambayi wanene?.

Cikeda girmamawa sarkin k'ofar yace,  nime ranka ya dad'e, dama an kawo sak'one .

Kansa ya jingina da kujera, sannan yace  su shigo .

Kuyangi kusan biyarne suka shiga falon da sallama, duk muka amsa akan la66a, suka dire kayan hannunsu sannan suka zube suna kwasar gaisuwa agaremu, hannu kawai ya d'aga musu, nidai koma motsi banyiba, dan nima kunyama nakeji idan naga sun durk'usa suna gaidani, danfa wasuma sun girmeni sosai wlhy, wasuma sun haifeni, kai sarauta dabance gaskiya, al'amuransu sunada wahalar gaske, nidai harma yanzu ban fahim ci komaiba wlhy.

Bayan fitarsu da kusan mintuna 4 naji alamar mik'ewarsa, yanzu ma baice dani uffan ba yashige wani d'aki danake k'yautata zaton bedroom d'in sane a wajen.

Guntun tsaki naja, a raina nace ALLAH ka rabamu da girman kai dai wlhy.

Ban damu da cire hular alk'yabba d'inba, dan sanyin Ac yasa ban takura ba, sai zamana dana gyara sosai yanda zanji dad'i da k'yau a saman lallausar kujerar, duk da har yanzun a tsoracen nake kuwa. dan wannan d'an jinkan yafi k'arfina, zai iya amfani da k'arfinsa ya cutamin batareda yayi la'akari da matsayin auren namuba.



Shikam yana shiga d'akin nasa yafara k'ok'arin cire bottom d'in rigarsa, idon sane ya sauka akan gadonsa dake lailaye da zanin gado blue, dan komai nasa na nan white and blue ne, sa6anin na India dasuke White and Golden, kuma matsawa yayi sosai saboda ganin farin k'yalle dake saman bedsheets d'in.

Tsaki yaja yana fad'in  waisu wad'annan mi suke nufi da shinfid'amin wannan farin abun a saman gado? samazo su d'auki kayansu yanda suka ajiye, motsww . Yakuma jan tsaki sannan ya shige bathroom.

Acanma yana wankan yana jera tagwayen tsoki, bai wani dad'eba yafito sanye da bathrobe milk, hannunsa rik'eda k'aramin towel yana goge fuskarsa zuwa kansa.

Bai shafa maiba, wando yasaka da t-shirt duk milk color marasa nauyi, da alama yayi shirin barci kenan, ya d'auki turarensa na barci mai sanyin k'amshin ya faffeshe jikinsa, sannan ya saka silifas bak'ak'e a k'afarsa yakuma fitowa..

Kallona yayi da mamaki ganin ko fuskarta na kasa bud'ewa, ya ta6e baki da cije lips nashi saman ya zauna bisa tattausan carpet d'in tsakkiyar falon inda kuyangin suka ajiye kayan d'azun.

Tankwashe kafafunsa yayi yashiga bud'e kwanikan domin duba abinda ke ciki.  halan kekam bak'ya jin zafi? .

Yayi maganar yana zuba fruits salad a k'aramin bowl na tangaran mai k'yau.

Shiru nayi tamkar ban jishiba, shima saiya shareni yaja bowl d'in gabansa yafara sha a hankali tamkar bayaso.

Duk abinda yakeyi ina kallonsa ta k'asan ido, saboda kaina Dana jingina da kujera.

Kusan mintuna 5 yana shan fruits salad d'in tamkar wani k'aramin yaro, dan ko Rabin Wanda yazuba baiyiba, araina nace abincinma sai an masa sarauta kenan.

Idanunsa ya d'ago yana kallona,  k wai bakijin ana Miki maganane? bazaki bud'e face nakiba? .

Saida naja kusan seconds 20 sannan na janye hular alk'yabba d'in.

Janye idonsa yayi yacigaba da shan kayansa, nikuwa saima na zame na kwanta a kujera, dama 3setter ce, idanuna na maida na lumshe saboda ciwon da kaina yakeyi kad'an-kad'an, ga kewar innarmu da munubiya dasu Aryaan na damuna, ga wannan auren na fargaba na addabar zuciyata.



Dukda yaga kwanciyar danayi bai tankaba, ya kammala shan fruits salad d'in yamik'e, saman kujera yakoma ya zauna, ya d'auki wayarsa yana latsawa, saikuma ya ajiye ya d'auki remote ya canja tasha zuwa labarai.

Haka muka zauna tamkar kurame, shi yana kallon labarai yayinda nikuma barci 6arawo ya saceni batareda na shirya ba, to gajiya na nuk'urk'usata.

Shi duk bai farga barci nakeba harya kammala kallon labaransa ya kashe tvn, kallona yayi da nufin min magana saiyaga kamarma nayi barci a haka.

Yay d'an jim yana tunanin tayaya zai tasheni, danshi soyake ya shige yayi shafa'i da wutiri ya kwanta, a ganinsa kuma bai kamata ya barni a wajenba.

Matsowa yayi kusada kujerar, ya d'an bubbuga hannun kujerar, dama barcin nawa baiyi nisaba, na bud'e idanuna dasukayi d'an jaa a hankali, saboda barcin dana fara.

 tashi muje ki kwanta .

Gabana ya fad'i, amma saina yunk'ura da k'yar natashi zaune.

Ganin ya nufi k'ofar futa sainaji d'an sanyi, tashi nayi nabi bayansa muka fita, bakowa falon alamun duk suntafi makwanci. Wani falon muka shiga daban kuma, gaskiya shima ya had'u, komai na cikinsa lemon green ne da milk, sai tashin k'amshin turaren wuta da air fresheners masu dad'i yake. bai tsaya ananba yay gaba, nidai ina binsa abaya kawai, munshiga k'aton bedroom tamkar nasa, saidaifa aganina nasan yafi had'uwa duk da ban ganiba, nanma komai lemon green ne acikinsa, sai labuloli milk kamar falon, shima yanata tashin k'amshin.

Juyowa yayi ya kalleni  nan shine d'akinki .  yayi maganar tamkar an masa tilas .

Uffan bance masaba, sai d'aga masa kai nayi alamar naji, shima bai sake cewa komaiba ya fice abinsa.

d'akin na shiga bi da kallo, yamin k'yau sosai, na cire alk'yabba jikina ina sauke numfashi, sanan na cire sark'a da 'yankunne da bangles d'in duk na zube saman madubi. Suma kayan na hau cirewa dan bazan iya barci da suba, sai kuma na shiga tunanin inda zan samu kayan barci? tunda lefena suna gidanmu ba'a kawoba, akwatin da'a kawoni dashi kuma jiya ban Ganshi a d'akinba, zuciyatace tabani shawarar duba wardrobe d'in dake d'akin, banyi musuba naje na bud'e, a mamakina saina ganta da kaya, sai dai duk k'ananune, kayan barcinma babu na mutunci, tamkar zan fasa kuka haka naji, da k'yar nasamu wasu Riga da wando masu sauk'in fidda tsiraici, duk da suma d'in dai sai a slow.

Gadon na hau amma saina kasa barci, kewar 'Yar uwata yadawomin sabuwa, na tashi zaune na fashe da kuka.

Ina zaune ina kukana sai kawai naga mutum yashigo min da sallama ciki-ciki.

Da Sauri na jawo gyalen dana ajiye gefe na yafama jikina, plate d'in hannunsa ya ajiye a table d'in dake jikin gadon, dan harya kwanta yatuna banci komaiba, gani yayi bai dace ya barni da yunwa ba, danni bak'uwace yanzu a gidan, dole sai an bani zanci.

Tamkar bazai tankaba saikuma ya kalleni,  mike faruwa kike kuka? .

Wasu kwallanne masu zafi suka sake kwararomin, na sharesu da gefen gyalena nace,  wlhy ni tsoro nakeji, ban ta6a kwana ni kad'aiba, dan ALLAH ka kiramin Samha ta tayani .

Shiru yay ya tsaya kawai yana kallona, azuciyarsa yace kajifa wannan yarinyar dawani batu, kawai saina tafi kiran Samha ta tayata kwana?. guntun tsoki yaja, Wanda yasakani d'agowa na kallesa. Ya cije lips d'insa sannan ya juyo yakuma kallona  mikike nufi da bazaki iya kwana ke kad'aiba? kin san dai babu wanda yasan manufar aurenmu, daga ni sai ke sai muftahu, dolene ki koya ma kanki iya kwana ke kad'ai d'in, sannan inason kisanfa dolene ki dinga canja behavior naki agaban mutane, domin su agaresu aurene mukayi kamar kowa, sannan ta wannan hanyarne kawai zamu iya samun wani avoidance a kan case d'inan, nasan kinada wayo dan haka saiki bud'e idanunki dan kema zaki iya zama security d'in kanki da kanki, game da zaman gidannan kam za'a samu mai koyar dake komai, dan komai a tsare yake, sauran bayani zamuyishi daga baya, kisa a ranki zaman da zamuyi dake zamane na taimakon juna irinna abota, bayan aiki ya kammala zan baki sakinki kamar yanda nayi alk'awari .

Duk da hawayen dake neman zubo mini haka na had'iyesu, cikin aro jarumta nace,  insha ALLAH komai zai tafi yanda yakamata, kuma zaka sameni mai tsare gaskiya da amana, ALLAH yabamu nasara, ina fata da lokaci yacika komai ya bayyana zaka cika alk'awarin sakina? .

Batare da ya kalleniba yace,  zaki sameni mai cike alk'awari insha ALLAH koda ace bamu cika shekararba komai ya bayyana zan sakeki, idan kuma ashekara 1 bamu samu yanda Muke soba zamuyi 2 ne kamar yanda nafad'a miki tun farko, amma inama addu'ar kafin shekara komai yazama done OK?, ga abinci nan kici, kiyi addu'a ki kwanta, zakiyi barci insha ALLAH .

Batareda ya jira cewata ba yay ficewarsa, kusan mintuna biyu idona na kallon k'ofar, saikace zanga dawowarsane, mamaki yabani sosai, dama yana magana mai yawa irin haka? Kuma cikin kwantar da murya. na sauke ajiyar zuciya tareda bud'e plate d'in daya ajiye, gasashen namane mai rai da lafiya, yawu nane ya tsinke, gashi dama inajin yunwa, na mik'e na bud'e fright d'in dana gani ad'akin, ruwane kawai aciki aka zuba, guda d'aya na d'auka na dawo saman gadon na zauna, inacin naman ina hawaye, gaba d'aya kewar 'yan uwana ta gallabeni, musamman Munubiya, waya na d'auka na kuma gwada kiranta, amma still akashe, wasu hawaye masu zafi suka kuma kwararowa a kumatuna, naman na ture gefe naciga da kukana, saida nayi mai isata sannan natashi nashiga toilet d'in d'akin na wanko fuskata da bakina na d'auro alwala, a fright d'in na saka naman da sauran ruwan na kwanta kamar yanda yabani shawara, addu'ar barci nayi sannan narufe ido. tunani yace salamu alaikum, haka naita juye-juye a gadon, barci 6arawo bai saceni ba sai around 3. daga nan ban sake sanin inda nakeba saida naji ana bubbuga gefen filon danake kwance.

Da k'yar na bud'e idanuna dasuka kumbura saboda kuka da rashin isashen barci. Galadima ne tsaye a kaina, sanye cikin jallabiya ruwan hanta, tamasa k'yau dukda kallon fisha na masa.

Agogon d'akin ya kalla sannan ya juya zai fita yana fad'in  kitashi kiyi salla .

Da k'yar na iya sauka, dan jikina duk ciwo yakemin, ga barci danake masifar ji. daurewa nayi nafara wanka da ruwa mai d'an zafi sannan nayo alwala nafito, salla na gabatar ta asuba nayi addu'oina sannan namik'e na koma gadon, dan danan barci ya kuma kwasheni.







&&&&&&&





A gidanmu bayan kwashemu dukkan amare washe gari 'yan biki suka fara kama gabansu, sai makusanta ne kawai aka bari.

Lokacin da su Ayusher suka koma sun iske innaro na zuba tijara a tsakar gida, wai an munafunceta ba ace ta fitoba lokacin da akazo d'aukata, dama tasan innarmu bak'in ciki take mata karta dangwali arzik'i, to kuwa ita k'adangaren bakin tuluce, babu yanda aka iya da ita, duk wani makirci da innarmu zata shirya mana akan karmu taimaka mata dolene tanan matsayin uwar ubanmu.

'Yan gidanmu fa abin nema yasamu, saifa aka hau dariyar gatsa-gatsa suda sauran bak'in su.

Innarmu kam murmushi kawai tayi, zuwa yanzun ita ta wuce k'aramar yarinya, dama sarai tasan bawai nadamar gaskiya innaro tayiba, kawai dai wani abu dake a ranta kawai. Ko lek'owa batayi tsakar gidanba, barema tanuna tasan da ita takeyi.

Shigowar su Ayusher da kaya nik'i-nik'i na biki da mom tabasu yasa innaro waryar leda d'aya tana fad'in munafukai, Ashe kune aka tura domin Ku tattaro komai, to ALLAH ya fiku, kafin mai biri yaga mai gona mai gona yaga biri .

Ayusher zatayi magana mama Rabi'a ta hanata, haka suka shige da sauran kayan suna k'unk'uni.

Innaro na bud'ewa taga duk drinks ne aciki saita biyo bayansu, ledar ta dangwarar a k'ofar falon tana kunfar baki,  bazansha kayan ruwan ba kayan fitsari, yanzu-yanzu a canjamin kokuma na kwashe komai babu yanda za ayi dani dangin tsiya dangin rashin asali, kai ALLAH yarabamu da bak'ar zuciya mai cike da nunkufurci dai wlhy .

Babu wanda ya tanka mata, Mama Rabi'a ta bud'e komai ta d'iba mata, tanuna ledar datafi kowacce girma da mama Rabi'a bata bud'eba,  to uwar iya, ita waccan ledar miye aciki? .

Da sauri Bilkeesu ta d'auke tana murgud'a baki,  wlhy babu mai baki wannan, domin a lissafe suke, kuma mu aka bamawa bawaniba, zannuwane .

 to 'Yar karoro, kekuma asuwa gand'oki muje biki? Aiba uban wani ya Haifa min Auwalun ba daya haifi munaya, saiki bari sai ALLAH yabaki farin jinin auren koda kansilan anguwarkune sannan kimana iyayi, kujimin bak'ar banza kawai .

Baki Bilkeesu ta ta6e, suka ja ledar itada feena suka shige tsohon d'akinmu, yayinda su Ayusher da Ameera


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login